NOVELSUncategorized
YARIMA FUDHAL 41-45

*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY PHIRDAUSY JEEBOUR.
41
11:42am
Suka yi parking motarsu a parking space dake cikin harabar asibin.
Kai tsaye Anwar ya yi musu jagowa har zuwa cikin ɗakin da aka kwantar da Yarima Fudhal.
Lokacin Sarki Ubaiyd na zaune kan ɗaya daga cikin fararan kujerun dake ɗakin kansa na ƙasa Wanda hakanne zai tabbatar maka da cewar ya faɗa cikin wani zurfaffan tunani ne.
Gefe guda kuma Fulani Bingel ce tare dasu Aunty Sadiya sai ƴan biyunta dake kwance kan carpet ɗin ɗakin sunata haura-hauransu sunyi ɓulɓul abinsu gwanin ban sha’awa.
Anwar ne ya fara turo ƙofar ya shigo cike da sallama sannan Magaji Saif ya biyo bayansa.
Ba Fulani Bingel ba hatta Sarki Ubaiyd bai San sanda ya mƙe tsaye ba sabida jin muryar mutumin da ko a mafarki bai taɓa tunanin zai sake jin ta ba.
Sai kuma gashi yau har suna ido biyu da juna kallon kallo aka hauyi tsakanin Magaji Saif da Sarki Ubaiyd .
Abin da basu taɓa zata da tunani ba shine ya faru wato hawaye a cikin idanun Sarki Ubaiyd amma kuma sun kasa tan-tance shin na farin ciki ne kona me?.
Sarki Ubaiyd ya taka ƙafafuwansa cike da sassarfa har zuwa inda Magaji Saif yake tsaye baiyi wata-wata ba kawai ya rungume shi yana faɗin.
“Kaine Yaya?, a she zan sake ganinka?, a she da rabon zamu sake ganawa a duniya?, kayi haƙuri ka gafarce ni nasan nayi kuskure a rayuwata…”.
“Aa kabar faɗin haka.!”.
Magaji Saif ya katse shi yana mai ci gaba da faɗin.
“Ni ne mai laifi kuma tuni nayi nadama na yafe maka fatana Allah ya yafemu baki ɗayanmu”.
Ya kai maganar yana mai ɗan bub-buga bayan Sarki Ubaiyd.
Baki ɗayansu suka amsa da “Amin” kowanne daga cikin su yana matse kwallar data taru gefan idonsa.
Sarki Ubaiyd ya bawa Magaji Saif kujerar da yake zaune shi kuma ya nemi guri a ƙasan carpet ya zauna, Magaji Saif yayi nacin ya koma kan ɗaya daga cikin kujerun ya zauna amma yaƙi.
Nan aka gaggaisa Magaji Saif yana tambayar masu jiki kafin ya dawo da kallonsa kansu Fulani Bingel.
“Kudan bamu waje”.
Ba musu dukansu suka fice suka bar Magaji Saif da Sarki Ubaiyd sai Yarima Fudhal Mara lafiya da yake can kan gado kwance.
Suna fita Magaji Saif ya dubi Sarki Ubaiyd ya fara magana cikin tattausan harshe ya kira sunansa.
“Ubaiyd..!”.
Sarki Ubaiyd ya amsa.
“Na’am Yaya”.
Magaji Saif ya ci gaba da maganarsa.
“Naji komai a bakin Anwar sai dai ka bani mamaki sosai Ubaiyd a ce kamarka kana aikata irin wannan abin da girmanka da komai da tunanika haba Ubaiyd ya kake nema giyar mulki tayi rinjaye akanka har kana neman salwantar da rayuwar jininka har guda biyu”.
“Idan ka manta ni zan tuna maka, da talaka da mai kuɗi basu da wani banbanci a gurin Allah sai Wanda yafi tsoron Allah ya inganta lahirarsa, bazan tsaya dogon surutu akanka ba domin kuskure ne anriga an aikata sai dai a kiyayi gaba”.
“Sannan abin da ya kawo ni idan har na isa da kai kuma haryanzu ina nan a matsayin Yaya a gareka inaso a yau ɗin nan dani da kai zamuje gidansu yarinyar da Fudhal yake so ayi magana, kuma batun auren mata biyu ka a jiyeshi gefe shi kuma Jaleel shima a bashi wadda yake a zauna lafiya”.
“Amma Yaya…!”.
“A a Ubaiyd wannan Umarni ne ba shawara ba idan har kaji ka yarda to, idan kuma baka yarda ba zaka nunamin ban isa ba ga hanya nan yanzun nan zan tashi inkoma Inda na fito”.
Sarki Ubaiyd yayi shiru tsayin wasu lokuta baice komai ba, haka shima Magaji Saif bai sake furta wata kalma ba ɗakin inbanda karar fanka dake tashi kaɗan-kɗan bakajin komai.
Ganin shirun yayi yawa ya sanya Magaji Saif miƙewa ya nufi bakin ƙofa zai fita ya murɗa hannun kofar zai buɗe Sarki Ubaiyd ya riƙo hannunsa cikin zafin nama yana faɗin.
“Kada ka tafi naji na amince zanyi dukkan abin da kace wallahi, ƴaƴana ai naka ne kana da ikon zartar da kowanne irin hukuncin a kansu”.
Magaji Saif yayi murmushin jin daɗi har ƙasan ransa ya koma ya zauna har a lokacin murmushin bai bar saman fuskarsa ba.
Ya cigaba da faɗin.
“Ka amince zamuje neman auren yarinyar yanzu?”.
Sarki Ubaiyd ya gyaɗa kai ba tare da yace komai ba.
“Idan ta kama da ba da hakuri dole haka zaka bayar, duk wani girman kai da taƙamar mulki ka ajiye shi tun anan”.
Nanma Sarki Ubaiyd kai ya gyaɗa alamun ya a mince.
“To alhamdulillahi tashi muje”.
Magaji Saif ya faɗa yana mai wucewa gaba domin fita daga ɗakin, Sarki Ubaiyd ya biyo bayansa.
A tare suka fito Inda su Anwar ke zaune zaman jiransu, Magaji Saif yace.
“Ku koma ciki Sadiya, kai kuma Anwar biyomu zuwa parking space.
Ba musu Anwar ya biyo bayansu har zuwa bakin motarsa ya kunna Magaji Saif da Sarki Ubaiyd suka shiga baya suka zauna Anwar ya shige wajen driven yaja motar suka fita daga cikin harabar asibitin.
Sai bayan sun hau titi sannna Anwar yake tambayar.
“Abba ina zamu je ne?”.
“Gidansu yarinyar da Fudhal yake so zaka kaimu”.
Magaji Saif ya bashi amsa, Anwar ya take burki da sauri ba tare daya sani ba domin jin abin da Magaji Saif ya faɗa.
“Subhanallahi..! Lafiya Anwar?”.
Suka tambayeshi a tare.
“Babu komai burkinne yaɗan kwace mun”.
***
Tsaye suke jikin bishiyar darbejiyar dake ƙofar gidansu Aynu, sun shafe tsayin lokuta bayan gaisuwa ba tare da ɗaya daga cikin su ya sake furta ko kalma ɗaya ba, ko wanne yana saƙe-saƙe cikin ransa.
Ya Sayyadi Umar shine ya katse shirun tare da yin gyaran murya kafin yace.
“Ya shirye-shirye kuma ya gajiya?”.
Aynu taɗanyi murmushi tana mai bashi amsa.
“Alhamdullahi”.
“Masha Allah, sai dai kamar akwai abin da yake damunki duk naga kin rame sosai lafiya kuwa?”.
“Lafiya ƙalau wallahi, kasan zirga-zirga ma ta ishi mutum ya rame ya fita haiyacinsa”.
Ya Sayyadi Umar ya gyaɗa kai kawai, amma a zahiri bai gamsu da amsar data bashi ba.
“Na tambaye ki Aynu”.
“Uhm ina jinka”.
“Ina so ki faɗamin tsakaninki da Allah kada ki ɓoyemin dukkan abin da yake cikin ranki”.
“Insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na gaya maka gaskiya akan abin da nasani akan dukkan abin da zaka tambaye ni”.
“Masha Allah, Aynu dan Allah har yanzu a cikin ranki kina son Fudhal?”.
Dammm gaban Aynu ya buga take taji ƙwalla na shirin zubowa daga idanuwanta tayi ƙoƙarin mai da ita tare da dai-daita nutsuwarta kafin tace.
“Amma me ya kawo wannan maganar?, koma zan so wani ai a dane yanzu dole kai zan so domin nan da ranar juma’a kai zaka zamo miji agare ni”.
Ya Sayyadi Umar yaɗanyi gajeren murmushi kafin yace.
“Haka ne maganarki shikenan Allah ya nuna mana ranar”.
“Amin”.
“Babu wani abu da kike buƙata ko?”.
Aynu gyaɗa kai tayi ba tare data iya bashi amsa da bakinta ba.
Shiru ne ya sake ziyartar wajen tsayin lokaci Ya Sayyadi Umar na kallon Aynu yana karantar yanayinta yana son yi mata magana akan Fudhal sai dai ya rasa ta Inda zai fara, kuma yana fargabar yanda zata ɗauki maganar.
Har dai daga ƙarshe sukayi sallama ya tafi, tana tsaye har ya ɓacewa ganinta mai makon tayi gida sai ta wuce gidansu Zainab sabida gidansu jama’a bazata samu damar sakewa ba.
Tana shiga gidan suka gaisa da Baba Ta Sallah kai tsaye ɗakin Zainab ta wuce ta faɗa kan katifa tahau rera kuma sosai tsananin son ganin Fudhal da tausayin halin da yake ciki yana taso mata har bata san sanda Zainab ta shigo ɗakin ba tana yi mata magana.
Aynu ta ɗago jajayen idanuwanta tana duban Zainab ba tare da tace komai ba, Zainab tazo ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗarta tana faɗin.
“Haba Aynu har zuwa wanne lokaci ne zaki yi haƙuri ki danganawa Allah komai akan al’amarinki da Fudhal ne?”.
“Bawai rashin dangana bane Zainab ina tausayawa halin da Fudhal ya shiga akai nane, shi kuma haka ƙaddararsa tazo a kaina?, duk yanda naso daurewa zuciyata kasawa nake Zainab, wallahi inason sake ganin Fudhal ko da sau ɗaya ne a rayuwata, ina takaici tare da jin haushin kaina a kan abin da nayi masa nasan duk nice sila..!”.
Takai maganar tana mai sake fashewa da kuka, Zainab ta dafa bayanta.
“Kiyi haƙuri Aynu kada ki ɗorawa kanki laifin abin da bake kika aikata ba, kisa a ranki haka Allah ya ƙaddarowa Fudhal kada kidinga ɗorawa kanki laifi kisa damuwa a ranki har tazo tajawo maki wani ciwon”.
HELLO MY FANS
TEAMS AYNUL-FUDHAL
TEAMS AYNUL-UMAR
Nidai nace AYNUL……! Lol
ASHA KARATU LAFIYA SAI TOMORROW INSHA ALLAH.
BYEEE.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausy Jeebour.
42
Suna isa dai-dai kan layin gidan Anwar yayi parking motar suka fito suka taka da k’afafuwansu.
Tun da suka shiga layin Magaji Saif da Mai Martaba suke bin gidajen da kallo tunaninsu bai ta’ba kawowa akwai unguwar da talauci yayi k’atutuba irin wannan unguwar musamman Sarki Ubaiyd sai gashi yazo da k’afafuwansa nemawa kansa suruka a cikin unguwar da ko a cikin taswirar garin bai ta’ba tunanin akwai ta ba bare a taswirar kansa.
Suna isa k’ofar gidan Anwar ya nemi yaro ya aike shi domin yayi musu sallama da Baban Aynu.
Bayan mintuna kad’an yaron ya fito tare da fad’in.
Bayan mintuna kad’an yaron ya fito tare da fad’in.
“Wai ance yana zuwa”.
Anwar ya zaro Naira d’ari a aljihun wandonsa ya bawa yaron tare da fad’in.
“Nagode kaji”.
Yaron ya tafi cike da murna, bayan wani lokaci sai ga Baban Aynu ya fito domin ganin wad’anda ke sallama da shi, duk jikinsa ruwa da dukkan alamu fitowarsa kenan daga wanka.
Ganin Mai Martaba yasa shi fad’ad’a murmushinsa yana yad’in.
“Ashe kune ?, sannunku da zuwa bari in fito da tabarma ciki mutane sunyi yawa da mun shiga daga ciki.
Magaji Saif ne ya amsa da.
“Babu komai wallahi “.
Baban Aynu ya koma ciki Jim kad’an sai gashi d’auke da tabarma ya shimfid’a musu k’ark’ashin bishiyar darbejiyar suka zauna tare da gag-gaisawa, Magaji Saif ya bud’e baki ya fara magana.
“Nasan kayi mamakin ganinmu a dai-dai wannan lokaci, kuma nasan ni ba zaka shaida ni ba, ni sunana Magaji Saif yaya ne ga Sarki Ubaiyd na wannan gari, mun zone ba dan komai ba sai dan mu baka hak’uri akan abubuwan da suka faru, ka sani duk abin da yake faruwa bani da masaniya wallahi kasancewar na shafe tsayin shekaru bana garin nan, sai yau Allah ya dawo dani kuma ansanar dani komai hak’ik’a Ubaiyd ya biyewa son zuciya da giyar mulki ina fatan zaka gafarce mu?”.
Baban Aynu yad’an gyara zama tare da gyaran murya.
“Babu komai wallahi dama can ban rik’e Sarki Ubaiyd acikin raina ba ko kad’an, kuma naji dad’i da kuka gane gaskiya dama anaso idan mutum yayi kuskure ya gane kuskurensa hakan yayi kyau nima na gode sosai”.
Shiru ya gauraye wajen har nawasu tsayin lokuta kafin Magaji Saif ya ci gaba da magana.
“Sai dai kuma muna tafe ne da wata buk’ata mai girma ina fatan ba zaka duba abubuwan da suka faruwa ba a baya ba”.
“Insha Allahu ai komai ya wuce wacce buk’ata ce wannan?”.
Magaji Saif yad’anyi shiru kafin yace.
“Akan dai maganar yarinyarka da d’an namu ne Fudhal muna rok’onka ka dubi Allah ka dubi halin da d’anmu yake ciki ka taimaka ka bamu auren ‘yarka”.
Baban Aynu ya d’an girgiza kai.
“Amma da kadaina had’ani da Allah Magaji hak’ik’a kazo da batu mai girma kafin kuzo nan basu sanar maka cewa jibi wato ranar juma’a za’a d’aura auren Aynu ba?”.
“Sun sanarmin amma ba wannan za’a duba ba halin da yaron yake ciki shine abin dubawa”.
“E hakane amma sai dai kunzo a k’urar-ran lokaci bani da damar da zan iya yi muku wannan alfarmar kuyi hak’uri Allah ya bawa Fudhal lafiya ya kuma bashi wadda tafi Aynu”.
“Amin”.
Suka amsa Sarki Ubaiyd dake zaune gefe tun zuwansu ya kasa furta komai haka kawai yau yaji Baban Aynu yayi masa kwarjini sosai jin amsar da Baban Aynu ya bayar shine ya sanya shi bud’e baki da sauri yana fad’in.
“Nima bazanyi k’asa agwiwa ba wajen baka hak’uri ba, dan Allah ka ceci rayuwar d’ana ka bashi Aynu”.
“Ai rayuwar d’anka na wajen Allah ba waje na ba, idan yaso ya rayu ko ya auri Aynu ko bai aurata ba tabbas zai rayu, haka kuma idan lokacinsa yayi koya aure ta Kobe aure ta ba tabbas zai mutu kama daina danganta rayuwar d’anka da Aynu, idan banyi kuskure ba zan iya cewa dukkan abin da ya faru da d’an ka Kaine babban mai laifi”.
“Ka sani arziki da talauci babu abin da basa bayarwa a rayuwa ka inganta rayuwarka data iyalinka shine abu mafi ma’ana da mafita “.
“Ka sani bawai ina fad’a maka bane domin in rama abin da kaimin ko kusa wallahi, ina fad’ane kawai domin intuna maka da abin da ka mance”.
“Allah gafururrahim ne idan yaso ya azurtaka babu Wanda ya isa ya hana, haka kuma idan yaso ka da talauci babu Wanda ya isa ya azurtaka, daraja dan Adam da girmamashi kowanne iri ne yana da fa’ida sosai domin Allah subhanahu wata’ala da kansa ya fad’a a cikin alk’ur’ani cewa.
“(WALAK’AD KARRAMNA BANIY ADAMA WAHAMALNAHUM FIL BARRI WAL BAHRI WARAZAK NAHUM MINAL ‘DAYYIBATI WA FADDALNAHUM ALA KASIYRIM MIMMAN KALAK’ NA TAFDIYLA)”.
Ma’ana:-(Kuma lallene mun girmama d’an Adam kuma muka d’aukesu a cikin k’asa da teku, kuma muka azurtasu daga abubuwa masu dad’i, kuma muka fifitasu akan masu yawa daga wad’anda muka halitta fifitawa).
“Hak’ik’a wannnan ayar ko ita kad’ai ta isa mu girmama junanmu mu ‘yan adam tare da mutun tawa , domin agurin Allah bamu da wani ban-banci duk abu d’aya ne mu bayi ne a gareshi dole ne mu bauta masa indai muna son dace wa da samun cikawa da imani, Allah ya yafemu baki d’aya abisa laifin da mukayi masa na fili da na b’oye”.
“Amin”.
Suka sake amsawa.
Suka sake amsawa.
Sarki Ubaiyd baiyi k’asa a gwiwa ba ya matsa har Inda Baban Aynu ke zaune ya rik’o hannunsa yana fad’in.
“Mai kake so a duniya? Wanda zanyi maka da zai sanya ka bawa dana auren ‘yarka, kud’i ko mulki? ka fad’i dukkan abin da kake so zanyi maka indai har zaka bawa Fudhal auren Aynu ko sarautar tawa kake buk’ata zan baka wallahi akan dai in rasa d’ana mafii soyuwa a cikin raina”.
Baban Aynu ya girgiza kai yana mai k’arewa Sarki Ubaiyd kallo domin ya tabbatar da gaskiyar abin da yake fad’a, tabbas yaga tsan-tsan nadama sosai a idanun Sarki Ubaiyd, Baban Aynu yayi hamdala cikin ransa afili kuwa ya furta.
“Bana buk’atar komai naka Mai Martaba, sai dai abin da bakina ya furta d’azu har a yanzu shi d’in zai sake furtawa kayi hak’uri zan taya d’anka Fudhal addu’ar samun macen da tafi Aynu tare da fatan samun lafiyarsa s…!”.
Maganar Baban Aynu ta katse a dai-dai sanda suka tsinkayi sallamar mutum a kusa dasu ko wannansu ya d’aga kai sama domin ganin mai Sallamar.
Ya Sayyadi Umar ne ya cire takalminsa ya nemi guri d’an nesa da su ya zauna akan tabarmar tare da gaishesu dukansu suka amsa.
Ya Sayyadi Umar ya bud’e baki zaiyi magana Baban Aynu yq katse shi da fad’in.
“Wannan shine yaron da zai aureta ai”.
Magaji Saif da Sarki Ubaiyd sukabi Ya Sayyadi Umar da kallo.
Ya Sayyadi Umar yad’anyi gyaran murya.
“Baba daman nazo ne kan wata magana”.
“To intaso kenan “.
“A a muyi maganar anan, dama maganar nan ne huruminta”.
“To masha Allah ina jinka Mallam Umar”.
Cewar Baban Aynu kenan yayin da dukansu suka bada a tension wajen Ya Sayyadi Umar domin jin abin da zai fad’a.
“Baba nasan zaku ji maganar da baku tab’a zata ba kuma bakuyi tsammani ba, na riga na yanke hakan kuma inaji a raina alkhairi ne yin hakan banajin zanyi kuskure ko kad’an, Baba tun ranar da abokin Fudhal yazo ya d’auke ni wato Anwar ya kaini na dubo Fudhal tun daga ranar zuciyata ta kasa samun nutsu inaji araina kamar nine na yiwa rayuwar Fudhal karan tsaye a yau inajin dad’i tare da godiya ga Allah har cikin raina zanyi abin da ba duk wani masoyi ne zai iya ba, bantab’a tunani ko ji araina zan iyayin sadakar soyayata ba amma ayau ni UMAR FARUK na SADAUKAR GA SOYAYYATA GA YARIMA FUDHAL, Ma’ana na barwa Fudhal Aynu ya aura duniya da lahira ina fatan nima Allah yayi min zab’in mafificin alkhairi…;”.
“Kai Umar..! Kasan me kake fad’a kuwa?”.
“Na sani Baba.!, Idan banyi hakan bane banajin kona auri Aynu zuciyata zata zauna lafiya domin Aynu babu Wanda take so aduniya fiye da Fudhal ni nasan hakan, Aynu ta yarda zata aure ni ne kawai domin yin biyayya agareku amma bawai dan tana so naba”.
“Amma Umar kana ganin hakan ya dace?”.
“Sosai ma Baba kayi musu fatan alkhairi kawai, sai dai ina rok’on wata alfarma Baba”.
“Ina jinka Umar”.
“Kamar yanda aka sanya d’aurin auren nan banaso a fasa a d’aura auren Aynu wa Fudhal ranar juma’a dan Allah Baba kayimin wan nan alk’awarin”.
Baban Aynu yayi shiru tsayin lokaci yana kallon fuskar Ya Sayyadi Umar yama rasa abin da zaice domin ya Riga ya d’aure shi da jijiyoyin jikinsa akan dole yace.
“Nayi maka alk’awari Umar kamar yanda kace insha Allahu ranar juma’a za’a d’aura auren Fudhal wa Aynu bi iznillahi ta’alah, Allah yayi masa albarka yasa ka gama da duniya lafiya ya baka dukkan farin ciki duniya da lahira kamar yanda ka faranta rai kaima “.
“Amin Baba babu komai ai”.
Magaji Saif, Sarki Ubaiyd, Anwar sakar baki da hanci sukayi suna kallon Ya Sayyadi Umar tare da jinjinawa tsananin jarumtarsa wajen iya sadaukar ga soyayyarsa lokaci guda haka.
Fuskar Sarki Ubaiyd tuni ta jik’e da hawaye yama rasa mai zai cewa Ya Sayyadi Umar da k’yar dai ya iya furta.
“Mungode Umar Allah yayi maka albarka yayi maka sakayya kan abin da ka aikata na alkhairi nayi alk’awari dukkan abin da kake so a duniya ka fad’amin zanyi maka kada kaji nauyi ko kunya domin bani da abin da zan saka maka dashi nan duniya sai dai Allah ya saka maka”.
Anwar kuwa mik’ewa tsaye yayi ya rungumeshi yana fad’in.
“Mungode.! Mungode..!! Mungode…! Sosai Umar bani da bakin da zan iya yi maka godiya kayi abin da wad’anda zasu iyayin hakan basu da yawa a duniya Allah ya baka wadda tafi Aynu Umar mungode”.
“Amin ya Allah”.
Magaji Saif kuwa murmushi kawai yake dokawa domin yama rasa bakin magana daga k’arshe dai yace.
“Babban albishir d’in da zan iya yimaka kawai shine ni Magaji Saif na bawa Umar auren Jalilah ‘ya ga k’anina Sarki Ubaiyd sauran tukwicinka kuwa sai mun zauna”.
Ba Ya Sayyadi Umar ba hatta Anwar da Baban Aynu basu san sanda murmushi ya kufce musu ba dan tsabar farin ciki da jindad’i jin wannan babban tukwici da Magaji Saif yayi masa, Sarki Ubaiyd kuwa girgiza kai kawai yake hawaye ne a fuskarsa amma kuma murmushi yake.
YAU DAI NASAN TUKWICINA NA MUSAMMAN NE AGAREKU *AYNUL-FUDHAL* INA JIRA NA CIKA MUKU BURIN KU YAU.
TO AYNUL-UMAR YA KOMA JALILAH-FARUK
KU KUMA WANNE IRIN TUKWICI ZAKU BANI INA JIRA
BYEE..!
*YARIMA FUDHAL*
NA
FIRDAUSI S.A(AURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A(AURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY PHIRDAUSY JEEBOUR.
43
Ya Sayyadi Umar ya durƙusa yayi godiya duk da cewar bai san wacece Jalilah ba? bai taɓa ganinta ba amma ba zai iya cewa baya so ba, a kan dole ya amince kenan da auren Jalilah?.
Su Mai Martaba sukayi addu’a tare da roƙon Allah ya sanyawa auren albarka Ya Sayyadi Umar yayi musu sallama ya tafi amma kafin ya tafi ya roƙesu akan kada asanarwa Aynu komai har sai anɗaura auren kuma ko wanne daga cikin su ya amince da wannan batun.
Sannan suma sukayiwa Baban Aynu sallama suka tafi kowa zuciyarsa cike fal da farin cikin wannan rana.
Suna komawa asibitin kai tsaye Magaji Saif da Sarki Ubaiyd office ɗin doctor suka nufa, Anwar kuwa ɗakin da Fudhal yake jinya ya nufa yana shiga su Hajiya da Aunty Sadiya suka tsare shi da tambayar abin da ya faru.
Bai wani tsaya tunanin komai ba ya sanar musu duk kan abin da ya faru zuciyar Fulani Bingel da Aunty Sadiya suka cika da farin ciki Sa’idah kuwa ba zaka iya shaida yanayin da take ciki ba farin ciki ne ko akasin hakan.
“Doctor ya jikin Fudhal ɗin kuwa?”.
Cewar Magaji Saif kenan tare da tsare Doctor da idanuwa domin jin amsar da zai basu.
Ya cire farin glass ɗin dake manne bisa idonsa yana kallonsu fuskarsa wasai.
“Jikin Fudhal alhamdulillahi kullum yana ƙara samun lafiya may be nan da Friday muna saran farfaɗowarsa sai dai abin da nake ƙara tuna muku idan har ana son ɗorewar samuwar lafiyarsa dole ne idan ya farka ya fara sanya abin da yafi so a cikin idanunsa, amma idan aka samu akasin hakan ba zan iya cewa wani abu ba domin rayuwa da mutuwa duk na Allah ne amma mudai fatanmu ya samu lafiya”.
“Haka ne Doctor insha Allahu komai yazo ƙarshe ai, zai samu abin da yake so da yardar Allah”.
Faɗin Sarki Ubaiyd kenan yana mai miƙewa domin fita daga office ɗin, sukayi musabiha suka fito kai tsaye ɗakin da Fudhal yake suka nufa domin ƙara dubo yanayin jikin nasa.
***
WASHE GARI
Baban Aynu na zaune ƙofar gida tare da muƙar-rabansa sai ga samari nata shigowa layin ɗauke da kayan abinci suna ajiyewa ƙofar gidan nasu Aynu.
Baban Aynu ya cika da mamaki sosai ya miƙe ya tari ɗaya daga cikin samarin.
“Yaro anya nan akace ku kawo kayan nan?”.
“E nan ne Baba”.
“To amma waye ya aiko ku?”.
“Mai Martaba ne yace mu kawo nan ai muna tare da abokin Yarima Fudhal shine ya nuna mana gidan ma”.
Daga nan Baban Aynu bai kuma cewa komai ba ya zuba ido kawai yana kallon yanda ake jere kayan abinci ƙofar gidansa Wanda har bayan biki sai sun shafe tsayin watanni shida basu nemi abinci ba.
Suna gama kawo wa Anwar ya ƙaraso zuwa inda Baban Aynu da mutanansa ke tsaye cirko-cirko ya durƙusa ya gaishe su, suka amsa .
“Amma Anwar irin wannan hidima haka?”.
“Baba babu komai ai daga Mai Martaba ne wannan aiken yace a gaisheka”.
“Ina amsawa Anwar kayimin godiya sosai, sai nazo da kaina”.
“Babu komai Baba”.
Ya kai maganar tare da zaro rafar yan ɗari biyar ya miƙawa Baban Aynu yana faɗin.
“Ga wannan yace kuɗin cefane ne”.
“Bayan wadan nan kayan kuma?”.
“E Baba “.
“To angode Allah ya saka da alkhairi”.
Baki ɗaya ƴan gurin suka amsa da “Amin”.
Su Aynu nacan gidan lalle da gyaran jiki anata fama wanda duk wannan abubuwan ƙoƙarin Zainab ne dan dai ta Aynu da babu abin da zatayi sabida abin da yake damunta kaɗai yasa baki ɗaya bata sha’awar komai ba kuma tajin farin ciki da wannan auren ko kaɗan ji take acikin ranta tamkar wannana auren yayiwa rayuwarta karan tsaye.
Damuwa da faɗuwar gaba sun tsananta agareta cikin kwanakin nan, hakan ne yasa baki ɗaya ta rame ta zama kamar wata mai ciwo, mutane sai cewa suke fargabar biki ce sai dai ita kai tasan abin da yake damunta.
A ranar da yammaci akayi walima kamar yanda suka tsara amarya tayi kyau sosai cikin wata doguwar riga pink data sha stone fari mai ratsin blue tayi rolling kanta da mayafin doguwar riga Wanda shima pink ne, ƙawar amarya kuma aminiya doguwar riga blue ta saka mai ratsin stone pink yayin da sauran al’umma sukayi shigar after dress baƙa maza kuma jallabiya abin gwanin ban sha’awa ankira malamai mata sunyi wa’azi sosai akan aure da zamantakewar rayuwa tayau da kullum, anci ansha a walimar abin da al’umma basu taɓa zata za’ayi ba a taron walimar shine ya faru.
Duk yanda Aynu taso su haɗu da angonta Ya Sayyadi Umar ƙi yayi sai taga kamar ma gudunta yake yi abin da ya ƙara dagula mata lissafi kenan ba ita bama hatta Zainab abin yaɗaure mata kai sai dai kawai tana ƙoƙarin kwantarwa da Aynun hankali ne amma a can ƙasan zuciyarta damuwace ita ma a cunkuce.
RANAR JUMA’A…!.
Bahaushe yace “Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya”.
A ranar juma’a ƙarfe goma da rabi na safe za’a ɗaura auren.
Mai Martaba da Magaji Saif tare da muƙar-rabansu tun ƙarfe goma da ƴan mintuna suka halacci wajen ɗaurin auren kar kuso kuga gayyar jama’ar dake tare dasu wai danma auren yazo a ƙurarren lokaci.
Tuni unguwar ta kaure da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe yara maza da mata sai gudu suke zuwa cikin gidansu Aynu suna bada bayanin ɗaurin auren Aynu har dasu Sarkin garin Umman Aynu dake tasan komai sai dai kawai tayi murmushi sauran jama’a kuwa faɗi suke.
“Ohh auren Aynu da farin jini yake harda sarki yazo da kansa.
“Ohh auren Aynu da farin jini yake harda sarki yazo da kansa.
Su Aynu na can gidansu Zainab anata shirye-shirye ita kuwa ta shige cikin ɗaki ta kwanta kawai ita kanta ba zata iya cewa ga abin da yake damunta ba, Zainab ce ta dage mata har dai ta tashi ta hau shiri itama.
10:30Am
Goma da rabi dai-dai Baban Aynu ya fito cikin wata da kak-kiyar farar shadda hula da takalmin ƙafarsa ma duk farare ne wanda duk aikin magaji saif ne, aka ɗunguma baki ɗaya zuwa masallacin da za’a ɗaura auren.
Magaji Saif shine ya miƙa kuɗin sadakin Aynu dana jalilah Naira dubu hamsin hamsin tare da kuɗin aure shima dubu hamsin nan take aka ɗaura auren.
FUDHAL UBAIYD SALMAN
Da
AYNUL-HAYAT ABDALLAH
Da
UMAR FARUK KHALEEL
Tare da
JALILAH UBAIYD SALMAN
Kan sadaki dubu hamsin hamsin wanda duka Magaji Saif ne ya biya.
Abin da masu shela suka hau faɗi kenan take gurin ya kaure da kaɗe-kaɗe.
Mai Martaba dai Allah-Allah yake ayi agama komai sabida a yaune ake saran farkawar Fudhal yana gudun faruwar wani abun.
Mutanan da sukaje ɗaurin auren baki ɗaya saranda sukayi jin da wanda aka ɗaura auren sai sukaji tamkar kunnuwansu bai jiye musu dai-dai bane, sai da suka sake ji masu shela nata mai-maitawa nan fa kawunan kowa ya kulle masu farin ciki nayi akasin haka nayi.
Kanwar Zainab ce mai suna Jamila ta shiga gidan da gudu tana faɗin.
“Aunty kinsan da wa aka ɗaura auren Aunty Aynu?”.
Zainab ta dubeta a gaggauce tana shirya Aynu.
“Dawa za’a ɗaura banda Ya Sayyadin mu”.
Jamila tayi dariya.
“To baki canka ba Aynu dai da Yarima Fudhal aka ɗaura aurenta”.
Zee tayi tsaki tana faɗin.
“Aikin banza aike kin shiga uku da ƙarya”.
Jamila tayi kwafa taji haushin maganar Zee hakan yasa ta shiga ɗakin Baba ta Sallah ta ɗauko redio ɗinta ta kunna musu.
Jin abin da ake sanarwa a radio yasanya duk yan matan dake gidan kasa kunne domin tabbatar da a abin da suka fara ji da farko.
Ai ana sake mai-maitawa Zee ta rungume Aynu tana faɗin.
“Alhamdulillahi Aynu yau addu’armu ta karɓu kin zamto mata ga Fudhal mai yafi wannan daɗi?”.
Aynu kuwa ta kasa furta komai illa ruwan hawaye dake bin fuskarta kona Mene oho?.
“Amma ya akayi abubuwa suka canja haka?”.
Cewar Zee kenan harara Aynu ta jefa mata.
“Ta ina zan sani nima “.
Sukayi dariya tare da tafawa.
“Yanzu Ya Sayyadinmu ya zama angon Jalilah ƴa ga Sarki Ubaiyd, Fudhal ya auri Aynu? abin mamaki Allah mai yin yanda yaso”.
Abin da sauran ƴan matan dake gidan suke faɗi kenan.
Zee tayi dariyar jin daɗi tana mai ƙarewa ƙawarta kuma aminiyarta kallo sosai taji daɗin wannan al’amari kuma tana matuƙar taya Aynu murna da farin ciki.
Mai Martaba kasa jurewa yayi har sai da yaja Baban Aynu gefe ya sanar dashi buƙatarsa da kuma abin da Doctor yace.
Baban Aynu shima ya amince domin yana ganin yanzu sune suke da iko da Aynu ba shi ba.
Mai Martaba yayi murna sosai da amincewar Baban Aynu.
Magaji Saif kuwa na can ya sanya samari sai jido akwatuna suke suna shiga dasu gidansu Aynu akwati goma sha biyu haka aka jeresu a filin tsakar gidansu Aynu, Umman Aynu da Baba ta Sallah ta sanar mata kayan da aka kawo tsabar farin ciki saita fashe da kuka abin da bata zataba abin da ko a mafarki bata taɓa kawowa ba wai Aynu ce yau ta zamto mata ga ɗan sarki jikan Sarki Allah mai yanda yaso da bayinsa.
Baban Aynu ya sanya aka kira masa su Aynu mintuna kaɗan sai gata tare da Zainab.
Ya sata cikin ɗakinsa ya sanar da ita komai sannan yace zata bi su Mai Martaba yanzu asibiti inyaso idan komai ya dai-daita zata dawo.
Aynu tace babu komai domin yasan dama ba zata taɓayi masa musu ba ya sanar da itane dama domin ya fidda ita daga cikin duhu ne.
Anwar shine yake driving yayin da Magaji Saif yake zaune kusa dashi a baya kuma Mai Martaba tare da wazirinsa.
Sai motarsu Aynu driver ne kawai yake ja sai Aynu da ita da Zainab kawai a motar domin ance babu wanda zai bisu sabida asibiti zasuje itama Zainab ɗin dan dai kawai kada a bar Aynu ita kaɗai ne ba zataji daɗi ba.
Tun da suka tafi basuyi parking ko ina ba sai cikin harabar asibitin a parking space.
Kai tsaye ɗakin da Fudhal yake jinya suka shiga Fulani Bingel da Aunty Sadiya suka taso cike da farin cikin ganin Aynu ita kuwa sai ta sanya kanta cikin mayafi sabida wata irin kunya da taji ta lulluɓeta.
Ta gaishesu tare da samun guri ta zauna ta takure waje ɗaya Zainab ma ta nemi guri kusa da ita ta zauna kowa ya amsa gaisuwarsu amma ban da Sa’ida dake ta cika tana batsewa.
Sai dai kuma babu wanda ya lura da hakan illa su Aynu.
*YARIMA FUDHAL*
NA
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
44
Babban ɗan yatsan ƙafarsa ne ya fara motsawa sai kuma leɓansa da yake buɗe shi a hankali alamun yana ƙoƙarin furta wani abu ne.
Anwar shine ya fara lura da hakan da sauri ya miƙe daga inda yake zaune ya nufi bakin gadon yana faɗin.
“Abba kamar ya farka fa?”.
Da sauri dukansu suka mime suka ƙarasa bakin gadon a dai-dai sanda yake ta ƙoƙarin buɗe idanuwansa dishi-dishi ya fara ganinsu baya iya shaida ko suwaye hakan ne yasa shi mai da idonsa ya rufe kafin ya sake buɗewa yana ƙoƙarin ɗago ƙafafuwansa da yake ji sun zame masa tamkar dutse a jikinsa.
Da sauri Anwar ya fice daga ɗakin domin kirawo Doctor.
Yana fita Yarima Fudhal yana buɗe bakinsa sosai yana salati ya sake buɗe idanunsa akaro na biyu yana duban dukkan waɗanda ke tsaye jikin gadon domin jiran farfaɗowarsa.
Idonsa na gama wayewa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya alamun yanason tuna wani abu.
A dai-dai lokacin Anwar da Doctor suka shigo ɗakin, Doctor da Anwar suka miƙar da shi zaune tare da karashi jikin pillow.
Doctor ya lura da matso leɓansa da yake lokaci zuwa lokaci hakan ya sanya shi kara kunnensa dai-dai bakin sa.
“Ina AYNU?”.
Kalmar da yaji ya furta kenan.
Doctor ya juyo yana duban su mai martaba dake ta sharar kwallar farin ciki.
“Tambaya yake ina Aynu”.
Dukkansu suka juyar da kallonsu inda Aynu ke zaune kanta na ƙasa tana ta wasa da zoben hannunta.
Aunty Sadiya ta ƙarasa da sauri ta riko hannunta har zuwa jikin gadon ta tsai da ita tana mai kallon fuskar Fudhal.
Aynu dai kanta na ƙasa hannunta na rike da gefan karfan gadon tana murzawa ko kaɗan ta kasa ɗago kanta bare har ta iya kallon Fudhal.
Shi kuwa Fudhal ƙura mata ido kawai yayi babu ko kiftawa yana son gasgata abin da idanuwansa ke nuna mana ne, domin gani yake tamkar irin mafarkin daya saba yi ne a kullum.
Doctor yaɗan dafa kafaɗarsa yana faɗin.
“Ga Aynun taka nan”.
Sannan ya juyo kansu Fulani Bingel yace.
“Kuɗan bashi ko da tea ne idan ya buƙaci wani abu bayan wannan zaku iya bashi”.
Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin ya barsu.
Sarki Ubaiyd ya ƙarasa gefan gadon da Fudhal yake ya zauna tare da kallon ɗan nasa yana faɗin.
“Sannu ya jikin naka?”.
Fudhal dai bai amsa ba illa kawai kallon Baban nasa da yake.
Sarki Ubaiyd ya ci gaba da faɗin.
“Ga Aynu nan yanzu ta zama taka halak malak, domin a yau ɗin nan aka ɗaura aureta da kai, tare da Amince wata da ta iyayenta”.
Yarima Fudhal bai san sanda wani murmushi ya suɓuce masa ba sai a lokacin ya buɗe bakinsa da ƙyar yace.
“Amma Abba Umar ɗin ya yarda?”.
“E mana shine yace ma ya barmaka ka aura, yanzu Umar surikinka ne domin Babanku Magaji Saif ya bashi auren Jalilah”.
Yarima Fudhal yayi murmushi har sai da fararen haƙoransa suka baiyana, sai kuma yayi shiru tsayin lokaci yana nazarin maganar tare da kafe Aynu da ido.
“Abba tace ai bata so na”.
Jin Kalmar da ya furta ya sanya Aynu ɗago kai da sauri ta dube shi tuni idanuwansu suka sarke da juna wani irin abu ya ziryaci Aynu tun daga babban ya tsan ƙafarta har kwakwalwarta da sauri ta sauke kanta ƙasa domin ba zata iya jure kallonsa ba.
Yarima Fudhal yayi wani irin murmushi dana kasa gane fassarar sa kafin ya mai da kallonsa kan Anwar yana faɗin.
“Zanyi brush”.
Magaji Saif dake gefe ya taso da sauri ya kamashi kallon kallo aka hauyi tsakanin Fudhal da Magaji Saif Fudhal ya ƙarasa saukowa ya taka kafafuwansa bisa kasa, amma can ƙasan zuciyarsa cike take da tambayar.
“Waye wannan mai matukar kama da Abbansu sai dai kawai yafi Abbabsu girma”.
Magaji Saif kamar yasan mai FUDHAL yake tunani, murmushi ya ɗanyi kaɗan yace.
“Ni ne Magaji Saif da kaji Abbanku ya faɗa wato Yaya ga mahaifinku”.
Yarima Fudhal yaɗanyi murmushi kaɗan tare da guam kai alamun gamsuwa da maganar Magaji Saif, Magaji Saif ya kamashi har toilet ya raka shi ya dawo.
Yarima Fudhal yayi brush ya fito ya zauna bakin gado, Aunty Sa’ida ta miƙo masa cofin tea ya karɓa yahau sha, yana sha yana duban Aynu dake zaune bisa tabarma ita da Zainab suna hira jefi-jefi murmushin da takeyi kaɗan-kaɗan shine abin da yafi komai Jan hankalinsa sosai .
Abba dake zaune gefansa yana lura da yanayinsa shi kanshi sai yanzu ya ƙara tabbatarwa da irin ƙaunar da ɗansa kewa Aynu.
Gyaran murya ya ɗanyi kafin yace.
“Hajiya ku shirya ke dasu Sadiya muje gida a ɗauko masa abin da yake ɓukata sai driver ya dawo daku sabida ni yau muna da meeting”.
Magaji Saif yayi caraf yace.
“Sai mu tafi tare dama zanje wani waje nima, Anwar da su Aynu sai su zauna kafin su Hajiyar su dawo sai Anwar ɗin sai ya mai dasu gida”.
Haɗa kayansu Aunty Sa’ida tahauyi Yarima Fudhal na zaune gefan gadon baice dasu komai ba, domin tun da kowa dama yasan halinsa da rashin son yin magana bare kuma yanzu.
Suna gama haɗawa sukayi masa sallama tare da fatan Allah yakara masa lafiya suka fice suka tafi.
Suna fita Anwar ya koma inda Mai martaba ya tashi ya dubi Fudhal cike da murmushi yana faɗin.
“Mutumina yaufa buri ya cika gaka ga Aynunka ya kamata mu Baku waje ku gaisa domin naga alamun kuna buƙatar hakan”.
Yarima Fudhal murmushi kawai yayi ba tare daya bashi amsa ba.
Anwar ya dubi Zainab.
“Muɗan basu waje Zainab su gaisa ko”.
Aynu tayi saurin faɗin.
“Aa ku zauna wallahi a hakanma zamu gaisa”.
Tayi maganar ba tare data ɗago kanta ba.
Anwar ya dubi Yarima Fudhal daya Kafe Aynu da ido kawai, yayi murmushi yana mai bata amsar.
“Idan ke bakya buƙata mijinki na buƙatar hakan, tashi mu fita Zainab”.
Zainab babu musu ta miƙe tana dariya suka fice daga ɗakin, suka bar Yarima Fudhal da Aynu.
Tsayin lokaci ɗakin yayi shiru tamkar babu mutane a cikin ɗakin, sai can Fudhal yayi ƙarfin halin faɗin.
“Zo nan Aynu”.
Ba musu ta miƙe ta tako har zuwa inda yake zaune gefan gado ta tsaya a gefansa ba tare data dube shi ba.
“Babu gaisuwa bare tambayar ya jikin nawa ko haryanzu kina jin haushi nane?”.
“A a, ya jikin naka?, Allah kara sauki”.
Takai maganar cikin siririyar muryarta.
Yarima Fudhal yayi murmushi yace.
“Bana buƙata sai da na roka?”.
“Aa kafinnayi ne ka rigani tambay…!”.
Kafin takai ƙarshen maganar sai ji tayi ya kamo hannunta ya haɗa da nata, da sauri ta ɗago kai suka hada ido ya sakar mata wani irin tsadaddan murmushi wanda itama bata san sanda ta mayar masa da Martani ba tare da yin ƙasa da kanta.
Yarima Fudhal ya jawo ta zuwa dai-dai inda yake zaune gefan gado suna fuskantar juna ita na tsaye.
“Na tambaye ki mana Aynu.!”.
“Har yanzu kina sona kuwa?”.
Aynu ta ɗago kai da niyar bashi amsa sai dai kuma taji nauyinsa game da kunyarsa sun lulluɓeta ta sakeyin ƙasa da kanta.
Tattausan hannunsa ya sanya ya ɗago haɓarta tare da kafeta da idanuwansa mai sanya wanda yake kallonsa jin kasala.
Aynu kasa juran kallon nasa tayi ta rintse idonta gam, Yarima Fudhal yayi ƴar dariya kaɗan.
“Wai duk kunyata kike ji haka?”.
Bata bashi amsa ba haka kuma bata buɗe idon ba.
Fudhal ya saki haɓarta ya sake kamo hannunta da hannunsa duka biyun yariƙe yana kallon zanan Jan lallan da fulawan da akayi mata.
“Kai amma yayi kyau flawer ɗin yakai hannun nata bakinsa ya sunbata, Aynu ta janye hannunta da sauri tana kallonsa sai kuma ta sake sauke idanuwanta kasa.
Yarima Fudhal bai kuma cewa komai ba ya jawo pillow ya kwanta abinsa ya barta nan tsaye, tsayin lokaci a haka.
Aynu na ɗago kai taganshi kwance abinsa idanunsa a rufe yanayin yanda yake fid da numfashi ne ya tabbatar mata da yayi bacci sosai abin ya bata mamaki ƴan mintuna kaɗan amma ace yayi bacci?, sai kuma ta tuna ai bashi sa lafiya ne.
Ƙarasawa tayi dai-dai kansa ta gyara masa pillow ɗin tare da ɗora masa hannunsa dake miƙe kan gado bisa ƙirjinsa ba tayi aune ba sai jinta tayi ta faɗa kan ƙirjin nasa da sauri ta zaro ido waje sabida tsorata da tayi.
Yarima Fudhal ya sanya dariya.
“Ba kyaso inga kwalliyar in yaba ne?”.
Kai kawai ta girgizama masa alamun Aa tana kici-kicin kwace hannun amma ta kasa sabida irin riƙon da yayi mata, turo ƙofar da akayi ne yasa ta samu damar janye hannun nata tana duban mai shigowar.
Anwar ne tare da Doctor suka shigo.
Yarima Fudhal yaja guntun tsaki tare da kau da kai gefe, Anwar yayi murmushi kawai, Aynu kuwa kunyace ta lulluɓeta taji kamar ƙasa ta tsage ta shige.
Doctor ya tambayi jikin nasa tare da dubashi sosai ya juyo kan Aynu yana faɗin.
“Ya kamata a dinga bashi Magani akan lokaci sabida gujewa samun matsala”.
Aynu ta gyaɗa kai dai-dai sanda Zainab ta shigo ita ma ta nemi guri ta zauna, Doctor na gama duba shi zai fita kenan su Hajiya sukayi sallama suka shigo ɗauke da kulolin abinci da kayan Fudhal.
Aunty Sadiya ce ta buɗe baki tana tambayarsa mai zai ci yanzu?.
Ya bata amsa da faɗin.
“Ko mene ma bani inci”.
Ta koma kan kulolin tahau zubo masa makaroni da miya taji naman rago, tare da tsiyaya masa lemo a cofi.
Ta kai masa gabansa ta ajiye.
A hankali ya ɗauki cokali yahau ci jefi-jefi yana kai kallonsa kan Aynu shi kan shi ya rasa dalilin da yasa ya kasa daina kallonta haka kawai yake jin daɗin kallon nata duk da ita bata sanma yanayi ba hirarsu kawai suke da Zainab.
“Ku tashi muje in mai daku gida ko?”.
Cewar Anwar kenan yana mai miƙewa daga kan kujerar da yake zaune, Yarima Fudhal najin haka ya ajiye spoon din dake hannunsa take yaji ya ƙoshi ya ture abincin gefe.
Suka miƙe tare da yiwa Hajiya da Aunty Sadiya sallama, sannan suka ƙarasa inda Fudhal yake zaune sukayi masa sallama tare da faɗin.
“Allah ya ƙara lafiya”.
Wanda duk Zainab ce take maganar Aynu kunya ta hanata ko ɗaga kai.
Haka suka fice daga ɗakin koda sau ɗaya Aynu bata kuma bari sun haɗa ido da Yarima Fudhal ba, shi kuwa abin da ya ƙara baƙanta masa rai kenan take yaji zaman asibitin ma baki ɗaya ya gundure shi.
*YARIMA FUDHAL*
NA
FIRDAUSY S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSY S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
45
Zaune take cikin lambun dake farfajiyar gidansu akan wata tat-tausar darduma gefanta matane su biyar zagaye da ita ga kayan mar-mari kala-kala ajiye a gabanta.
Ƴan matan sai hira suke mata na ban nishaɗi tana dariya can ta ɗan bata rai tana duban su dukansu suka sha jikin jikinsu.
Tsaki ta ɗanyi tana mai duban matar dake gefan hannun damarta.
“Ku bani shawara Jummai akan batun aurena da Yarima Jaleel mana”.
Wacce aka kira da Jummai ta gyara zama tare da rissinawa.
“Haba Gimbiya aike kanki kinsan yanzu kin wuce ajin Yarima Fudhal, Yarima Jaleel shine wanda yafi dacewa dake a wannan lokaci, sabida ba girmanki bane ba kuma ajinki bane ace ki auri mai mata matarma Baiwa gaskiya da ance kin ci baya”.
“Yanzu kuna ganin aurena da Jaleel shine yafi?”.
“Sosai kuwa ranki ya daɗe”.
Sukayi maganar cikin haɗa baki, Gimbiya Safiyya tayi murmushi wanda har sai da fararen haƙoranta suka baiyana waje.
“Kuce ingayawa Babana na amince kenan?”.
“E mana”.
Suka sake bata amsa.
Gimbiya Safiyya tamiƙe da sauri ta nufi cikin gida suka take mata baya.
***
“Ladidi duk laifin kine wallahi kece kika haddasamin wannan masifar.!”.
“Kamarya Hajiya?, ai bokan da kansa yace sawun Yarima Jaleel aka kai bana Yarima Fudhal ba, kinga kenan laifin na wanda ya ɗebo sawun ne bana wanda ya kai ba”.
Fulani Sokoto tayi shiru tsayin lokaci tana kallon Ladidi kafin tayi ajiyar zuciya tace.
“Yanzu kenan meye abin yi?”.
“Mene kuwa abin yi?, Yarima Fudhal dai ya samu abin da yake so, Yarima Jaleel ma haka, Gimbiya Jalilah kuma an ɗaura mata malamin islamiyya, ke ya kamata ki yanke wannan hukuncin Hajiya ba ni ba”.
Fulani sokoto tayi tsaki mai tsayi tana huci.
“Ni auren Jalilah da wancan faƙirin shine yafi komai ɗaga min hankali wallahi taya zan samu a wargaza komai idan yaso maji da matsalar Fudhal da Jaleel”.
“To ki kira shi awaya muji mana”.
Fulani Sokoto ta janyo wayarta dake gefanta tahau dad-dan nawa alamun tana neman layin nasa, ringing biyu ya ɗaga tare da ƙunduma wani ashar itama Fulanin ta mayar masa kamar yanda yayi kafin ya kece da wata irin dariya yana faɗin.
“Basai kin faɗa ba munsan komai ai sun sanar damu”.
“To annemo mafita akan matsalar?”.
“Aure dai mutu ka raba ne babu yanda za’ayi mu iya raba auren, kuma zan faɗa miki abu guda ɗaya muddun kika matsa akan raba auren to tabbas zaki mutu..!”.
Dammm gaban Fulani ya buga ta saki wayar ta faɗi bisa carpet ɗin tsakar falon tana duban Ladidi, Ladidi tayi saurin ɗaukan wayar tana faɗin.
“Lafiya Hajiya?”.
Da ƙyar Fulani Sokoto tayi ƙarfin halin faɗin.
“Yace aure babu rabuwa kuma idan muka matsa akan raba auren tabbas zan mutu”.
Ladidi taja tsaki.
“To kuma Sai ki yarda da abinda da yafaɗa?, yanzu hakama kawai gani yayi bazai iya aikin ba shiyasa yace dake haka, kawai tun da abin hakane mu canja wani malamin kawai”.
Fulani Sokoto shiru tayi tsayin lokaci tana nazari kafin ta gyaɗa kai.
“Kuma maganarki akwai ƙamshin gaskiya fa, dannima kwanakin nan naga aikinsa baya tafiya yanda ya kamata yanzu wajenwa kike ganin zamu je?”.
“E to akwai wani acan kauyen SAMU NAKA ance shima aikinsa kamar yanda wuƙa inaga muje muji mai zaice shima”.
“Yanzu yaushe zaki je?”.
“Yanzuma idan kin bani dama sai in tafi inyaso gobe na dawo da safe”.
“Ai hausawa sunce da zafi-zafi akan daki ƙarfe ungo wannan maza kije”.
Ta miƙo mata rafar ‘ yan ɗari biyar-biyar, Ladidi tayi godiya ta miƙe tare da ficewa
daga cikin ɗakin.
daga cikin ɗakin.
“Sannu Jaleel ya jikin naka?”.
“Da sauƙi Abba sai dai ciwon ciki yana takuramin sosai cikin kwanakin nan”.
“OK Allah ya ƙara lafiya, ai likita yace babu wata matsala indai kana shan magani cikin ƙa’ida zai dai na”.
“To zan kiyaye Abba”.
Magaji Saifa dake gefe ya dubeshi tare da faɗin.
“Wani babban albishir zan maka yanzu amma sai kayimin alƙawarin ba zaka kuma shan wani abin maye ba”.
“Nayi alkwari wallahi bazan kuma sha ba”.
Magaji Saif da Sarki Ubaiyd sukayi murmushi
“Kasan dai mahimmancin alƙawari dai?”.
“Na sani Abba kuma zan kiyaye”.
Magaji Saif yayi murmushi a karo na biyu tare da dafa kafaɗar Yarima Jaleel kafin yace.
“An sanya ranar auren ka da Safiyya Sati mai zuwa idan ka fito daga asibiti”.
Take wani sanyin daɗi ya lulluɓe Jaleel bai san sanda ya rungume Magaji Saif ba yana godiya har da guntun hawayensa.
Sun jima sosai suna hira kafin su koma ɗakin Yarima Fudhal suka barshi daga shi sai Jalilah domin Fulani Sokoto bata dawo ba.
Yana zaune gefan gado yayi shiru can gefe kuma su Hajiya ne da Aunty Sa’ida yau Aunty Sadiya bata zo ba sabida anjima kaɗan da yamma zasuje ɗaukan amaryar Fudhal wato Aynu amma shi Fudhal bai san da hakan ba.
Magaji Saif ya dubeshi yana faɗin.
“Yadai Fudhal tunanin me kake kuma?”.
Fudhal yayi murmushi.
“Babu komai Kawu”.
Murmushin sukayi dukansu yace.
“Yau dai muna fatan Doctor zai sallameka mu huta da mita kullum akan angaji da zaman asibiti”.
“Kawu ai gani nayi na warke sumul mai kuma zanyi anan?”.
“Gaskiyarka babu abin da zakayi kuwa”.
Yakai maganar tare da ƴar dariya.
Doctor ne ya shigo a bayansa Anwar ne suka gaisa Anwar ya nemi guri ya zauna yayin da Doctor yahau duba Fudhal har sai da ya gama sannan ya dubi su Sarki Ubaiyd yace.
“Ga takardar sallama nan akula da maganinsa kuma sosai, Jaleel ma inaga zuwa gobe zamu sallameshi”.
Wani irin daɗi ne ya lulluɓe Fudhal har sai da farin cikinsa ya kasa ɓoyuwa.
Tuni Aunty Sa’ida da Hajiya suka miƙe suka hau haɗa kayansu, Anwar na kaiwa mota yana sakawa har sai da suka gama kaf sannan suka fita zuwa harabar asibitin.
Anwar ne yayi driven ɗinsu Hajiya da Fudhal, su Abba kuma driver ne ya ɗaukesu.
Suna dosar layin suka fara jin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe na tashi na murnar dawowar Yarima Fudhal.
Gidan cike dam-ƙam da al’umma sai kaiwa da komowa suke haka suka yi ta ratsa mutane ana gaishesu suna amsawa har zuwa cikin fada Sarki Ubaiyd ya zauna Anwar da Fudhal suka wuce ciki zuwa ɗakin Fudhal.
Suna shiga kai tsaye Fudhal toilet ya nufa domin ya watsa ruwa yana fitowa yahau shiri cikin wata da kakkiyar farar shadda wadda tasha aikin zare light blue hular kansa da takalminsa har zuwa agogonsa duk light blue ne ba karamin kyau yayi ba a wannan lokacin.
Anwar dai na kallonsa bai ce masa komai ba har sai da yagama sannan ya dube shi yace.
“Wai ina zaka haka kake ta faman shiri?”.
Yarima Fudhal ya ɗan tsaya daga fesa turaren da yake ya dubi Anwar yana bashi amsa.
“Ina zanje wanda ya wuce wajen mata ta,”.
Anwar ya sanya dariya yana faɗin.
“Tab..ai tuni ka makaro domin yanzu haka ana kan hanyar zuwa kaita gidan Aunty Sadiya ne.
Yarima Fudhal ya ajiye kwalbar turaren ya juyo gaba ɗayansa yana duban Anwar.
“Mai zatayi a gidan Aunty Sadiya kuma?”.
“Wannan sai dai ka tambayi Hajiya kuma itace ta bada wannan umarnin”.
Yarima Fudhal yayi tsaki take wata irin gajiya ta ziyarce taking yayi wurgi da hularsa bisa katifa ya cire babbar rigar ya wurgar ya nemi guri kan katifar ya kwanta.
Anwar ya bishi da kallo kawai abin sosai ya bashi dariya amma sai dai ya kanne domin sanin halin mutumin nasa.
Har akai kiran sallar maghriba yana nan kwance shi bai ma san sanda Anwar ya fice daga ɗakin ba sai da ya buɗe idonsa sannan yaga baya nan.
Miƙewa yayi yayo alwala yayi sallah ya ɓata tsayin lokaci azaune yana addu’o’i tare da godewa Allah.
Can ya miƙe ya nufi inda babbar rigarsa take ya sanya ya mai da hularsa ya sake feshe jikinsa da turaruka ya ɗauki wayarsa ya kunna tare da key din mota ya fice daga gidan.
Akan hanya ya kira Anwar yana tambayarsa yana ina?, gashi nan zuwa, Anwar ya bashi amsa da yana gidansu Saima, tsaki Fudhal yaja yana faɗin.
“Da maghribar nan me zakayi mata me zatayi maka?”.
Dariya sosai Anwar yasa ka yana faɗin.
“Idan kazo zan baka wannan amsar “.
Ya kashe wayar, Fudhal ya ajiye wayar a gefansa yana mai ci gaba da kallon titi tuƙinsa yake a nutse yayinda kira’ar sudes ke tashi kaɗan-kaɗan cikin motar.
Yana isa bakin gate yayi parking motarsa ya fito ya knocking ƙofar gidan mai gadin ya leƙo ganin Fudhal yasanya shi buɗewa da sauri domin ya sanshi sosai.
Yana shiga ya kirashi yazo mintuna biyar sai gasu sun fito a tare da ka gansu kaga waɗanda suka jiƙe a mayen so da kaunar junansu.
Duk da Saima yanzu Anwar take so kuma take burin aure Amma ganin Fudhal bai hana ƙirjinta bugawa ba sosai taga yayi mata kwarjini fiye da koyaushe haibarsa ta ƙaru wani irin sihirtaccen kyau na bayyana a jikinsa ganin kallon da take masa ya sanya shi kau da kai yana murmushi ya dubi Anwar.
“Sai ka janyota jin gulma kuma?”.
Saima tayi ƙarfin halin yin siririyar dariya, Anwar yace.
“To meye a ciki ?, abin da nan da sati muma zamu angwance gara tasan irin matsayinta a wajena tun yanzu”.
Yarima Fudhal ya gyaɗa kai kawai yana faɗin.
“Baka koya mata gaisuwa ba kenan?”.
Saima tayi saurin faɗin.
“Barka da dare”.
“Riƙe gaisuwarki bana buƙata”.
“Kaga mallam sauri fa nake ka sallameta mu tafi kawai”.
Saima ta danne ɓacin ranta kawai domin tasan halin Fudhal shi ba abin damuwarsa bane disga mutum gaban kowa, hakan kuma ko a takalminsa bare abin ya dameshi kai da akayiwa sai dai haushi ya kashe ka.
Anwar yace.
“Ai munyi sallama dama zuwa tayi ku gaisa kawai”.
“OK mutafi to muna bata time, nagode Saima ki gaida su Mama”.
Abin da yace kenan yana mai kama hanya ya fice daga cikin harabar gidan, Anwar yabi bayansa yana ɗagowa Saima hannu itama ta mayar masa da martani.
Anwar ne yayi driven nasu har zuwa ƙofar gidan Aunty Sadiya yana parking Yarima Fudhal ya fice daga motar baiko jira Anwar ɗin ba.
Gidan shiru kamar babu kowa sai da yayi sallama kusan sau biyar daga bakin ƙofar falon sannan Aunty Sadiya dake can saman mijinta ta sauko tana amsa masa.
Ya shigo tare da neman guri kan kujera ya zauna yana tambayarta ƴan biyu.
“Suna ɗaki sunyi bacci ne”.
Anwar yayi sallama ya shigo yana faɗin.
“Nagode Fudhal”.
Ya juya gun Aunty Sadiya suka gaisa Fudhal dai baice komai ba illa baza ido kawai da yake can dai ya kasa haƙuri yace.
“Ina Aynu take ne?”.
Dubanshi Aunty Sadiya tayi tana faɗin.
“Ganin Aynu ba yanzu ba”.
“Kamarya ba Yanzu ba?”.
“E mana umarmi aka bani”.
“Nasanma wasa kike nidai dan Allah tana ina?”
“Allah ba wasa ba, umarnin Hajiya da Abba ne”.
“Ya Allah..!”
Yarima Fudhal ya furta yana mai dafe kai.
“Sai yaushe to ?”.
“Sai nan da sati wato randa za’a kawo matar Jaleel ranar za’a kai maka taka kai ma”.
Tsaki yaja mai tsayi tare da kwafa.
“Amma dai gaskiya ba’amin adalci ba inason ganin Aynu wallahi Aunty”.
“Sai dai fa kayi haƙuri aikin gama ya gama”.
Yarima Fudhal yayi shiru yana duban Aunty Sadiya da Anwar kawai yama rasa mai zai ce.