NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 2) 12&13

   ~Book 2~ ????????12
……………Maman Fauziyya tamatso ta kama hannunmu ni da Munubiya tana lallashinmu, da fad’a mana mu bisa da addu’a, insha ALLAHU da k’afarsa zai dawo.

    Ganin mun fara shirin tafiya na taka inda Galadima yake tsaye da Nuren suna magana, tun d’anzun ina lura dashi ya kafeni da idanu, yanzunma suna maganar amma idonsa na kaina na k’araso garesu.
     Nuren daketa fara’a yace, “gimbiyarmu barka da hantsi”.
    Murmushi nayi sannan na gaisheshi, ya amsa yana tambayata yaya jikina?.
   Nace “Alhmdllh na  warke ai”.
      “to ALLAH ya k’ara afuwa gimbiya”. ‘yafad’a yana matsawa gefe domin bamu waje.
     Galadima dake kallona hannunsa duk biyu cikin wandon sky blue d’in shaddarsa da tsawon rigar iyakarsa rabin cinyarsa, yace, “Lafiya?”.
      Dakewa nima nayi, cike da jan ajina nace “k’alau. Dan ALLAH zanbi Munubiya please yalla6ai”.
       Janye idanunsa yayi daga kaina yana fad’in “awane farashi?”.
       “kamarya farashi? ciniki mukeyi?”.
    Hannunsa d’aya ya fiddo daga aljihu ya shafa sajensa zuwa gemu, cikin kafeni da idanu yace “kusan haka, kinsan rayuwar bani gishiri in baka manda akeyi yanzun”.
       Cikin son tura masa haushi nace “Ai ni bana gane Hausa cikin hausa”.
      “really? lallai kin fad’o kuwa, kuma saiki ce ke bahaushiyace?”.
        Baki na tunzura masa saboda haushin rainin wayon da yake min, gasu Munubiya kuma shirin tafiya sukeyi.
       “Kinsan wannan bakin kika bari na kamashi a airport d’innan….., hummm”.
      Idanuna na waro, “mi kake tunanin zakayi kenan?”.
      “kuma turowa saina nuna miki”. ‘yafad’a yana matsowa’.. 
       Baya na matsa da sauri zuciyata na harbawa, anya kan Galadima d’aya kuwa?.
     Kwafa yayi yana kallon agogon hannunsa yana k’ok’arin zaro waya daga aljihun gaban rigar datake ring.
    Nikuma na hararesa a zuciyata ina fad’in mara kunya ai nasan zaka iya. A fili kuma nace “please yalla6ai nidai badan halina ba”.
     Bai bani amsaba, sai sallamar danaji yayi wayarsa akan kunne.
     Jinai kawai yace, “Harun kana inane?”.
       Bansan wace amsa ya bashiba, naji yana fad’in “ok idan ka tashi saimu had’u”. daga haka ya yanke wayar sannan ya kalleni.
     “uhm mikike cewa?”
      Haushi tamkar zai karni nace “please mana autan Momma”.
     Murmushi yayi yana cije lips, “wlhy yarinyarnan kin gama rainani, ninema Autan?”.
       “lah nama manta ashe kaifa na tsakkiyar momma ne, karma Yaa Sauban ya jini”.
       “kinsan ALLAH na damk’eki a airport d’innan saikin fad’amin dawa kike”.
         Dariya nayi ina d’aga masa yatsu biyu, “karka damu yalla6ai zanyo maka tsarabar sweet and biscuit yeah”.
     Da sauri yay yunk’urin damk’o hannuna ganin zan gudu. yana rik’owa mukaji ance “hallo”. A bayanmu.
       Batareda ya saki hannuna ba duk muka waiga ni da shi.
     Matashiyar budurwa fara k’al, kuma k’yak’yk’yawa masha ALLAH.
     Dan danan ya tsuke fuska, tamkar ba shine yagama murmushiba yanzun.
    Nima bansan murmushi ya gushema tawa fuskarba, baiyi magana ba, sai nice nace “lafiya kuwa?”. yanda nayi maganar cikin rainin hankali yasaka yarinyar rik’e ha6a tana ta6e baki tana fad’in “ke kuma fa?”.
          Kamar zanyi magana saikuma Na shareta kawai, galadima Na kalla fuskata a cunkushe alamar fushi, d’ayan hannunsa ya d’agamin yana ta6e fuska alamar shifa babu ruwansa.
     Na tura baki tareda juyawa zan bar wajen.
      Hannuna dake cikin nasa ya kuma damk’ewa da k’yau, hakan yasani dawowa baya tamkar zan fad’a jikinsa, amma nayi jarumtar tirjewa kodan jama’ar gidanmu.
    Dama ajikin wasu motoci muke, sai kawai ya fisgi hannuna muka shige tsakkiyarsu ya mannani jikin mota shikuma yamin rumfa. ban ankaraba naji bawan ALLAHnnan ya ha…….????.
     Jikina kawai rawa yakamayi saboda tsoro, wlhy ban ta6a tunanin da gaske yake zai iya hukunta bakin nawa a airport d’inba.
     Ita kanta budurwarnan idanu ta zaro waje cikin wangale baki.
      Nuren dashi kad’ai yake saitin dazai iya ganinmu saikuma wasu tsirarun mutane dake nesa damu, wad’anda ba lallaine ma su fahimci abinda akeba, kaucewa kawai yay daga wajen yana tuntsura dariya.
     ‘Yan gidanmu sunga lokacin da Galadima yaja hannuna muka shige tsakkiyar motocin, amma basa hangomu. tsabar gulma irinta mamansu Yaa Hameed da Momy da Maman Safara’u sai suna shiga k’ok’arin son ganin mi mukeyi a wajen????? su duk tunaninsu wata maganar banza nama budurwarnan yake shukamin rashin mutunci Dan duk agaban idonsu tazo wajen har rik’omin hannu da yayi, dukda basa jin mi Muke fad’a Dan muna nesa dasune.
     Yaa Sabi’u dabasu lura da abinda ke faruwa ba suka Shiga musu maganar INA zasuje? suzo su ajiyesu gida sufa wajen aiki zasuje.
    Ina basu saurareshiba saida sukazo saitin dazasu iya ganinmu.
      A tare suka zaro idanu, Baki da hanci, duk sun shiga mamakin ganin Galadima Na kissing d’ina, ai babu shirin suka koma baya zukatansu Na tukuk’i da jifanmu da kalmar ‘yan iska fitsararru.
    (????Yo wayace kuje gani? kazantar dabaka ganiba sunanta tsafta????????).
      
    Yana Sakina kunya tasakani fad’awa k’irjinsa Na 6oye fuskata, hannayensa yasaka ya zagaye bayana yana dallama yarinyarnan wata muguwar harara data saka hanjin cikinta kad’awa, babu shirin tabar wajen tana mak’yark’yata da tunanin Galadima ko dai kurmane da gaske.
      Driver d’inta dake kallon komai tun d’azun ya tuntsure da dariya yana fad’in ALLAH ya k’ara, bana fad’a miki Shiba Na wasan yara bane ba, banda jaraba kinbi kin nanik’ema bawan ALLAH daga had’uwa a jirgi, kinbi kin addabi rayuwata saina nemo miki number sa, aini nama godema ALLAH da kuma sake had’uwa ya kuma nuna miki ainahin halinsa, saida Na fad’a miki baima dad’e dayin aureba, ke gadararriya kikace aurensa bai damekiba……..
    Yanda ta daka masa tsawa yasakashi firgita ya russuna yana Neman afuwarta.
      Cikeda masifa tace “tada mota mukoma gida”.
      “Amma ma’am kin manta jirginku yakusa tashi?”. A tsorace yayi maganar.
          Harara ta Dalla masa tace “Ubanka ne ya viyamin kud’in jirgin”.
       Wasu yawu masu rad’ad’i driver ya had’iye yana girgiza mata kai, ya bud’e motar ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya mazauninsa suka koma Inda suka fito????.
    
   Nasan dai kun fahimci yarinyarnan Ce da suka zauna waje d’aya a jirgi itada Galadima randa zaizo????????.
     Ganin tabar wajen Galadima yay murmushi sannan yafara k’ok’arin d’agoni daga k’irjinsa, ban yarda mun had’a idoba na  bar wajen.
       “Saikin dawo” ya fad’a a hankali.
    Kasa daurewa nayi saida Na waigo Dan tabbatar da shine yay maganar kokuwa dai wanine?. Ido muka had’a ya janye nasa cikeda basarwa yana la6e baki.
        Nima harara Na watsa masa ina barin wajen.
      Tunda Na taho Maman safara’u da mamansu Yaa hameed da Momy suka zubamin ido.
    Nikuma fahimtar kallon k’urillar da sukemin saina canja salon tafiya da kuma had’e fuska na nufi zuwa wajen gungun yaran gidanmu masu aure dasuke hira.
    Suma duk kallona sukayi, namusu murmushi ina fad’in “lallai munada cin ragunan suna kwannan nan ashe”.
     Dariya duk sukayi, Fiddausi tace “yariman namu shikuma da kwad’ayin naman suna yazo?”.
     Harara Na zuba mata ina kai mata bugu ta waske itama tana dariya, yayinda su Munubiya ke tayata.
     Mun gaggaisa tareda tambayar lafiyar juna, muka d’an ta6a hira kad’an da alk’awarin duk zanje mu gaisa, suma sukace zasuzo tunda ba yanzu zan koma ba. daga nan mukai shirin tafiya, Siyama da Zarah anata mana iyayi su masu motar hawa, (dayake kowacce a motarta tazo).
    Ni dai ni da Munubiya Yaa Marwan ya d’aukemu muka tafi.
____________________________
       Tunda nabar wajen Nuren yazo ya tasa Galadima da tsiya, wai dama haka yake ashe?, rashin kunyar tasa har agaban surukai?.
       Banza Galadima yamasa yay shigewarsa mota yabarsa yana iskancinsa.
     Anan suka tafi suka barsa dayake da mota yazo shima.
  
       Galadima na barin airport gidanmu ya nufa shima.
     A lokacin ‘yan gidanmu suma sun Isa gida, sunata k’ananun magana akan abinda Galadima da munaya sukayi, dan saida suka bama sauran labari, nanfa suka kacame da zancen harda k’arin k’arya akai wai ba kiss kawai sukaiba (‘yan gidansu munaya annamimatu????????????).
      Itadai Maman Fauziyya batace k’alaba, saima dariya da zancen ke bata, Dady kuma bai dawo gidanba, daga nan wajen aiki ya wuce, yaran gidan ma kowa gidanta ta koma basu biyo nanba. Innaro da gwaggo Safiyya kam gida suka shige ana saukesu, dan haka basuji komaiba.
        Galadima bai shiga gidan ba, saiya nemi iso gidan Innaro, Habiba ta fito tamasa jagora.
     Innaro na falo tana cika da batsewa gwaggo Safiyya na lalla6ata akan ta kwantar da hankalinta.
       Koda Galadima ya shigo innaro sai antaya masa harara takeyi, yana kula da ita ta gefen ido, ya murmusa yana zama saman kujera, cikeda tsokana yace “Sweet Granny Yaya dai?”.
       Harara innaro ta zuba masa sosai, tana fad’in mikuma kazo min nan?”.
     Galadima ya murmusa yana maida hankalinsa ga gwaggo Safiyya, gaisheta yayi ta amsa masa cike da kulawa, sannan ta d’ora da godiya da kwarara masa addu’ar fatan alkairi.
   Yaji dad’i sosai, ya amsa cikin fara’a, sannan yace, “Granny ina furar tsufa?”.
      “ai bazaka shata ba ”.
    Nanma murmushin Galadima yayi yana mamakin wannan rikitacciyar tsohuwa. Yace “tunda bazan shaba Ashe kema kuwa bak’yaje India ba”.
     Zabura innaro tayi, ta maida hankalinta ga Galadima tana fad’in “da gaske kake ko shak’iyancine?”.
      Mi su Naja’atu zasuyi inba dariya ba, Galadima ma handkerchief ya saka ya rufe bakinsa kawai. Gwaggo Safiyya kanta saida ta dara.
     Galadima ya gyara zamansa yana fad’in “karki damu Granny ninmu, insha ALLAH tare dake zamu tafi idan zamu koma”.
      Dad’i ya kama innaro ta shiga sakama Galadima albarka.
     Shidai murmushi kawai yakeyi. saida yaga sun nutsu sannan yace yazo tafiya dasu Aiyaan ne, babu musu innaro ta mik’e da kanta zuwa gidan danta kawo masa su.
    Bayan fitarta gwaggo Safiyya tabama Galadima hak’uri akan darun innaro.
    “karki damu gwaggo, ai dama kowa yasan idan sunkai irin wannan age d’in saida lalla6awa, ALLAH dai yaja mana ransu”.
     Amin gwaggo Safiyya tafad’a cikin jin dad’i.
      Tunda ‘yan gidansu Munaya sukaji wai Galadima ne da kansa yazo tafiya dasu Aryaan sai zukatansu suka kuma tunzura, kowa tana ganin hakan salon munafurcine, Maman Fauziyya ta kawoma innaro su, dama suna d’akinta, dan mamansu yaa hameed suna dawowa ta d’auki jakkarsu Aiyaan ta kaimata, wai sai dai su zauna wajenta ita d’akinta babu fili.
     Maman Fauziyya batace komai ba ta kar6i su Aiyaan tana jinjina bak’in hali irinnan jama’ar gidan.
   Amma kuma yanzu sai gasu sune dajin haushi.
    Ita dai innaro ko’a kanta ta jawo hannunsu Zainab ta d’akko jakkar kayansu suka taho.
       Koda sukazo ma sai Galadima yace abar kayan nasu su kad’ai yake buk’ata. ya ajiyema Gwaggo Safiyya da innaro alkairi ya fito rik’e da hannun su Aiyaan daketa murna.
    Innaro har wajen mota ta rakosu, bata komaba saida taga tafiyarsu. tana komawa gida tahau had’a kayan tafiya, wai gara ta had’a ta huta, duk randa Galadima yazo sai tafiya kawai.
    Ita dai gwaggo Safiyya dariya kawai tayi, dan maganar Galadima gaskiyace, lamarin innaro yana buk’atar uziri, ta tsufa sosai, kawai dai ALLAH yabata lafiyane, dan da wuya kaga innaro na kukan wani waje namata ciwo irin na tsufa. (masifarta kam dai kunsan ance abinda kayi a k’uruciya shi kake maimaitawa lokacin tsufa, ALLAH ka azurtamu da k’yak’yk’yawar k’uruciya to????????).
★★★★)()(★★★★
        A k’ofar sabon  matsakaicin gidan motocin biyu suka tsaya, cikin wad’anda suke a motar baya d’aya ya fito ya bud’e motar farko, hamshak’iyar macece mai ji da mulki da kud’i ta fito, kallo d’aya zaka mata ka tabbatar tagama samun duniya, cikin tsantsar tink’aho da homa take zuk’ar iska tareda taku d’ai-d’ai irin na manyan mata.
      Cikin sauri aka bud’e mata k’ofar gidan ta shiga guard d’inta na take mata baya.
       A tsakkiyar tsakar gidan taja tunga, sai hura hanci takeyi tana harare-harare.
    d’aya a cikin guards nata yace, “ ma’am nan shine d’akin da yake”.
     Batace uffanba taci gaba da takawa d’ai-dai har zuwa k’ofar d’akin, hannu ta d’aga musu alamar su dakata. Dukkansu baya sukaja domin cika umarninta.
     Zaune yake a kujera an d’ad’d’aureshi, kallo d’aya zaka masa ka tabbatar a galabaice yake.
   Shigowarta baisa ya d’aga kai ba balle ya motsa, yasan dai bazai wuce k’artan dasuka kawosa wajen baneba. sai dai jin k’amshin turaren mace yabashi mamaki, hakanne ya sakashi d’ago idanu domin tabbatar da yaren hancinsa.
       Bakinsa na rawa yace, “Wacece ke?”.
    
     Bata bashi amsaba, saima kujera data ja irin wadda yake kai ta dinning ta zauna, k’afa d’aya ta d’ora akan d’aya tana wani cika da batsewa. “yaro baka isa sanin ni wacece ba, Sai dai cigaba da 6atamin aiki zai sakaka sanina”.
    Murmushi Muftahu yayi, ya d’ago idanunsa yana mata kallon rainin wayo, “Saninki dama aikin banzane a gareni, aikin ki kuma da kike ik’irarin ina 6atawa duk da ban sanshi ba, kisa a ranki yanzu ne na fara 6atawa, saiki shirya nunamin ke d’in wacece?”.
       “hahaha, yaro baisan wutaba saiya taka”.
      “Humm, wuta bata san yaroba saisu k’ulla”.
      “karan farauta yaushe uban gidan naka yafara koya maka irin izzarsa haka?”.
       “Kinsan zama da mad’aukin kanwa aishi ke kawo farin kai”.
      “lallai zan had’a da kanwar da mad’aukin nata duk na koyar dasu darasi. Shi kansa Sameer d’in baikai darajar karen gidana ba balle kai yaronsa”.
       Murmushi Muftahu yayi, “ Uhmm sai yanzu na fahimta, sai dai zan tunatar dake abinda kika manta, Wanda kikeyi danshi baima San da zamanki ba, kinga ashe ihu kikeyi bayan hari……….”.
           “hhhhhhhh! Abin dariya, inbai fahimta ba ai zai fahimta lokacinda sak’on sunana da gawarka suka isa a gareshi, yanda ban haifi magajin masarautar gagara badauba, zeenah bata isa haihuwar magajinta ba wlhy”.
      Idanu Muftahu ya tsura mata, sai yanzu yafara hango kamannin d’aya daga matan tsohon Sarki Abie da suka bar masarauta bayan shekaru biyu da fara jinyarsa, bashida wayau a time d’in, Dan dagasu har Galadima bazasu wuce 7-7 year’s ba, saida suntaso sunji labarin bijirewar matan a lokacin da za’a tafi da Abie India, dama shekaru biyun da suka zauna basu ta6a saka hannu a jiyarsa ba, sai Momma keta fama………..
      Marin da aka zuba masane ya sakashi dawowa daga dogon tunanin daya tafi….
       “tunanin mi kakeyi Karen farauta?”.
     Jajayen idanunsa ya zuba mata, sai kuma ya kwashe da dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya dakata tareda tsuke fuska, “ina tunano mummunan fuskarkine, in banda abinki miye na kishi da abinda kika bari da kanki? nasan dai Momma ba itace ta hanaki haihuwa ba ai, inason kisan ni ban isa kare Galadima ba dama, amma kulum cikin kariyar Wanda ya haliccesa yake, a tunaninki 6ata sunansa da kikayine ke nufin bazai mulki masarauta mai d’unbin tarihi da girmaba? kinyi kuskure babba wlhy, Dan kinsaka kanki a ramin damisa. duk ranarda Galadima ya gane kece kika saka amasa 6atanci a jarida wlhy saikinyi nadamar rayuwarki……….
      Bayan Hannu tasaka ta bugi bakinsa, gefe yay da kansa yana murmushi, ga jini na zuba a gefen bakin, dayake hannunsa a d’ure suke.
    Tace, “kafin ni nayi nadamar kai ne da shi zakuyi, Dan yanda kake a tarkona shima yanacan a cikinsa, wawa kawai, kai aboki mai gaskiya ko? zan shayar dakai mamaki, domin saikaga gawar Sameer a gabanka kwance kafin kaima kabishi baya”.
      Dawo da kallonsa yayi gareta yana murmushi, “miyasa kika tsorata tunban k’arasaba, Galadima maruci ne, kuma kainuwane, gashi dakalin majina, kina hawansa zamewa zakiyi wlhy, ina tausaya miki yayinda tunaninsa ya waiwayo kanki, Dan yanzu aikin manyanki ne a gabansa ba nakiba, d’ana masa tarkonki kuwa tamakar kin tado damisane daga barci, hakan kuma fitinace babba a gareki da shi kansa Karen farautar taki Harun, tirrr da zuciyarki, ni kaina danasan ma kece bazan 6ata lokacina wajen bibiyar ki ta hanyar Harun ba, amma banyi bak’in cikiba, ko babu komai na ribantu da abubuwa masu yawa, domin ta silar hakan na had’a auren sunna, gashi harda ribar ciki, magajin Galadima Sameer kenan…….
     A fusace ta d’aga kofin glass zata kwala masa.
    Yace, “relax relax mana giwar mata, ai bangama fad’aba OK?” ba kince zaki kawomin gawar Galadima ba sannan, to miye kuma na fusata haka da wuri?, ni ina kuma tabbatar miki indai Galadima ne zaizo, daga lokacinda yasan ina nan tabbas zai zo, banza karyar farautar wasu, na tabbata k’arya kikeyi ba aikin kanki kikeba kema, sakaki akayi, lallai ke farashinki ya fad’i k’asa, matar sarki mai fad’a aji irin Sarki Saifudden Ce ta k’are ahaka? Abin kaico abin jaje, tirrr”.
          Dariya ta kwashe da shi tana tafa hannaye, saikuma ta matsa gabda Muftahu tana magana cikin kunnensa “lallai bayan Sameer akwai magajin sa a gagara badau ashe?”.
     “oh sai yanzu kika fahimta ashe?”.
       “karen Sameer zaka mutu kaida uban gidan ka, saina saka wannan zuciyar tasa ta buga wannan shine k’udirina”.
            “hhhhhhh abin dariya, kudirin wasu dai, danke naki bamai muhimmanci baneba, tunda kuka kasa saka zuciyar Sameer bugawa a lokacin da k’uruciya da rashin sanin kansa ke damunsa, miyasa kuke tunanin zata buga a lokacin da yagama tanadar makaman yak’insa, ranar shiga filin daga kawai yake jira, nagaji da tattaunawa dake please”.
        “kaima kace wani Abu yaro, Dan haka mu zuba, kwana uku kawai zakaga gawar Sameer a gabanka!!!!!”.
     Bata jira yabata amsaba ta fice daga d’akin, tareda jan k’ofa da k’arfi.
    Idanunsa kawai ya rintse. Baya tsoron makircinta, amma yana tsoron na Harun, dan Galadima ya rigada ya yarda da Harun 100%, bazai ta6a kawo zai cutar da Shiba. Waige-waige yashiga yi, yasan babu wani abunda Galadima zai iya bibiya tare dashi.
    Da sauri ya girgiza hannunsa saboda tunowa da agogo, jin agogon tare dashi ya sakashi lumshe ido yana ambatar Alhamllh. Matsala d’ayace baya ganin agogon, saboda hannunsa yana a baya ne. Amma dukda haka zai gwada idan za’a dace.
___________________________
      Yau na kasance cikin farin ciki, saboda gani tsakkiyar ‘yan uwana, dukda ma zazza6ine mai zafi ke nuk’urk’usata, amma kewarsu ta hanani gajiyawa, mun bud’e babin fira a tsakkiyar falon mama Rabi’a, duk abinda akayi bana nan shine ake labarta min, yayinda Nima nake basu labarin India da nuna musu hotuna.
    Haka mu kai wannan yini cikin farin ciki da annashuwar kasancewa da junanmu, musamman ma ni da ‘Yar uwar tagwaicina da k’addarar aure ta tilasta mana nisantar juna, ji muke tamkar mun shekara ba’a tareba. Kowannenmu k’ok’arin ganin farin cikin d’an uwansa yakeyi.
_____________
      Tunda Galadima yabaro gida dasu Aryaan saiya wuce wajen wani hutawa dasu, ya yawata dasu sunata farinciki, yayinda shi kuma yake biyema shirmensu dan d’auke musu kewar mahaifiyarsu, yana son yara, shiyyasa ko yaushe Khaleel d’in aunty Mimi zakigansa manne dashi, sa’annin Khaleel dasu Aiyaan kuwa zai iya zuwa d’aya.
    Cikin lokacin k’ank’ani suka saki jikinsu dashi.
    Daga nan plaza ya nufa, haka kawai zuciyarsa keta tsikara masa zancen 6atan Muftahu, dukda k’ok’arin wofantar da lamarin da lamarin da ya keyi.
     Waya ya d’auka ya shige danne-danne, alamu sun nuna masa wayar Muftahu na cikin masarauta, kenan bai d’auki wayarba, yad’an murmusa kawai yana cije lips, yayinda idonsa ke kansu Aiyaan da Saleem yazo d’auka suje wajensa danya huta.
     Bye suka masa, shima ya d’aga musu hannu yana murmushi.
    Suna ficewa ya sauke ajiyar zuciya tare da mik’ewa tsaye. zagayen office d’in ya farayi hannunsa goye a baya, a wannan karon bazai ta6a k’yale Muftahu ba, dolene yayi wani Abu akansa, dama yana d’aga masa k’afane domin son ganin gudun ruwansa kawai, yanzu kuma lokacin yayi dazai San mi yake k’ullawa………..????
*_Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, cakwakiyar network tasani clearing charts d’ina batareda na dubaba, tun around 3:47pm nayi posting amma yak’i tahowa._*
Dan haka ina gayyata kowa gobe a court, zamu shiga shari’a ni da  network ne????.
Wad’anda suka ga basa ganin posting d’ina gaba d’aya a satinnan duk aikin network ne????.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmhiyayenmu????????????_*
*_typing????_*
 ???? *_HASKE WRITERS ASSO….._*
           *_RAINA KAMA…..!!_*
                  _(Kaga gayya)_
              *_Bilyn Abdull ce????????_*
   ~Book 2~ ????????13
……………Muna tsaka da hira saiga Aunty salamah tazo, daga ni har Munubiya da Ayusher rungumeta mukayi.
    Cikin tsokana ta ture Munubiya da Ayusher tana fad’in “ku matsamin, kullum Ku ina ganinku, kewar gambo nakeyi”.
     Gwalo na shiga yi musu, mama Rabi’a da Feena namana dariya.
    Bayan mun zauna Aunty Salamah ta shiga yaba canjawar danayi tanamin shak’iyanci, nanfa su Munubiya ma suka samu abinyi, sosai suka tasoni gaba sai mama Rabi’a ke kareni.
    Can muna tsaka da hira takamo hannuna tana fad’in “zo nabaki wani sirri nan autana”.
      Mik’ewa mukayi inamasu Ayusher gwalo, yayinda suma suka tubure basu yardaba sai an bada sirrin dasu. da k’yar muka samu muka shige d’aki muka kulle.
      A bakin gado muka zauna Aunty slamah ta sauke ajiyar zuciya tana kamo hannuna cikin nata, serious nima na zama na maida hankalina gareta.
   Tace, “Munaya! Aiki yatafi yanda ya kamata, saidaifa labarin ya canja daga yanda kike zato, Muftahu ba munafuki baneba”.
       A matuk’ar razane naja baya ina ture hannunta daga cikin nawa, “Aunty kinsan mi kike fad’a kuwa? Anya yaranki Muftahu suka kama?”.
     Hannuna ta kamo tana murmushi, kinga zauna, shiyyasa na saka aka d’auki komai dan kema ki gani da idonki”.
    Zaman nayi kuwa, ita kuma tayi ‘yan latse-latsenta a iPad d’inta ta mik’omin. kar6a nayi cikeda fargaba, da kaina nayi playing d’in video n, tun daga fitowar Aunty salmah daga mota har shiganta cikin gidan zuwa shigarta d’akin, tsayarwa nayi na kalli Aunty ina dariya, “kai Auntynmu kinfa iya Acting wlhy, wanifa saiya d’auka da gaske irin mugayen hamshak’an matan nanne”.
        Dariya Aunty Salamah tayi, “wlhy koni dai nayi mamakin dakewata, bakiga sai wani hura hanci nakeba, sukuma su Ameer saikace guards d’in irin manyan mutanan nan”.
     Dariya mukayi, sannan nakuma playing na cigaba da kallo.
     Shigar Aunty Salamah d’akin da tattaunawarsu da Muftahu. gaba d’aya jikina yayi sanyi, zuciyata sai wani tsitstsinkewa takeyi, idona cike da kwalla nace, “anya gaskiya Muftahu yake fad’a Aunty Salamah?, wlhy da gaske fa shine ya saka mana desire tablets, inhar bada wata manufaba miyasa yay haka?, kumafa ni banta6a ganin wani alamar rashin gaskiya ba ajikin Harun”.
      Murmushi Aunty Salamah ta yi, ta dafa kafad’ata tana fad’in, “Munaya mugu bashida kama, Ai Muftahu baisan nid’in ba matar sarkin bace ta gaske, mizaisa ya za6i 6oyemin? yanda yanuna akan k’yamar matar sarkin tabbas akwai mai mugun hali a cikin su da gaske, kinga ai kince bakiga fuskar wanda kika kama yana wayarnanba a bayan window d’inki randa kuka iso”.
     “Eh hakane, ban ganiba, maganganun kawai naji”.
     “to kin gani, kifa tuna kuma firar da kika ta6aji Galadima nayi a asibiti shida aunty Mimi. wad’annan alamomin sun nuna akwai wata a cikin matan Sarki dakeda hannu a ciki, maganar Harun kuma idanu zamu saka masa tamkar yanda mukaima Muftahu, dan ayanzu idan mun saki Muftahu zakiga sun cigaba da takun sak’ar datafi ta da zafi, dan nariga da nasaka rud’ani a zuciyar Muftahu cewar zamu kashe galadima, tabbas ta wannan hanyar Harun zaizo hannunmu. Maganar Galadima kuma har yanzu karki fara kwantar masa da kai, dan kwantar da kanki zai d’arsa masa rashin aiminci a kanki, ke dai kinsan halin mijinki ai yanzu, kinkuma fi kowa sanin yanda yakamata ki cigaba da tafiya da shi”.
     Insha ALLAH Aunty zan cigaba da k’ok’ari nakuma gode da gudunmawarki akanmu, sai dai akwai matsala, dan na lura agogon hannun Muftahu kamar akwai wani sirri a cikinsa, dolene a daren yau a fitar da Muftahu daga gidanan, zanma sarkin mota bayanin yanda zai taimakeku a maidashi masarauta kamar yanda yaymana aikin d’akkoshi, shima Galadima zansa ido akansa saboda tsuntsune shi nai azabar wayo”.
       “Hakan yayi Munaya, ALLAH ya cigaba da bamu nasara, insha ALLAH zamu gano komai, ALLAH dai yabama Abba lafiya, yasa mu fahimci komai cikin sauk’i, akan Galadima kuma kici gaba da k’ok’arin da kikeyi Fiyeda da, dan dolene saimun samu had’in kansa kafin musan komai, ALLAH ya ku6tar damu baki d’aya, dan kina dai ganin yanda suka maida Abba”.
        Hawayen da suka ziraromin a kumatu na share, cikin Murmushin k’arfin hali nace, “insha ALLAH Aunty Salamah, domin raina da farin cikina fansane akan mahaifina, kuma zuwa yanzu Auren Contract bai damuna, sai dai bazan 6oye mikiba aunty Salamah wannan cikin shine damuwata a yanzu, inaji ina gain zan haifishi na barsa inda yafi k’arfina, bansan wace rayuwa zaiyiba a wannan gidan da kowa zuciyarsa takeda k’arancin imani, Aunty Salamah gidan sarauta tsantsar matsalace kawai, bazaki fahimci hakaba saikin tsinci kanki a ciki, Aunty dan ALLAH ki amince na zuba da cikinnan”.
       “munaya waishin miyasa bakida hankaline? to idan baki saniba wannan cikin shine zai zamemiki tsanin mallakar cimma nasara, kuma ta hanyarsane kawai zamu samu had’inkan Galadima domin fidda Abba daga wannan matsalan da Ku kanku ahalinsa, kina tsammanin koda Abba mutuwa yay masu farautar rayuwarsa zasu barku Ku6utane? Dolene saisun samu abinda suke nema koda ace dukkan gidanku zai k’are, bak’ya tunanin aurenku yana cikin abinda yakuma hasala zukatansu, a zatonsu Abbanki yasamu damar had’a kan mijinkine, ya ina jinjinama fik’irarki ke da munubiya kuma zaki 6ata shirin, karma ki bari ‘Yar uwarki taji maganar zubda cikinnan, wlhy zaku samu Matsala ne babu ruwana”.
      Munaya ta share hawayenta, “shikenan Aunty Salamah nabar maganar insha ALLAH. Amma a yaran nan masu mana aiki bak’ya tsoron wani yaci amanarmu?”.
      “komai zai iya faruwa, domin amana tayi k’aranci a rayuwa, tunda yau gashi Harun yafito cikin masu cin dunduniyar Galadima, amma ki kwantar da hankalinki, su duka ukunnan da kike gani amintattunane, kuma Saleem ya saka mana idanu sosai a kansu”.
      “to Alhmdllh aunty, ALLAH kamana jagora”.
     “amin dai, saikima Munubiya dukkan bayanin da mukayi, ki bata itama ta gani, zuwa gobe zan aiko Bilkisu ta kar6a min, kuma ki fad’a mata yakamata ta koma gidan ta, dan gaskiya aiki bazai cigaba da yuwuwaba tana gidannan, saboda kinga ba ita kad’ai baceba, yanzu haka randa zaku zo da zamu kama Muftahu wlhy nasha wahala wajen nemanta naji kokin iso? dan ta tabbatar min inhar kin iso k’asarnan saitaji a jikinta, amma naita kiranta batayi picking ba, ashe wai wayar na hannun Feena”.
      murmushi nayi nace, “sorry sweet auntynmu, insha ALLAH zata koma gobe”.
     “shikenan, bara na wuce to”.
     “to Aunty ngd sosai, ALLAH ya bada ladan zuminci, ammafa gaskiya kinci zalin muftahu da yawa”.
      Dariya tayi sosai, “kibari kawai, nima wlhy ina marinsa tausayinsa Na ratsani, insha ALLAH zan nemi yafiyarsa zuwa nan gaba, ALLAH yasa ya yafemin dai”.
      “hhhh zai yafe miki aunty ai duk cikin aikine”.
      Mun rakota har tsakar gida, su Munubiya na tsokanarmu wai nad’an sammusu sirrin suma.
    Daga ni har aunty Salamah dariya mukayi kawai.
       Bayan dawowarmu na turama Munubiya massage akan taje tagani itama.
    Sai da taja wasu times sannan tamik’e tana fad’in bara tad’an watsa ruwa. duk muka amsa da to saita fito.
**************************
     Su Abba sun isa lafiya, anzo da motar Ambulance d’in asibiti aka d’auki Abba, yayinda Sauban da baba k’arami da inna khumar yazo d’aukarsu su kuma.
     Inna da baba k’arami sai baza ido suke suna kallon gari.
    Gida suka wuce kai tsaye, yayinda aka wuce da Abba hospital shikuma.
     Sun iske jakadiya a gidan, dandanan aka shirya musu abinci, itadai inna sai jinjina k’yawun wannan gida take, yanzu anan gidan jininta ta rayu?. shi kansa baba k’arami ya yaba, Yakuma k’ara tabbatar da manyan k’asarmu Na hutawarsu.
**************************
       Babu yanda Muftahu baiyiba dan ya sarrafa agogon hannunsa amma hakan ya gagara, Dan bak’aramin d’auri ya shaba.
   Kusan gab da magriba Wanda ke kawo masa abinci ya shigo, ajiye kular abincin yayi sannan ya matsa kusada muftahu zai kwanceshi, cikin murya k’asa-k’asa kamar mai rad’a yace “yalla6ai inhar zaka biyani wlhy zan ku6tar dakai”.
    Kallonsa Muftahu yayi sosai nawasu mintuna, “ka tabbatar?”.
     “wlhy Oga da gaske nakeyi, Dan wannan matar da kake gani bata wasa bace, duk abinda ta fad’a zata iya aikatashi wlhy”.
      Murmushi Muftahu yayi, yace, “nawa kake buk’atar Na baka?”.
       “tab aini Oga dubu 100 ma ta wadatar”.
      Muftahu yakuma Murmusawa, “zan baka 200”.
     Da sauri yaron yaja baya cikin razana, “oga dubu 200 fa? Yo ai sai a d’auka nafara yankan kaine”.
     Sosai abin yabama Muftahu dariya, Dan haka ya dara, yo dubu 200 a wajensa ai bata wuce ta siyen agogo ko takalma ba, amma shine shi yake ganin 200k a matsayin wasu kud’in da har za’a iya d’auka yayi yankan kai.
     Kallonsa yayi yana murmushi, “karka damu to, amaimakon nabaka kud’in a hannu a zargeka mizai hana Na bud’e maka wata Sana’a da zakabar wannan aikin da kakeyi yanzu”.
      “to ai Oga karkaje kasa a kamani wataran, nikuma inhar zan samu Sana’a to zan nutsu”.
      “haba abokina, ya zakamin rana nikuma Na maka dare, karka damu kaidai ka aminta dani kawai”.
     “to Na amince,  yau sai k’arfe 11 zan kawo maka abincin dare, a time d’in sauran sun fita club, insha ALLAH nikuma zan dawo baya nace Na manta da abincinka, daga nan saina ku6tar dakai, sukuma na sanar dasu Na dawo ban gankaba”.
     “shikenan babu damuwa, idan zaka dawo kazo da account number, dana koma zan maka transfer insha ALLAH”.
       “to Oga Na gode sosai”. Ya fad’a cike da d’oki.
     Murmushi kawai Muftahu yayi.
      “yauwa Oga bara Na kwanceka kaci abincin to”.
       Girgiza kai Muftahu yayi, yace, “a’a ka barsa kawai, banajin ci, in kanaso d’auka kaci kawai”..
       “amma Oga ai…….”.
      Kai Muftahu ya girgiza masa alamar karyace komai.
     Shiru yaron yayi ya d’auki kular ya fice kawai, Muftahu kuma ya bishi da kallo.
**************************
     Har akayi isha’i Galadima yana birnin gayu, saida aka kira sallar magriba ne yafita zuwa massalacin dake plaza d’in yay salla tare da ma’aikatan wajen masu salla, daga nan ya gaggaisa da makwaftan wajen dakan zo masallacin yin salla suma, bai fitoba saida akayi sallar isha’i. daga nan yacema saleem yaje dasu Aryaan su za6i dukkan abinda sukeso ya mik’a mass ATM d’insa, shikuma ya kuma shiga office ya kulle kansa ya d’ora tunaninsa daga inda ya tsaya.
       Ya dad’e yana zagaye office d’in, yayinda zuciyarsa ke k’ulawa da kwancewa, agogon hannunsa ya kalla, ganin time yayi nisa yasashi furzar da huci, kayansa ya tattaro ya fito, dogaransa duk suka mik’e, suna gaisheshi, amsawa ya shigayi tamkar baya so.
       d’aya aciki yace, “zamu tafine ranka ya dad’e?”.
    Kansa ya jinjina masa alamar eh, sannan yace “ama saleem magana”.
     Da sauri suka amsa da to.
        Ficewa yayi, sauran dogaran sukabi bayansa. Mota aka bud’e masa ya shiga, za’a rufe murfin ya hana, idonsa akan k’ofar plaza d’in harsu Aiyaan suka fito tare da saleem, dogarai biyu d’auke da manyan ledoji.
     Suna hangoshi suka k’arasa da gudu, murmushi yayi ya d’aukesu d’ai-d’ai da kansa ya saka a motar, sannan aka rufe musu k’ofar.
    Sudai dogaransa sai mamakin yanda yake sakema su Aryaan sukeyi.
       Har sun fara tafiya ya fad’ama  sarkin mota suje zasu taho da Munaya.
     A ladabce sarkin mota ya amsa da to.
    
         *****************
       Muna tsaka da hirarmu aka kira wayata, sharewa nayi tamkar bazan amsaba, Munubiya ta harareni, ramawa nayi nima sannan Na d’aga.
      Ciki-ciki nayi sallama, ya amsa daga can, mamaki ya kamani danjin muryar Galadima, katseni yayi da fad’in “ki fito”. Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
     Kamar zanyi kuka haka naji, Yaa Marwan ya fito daga d’aki yana saka rigarsa, kallona yayi yana fad’in “k ba jiranki akeba ne?”.
      Sai da Na kumbura baki sannan Na mik’e. shikuma ya fice.
    Da taimakon feena Na had’a komaina, har abubuwan da mama Rabi’a ta bani, sannan suka rakoni.  Mun iske Yaa marwan tsaye jikin motan ya dafa k’ofar suna magana da Galadima dake ciki bai fitoba.
       Dogari d’aya ya zagaya ya bud’emin, ido muka had’a da Galadima Na janye da sauri, shima janyewa yay ya maida hankalinsa ga Yaa marwan dake masa magana.
      Mamaki ya kamani ganin su Aiyaan, suma cikeda d’oki suka fad’amin a jiki suna dariya da fad’in “Auntynmu!”.
     Juyowa Galadima yay yana kallonmu, shima Yaa marwan yay dariya kawai, sannan ya rufe mana murfin yanama Galadima sai da safe.
       Su Aryaan sun kacame da bani labari, yayinda nikuma naketa musu dariya da biye musu, mamaki ya kama Galadima, bai ta6a tunanin ina magana hakaba, ya lafe jikin seat yana kallonmu cikeda birgewa.
    Nikam nama manta ko gaisheshi banyiba, saida yay gyaran murya sannan Na d’ago Na kallesa, murmushi namasa ina fad’in “yalla6ai barka da dare”.
      Shima wani miskilin murmushi ya min yana d’agamin hannu batareda yayi magana ba.
     Aiyaan yay saurin fad’a “auntynmu bafa yalla6ai sunansa ba, sunansa Uncle”.
    Kamar zan harari yaron sai kuma nad’an murmusa ina kallon Galadima dake kallonmu shima. janye idona nayi daga gareshi Na cema Aryaan to naji zanke fad’a.
         Har muka kai gida basu barmu mun hutaba, sai surutu suke da bani labarin abinda yafaru a gida bana nan, danaji zasu kauce hanya kuma sainai saurin waskewa.
      
 ★★**★★**★★
            Sarkin mota yana ajiye su munaya ya duba gefen seat d’in data zauna, takarda ya gani ya d’auka, dan sanda zasu shige tamasa wata inkiya da hannu.
     Dubawa yay yaga mita rubuta. Sallama yayma sauran ‘yan uwansa sallama akan zai shiga gida.
    Daga nan ba gidan ya shigaba, saiyay dabarar da yabar masarautar gaba d’aya.
         Sun had’u da Saleem a inda suka shirya, saleem Ya bama sarkin mota handkerchief d’in da zasu shak’ama Muftahu.
     Sarkin mota ma yaje ya bama Ameer ne, daga nan ya dawo k’ofar fada amma k’aramar k’ofa tacan baya inda keda k’arancin tsaro.
      Agaban idonsa su Ameer suka sauke Muftahu a mashin yana cikin yanayin barci saboda abinda suka shak’a masa, saida ya tabbatar sunbar  wajen sannan shima ya koma ciki.
        Yau dai kam ni kad’ai Na kwanta a d’akina, Galadima ko lek’e bai lek’oba, yana can tare da su Aiyaan a d’akinsa.
    Nima kawai saina kira Momma mukasha hirarmu, tana bani labarin yanda jikin Abie yaketa k’yau a tsakaninnan, dukda kar yanzu maganar bata fita amma yakanyi bamai tsawoba, naji dad’i sosai, na masa addau’a mai tsawo tareda fatan alkairi, daga nan muka cigaba da tattaunawa akan maganar Abbana, da zancen su innarmu dasuka k’i yarda su zauna a gidan, innarmu ta dage bazata zaunaba tunda muma anan muke, saida Momma ta saka baki da mata bayanin da zata gamsu sannan ta amince zata zauna. Nasha dariya, dan dama nasan za’ayi hakan, innarmu kawai kunya da kawaici.
     Daga nan har muka dawo kan ta Muftahu, dayake tasan komai a kai, da taimakonta nima nake samun k’arfin gwuywa.
    Itama tasha mamakin jin Harun a lamarin, ta dad’e tana jinjina maganar nan. ta bama Samha muka d’ora da hira, saida naga time yaja ga zazza6in fama ya rufeni, sallama mukayi nai addu’a Na kwanta.
    Masu iya magana since sabo tirken wawa, saina kasa barcin, naji kawai ina kewar Galadima.
    Shima kansa yanacan sai juye-juye yakeyi, yakasa barci, bayan sun gama hirarsu dasu Aryaan yay musu shirin barci da kansa suka kwanta, aiki yad’an ta6a yana Neman dabaru akan binciko Muftahu, baiwani dad’eba ya kwanta shima, amma saiya kasa barci, juye-juye yaytayi agadon, ganindai da gaske ya kasa barcinne saiya mik’e yana jan guntun tsaki, kwanciya ya gyarama su Aryaan ya lullu6esu da bargo sannan ya fito da nufin wai zai duba munaya ????????.
        Jin shigowarsa yasani k’ara lafewa tamkar nayi barci, ya kunna fitilar d’akin yana kallona, yaja wani dogon lokaci sannan ya kashe ya tako zuwa gadon, “nasan idonki biyu ai, dama kin tashi kinbar wani kumshe-kumshe”.
    Shiru nayi nakumak’i motsawa.
       Kwanciya yayi a gefena, yaja bargon shima ya lullu6a, tareda juyamin baya, yace “miya hanaki barcine?”.
        “farkawa nayi”. Na fad’a batareda ba kalleshi ba.
    Murmushi yayi yana fad’inn “ Hummm”.
     Daga nan duk mukayi shiru nawani lokaci, kamar an matse bakina nace “yalla6ai na tambayeka please? ”.
     Yace, “Uhmm”.
  Juyowa nayi ina fuskantar bayansa, a nutse nace, “wai dan ALLAH ina sauran matan Abie yanzu?”.
     Da sauri naga ya juyo gareni, ni harma tsoro ya kamani nai baya da sauri, nazata makeni zaiyi, amma sainaji ba hakaba, yace “Munaya mi kika sani a kaina ne?”.
     “yalla6ai kamarya mina sani a kanka? daga tambaya?”.
      Yace, “Humm yana matsowa gareni, zan matsa ya rik’o hannuna…………….????
Kuyi manage da wannan please????????

*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu????????????_*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button