MATAR UBA 34
???????????????????????????????? *MATAR UBA*
????????????????????????????????
Daga Alkalamin ✍️
*Milly*
Fadilah Yakub
*(MILHAAT)*
*????MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION????????️*
*M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
CHAPTER 34
Riko hannun Asiyah tayi ta fara zare mata kayan jikinta, har ta cire mata su tass, Baraka na ganin kirjin Asiyah ya bayyana ta kuma rikicewa, Asiyah kasa motsi tayi sai yanda Baraka tayi da ita,kwantar da ita tayi Tana mata wassani da taimakon turaren da ke jikin Baraka Asiyah ta fara Maida mata da martani.
????????????????????????????????
…………Baraka Jin ta take a wata duniyar daga ita har Asiyah sun manta inda suke, Sai da duk suka gamsar da junan su kana Baraka ta tashi tayi wants, ta bar Asiyah a kwance duk jikin ta ba karfin Banda kuka Babu abinda take yi, Baraka na fitowa daga Ban ‘daki ta daka mata tsawa Tace “Munafuka tashi ki sa kayan ki ki fice min a d’aki”
Jiki na rawa Asiya ta hau sa kayan ta, Baraka tace “Daga yanzu irin horin da zan Rika Miki Kenan kin ci sa’a naji dad’in ki fiye da yanda nake jin dad’in Safiyya da Wallahi yau sai kin d’an d’ana Kud’arki”
Ganin Asiyar ta gama sa Kaya a tsawace Tace “Get out!!!
Da gudu ta fita tana kuka, d’akin ta tashiga ta fad’a Kan gado ta Shiga rera kuka, wayar ta taji yana ringing d’ago kanta tayi ta duba don ganin wa ke karinta tana ganin number Hashim ta sake fashewa da kuka, kuka take sosai har bacci ‘barawo ya kwashe ta.
Baraka dariya take tana jin Dad’i bata da sauran damuwa, kwasam taji hankalin ta ya kuma tashi, Murmushi tayi ta kuma d’auko turaren Nan ta fesa a d’akin ta Kuma sawa a jikinta, wayarta ta d’auko ta kira Safiyya, Safiyya na Shiga ta nemi wuri ta zauna a Lokacin Baraka na sallar karya.
Safiyya a zuciyar ta tace “Yau water rana Mummy da sallah”
Bata daina sallar ba har Saida ta tabbata yanayin Yesmin ya cabza dake Yesmin jarrababbiyace kamar uwarta ita da kanta ta fara neman maman, suka sheke Aya su son ransu.
“Ni a gaskiya na gaji,Dole Asiyah ta bar gidan nan,Taya za a yi a Maida ita kamar wata baiwa a cikin gidan uban ta,ka duba kaga yanda ta mare ta,wato ni na lura ma cin zalin Asiyah a jinin jikin ta yake” Hashim ke wannan maganar Yana driving.
Girgiza Kai a farees yayi yace “Ya Isa haka man Hashim tun fitowar mu kake ta surutai,wasu maganganun baka San kana fad’a ba”
“Baza ka gane bane,wani irin ciwo nake ji a kirjina ba,a gaban idona fa ta mari Asiyah”
“Na sani,na sani, da ciwo Amma babu abinda zaka yi a kai , tabbas Asiyah abar tausayi Ce addu’a kawaii zamu mata”
Cike da takaici ya ciza laben sa tace”Hmm Wallahi akwai abunda zan yi a kai”
“Kamar me Kenan fa?”
“idan na aure ta akwai Wanda ya Isa ya tab’a min ita ne, Wallahi ko da Wasa aka tab’a min ita sai munyi shariya da koma waye”
Farees Yar karamar dariya yayi yace “Think straight yallab’ai, maganar Asiya da Baraka fa ake a Nan, idan Kuma so kake Baraka ta kashe Asiyar ita ma to bismillah”
Taka birkii yayi Wanda baisan sanda ya taka ba, wani irin Kara motar tayi farees sai ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un yake a tsawace yace “Hashim so kake ka kashe mu?”
Kansa ya d’aura a Kan sterin motar sa ya dad’e a haka kana yayi ajiyar zuciya yace “am sorry Wallahi na rud’e ne Dana ji ka ambaci mutuwa,yanzu Kai Dan Allah farees yanda nake a yanzu sai ka tsaya danganta Asiya da mutuwa? Fisabilillah kamin adalci Kennan?”
” Mene ne rashin adalci a nan mutuwar Nan fa Dole ne duk zamu mutu tunda duk jiranta muke”
“Na San da hakan amma……”
” Ya Isa haka Hashim ka tada motar Nan mu tafi dan Allah kaga Faisal sai kirana yake tun ‘dazu”
“Dole yau din nan a d’auki mataki akan Baraka, Abun nata gaba gaba yake,Allah ne kad’ai yasan abinda zata Mata yau,gashi ina ta Kiran ta bata picking”
Farees yace ” Hashim” Shiru Bai amsa ba
Ya Kuma cewa “Hashim”
‘dago Kai kawai yayi ya kalle sa, farees yace “ka sauka”
Kallon ban fahimce ka ba yake Masa.
Farees yace “zan jaa motar ne,don na lura Sam baka hayyacinka so ni ban shirya mutuwa yanzu ba”
Ba musu ya sauka, farees ya koma wurin Zama driver hashim Kuma ya koma wurin zaman Mai zaman banza.
Key ya sa wa motar suka cigaba da tafiya, Babu Wanda ya sake magana har suka Isa gidan su Yesmin Faisal na ganin su ya taso Yana Shirin rufe su da masifa, ganin fuskar su ba annashiwa yace “Lafiya na ganku haka?”
Yesmin dake biye da Faisal tace “Yaya Hashim ya na ganku haka wani abune ta Faru?”
Kallon ta yayi da idanun sa Wanda suka kad’a sukayi jaa yace “Ina Mummy da Daddy suke?”
Cikin sanyin murya Tace “Suna ciki”
Bai tsaya Bata amsa ba ya nufi cikin gidan,su kuwa suna ganin haka suka mara Masa baya.
Kai tsaye Bud’e kofar parlor yayi hade da Sallama, yayi sa’a suna zaune a parlor, har kasa ya durkusa ya gaida cikin sakin fuska suka qmsa gaisuwar tasa.
Cikin nuna kula da damuwa Nana tace “Hashim kana lafiya kuwa? Naga kamar kana cikin tashin hankali Ko dai baka da lafiya ne?”
Cikin tashin hankali yace “Bana Lafiya Kuma bazan tab’a samun sukuni da kwanciyar da hankali ba muddun ba a Kama Baraka ba”
Gyara Zama khamal yayi yace “Wani abun ta Kuma yiwa Asiyah?”
“Eh yanzu daga gidan mule……” Sai ya jero masa duk yanda sukayi.
Girgiza Kai yayi yace “Ni kaina na gaji da abin Nan,babban tashin hankalina ma anan shine Kar ta gane plan d’in mu ta cutar da Asiyah”
Nana Tace “Safiyya ce zata kawo Mana saukin abun nan, haryanzu jira nake Tace min ta fasa kwaryan Nan,daga Nan fa Shikenan sai yanda mukayi da Baraka”
Hashim yace “To a Kira ta Mana a Sanar da ita abinda zatayi don Wallahi in dai zata cigaba da musguna mata zanje Ni har gidan in asa a Kama Baraka Kuma na tafi da Asiya”
A tsawace Nana Tace “Kul Kar ka kuskura ka aikata wannan gangancin, don Wallahi ba Kai ka d’ai ba har mu saita shafa”
Faysal yace “Ni ma fa nayi tunanin gara a yiwa Safiyya magana”
“zan kirata anjima kad’an muyi magana”
Khamal yace “Ka kwantar da hankalin ka Hashim yanzu dai ku tashi Muje masallaci Lokacin sallar Maghriba tayi”
Ba musu duk suka fita,Nana ta Mike ta haura d’akin ta,Yesmin ma haka.
Suna idar da sallan suka dawo gidan, a dai dai Nan Kiran waya ta shigo wayan Hashim Yana dubawa yaga Asiya ce hannu na Rawa yayi picking.
Yace “Kina lafiya ko? Ina fatan dai Babu abinda ta Miki?”
Magana take kokarin yi Amma ta kasa sai kuka ya kwace mata,ai kuwa hankalin Hashim ya Kara tashi fiye da na baya.
Sai cewa yake “Hello Asiyah kimin magana Mana me ta Miki”
Khamal ne ya fizgi wayar a hannun sa ya kashe wayar.
Hashim binsa kawai da kallo yayi kamar wani soko, khamal yace “Kai farees Kira Safiyya muji me ke faruwa ne Kam”
Ba musu yayi dialling har sau biyu bata d’aga ba, khamal kallon Nana yayi yace ki d’auko mayafin ki kine gidan nan Muji me ke faruwane, hankali na ya tashi ita wanchan tana kuka ita Kuma wannan bata d’aga wayar”
Ba musu ta d’auko ta nufi hanyar fita Faisal yace “Mummy barin kaiki in case in akwai wata matsala akwai na Miji a kusa”
Murmushi tayi Tace “Toh” key d’in motar Hashim ya karb’a, suka fice daga gidan, connecting na laptop d’insa yayi da cameran da ke gun Nana,suna Isa kofar gidan yayi horn Mai gadi ya Bud’e musu,sabida ya ga motar da ta shigo d’azune.