MATAR UBA COMPLETE

MATAR UBA 35

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

CHAPTER 35

Motar ta nufa Kai tsaye a dai dai Lokacin da Nana da Faisal ke kokarin sa ka kwaryar a cikin Booth na motar, kanta tasa tana leken cikin Booth d’in Tace “Nana me kike sawa a Nan,Kuma meyasa Kika fito ba tare da kin min Sallama ba?”

Nana ta tsorata matuka hatta Faisal kasa magana yayi sai kallon kallo sukeyi wa juna.

💦💦💦💦💦💦💦💦

……….. Safiyya dake leke hannu ta d’aura aka Tana fad’in “Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un, Shikenan mun mutu”

Asiyah na ganin Hakan tayi saurin saukowa tana tambayar ta “Safiyya lafiya dai ko? Ko dai Mummy ta gani ne?”

Cike da damuwa Tace “Allah masani gashi dai naga tana leka Booth d’in”

Asiyah tace “Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un”

Faysal gyaran murya yayi yace “Aunty ai na fad’a miki babu jakar nan, naga Lokacin da Yesmin ta d’auka Amma baki yarda ba”

A tsorace daga gane dalilin da yasa faysal yace haka ita ma ta lauyen ce Tace “Eh Wallahi kasan nace maka gidan marayu za a kai shiyasa, Amma Ni bance mata ta d’auka ba.”

Gyaran muryar da Baraka tayi ne ya dawo da hankalin su gare ta, Nana kuwa har Saida hanjin cikin ta suka kad’a murya na rawa tace “Qawata nayi magana da Safiyya ta kawo min kararki amma yanzu sauri nake, zan dawo gobe” ta Maida kallon ga faysal tace “Kai tada motar nan”

Ba musu ya Shiga ya tada motar hannun sa na rawa, Nana rungumar Baraka tayi tace “Zamuyi waya sai da safe”

Bata jira abinda zata ce ba ta shige motar Faysal na ganin haka yayi saurin jaan motar tun Kan ya iso bakin gate ya ke danna horn na motar, da gudu Mai gadi ya Bud’e musu gate d’in don horn d’in yayi matukar tsorata shi.

Baraka kuwa kallon bayan motar ta tsaya yi har suka fice tana tsaye tana kallon gate d’in girgiza Kai tayi Tace “Allah ya kyauta”

Asiyah da Safiyya na ganin Baraka ta nufo parlor da gudu Asiya tayi hantar kitchen, Safiyya Kuma ta koma Kan kushin ta zauna, Baraka na shigowa tace “ke kuma me kike yi anan?”

“Ni….?”

“Eh ke”  

“Umm…. ummm kallo nake yi”

“wani irin kallo kike yi,TV a kashe?”

“ohhh ina nufin Kallo nake son yi Amma na kasa tashi” tana maganar ta tashi ta kunna TV.

“Safiyya!!! ‘dago kanta tayi tace “na’am Mummy”

“Me Nana ta d’auka a gidan Nan?”

Just tayi kirjin ta ta buga Rass,ba ita kad’ai ba har Asiyah dake sauraron su sai da taji  kamar tayi fitsari a wando.

Safiyya tace “Babu fa tunda ta ahigoy d’akina mukayi magana ta fita bata Ce min komai ba”

“Tace min kin Kai Kara ta me Kika ce mata?”

“Ce mata nayi bana son turaren da kike Shaka min,daga Nan ta bani hakuri sai Kuma maganar auren Yesmin”

“Yesmin Aure zata yine?”

” Eh Aure zata yi”

” Dakyau ko wa zata aura ne Oho”

” Abokin Hashim zata aura”

“Kar dai Wanda suka zo d’azu”

Yar karamar dariya tayi tace “A a bashi bane wannan Abokin NASA da suke yawan zuwa Faysal”

“Tabbas yanzun ma ai tare suke,Ni dai hankali na Bai kwanta da Nana ba , akwai abunda take kullawa” Dariya tayi tace “Ina ga Nana ta manta wace ce Baraka idan na gano tana munafurta na ko to Wallahi Wallahi kwanan ta ya Kare a duniya”

Tana Kai Nan ta haura d’akin ta.

A tare Safiyya da Asiyah sukayi ajiyar zuciya, Asiyah da sauri ta haura d’akin ta yayin da Safiyya ta harde kafa tana kallo Wanda kallo take Amma bata fahimtar me ake.

Suna Shiga gidan, khamal, farees Hashim da Yesmin suna Jin karar motar sukayi saurin fita waje, faysal jiki na rawa ya Bud’e booth d’in ta Ciro jakar khamal karb’a yayi yana kokarin Bud’e jakar,Nana murya na rawa Tace “Mu Shiga daga ciki mana Ni Wallahi gani nake kamar zata biyo mu”

Farees yace “Nima dai a tsorace nake”

Khamal yace “To mu Shiga daga ciki”

Suna Shiga a tsakiyar parlor suka ajiye kwaryar sai aikin kallon sa suke ko wannen su day abinda yake aiyanawa a ransa.

Khamal yace “Nifa so nake na kwance kyellen Nan naga abinda tasa a ciki”

Nana Tace “A a Abban Yesmin abin Nan Yana da hatsari fiye da tunanin ka, Dan Allah Kar ka tab’a”

Hashim yace “Nima fa tunanin mu d’aya dashi don Wallahi ina son gani, idan mukayi addu’a ai zamu iya Bud’ewa”

Yesmin Tace “A dai Bari d’in zai fi, Kar a Zo a samu mats…….” Karan buga kofan da akayi ne ya Hana ta karasa maganar da take niyan yi, Shiru sukayi dukkanin su suna kallon kofar, sake buga kofar akayi da karfin gaske hakan yasa duk suka tsorata.

Khamal yace “Waye anan?”

Shiru ba a ce komai ba sai ma Kara buga kofar akayi, bindigar say Yar karama ya d’auko dake karskashin kushin yayi, ya nufi kofar Nana tace “Kar ka Bud’e kofar nan,ina tunanin Baraka ne ta gano babu kwaryar”

Khamal yace “Idan Kuma ba ita bace fa,Bari dai na duba”

A hankali ya karasa kofar ya Bud’e, sai ganine Asiya yayi tare da Safiyya a jiyar zuciya yayi yace “Ashe kune?”

A tare sukace “Eh mune”

“Bismillah ku shigo” suna Shiga ya sa key ya rufe kofar, parlor suka karisa suka zauna Nana tace “Yaya Lafiya dai ko?”

Safiyya tace “Lafiya Lau, mun kasa hakura ne gara a samu a fasa abun Nan kowa ya huta”

“To Masha Allah Kinga gashi Nan ma tunda muka dawo muka ajiye a tsakiyar mu, duk mun kasa tab’awa, yanzun ma ki sake addu’o’in da na fad’a miki d’azu ki d’auka ki fasa”

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button