HAUSA NOVELSURBAJO Complete Hausa Novel

SURBAJO Complete Hausa Novel

*page 1*
Sauri yake ya isa gida sabida yaga bakwai na safiya tayi.
Tunda yaje sallar asuba bedawoba yana masallaci seyanzu
Addua yake Yi azuciyarshi Allah de yasa Aisha taga dama ta
tashi daga baccinnata na qaddara
Tundaga shigarshi falo yafahimci adduarshi bata amsuba
duba da ganin falon dayayi ahargitse kamar filin dambe duk
da de dama sabon falonne zama acikin wannan yanayin
Jikinshi asanyaye yahaura sama inda dakinta yake
Ilai kuwa Tana kwance akan gado tana sharar bacci
Binta yayi da kallo zuciyarshi nakuna sabida tun jiya yashaida
mata zekoma bakin ayki yau jirgin karfe takwas zehau zuwa
phortercot amma shine ko tashi a bacci batayi ba
Inda sabo yasaba da halinta
Juyawa yayi yakoma dakinshi domin yayi wanka sabida yasan
ko toilet dinta yace zeshiga yayi wanka seyakusa amai sabida
karni da zarnin da toilet din yakeyi
Cikin Rabin awa har yagama shiryawa cikin kakinshi na soja
yayi kyau sosai sabida dama kyakkyawanne
Jakarshi yadauko sannan yadauko key din motarshi dakinta
yanufa
haryanzu Tana bacci
Tashinta yayi
Koda tabude ido taganshi tsaki tayi sannan tace Amman
wallahi al-ameen kaidan rainin wayone yanzu fisabilillahi ina
bacci zakazo katasheni
Beyi mamakiba Dan yasaba dajin abinda yafi haka daga
gareta
Nizan wuce yabata amsa
Kudi yaajiyemata kimanin dubu Dari uku a kan bedside drower
kallon kudin tayi awulakance sannan tace namenene wannan
Nacefanene kiyi amfani dashi kafin nadawo sabida inna tafi
wata uku zanyi kafin nadawo
kan ubance inji Aisha tafadi tana sakkowa daga kan gadon
sannan tace wallahi kayi kadan zakayi wata ukunne zaka
mikomin 300k wallahi baze yiwuba tafada yayinda ta zubar da
miyaun daya taru abakinta ajikin bangon dakin
Al-ameen bameson hayaniya bane Dan haka yace se nawa
kike so
500k tabashi amsa bemusaba yadauko yakara mata sannan
yace senadawo pls kiyimin addua
Agayas tabashi amsa gamida komawa takwanta
Fita yayi wani kurtun sojane yazo dasauri yaamshi kayansa
yasa aboot sannan yabudemasa bayan motor yashiga sannan
Shima yazaga mazaunin direba yatada motor sukafita yayinda
motoci biyu na sojoji sukasa motor atsakiya suka nufi Airport
suna zuwa kai tsaye jirgi yashiga Dantuni aka gama shirya
komai
jirginsu yadaga zuwa rivers state
Safe trip alameen
Love you all Maman Yusuf
[3/18, 09:43] Zahra muhd mahmud????: ????????????????
????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*page 2*
Tunda alameen yafita taci gaba da baccinta bata tashiba se
Tara sannan tamike tashiga ???? tayo alwala tayi sallar asuba
????
Tana idarwa kitchen tanufa madara ta kwaba akofi da Milo
tazuba ruwan sanyi tajuya yayi kauri kamar chocolate
Tadauko gorar faro tadawo falo tafarasha
Aduniya babu abinda Aisha ta tsana irin girki Sam batason
yinshi shiyasama bata iyaba
Zamanta keda wuya taji ana ringing bell dasauri taje bakin
kofar taleka Dan ganin waye
Ihu tasa tun kafin ta bude kofar
Tana budewa suka rungume juna ita da bakinnata
kawayentane su biyu
Kai tsaye dakin Al ameen tamusu masauki dan batason su
rainata insukaje nata dakin
Afalonshi suka zauna hira suka shigayi dawadda tadace
dawadda bata daceba suyi gulmar wannan suyi ta waccan
Can kuma tafara basu labarin yadda suke kwanciyar aure da
mijinta kamar yadda suka saba (waiyyazu billah)
Shewa suke kawai suna kara zugata suna fadin eshat baby
baki da wasa
Dariya tayi tabasu labarin yadda suka rabu yau da alameen
Daya daga cikin kawayennatane mesuna Ruky tace wo
mutuniyar kina wuta muna binki da petur ina namu salary din
tunda kin tatsa muma seki sammana koya kikace zuly baby
A wannan gaskiyane wacce aka Kira da zuly tabada amsa
eshat ce tafara mgn haba sisters harse kun roka ay kunwuce
hakan agurina danhaka ku kwantar da hankalinku nifa wlh
kunfiyeminshi so dubu agurina Danni Al ameen dashi da
banza duka daya Suke. Kuma sabida nasan zanbaku naku
kasonne yasa nace seyakaramin kudin Dankaka zanbaku 200k
kuraba
Ihu sukayi suka rungumeta suka hada baki gurin fadin heyyy se
madam Allah de yabiya Hajiya.
*ASALIN LABARIN*
al-ameen jibrin sulaiman shine cikakken sunanshi matashine
Dan shekaru 35 da haihuwa. dane ga rt major general jibril
sulaiman
Mahaifinshi Dan asalin garin kanone awata anguwa daake Kira
lungun gabari canne asalin tushensu amma sanadin aykin soja
yasa yadawo kaduna da zama a malali yake da zama alayin
sultan road
Hamshakin mekudine ajihar kaduna domin ajerin masu kudi
nagarin in akace daya to tabbas shine nabiyu
Matarshi daya mesuna Hajiya binta suna kiranta da umma
yaransu hudu. Kabeer shine nafari sannan alameen se
munawwara da autarsu amal
gidan alhaji jibrin gidane gidan tarbiyya Dan yaransu gaba
daya babu mehalin banza
Mahaifiyarsu nabasu tarbiyya Dede gwargwado kudi besa tayi
watsi da tarbiyyar yarantaba
tunbayan da mahaifinsu yayi rt yakoma fannin business
nakasa da kasa yanada kamfanoni a fadin jahohin nigeria
mutumne shi metsoron Allah bashida buri dawuce a yaransa
yasamu megadonsa a gidan soja kullum adduarshi kenan inda
Allah yataimakeshi ya bashi alameen
tunda alameen yafara mallakar hankalin kanshi yaji yana
shaawar zuwa aykin soja
Koda yatuntubi mahaifinsa da batun bakaramin farinciki yayiba
baayi satiba yasamomishi aykin dayake akwai hanya
shiko kabeer accounting yakaranta yanzu haka yana ayki a
cbn yanada mata daya Da yaronshi guda daya mesuna
Waleed kasancewar sunan abbansu yaci
munauwara kuwa yanzu Tana js3 yayinda auta amal ke
primary 4
tunda alameen yafara aykin soja gabadaya hankalinshi
yamaidashi abangaren aykinshi kullum burinshi yataimaki
kasarsa
lokacin a kaduna yafara aykin kamin ayi posting dinshi zuwa
Abuja
kamar kullum yauma yataso daga ayki da misalin karfe
shadaya nadare a nda yake aykin dan haka ta Badarawa
yabiyo dan zefi mishi saukin isa gida
yawuto bustop kadan Dede galadima road jikin katangar
gidan Baba boss yaganta tsugune Tana kuka ga gurin yayi
shuru babu mutane har yawuce seyaji yanason sanin meyasa
ta kuka kuma take zaune abakin titi
ribas yayi yadawo gurinta layin galadima road din yashiiga
Dede gidan kallon kwallo yayi parking sannan yafito yatako da
kafarsa zuwa inda take
sallama yamata agigice tadago kanta tana kallonshi kara
matsawa kusada ita yayi yace yanmata meyafaru ne kika
zauna anan kina kuka
ganin uniform din soja ajikinshi ne yasa tace aranta bari
infada masa maybe yataimakamin
cikin kuka tace wlh mamanace tawuni yau Tana wankau har
zuwa dare sannan tasamu kudin dazamuci abinci dashi
tunsafen bamuci abinciba shine yanzu ta aykoni insiyo garin
rogon dazamu sha bansan yaakayiba kudin suka fadi shine
nake kuka dannasan yau seta kasheni tafadi Tana sake
rushewa da kuka
yaisa haka alameen yafadi yana kallonta balaifi tanada kyau
dede gwargwado kuma yarinyace dabazata wuce 18years ba
yasunanki yatambayeta
sunana AISHA tabashi amsa
inane gidannaku nunamasa gidan tayi da hannunta danba nisa
taso muje yace da ita
zaromishi ido tayi tace wlh najemata ba sakonnan yankani
zatayi Dan Allah kawuce ka kyaleni anan
bazata yankakiba nizan biyata kudin
Amman Anshi Wannan Kijewancan shagon kisiyomuku kayan
tea 2k yabata godiya tashiga yimasa kamar zatayi sujada
dagudu ta tsallaka titin tasiyo kayan tean dawowa tayi tace
nasiyo
gaba tayi yana binta abaya harsuka isa kofar gidan yace shiga
kiyimin Sallama da mamannaki wucewa tayi tana murmushi
Dan ita yau jitake kamar sallah saboda zasu sha tea Wanda
rabonta datashashi tun kafin babanta yarasu yanzu ko kimanin
shekararsa hudu da rasuwa ????
mamanta Data fito taga sojane ke sallama da ita cikintane ya
murda dakyar suka gaisa sannan yamata bayanin abinda
Aisha tafadamasa
yakara dabata hakuri sannan yadauko kudi a aljihunsa
kimanin50k yabata yace tayi hkr duk sanda yasamu lokaci
zedunga lekosu godiya Mama takeyi harda hawaye
sallama yamata yakarasa gurin motarshi yashiga yanufi gida
*wacece Aisha*
love you all Maman Yusuf
[3/18, 09:47] Zahra muhd mahmud????: ????????????????
????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*Page 3*
Aisha Bello Musa shine asalin sunanta haifaffiyar garin
kadunace acikin anguwar Badarawa
Sunan mahaifinta malam Bello mahaifiyarta kuma sunanta
maimuna suna kiranta da inna
Su ukune agurin iyayensu Aisha itace tafarko se kannanta
guda biyu zaituna da Umar
Shekarar Aisha 18 mahaifinsu yarasu tun Tana js1
Mahaifiyar itace taci gaba da kulawa dasu har zuwa yanzu da
Aisha ke ss2 awata makarantar gwamnati dake anguwarsu
Kannanta ma duk government schools sukeyi
Rayuwace suke mecike da kunci Dan abunda zasuci yafi
karfinsu se inna tayi wankau suke samu suci abinci so daya
arana
Aisha yarinyace me dogon buri arayuwarta kuma bata da
godiyar Allah ko kadan
Tahadu dasu Ruky da zuly ne amakarantarsu inda halinsu
yazo daya suka kulla kawance
Basuda ayki dayawuce suyi gulmar kawayensu har gida ansha
biyo Aisha akan tayi gulmar wata akureta
Mahaifiyarta macece me sakaci da tarbiyar yaranta tun bayan
mutuwar mijinta Wanda hakan yasamu asaline asanadin zafin
talaucin dasuke fama dashi
kwasam segashi Allah yaturomusu alameen
Tunda alameen yatafi besake zuwa gidanba hasalima baya
biyowa ta unguwarsu
Aisha tafi inna Damuwa darashin zuwannashi sabida tunda
tadora ido akanshi taji takamu dasonshi
Har bakin titin anguwarsu take zuwa tatsaya kozata ganshi
babban abinda yasa takesonshi mijine na nunawa kawa itako
bata da buri dayawuce ace taburge kawayenta
Yau jummaa dawuri alameen yataso daga ayki ta Badarawa
yabiyo har yawuce layin Su Aisha se yatuno da ita danshi
harga Allah yamanta dasu tun bayan barinshi gidansu kwana
yayi yashiga layin Dede kofar gidan yatsaya
Aisha ce atsaye azauren gidan Kai ba dankwali takira me
agwaliba Tana siya tun agurin tafarasha fadi take Kai malam
wannan da tsami
Mamakine yacika alameen ganinta dayayi ahaka gashi tasa
wata ???? Data bayyana halittar kirjinta Dan har ta saman rigar
ana ganinsu
Hon yamata dasauri takai dubanta inda taji hon din dagudu
takarasa fitowa tanufeshi dasauri alameen yadauke idonshi
daga kallonta sabida yadda take gudun yasa halittar kirjinta
yin wani juyi na musamnam sabida Allah yawadata ta dasu
Karasowa tayi jikin motor Tana dariya
Sannu dazuwa soja sunan data kirashi dashi kenan
daurewa yayi yayi murmushi yace yauwa kanwata
Kashigo mana daga ciki tabashi amsa
Fitowa yayi suka shiga zauren gidan gaisheshi tayi
Yaamsa sannan yace
lalle bakyason shiri Dani tunda bakya muamala da dankwali
kunyace takamata dagudu tajuya Tashiga gida tasako hijab
sannan tafadawa inna sojan rannan yazo murnace takama
inna dasauri tace uwaki Aisha shine kika barshi awaje yisauri
kije ki kirashi yashigo dasauri tadawo gurinshi tamishi iso
zuwa cikin gidan
Kan tabarmar da inna tashimfidamasa yazauna gaisheta yayi
cike da girmamawa sannan yasanar dasu sunanshi dana
mahaifinshi
Inna da Aisha ne suka hada baki gurin cewa Alhaji jibrin
sulaiman de Wanda mukasani
mamaki tambayar tabashi sabida arude suka masa ita
eh shi yabasu amsa
Ajiyar zuciya sukayi dukansu daganan inna tabashi tarihinsu
yatausayamusu sosai inda daga karshe yayi musu alkawarin
kulawa dasu
tundaga wannan lokaci alameen yamaida gidan inna kamar
gidansu inyazo sallama kawai yake yashiga sosai yake musu
hidima dantuni yasauyawa su Aisha makaranta ita da
kannenta
Yayinda ita kuma Aisha kullum sonshi Karuwa yake azuciyarta
zuwa yanzu har waya yasemata iPhone6+ burin aisha yafara
cika dantuni tasauya tayi kyau namusammam ga sutura Tana
shiga ta alfarma bata da wata damuwa data wuce ta auri
alameen
insuna waya so tari tasha yunkurin sanardashi halin datake
ciki seta kasa
yau alameen ne yakawomusu ziyara bayan sungaisa da Inna ta
tashi tafice dama zata barkane Aisha dawowa tayi kusa dashi
tazauna tace Yaya alameen kamar yadda take kiranshi juyowa
yayi Yana kallonta ganin yadda tanatsune yasa yagane mgnr
dazatayi me muhimmaci ce sabida kwatakwata Aisha bata da
natsuwa
yaakayine kanwata yatambaya
kunyace tarufeta amna bata dazabi dayawuce tasanar dashi
yaya Don Allah zaka iya aurena? Jin tambayar yayi kamar
saukar aradu danshi Sam bayason Aisha amatsayin wacce ze
Aura danyafison mace me natsuwa
AA yabata amsa
kuka tasamishi tana Don Allah kataimaka kaaureni wlh tunda
nafara ganinka naji inasonka katausayamin sonka zeiya
kasheni wlh tafadi Tana ruko kafarshi
dasauri yamike yace amma Aisha bakida hankaliko taya zan
iya auranki Bari kiji infadamiki bakya cikin jerin macen
danakeson in Aura Danhaka bazan boyemikiba wlh banasonki
kiyi hkr kinemi wani yana gama fadin hakan yajuya yafice daga
gidan ranshi abace
innace tashigo taga Aisha kwance akasa dasauri takarasa
kusa da ita ga mamakinta farin kumfa tagani yana fitowa
daga bakinta agigice tadagota ina babu numfashi ajiyeta tayi
tafita tsakar layin Tana neman taimako napep akasamo akasa
Aishan aciki inna Tashiga suka nufi asibiti
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
zahra Muhammad mahmud
*page 4*
Koda isarsu asibitin likitocine suka rufu akanta seda suka
share awanni biyu sanna suka fito
Inna dasauri ta sha gaban daya fara cikinsu
Likita ya jikinnata
Dasauki yabata amsa
Sannan yace kibiyoni office yajuya yanufi office dinshi inna
nabinshi abaya
Bayan sunzaunane likitan yace mama meyasami yarinyarki
hartake yunkurin kashe kanta tahanyar shan fiyafiya
Hankalin inna ne yatashi dajin abinda likita yace
Dakyar tabashi amsa da wlh bansaniba nide nasan bata
dawata damuwa danko yauma lfy nafita nabarta dawowa nayi
naganta a yadda nakawomuku ita
Murmushi doctor din yayi sannan yace kituntubeta tabbas
akwai abinda yake damunta zaki iya zuwa kiganta dan tajima
dafarkOwa godiya Inna tayiwa doctor din sannan tanufi dakin
da Aishan take
Tana shiga suka hada ido daita dasauri takarasa bakin gadon
tarukota
Kuka Aisha keyi tanacewa Inna nashiga uku alameen yace
baya sona wlh inna įnasonshi zan iya rasa raina akansa
kitaimakeni Inna
Dankari itace kalmar data fito abakin Inna ajiyar zuciya tayi
sannan tace Aisha inbanda rigima irin taki inake ina Aminu
yafi karfinki nesa bakusaba shine Dan shirme harda yunkurin
kashe kanki sabida shi to wlh inbacci kike kifarka Aminu baze
sokiba sabida ke ba tsarar auransabace
Kuka tasawa Inna kamar zata mutu hankalin Inna tash yayi
rarrashinta tashigayi dakyar tayi shuru bacci yayi awon gaba
da ita
Yau Monday Alameen ne yataso daga ayki gidansu Aisha
yanufa sabida tunda yajita shuru kwana biyu bata dameshi
dawayaba yasan tahakura dason datake mishi
Shiga gidan yayi kamar kullum kannen Aishan ne kawai agidan
suma daalamun fita zasuyi ganinshi yasa suka nufeshi
gaisheshi sukayi sannan yatambayesu inasu innanfa
Suna asibiti suka bashi amsa
meyafaru sukaje asibiti waye ba Lafiya
Aunty Aishane tasha fiyafiya tun shekaranjiya shine aka
kwantardasu
innalillahi wainna ilahirrajiun itace kalmar da alameen yake
nanatawa aranshi ko shakka babu yasan shine silar shan
fiyafiyanta
Arude yatambayesu wanne asibitine
amsa suka bashi dacewa suma can zasu Kai abinci juyawa
yayi yace to kutaho mutafi
Sun isa asibitin lokacin Aishan na bacci
Inna seda tayi mamakin ganinshi
Gaisheta yayi gami da tambayar me jiki
amsawa tayi cikin sakin fuska inda takara dabashi hkr abisa
katobarar da Aishan tayimasa
Kunyace takamashi matuka inda yagaza cewa komai
Muryar Aishan ce takatsesu dacewa yaya kazo dubanine
dasauri yanufi gurinta yayinda Inna taja kannen aishan suka
fice daga dakin
Gefen Gadon yazauna yakamo hannunta yarike yana kallonta
tausayintane yakamashi ganin wai duk akanshi takeson barin
duniya
Why Aisha? Itace yafurta
Kuka tasamishi tana Dan Allah Yaya ka aureni ko bakasona
wlh ni inasonka inka gujeni bansan yadda zanyiba tafadi cikin
kuka wanda yakarya zuciyarsa Dan alameen mutumne
metausayi
rarrashinta yashigayi da kalamai masu sanyi
Yace kiyi shuru kinji naamice zan aureki amma sekin yimin
alkawarin zaki cigaba dasona kobayan muñyi aure Kai tadaga
sannan tace har inmutu inasonka yaya nagode Da alfarmar
dakamin
hira suka sha tasoyayya wacce azahirin gaskiya alameen
tausayinta kawai yakeyi basoba kamar yadda tadauka se
shabiyun dare yamusu sallama yawuce da kannanta yaajiyesu
gida shima yawuce nasu Gidan da burin gobe zema
mahaifinsa mgn akan zeyi aure danso yake cikin wata guda
ayi auran dangani yake kamar Zatasake shan fiyafiyar.
maman yusuf
[3/18, 11:11] Zahra muhd mahmud????: ????????????????
????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*page 5*
Koda alameen yama mahaifinsa mgn akan yanason ya auri
Aisha be hanashiba sabida dama kullum adduarshi Allah yaba
aminun matar daze Aura tagari
Mahaifiyarshima fatan alkahairi tamishi jin cewa Aishan bayar
kowabace bedamesuba sude burinsu Allah yabasu zaman lfy
Tuni aka sallamo Aishan daga asibiti aka shiga hidimar biki
sosai mahaifin alameen yasaki kudi ahidimar bikin
Kowa yaga hotonsu da alameen acikin kawayenta mamakin
inda tasamoshi sukeyi itako Aisha abunnema yasamu se jijji
dakai take ita adole tawucema saa
Inna tagyara Aisha sosai inda aka kawo lefenta akwati goma
shabiyu cike da kaya na alfarma harda key din mota
Wayyo jamaa kuzo kuga murna gurin Aisha
Andaura aure akan sadakin naira dubu dari inda akabada
dukiyar aure naira miliyan biyu
Jamaa Sun sami damar Halattar daurin aure aciki harda
megirma gwamnan jahar kaduna inda shine yazama wakilin
ango yaamsama alameen auren Aisha ahannun waliyyinta
malam Adamu kani ga mahaifinta
bayan daurin aurene akayi walima da da misalin karfe biyar
kuma sukaje dinner agaskiya shaanin bikin yakayatar anci
ansha Masha Allah
Se misalin karfe takwas motocin daukar Amarya sukazo
Jamaa sukai tashiga da yan biki da yan gayyar sodi Dan aje
aga mazaunin Amarya
Aisha dakyar aka rabata da inna bayan tamata fada sosai
Tana kuka aka shige da ita mota
Ankai Aishan gidan iyayensa tukun
Sosai suka tarbesu hannu biyu cikin mutunci dazaa tafi da ita
dubu dari Momy taba Amarya
Sannan akawuce da ita gidanta dake rabah road babu nisa
sosai dagindan iyayennasa
gidan yatsaru matuka sabida mahaifin alameen ne yayi komai
yace Aishan base tazo dakomaiba
Yan rakiyar Amarya sunwatse inda yaraage daga Amarya se
aminanta Ruky da zuly
Abokan angone suka rakoshi su biyar bayan raha dasukayi
sukayimusu adduar zaman Lfy da, zuria dayyiba
sannan suka sallami su ruky da 50k sukadaukesu suka
maidasu gida
umartar Aisha yayi dataje tayi alwala tazo suyi salla bamusu
taje Tayo shidama tuni yayi
jansu sallah yayi rakaa biyu tanuna godiyarsu ga Allah
bayan sun idarne yake mata tambayoyi game da addininta
Yayi matukar mamaki daya tambayeta farillan alwala guda
nawane tace guda uku inda farillan sallah suka zama asirin da
bakwai ????
Hankalinshine yatashi yashiga tambayar kanshi wacce irin
Uwa nazabawa yaranane
Duk da yana cikin damuwa bebari taganeba inda yabarwa
ranshi nanda wata biyu ze sata a islamiyya tamatan aure Dan
baze zauna da jahilaba
Kajin daya shigo dasu yajawo gabansu inda yatashi dakanshi
yadauko musu plate da kofuna
Aisha bazancan kunya zagewa tayi taci kajin sosai Wanda shi
alameen abin kunya yabashi daga karshe yaso sashi dariya
dangama Amarya Aisha hardasu tauna kashi hakade suka
Gama ci sukaje sukayo brush
Suna fitowa Aisha gado tanufa alameen ne yakwashe
kwanukan yakai kitchen
Dakinshi yaje yasauya kaya zuwa na bacci sannan yakoma
dakinta tananan kamar yadda yabarta
Cewa yayi bazaki sauna kayan jikin kibane kika kwanta dasu
wata Mika tayi gami da wata gyatsa mekarfi sannan tasakko
akan gadon tanufi Wadrop Tana fadin wash wlh nagaji
Doguwar rigar bacci tadauko tasa duk yana kallonta sannan
tazo tasake hayewa gado kayan data cire tabarsu akasa shi
yakwashe mata yaadana shima hawa gadon Yayi bayan
yakashe wuta yajamusu bargo. Kwanciyarshi keda wuya yaji
Aisha tamirgino jikinshi inda tashiga bankaro kirjinta suna
gogarshi
hankalinshine yafara tashi sabida betaba jinn hakanba
nande cikin dabara har tagama daga mishi hankali
wayyo abunka da sabon shiga yasha wuya kamin yasan hanyar
daakebi shima seda taimakon Aisha
se alokacin tayi danasanin daukar shawarar su zuly dansune
sukace tayimishi abinda tayi da farko
kuka tasamishi Tana rokonshi Allah annabi akan yayi hkr
yakyaleta
ina alameen yayi nisa bayajin Kira duka dayakushi cizo babu
wanda batamishiba amma abanza araina nace dama taya zeji
bareshi dayake soja
besauraramataba se gefin asuba
kukako tayishi har muryarta ta dashe idanuwa sunkumbura
baabinda yafi damunta irin breast dinta dasuke Mata zafi
sabida sunji maza uwa uba kuma kasanta
shiyafara yin wankan sannan yahadamata nata ruwan dawowa
yayi yabude bargon dasauri Aisha tarufe idonta Dan ba kaya
ajikinta murmushi yayi yadaukota Kamar jaririya yakaita toilet
jinta aruwan zafine yasata kwalla masa kara dan wani
radadine taji yanashigarta
lallabata yashigayi har yasamu tabari yamata wankan
yanadota atawul yadawo da ita dakin
itako har yanzu idonta arufe yake azuciyarta ko se tsinema su
Ruky takeyi
agurin bacci yadauketa
shikuma kayansa yasauya yadauro alwala yatada sallah yana
godewa Allah dayasa rawar kai darashin natsuwar Aisha besa
ta zubar da mutuncinta
inda akarshe yaroki Allah dayasa sonta azuciyarshi dansuji
dadin zama tare
be tashi agunba sedaeyayi sallar asuba sannan itama yatsheta
tayi kuka tasamishi akan ita bazata iya tafiyaba daukarta yayi
yakaita toilet din tayi alwala yadaukota yadawo da ita
doguwar riga yadaukomata da hijab tayi sallar azaune
bayan ta idar daukarta yayi yanufi Gado da ita kuka tasamishi
tana bashi hkr dan tazaci zesake nemantane lakashemata
hanci yayi yana murmushi yace matsoraciya babu abinda
zanmiki bacci zamuyi
kwanciya sukayi yanata samata albarka abisa Kawobudurcinta
datayi gidan mijinta ahaka har bacci yadaukesu yana rungume
da ita
maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*page 7*
Basu tambayeshi meyasa baze tafi da Aishan ba sabida zuwa
yanzu sungama fahimtar dannasu beyi dacen mataba
Tunda yatafi kullum seya kirata awaya intayi raayi tadauka
inbatayiba kuwa inze kira so dari bazata dagaba
Haka inyasamu Hutu yazo gida sotari hutun baya karewa yake
komawa sabida balain aisha
Rayuwa tayiwa alameen zafi awaje mutane yisuke kamar su
goyashi sabida kulawa amma cikin gidanshi masaima yafishi
daraja wannan wacce irin rayuwace gashide yanada mata
amma bata da amfani agareshi Allah kakawomin agaji.
*cigaban labari*
Haka Aisha taci gaba da musgunawa alameen kullum Sabida
shimutumne me hkr kuma dama duk soja seka sameshi da
sanyi akan mace
Zuwa yanzu hakurin shi yasoma karewa dama dagamata kafa
yake tunda yakoma ayki besake dawowaba seda yakwashe
shekara guda sannan yadawo
Yauma bata gidan kuma tasan zedawo tatafi yawonta tunda
yake daita betaba jin bacin rai irinnayauba kuma yasha
alwashin yau seyayi maganinta
Yanazaune afalo tadawo kokallo be ishetaba tawuce dakinta.
Seda tajima dashiga dakin sannan yamike yabi bayanta
yanashiga kamar kullum yauma wayar take da kawayenta
Daga gidan ubanwa kike alameen yawurgamata tambayar
Seda tambayar tafirgitata amma dayake Kai na hayaki setace
daga gidan ubanka nake ubana
wani wawan Mari yakifeta Dashi seda tafado daga gadon
Belt din jikinshi yacire yashiga dukanta takoina ran yanmaza
yabaci haba ay yayi kokari tsawon shekara biyar yana hakuri
Aisha tun Tana ihu harseda ihunma yagagara seda yatabbatar
da tayi laushi dankanshi yakyaleta
Sannan yadakamata tsawa Tana kwance akasa jikinta duk jini
sabida tadoku ahannun soja Dan dukan kato yamata
yaci gaba dacewa cikin fushi anfadamiki tsoron ki nakeji ne
dazaki dunga yimin abinda kika dama ina kyaleki wallahi
Aisha nayi danasanin auranki danasani nabarki kinsake shan
fiya fiyar ki mutu wlh daan rage mugun irin
Damutuncina agari amma agidana bandashi to wlh kinyi
kadan dama nasamiki idone banza kazamiya kuma wlh kitashi
yanzu ki gyaramin gida awa guda nabaki inba hakaba nalahira
seyafiki jin dadi yafadi yayin dayayi kwallo da ita yafice daga
dakin
Jikinta narawa tamike tafara aykin dukda ciwon dake jikinta
besa tabar aykinba tanayi jiri nadibarta Dan yanzu wani mugun
tsoronshi takeyi hhhhhh nace su aee anji maza
kafin lokacin yacika tuni gidan yayi clear dattinko data kwashe
seda yacika katon dustbin
gidan se kamshi yakeyi komai yayi normal araina nace oh
Aisha tazama zuma seda wuta
alameen tunda yafito daga dakinta garden din gidan yashiga
seda yatabbatar lokacin daya dibamata yacika sannan yashiga
cikin gidan mamakine yakamashi ganin yadda gidan lokaci
kadan yasauya sewani kamshi yakeyi dakinshi yaleka komai
normal harda sabon bedsheet tashimfidamasa har cikin ranshi
yaji dadin ganin gidan ahaka sabida rabonshi daganin sa
hakan tunranar daaka kawota gidan
dakinta yanufa yana shiga yaga Tana morping a tsugunne tana
kuka tausayintane yakamashi amma yayi saurin kawar dashi
sabida sanadin tausayinne yajefa kanshi acikin halin dayake
yanzu
Tsawa yadakamata sannan yace Dan rashin mutunci a
tsugunne kike moping din dalla malama tashi
Jikinta se Bari yake tace Dan Allah Yaya kayi hkr bazan sakeba
Mamakine yakama alameen sabida rabonshi dajin irin wannan
kalaman abakinta tun sati biyu da auransu
dalla yimin shuru sumumu kasau kawai bacemin dagani
Jikunta narawa tadauki ruwan moping din taje toilet tazubar
tawanke toilet din fitowa tayi tana rabe rabe inda alameen
yakorata taje tayi wanka da gudu tashige bayin Dan tadauka
yabiyota abayane
so uku Tana fitowa bayan tayi wankan yana maida ita tasake
wani wai bata fitaba hakama brush seda makilin oral b yakusa
karewa dan seda bakinta yasoma jini sabida brush sannan
yakyaleta kantama adaren tatsefeshi tawanke shi tas haka ma
shaving duka seda tayi
ita dakanta taji dadin kanta Dan har wata iskace take ratsata
nace oh ji yiwa Kai mugunta
rigar vacci kawai tazira tahaye gado tuni bacci yayi gaba da
ita dayake alameen yabar dakin
dawowa yayi yaga Tana bacci duka yakaimata abaya afirgice
tafarka tadiro agadon
ubanwa yabaki damar bacci bayan baki sallameniba hkr
tashiga bashi Tana hawaye alameen bakunya yakamota
yashiga sarrafata bata hanashiba Dan Tana gudun shan duka
yau cikin nishadi yabiya bukatarsa inda besauraramataba se
asuba nace Kai alameen batausayi
wanka yayi yafice masallaci Tana kuka tamike tashiga toilet
tayi wankan tazo tayi sallah sabida kafin yatafi masallaci seda
yamata worning akan ta tabvatar kamin yadawo tahada break
fast sannan tayi gyaran gida tayi wanka tayi kwalliya idan
yadawo yaga batayi daya acikiba zatasani
shiyasa tamike tafarayi jiri nadaukarta sabida rashin bacci ga
jikinta dake mata ciwo ahaka tadaure tayi komai kamar yadda
yabukata har girkinma tayi duk da ba wani dadi yayiba amma
yafi babu
dayadawo abun yaburgeshi har wani nishadi yakeji amma idan
yatuno tilastata yayi seyaji duk ranshi yabaci
maman Yusuf
[3/18, 11:27] Zahra muhd mahmud????: ????????????????
????????????????????
*BALLAGAZA*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*pls yanuwa Dan Allah ina barar adduarku yaron Aunty nane
jariri bashida Lfy Dan Allah kusashi cikin adduarku a sallah
????????????????????????*
*page 8*
Tundaga wannan rana Aisha take tsoron Alameen Dan ko fita
bata sakeyiba sosai take jin maganarshi
Bangaren rayuwar aurema ko tanaso ko bataso inde shi
yanaso anwuce gurin
Yau alameen ze koma bakin ayki inda yakafamata dokoki
yakuma ce muddun ta karya daya takuka da kanta
Har airport Tamushi rakiya kamar gaske
Ay tundaga airport dinnan bata wuce gidaba kaitsaye gidansu
Ruky tasauka kamar fadi Tana zama Sega zuly tazo nan suka
shiga hirar yaushe gamo daga karshe Aisha tabasu labarin
abinda alameen yamata
Dariya suka samata harda hawaye
Zuly tace dankari amma wlh Aisha kinbada mata yanzu
tsayawa kikayi yadakeki tabdi ayko inde baki dauki matakiba
wlh kinzama filin training dinshi
Ruky taamsa ay yana cewa zedokeki gabansa zaki rike iya
karfinki inyaji zemutu wlh zedena ko ki dunga ajiye wuka
agefenki dazaran yamiki wani wargi kinuna zaki masa kachiya
wlh denawa zeyi amma taya zaki sakarmasa jiki yadunga labta
wlh kin rikito
nande sukasata agaba suna huremata kunne basu bartaba
seda suka tabbatar shawararsu taamsu agurinta Dan har
haushin kanta tadunga ji amma bata baciba tasha alwashin
inyadawo zegane kurensa.
*Photacot*
Alameen ne zaune a office dinshi shida amininshi Usman fira
suke gameda rayuwar duniya ananne alameen yashaida mishi
labarinshi da Aisha harda dukan dayamata
Major Usman ne yace haba abokina meyakaika dukanta
gaskiya baka kyautaba aysu mata insuna iskanci irin wannan
akwai dukan daake musu yasasu haukacema gaba daya
dasauri alameen yamatso yace Kai haba abokina
wlh yabashi amsa
to wanne irine shi dukan alameen yabukata
ka kara aure shine mafita
ajiyar zuciya yayi sannan yace major kafi kowa sanin raayin
mace daya ne Dani arayuwata so gashi nakuma Aura
bandaceba baka tunanin yin wani auran ze Kara daga
hankalinane
haba abokina wancan auran dakayi aurene bana soyayyaba
maana aurene natausayi so yanzu inzaka sake wani wacce
kakeso takesonka zaka Aura wlh inde kadace sekayimin
godiyar shawarar Dana baka amma taya zaka tsaya mace
tana gasaka bakadauki matakiba aywasu matan zumane seda
wuta
dariya sukayi gabadaya suka tafa inda daga karshe alameen
yace zeyi nazari akan zancan Usman
haka kwanaki sukai ta tafiya har Allah yadawo da alameen
gida koda yazo yaga Aisha tayi fatali da dokokinshi be
kulataba
anata bangaren tayi shirin ko ta kwana Amman ga mamakinta
setaga ko kallo bata isheshiba
hakan bemata dadiba taso yakulata tace zata masa kaciya
shiko bawan Allah bata ita yakeyiba
.
shurun dayamatane yasa tasake Mike kafa ita adole taci dubu
se Ceto kawayenta nakara zugata
*RUGAR YALLI*
wata rugace ta fulani agarin makarfi ta jahar kaduna jamaa
dayawa basu San rugarba sabida Tana cikin dajine sosai ko
yan garin se tsofaffin zamane sukasan da rugar sabida rugar
gida ukune kawai acikinta gidan alhaji babba dagidan alhaji
jume se gidan ardon rugar wato gidan alhaji yalli
duka gidajen Manyan gidajene sabida kowa dashi da zuriarshi
yake zaune agurin
zahrau wacce akafi saninta da surbajo “ya ce agurin alhaji
yalli wato ardon garin Wanda aynihin sunanshi muhammadu
Mahmuda asalinsu yangarin gwangolane dayake su fulanin
tashine shine suka dawo wannan guri dazama
matanshi biyu sumaye wacce itace uwargida se amina wacce
itace Amarya
yaranshi takwas inda sumaye takeda guda bakwai duka
Mazda ita Kumar amina takeda guda daya wato zahrau
amina asalinta yar garin kadunace awata anguwa mesuna
tudun wada layin kosai anan aka haifeta kaddarar aurece
takaita ga auren ardo dakuma rabo danginta Sam basason
aurannata dashi kasancewarta marainiya shiyasa tunda
taaureshi danginta suka tsameta acikinsu
bayan haihuwar zahraune da shekara biyar Allah yama amina
rasuwa ardo yayi kuka kamr ranshi zefita
yanuwantama dasuka sami labarin rasuwarta sunyi kukan
rashinta dasuka zo gaisuwa suka bukaci ardo yabasu zahrau
sutafi da ita fafur ardo yahanasu yace meze dunga kallo
amatsayin amina idan yabasu ita
ransu besoba amma yafisu iko da ita haka suka tafi suna
danasanin watsi da aminan dasukayi
Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*page 9*
Zahrau ta taso cikin tsana da tsangwama irinna kishiyar Uwa
Sumaye ganamata azaba takeyi tun tana karama aka fara sata
zuwa kiwo zuwa yanzu taiya sosai dama ga aladar gidan
insun fita kiwo dare yamusu to acan suke kwana ingari
yawaye su cigaba da kiwon sede laasar nayi zasu komo gida
Shiyasa inzasu tafi suke tafiya da kanzo Wanda aka daka da
gishiri da yaji da man shanu da tukunya sabida koda dare
yamusu acan sugirka suci
Kokadan zahrau batajin dadin zaman gidan inde mahaifinta
bayanan sabida inyananan bame dukanta sosai yake jida ita
kuma gata sunan mahaifiyarshi yasamata shiyasa ake kiranta
da surbajo
Yauma kamar kullum surbajo tafita kiwo ita da ya’u yayantane
Suna zuwa rafi suka hadu da arera yar gidan alhaji jume
itama tafito kiwon itada yaynta saidu
Suna ganin juna suka rungume juna ita da areran sabida
murnar ganin juna guri suka samu suka zauna suna hira
surbajo ayko inada wani albishir dazan miki inji arera
dagaske wanne irin albishir ne wannan kekuwa arera inji
surbajo
Aradu dama jae ne dan gidan alhaji Babba jiya yazo gurin
yayana zubairu danaganshi muka gaisa shine yace wai ince
miki yana gaisheki
ihu surbajo tasa sannan tarungume arera tace
kai madallah aradun Allah naji dadin wannan albishir
Aydama nasan zakiji dadin shiyasa nafadamiki
Ranar agurin kiwo wuni surbajo tayi tanajin dadi Dan harga
Allah sakon gaisuwar da jae ya ayko mata ta sanyaya
zuciyarta
*JA’E*
dane agurin alhaji babbah Dan kimanin shekara ashirin
kyakkyawane naajin farko dan duk mazan garin bawanda
yakaishi kyau shiyasa kowacce mace take kaunarsa gashida
da kyauta dan inde yace yanasonki to ko zakici soyayyar
gyada da burodi kimore gashi ranar kasuwa kullin kosanki da
yar yau na musammanne
Shiyasa kowacce mace burinta yace yana sonta
to surbajo ma Tana cikin jerin masu sonnasa
yau akwai biki agidan alhaji babba inda yake aurar da yarsa
Safiyya yar kimanin shekaru goma shadaya
Su surbajo sune kawayen Amarya sabida suma shekarunsu
sha dayanne
ga alada ta Fulani akwai wani wasa dasukeyi bayan shadi inda
maza da yanmatane zasu taru suyi layi layin maza dabam
haka namatama zasu fuskanci juna suna wakar
Wayyohoro hirobe gadaibe jadu jande wayyo horo hirobe
gadaibe jadu jande. Seme kalangu yasa kida to matanne daya
bayan daya zasu dunga fitowa su tsaya a tsakiyar filin se
tagama kallon samarin Wanda yamata acikinsu shi zataje ta
yalo da kafarta yin hakan nanufin tanason yafito suyi rawa
kenan kuma yawanci daga wannan rawarne soyayya take
shiga tsakani hartakai ga aure
to wannan bikinma anshirya irin wannan wasan
Danhaka surbajo taruga kowa zuwa gurin sabida tanada gaba
sabida basa son arugasu zaban jae sabida a alada irinta
wasan duk Wanda kika zaba fita zakuyi tsakiyar filin kuchase
sosai to inkuma yaji yanasonki zece kufita afili kusami guri
kuyi mgn
fili yacika bamazanba ba yanmatanba
su kuma mazan kowa burinshi Allah yasa surbajo tazabe shi
Dan itama duk yanmatan garin tafi kowa kyau
anfara waka inda surbajo ce farkon fitowa tashigo filin tafara
rawar Fulani irin wacce ake daga kafa dayannan ana saukewa
sannan takarewa mazan kallo can idonta yasauka akan jae
yanamata murmushi ayko batayi kasa agwuiwaba ta yaloshi
ihu yayi sannan yashigo filin da kwambe suka fara rawa tare
inda me kalangu yadunga wasasu dacewa kyakkyawa se
kyakkyawa
bayan sungamane jae yacewa surbajo Sudan fita afilin ay
sauran yanmatan naganin sunfita kowacce haushi yakamata
inda sukasha alwashin se summa surbajo dukan tsiya akan
yaloshin datayi
hakade yanmata da samarin suka ci gaba dawasansu har suka
gama
itako surbajo tunda jae yace sukebe farinciki yabi yacikata
dantasan yau tafi kowa saa a duniya
koda suka keben juya mishi baya tayi alamun jin kunya
shimade kunyar yakeji Danhaka shima bayan yajuyamata
sannan yafara mgn
wato surbajo nadade inashonki amma nakasa fadamiki
segashi yau Allah yakawo ranar dazan sanar dake danhaka Do
Allah do annabijjo kishe kina shona.nide aradu ina shonki
kunyace da dadi suka rufeta Dan haka ta ranta anakare
takoma gurin arera
gudun datayi shiyabashi tabbacin tanasonshi Danhaka agurin
yafara rawar cin nasara Dan yasan yama mazan garin nisa
maman yusuf
[3/18, 11:54] Zahra muhd mahmud????: ????????????????
????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*fans muna barar adduarku yaron da bashida Lafiya Allah
yamasa rasuwa to kutayamu da addua Allah yajikansa yasa
meceton iyayenshine sukuma iyayenshi Allah yabasu hakurin
jure rashin sa ,rest in paradise my baby*
*page 10*
Tundaga wannan lokaci syy me karfi tashiga tsakanin surbajo
da jae ko kadan basa son rabuwa da juna
Yauma kamar kullum jae yazo hira gurin surbajo
Akan wani ice suka zauna yayinda surbajo tajuyamasa baya
sabida kunya
Gyada takawomusu da burodi sunaci suna hirar
Can jae yace surbajo aradu inna aureki nahaye nasan duk
garinnan se andunga hirata saboda na auri sarauniyar mata
Dariya tayi tasake rufe fuskarta sannan tace aynima hakanne
Dan yanzu haka yanmatan garinnan haushina sukeji Dan
rannan munje kiwo nida arera su haulen gidan ku suka tsareni
wai sesunmin duka ayko nida arera muka hadu mukaimusu
dukan tsiya
dariya yayi sannan yace hauka sukeyi nibance inasonkowa
acikinsuba shima Baffa cewa yayi inzabi wacce nakeso inde
agarinnanne ze auramin nikuma nazabeki
Dadine yarufe surbajo harseda sautin dariyarta yafito
hakade suka gama hirar wacce yawancinta cin gyadar yafi
yawa
****************************
Al ameen yanzu yafita harkar Aisha kwatakwata harkar
gabanshi kawai yakeyi yayinda mahaifansa zuwa yanzu
sunfara bashi shawarar yakara aure kuma yabasu tabbacin ze
Kara yana neman wacce yake sone fatan alkhairi suka masa
alameen anturashi wani course kasar amurka inda seda
yakwashe tsawon shekara guda acan yanzu idonshi yakara
budewa ya waye fiye da tunaninku ko maganarshi yanzu
tasauya Alameen Kenan Dan kimanin shekaru arbain da
haihuwa amma babu me ganinshi yayi zaton yakai hakan
Aisha ma yanzu bata da lokacinshi Dan yanzu tazama yar
business Dan haka kasuwancinta yafiyemata komai
Mahaifiyarta tanasane da irin tsiyar da Aishan take tsulawa
agidan miji amma kda wasa bata taba tsawatarmataba sabida
gudun kar abin arzikin da Aishan take kawomata tadena
Su Ruky suma kullum cikin bata munanan shawara suke inda
ahalin yanzu har sata takema alameen din yasan tanamishi
satar Amman ko afuska be nunamataba Dan yafuskanci bata
da wadataccen hankali
***************
surbajo Ankara zama yanmata inda yanzu shekarunta sha biyu
da haihuwa Dankaka yanzu sumaye har tallan nono da fura
take doramata tabi yanmatan rugar sukai cikin garin makarfin
ranar dabata siyarba dukan tsiya take mata shiyasa surbajo
bata dawowa gida da wuri matukar tasan bata siyarda
nononba
Se tara nadare take baro cikin garin kamin tagama keto dajin
ta iso rugarsu goma tayi
haka baffanta zetamata fada itade sede tai tabashi hkr
itakuma sumaye na zugashi da cewa maza tafara bi shiyasa
take dare bata dawoba itade surbajo sede kuka
wasawasa seda kaiwa dare agurin talla yabi jikin surbajo
sabida bata da kan kasuwa Dan wani lokacin setakai laasar
baasiya ko na kwaboba gashi nonon yafi Nakowa yawa acikin
wainda suke zuwa tallan tare
duk sanda ta dawo se baffanta yazaneta sannan yamata fada
akan dolene setayi cinikin inbata siyarba ta dawo mana inya
tambayi sumaye ko itace take cewa surbajo karta dawo seta
siyar munafukar har kuka take sawa tace haba alhaji yazaayi
nacemata haka koban haifeta ba ay yatace kuma nasan
hatsarin dake tattare da hakan da irin wannan kalaman take
Rufe bakinshi
insuka koma daki ita da surbajo tashaketa takuma ce wlh
inkika kuskura kika dawo gidannan baki siyarba yankaki zanyi
itade sede tayi kuka tafadawa Allah
jae yasha yimata juyen nonon yabiya kudin Dan kawai tasamu
taje gida dawuri to yau da gobe tafi wasa
ba koyaushene yake da kudin juyenba seyafara rakata tallan
sui ta yawo agari har su samu asiye haka sukeyi sunfi karfin
wata guda suna zuwa tallan tare kwatsam rannan se sukayi
kwantai basu sayar da wuriba ranar basu dawo gidaba se
goman dare
lokacin Baffa yafito yabi hanya yagani meyasa bata dawo da
wuriba dayake basu San jae narakata tallanba seganinsu yayi
tare suna tahowa tsawa yadaka musu yace daga ina kuke
cikin darennan
tsugunnawa sukayi sannan sukace daga talla wankesu yayi da
Mari duka lokaci daya sannan yace nizaku maidar yaro wato
dama abinda innarki take fadamin akan maza kikebi Ashe da
gaskene to wlh yau zaki gane kurenki kaikuma zanga baffan
nakane wawa kawai kekuma munafuka shige mutafi dagudu
tamike tayi gaba Tana kuka koda isarsu gidan yaba sumaye
labarin abinda yafaru cewa tayi ay gwanda dakagani da
idonka Dan Dana fada baka yardaba aygashinan
ranar seda yama surbajo jinajina inda yakara da fadin
gobema ki kuma kaiwa dare awaje wlh Sena yankaki na huta
kuma tallan nono bazaa Dena doramiki ba sabida aladarmuce
kowacce yarinya tanayi Danhaka yazama dole kema kiyi daga
yanzu in magaruba tamiki awaje ki kuka dakanki
haka taci gaba da Kukanta har zuwa washe gari batayi
bacciba
maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*page 11-12*
Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano
zasu tafi gaisuwa duka family dinsu
Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da
yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar
acikin ayarin
Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki
yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki
Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu
Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da
karramawa
Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana
zasuyiba
**************
Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana
gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon
mutane zata dungayi akan su siya
Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata
da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin
kwalli gaba daya dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne
yasa baa siyan kayanta
sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce
Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota
rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane
akan su siya
haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum
Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa
haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta
tayi Don Allah Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan
Allah kifadamini
Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau
mota naira dari zaa kaiki a akori kura
Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah aradun Allah zani
Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata
hau motar
Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka
tafi
**************
Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy
bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin
kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya
tafiyar wahainiya ba
suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay
parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa
sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska
yasamusu suwuce
agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri
Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor
dasuke ciki
1k alameen yabashi mutumin se godiya yake
karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri
takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri
tace sannu bawan Allah Don Allah kataimakeni dasauri
alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn
arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta
durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah kataimakamin
kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh
inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade
agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka
alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi
mezeyi da fura da nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige
yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana
kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka
dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai
gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen
yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta
har rawa yakeyi
mommy ce tafara mgn dacewa yanmata Lfy cikin harshen
fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace
cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako
nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida
yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa
dukana zeyi Don Allah kutaimakamin
tausayintane yakama mommy
bayani tayiwa daddy game da abinda surbajo tace
tambayarta yayi da Hausa yace yarinya meyasa kika ga
muyadace damu taimakeki
share hawaye tayi sannan tace sabida naga kuna da kudi Dan
wancam tanuna alameen da haushi duk yagama cikashi
sabida batamusu lkcn datayi
taci gaba naga yabiya kudin sa iska naira dubu guda
amaimakon naira talatin shiyasa
dariya sukayi harda sumunauwara
daddy yace to tundaga ina kikazo nan tallan tundaga rugar
yalli tabashi amsa
jinjina Kai daddy yayi Dan yasan rugar duk sallah anan ake
siyo shanun dayake rabawa mutane kuma agurin shi yallin
wato ardon
ke yar wanne gidace a rugar daddy yatambaya
ni yar gidan ardoce
mamakine yakamashi yace nasan shi yanzu ke yarsace
washe baki tayi jin ance ansan baffanta tace eh Amman
innata ta rasu
no wonder inji mommy shiyasa ake doramata talla inbata
siyarba adoketa
shigo mota inji daddy yayinda yace munauwara dake gaban
motor tadawo baya surbajo tashiga gaban
arude alameen yawaigo yace haba daddy time is going fa
inakuma zamu da ita
gidansu zamu daddy yabashi amsa
dakyar surbajo tayarda tashiga motar Dan gani take guduwa
daita zasuyi seda sukasha fama da ita tayarda tashiga
utone alameen yayi sannan yadauki haryar makarfin daddy
kemasa kwatance
dan surbajo tunda tashiga tarungume kwaryar nononta sanyin
ac yafara dukanta tafara bacci yin baccinnata seda yabasu
daddy dariya ita me gudun asaceta gata Tana bacci
harsukazo makarfi surbajo baccinta take sha
maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*Banida Lafiya pls i need your prayers*
*page 13-14*
Daddy ne yace alameen yatashi surbajo Dan takarasa
kwatancen gidan
Wani uban duka Al Ameena yakaimata acinya
Hande in bonide itace kalmar da surbajo tafadi da karfi
asakamakon zafin dukan dataji
Arude tadago Tana kallonshi sannan tace Kai kado
menayimka Kake buguna da zafi haka aradun Allah ka kuma
senasa jae yabugemin kai
Dariya gaba daya motar akasa banda alameen Dan yaji
haushin maganar
Kwatance surbajo taci gaba damusu har suka iso kofar gidan
ardo
Ardo ganin motane yasashi tasowa yaiso gurin ga mamakinsa
seyaga surbajo tafito daga gaban motar
Begama mmkb yaga daddy yafito shima Wanda shi alhajin
burni yake cemishi
Dasauri yakarasa gurin daddy yana fadin ikon Allah alhaji
kaine agidana yau Kai lale lale
Mommy ce tafito itama Tagaida ardo tace nashori yace jam
sago
Iso yamusu zuwa cikin gidan sumaye jiki na Bari tafito Tana
lalelale kodo jabbama anan jabbeko
Ruwa takawo musu bayan sungaisa tabasu guri
daddy yace haba ardo yanzu mene amfanin dukiyarka dazaka
Bari ana dorawa yarka tallah harda samata dokar inbata
siyarba se anyankata daganan yakwashe labarin yarda suka
hadu da surbajo yafadawa ardo
mamakine yakama ardo jin ashe sumayece kecewa seta siyar
zata dawo gida amma munafukar tace ba ita bace tasa yana
dukan marainiyar Allah
shima fadawa daddy yayi abinda yasani danshi vashida
masaniya akan sumayece take cewa kar tadawo seta siyar
Nande daddy yayta mishi waazi akan yadena bari ana dorawa
surbajo tallah kuma yamasa alkawarin bazaa sakeba
da daddy zasu tafi dubu dari yaba ardo sannan yaba surbajo
dubu hamsin akan tasiyi kayan sawa ay surbajo dukawa tayi
kamar zatayi sujada Dan godiya duk da batasan yawan
kudinba ammade tasan masu yawane
sumayema daddy yabata murna kamar tayada zani
Rakosu sukayi bayan ardo yasa daya daga cikin yayanshi me
suna sammani yadebowa su daddy kwarya biyu ta Kwai
sannan jarka guda ta zuma me kyau
Sumaye ma kwaryar manshanu tabasu duka akasa abooth din
motor
Su daddy suka shiga duk abinnan daake alameen betako
kafarsa kasaba sabida takaici shi koda excode dinshi bayason
tafiyar dare bare yanzu shinema driver ranshi yagama baci ko
ardon daga cikin motar yagaisheshi
sungama shiga yayi ribar’s yajuya kan motar dagudu surbajo
tazagayo setin window dayake tace
kado arage mugun hali aradu bacin baffanka yabani kudi dase
na kira jae yabugeka tafadi Tana murguda masa baki afusace
yaja motar suka wuce ranshi namishi zafi suko su daddy se
dariya suke masa babu kamar munauwara gurin tsokanarshi
abu kadan tace kado aradu jae seya bugeka shide be
tankamusuba
.se Tara nadare suka iso kaduna agidan yakwana yaki zuwa
gidanshi Wanda ita Aishan ko ajikinta Dan itama tafiya
gidansu tayi takwana acan
kodasafe dayaje gidan bata dawoba se wajen tara sannan
tashigo ko ta tambayeshi ina yakwana kawai hidimar gabanta
taci gaba dayi
kuyi hakuri dawannan banida lfy ne
Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*page 15-16*
Tundaga wannan rana vaa sake dorawa surbajo tallah ba
sede taje kiwo
Ardo Dan Yi yayi kamar ze saki sumaye seda yaranta sukai
tabashi hkr sannan yahakura
Sosai sumaye tayi nadamar abinda taaykata tai taba ardon
hkr kuma tace bazata sakeba
Abangaren soyayyar surbajo da jae kuwa se abinda yayi gaba
Dan yanzu ma intaje kiwo shima yaje to hirarsu suke sha har
cikin zukatansu suke son junansu Dan yanzu jae yace
zefadama baffanshi aje nemarmasa auran surbajo Wanda
hakan bakaramin farinciki yasa surbajo ba danji take tafi
kowacce mace saa aduniya araina nace Anya surbajo harda
Aisha kuwa
***************
Alameen bejimaba yakoma bakin aykin Dan zamannashi baida
amfani tunda matar gidan batasan darajarshiba Dan
ahalayenta kaf babu abinda yasauya
Gidanshi kuwa inda kazanta nasawa gini yafadi datuni nashi
yajima da faduwa
Aisha ce zaune itada aminanta suna gulmar wata kawarsu
anmata kishiya carab Aisha ta amshe zancan dacewa kan
ubancan nahango alameen yamin kishiya Wlh dase nakonata
kurmus Dan alameen Danni kadai akayishi shiyasa koda wasa
betaba attempting Kara aureba Danni kadai naisheshi rayuwa
????dariya suka samata Dan zancan nata dole Adara su
sungama kokarin alameen da har yanzu besaki Aisha ba
dansu burinsu yasaketa tadawo gida suzama daya tunda su
har yanzu basuda mashinshini amma ita dayake ballagazace
bata gane nufinsu akantaba
Haka de taita cika bakin alameen be isa yamata kishiyaba
koze mutu inko yayi seta kona matar
aminan nata nazugata dacewa shi yama isa ay baze ma
faraba
Babbar sallah ta taho Dan haka ana saura sati daya Al ameen
yanufi gida danyin bikini sallah agida
wannan Karon Aisha tayi murna dazuwanshi Dan gaba daya
shaawarshi takeji kuma ita bata iya zinaba shiyasa takosa
yadawo Dan tasamu karbuwa agurinshi gyara ko ina nagidan
tayi har kudi taware takira masu yin penty sukayiwa ciki
dawajen Gidan turaruka kalakala haka tadunga sawa gidan
duk Dan tafaranta mishi rai ga abinci yakai kala goma Data
siyomishi a restaurant duk Dan yaji dadi. Itama wani gurin
gyaran gashi taje me suna maman Izzuddeen beauty Saloon
sukayimata gyaran kai hardasu eye lashes suka samata
dayake Maman Izzuddeen taiya aykinta shiyasa Aisha sosai
tayi kyau
Daga Saloon gurin wata Hajiya me gyaran jiki taje wacce ake
Kira da Maman Gidado tamata gyaran jiki sannan tamata lalle
wayyo fans naso kuna gurin dakunsha kallo araina nace ikon
Allah wato Ashe Aishan tasan abinda yadace Amman batayi
se yanzu datake dawata manufa tadaban aranta lalle taamsa
sunanta ballagaza
Bata dawo gidaba ranar se laasar Tana zuwa wanka tashiga
Wanda seda takusan share awa guda a toilet Dan rabonta da
wankan takusa sati guda sede tayi ciki tsami tafita Tana
fitowa kwalliya akasoma ba batun sallah danko alwala
batayoba haka tagama Kwalliyar ta ta cakare a wasu
tsinannun English wears masu bayyana surar jikinta
falon kasa tadawo ta harde zamanta ba jimawa taji alamar
bude get wani sanyine yaratsata Dan tuni magungunan data
shashsha dawanda ta matsa sunfara ayki????
dasallamarshi yashigo Dan tundaga kofar gida kanshi yafara
kwancewa daganin sabon penty
yanashigowa falo faduwa yakusan Yi sabida arba da Aishan
dayayi Tana takowa zuwa gareshi se girgiza kirji takeyi abinda
yafi tsolewa alameen ido suman tsaye yayi rungumar da
Aishan tamasace tafarko dashi kallonta yakeyi cike da
matsanancin mamaki Dan tunda yake da ita bata taba
rungumeshi Dan yadawo ba sede shi yarungumeta
mamakinshi be karuba seda Yaji muryarta Tana fadin sannu
da zuwa Rabin Raina
wani dadine yalullube alameen tabvas yanzu ya yarda Allah
yashirya mishi Aishan shi rungumeta yayi shima nanfa suka
shiga kissing din juna dakyar alameen yakwace kansa danta
Aisha bataki komai ayishi agurinba kan kujera suka nufa suka
zauna yayinda Aishan tahaye kan cinyarshi tazauna Tana
masa wani malalacin murmushi
sannan tace sannu dazuwa hubby na ya hanya cike da farinciki
yace hanya Lfy baby na yana sameki Lafiya tabashi amsa
gamida fari ????da idanuwanta
janshi tayi tarakashi toilet danyayi wanka ga mamakinsa Aisha
yau harda tayashi yin wankan
yana fitowa ta tayashi shiryawa sannan tajashi zuwa dinning
alameen murna kamar ta kasheshi ganin kulolin abinci
kalakala nande yashiga dibar gara yana samata alvarka bayan
yagama alwala yayi zefita masallaci sallar magrib dasauri
Aishan Tasha gabanshi tace haa hubby ina zuwa kuma
sallah zanyi Gimbiyata yanzu zandawo kema jeki kiyi sallar
yana gama fadin hakan yamata kiss agoshi yazagayeta
yawuce
tsaki Aishan taja Wlh Dan karta ja yafasa biyamata bukatane
da tamasa rashin mutunci Dan tsabagen rainin wayo yasan
abinda take nufi amma shine harda wani tafiya masallaci
sallah
dakinta tawuce tazauna Dan sallar cewa tayi tahada da asuba
danko azahar batayiba ????
alameen bedawoba seda yayi sallar ishai sannan yashigo gida
bata falo danhaka dakinta yanufa Yatura kofar yashiga
hasbunallahu waniimal wakeel itace tafito abakinsa sabida
arba dayayi da Aishan haihuwar uwarta babu kaya ajikinta
jikinshi ne yafara Bari dasauri yaje yarungumeta yashiga ayka
mata da sakwanni masu wuyar fassara to abinka daya jima
beyiba jinshi yake kamar ango ajan gado suka yada Zango
sosai suka Raya wannan dare Wanda se asuba alameen
yasaurara mata yayi farinciki sosai da canjin dayaji Aishan tayi
Danjinta yayi takara test
dasafe yashirya zeje gidansu gaida iyayensa yanemi Aishan
datamasa rakiya wata uwar harara ta wurga masa sannan tace
Bainda zani kajimu da mutum shikenan daga Dan sakar maka
fuska se raini yanemi yashigo to contract ne kuma yakare
bukatar maje hajji sallah Dan haka karka nemi ka takuramin
amfaninka nawannan lokacin agurina yawuce sewani jikon
tawuce tabarshi agurin
jiri ne yafara daukar alameen dasauri yazauna yadafe kanshi
yana karanta adduar datazo bakinsa wato Aisha
tayaudareshine da duk abinda tayi Dan yabiyamata bukata
badan Allah ba wannan wanne irin balaine
dakyar yasamu zuciyarshi tadena zafi yana zaune agurin tazo
tawuceshi tafita yawonta
mikewa yayi jiki bakwari yanufi gidan iyayensa sosai sukayi
murna dazuwanshi
daddy ne TaiwanYauwa aminullahi dama Kabir nake jira yazo
na aykeshi tunda gaka kazo sekai kaje
cikin ladabi da biyayya yace to daddy ina zanje
rugar yalli inda muka taba zuwa muka Kai wata yarinya
gidansu can Zan aykeka kasiyo shanu dazaa rabawa mutane
carab munauwara taamshe daddy cewa zakayi gidansu me
kiranshi kado budurwar jae zaka aykeshi gabadaya falon
sukasa dariya duka alameen yakaimata ta gudu
kudi daddyn Tamiko Yamiko masa a ledar viva yace gasu
miliyan ukune kasiyo yadda yakama murmushi alameen yayi
sannan yaajiyewa daddy kudinsa yace ze siyomasa danashi
kudin inda sabo daddy sunsaba da kyautatawa daga alameen
din albarka sukai tasamasa yamusu sallama yatafi bayan
daddy yatambayeshi zegane gidan yace eh zegane har
munauwara nacewa kode tazo tarakashine yamata banza
yawuce
da azahar ya iso garin yana faking surbajo nafitowa zata tafi
kitso tsayawa tayi Tana kallonshi yayinda shima tsayawar yayi
yana kallonta
cike da TaiwanTsiwa tace aradu wannan kadon bayan bakin
halin har maita gareka yoto inba mayeba taya zaka tsaya
kana kallona kamar nacimaka bashi nagade kudin daaka bani
kyauta aka bani kuma bakai kabaniba baffankane bare kace
sukazo ansa sede idan bakin halin nakane zaka gwadamin
aradu ko dakasha sanda Danni bani daukar raini tafadi harda
murguda baki
alameen dariyace takwacemasa tabbas ya yarda da zancan
mutane dasuke cewa yanfulani Nada katobara
surbajo ganin yanamata dariyane yasa takwance dankwalin
kanta tasake Damara dashi dama akwai wata damarar daure
akugunta karasowa tayi gabanshi tatsaya taruke kugu ita ala
dole zatayi maganinsa tunda yake mata dariya wata dariyarce
tasake kamashi yace ikon Allah yau nahadu da gamona inba
hakaba taya daga zuwana bancimikiba
ban shamikiba kitareni da balai
surbajo tsayawa tayi Tana kallonshi tunda yafara dariya
dimples dinshi suka lotsa hankalinta yakoma kanshi aranta
tace Ashe akwai Wanda yafi jae kyau dama bansaniba
hannunta takai dede setin dimples din ta taba dariyar
dayakeyine tatsaya sakamakon jin antabashi afusace yajuyo
zekaimata duka dagudu takwasa Tana cewa woo nacuceshi
nataba ramin nacuceshi nataba ramin harta kule yadena
ganota
haba alameen mezeyi inba dariyaba shi tunda yake betaba
nishadi irinnayauba yana dariyar ne ardo yafito yasameshi
ganinshine yasa yadena dariyar da faraa yanufeshi suka gaisa
ardo yamasa iso zuwa cikin gidan anan alameen yafadamasa
abinda yakawosa zagayawa dashi ardo yayi gardengarken
shanun yagama zaba yabiyashi kudinsa inda harda ihsani
yamasa sannan yabaShi kudin daze dauko motor dazaa zuba
shanun akawo musu kaduna Dan dama inaka siya ardonne
yake kaimusu sallama yamasa yatafi bayadda ardo beyi
dashiba yatsaya yatafi da nono amma yaki
yafara rakiyatafiya kenan yahadu da surbajo tadawo daga
kitson tsayawa yayi Dan yaga tanufoshi soyake tasake bashi
dariya Dan duk wani bacin ran da Aishaaisha tasashi dariya da
surbajo tabashi dazu yakawar masa dashi
karasowa tayi tace kado zaka tafine kai yadagamata yana
murmushi tace to Dan Allah kabarni nasake taba ramin
fuskarka aradu bazan fadawa kowaba inma bazaka Bari
nataba Dan Allah ba togashi kabarni nataba a naira goma
tafadi tana kwance habar zaninta tadauko naira goman
dariya alameen yakeyi danshi Wlh yanzu kallonta yake tamkar
katoon
Mika hannu yayi yaamshi kudin sannan yatada motarshi yatafi
yabarta dagudu tabi bayan motor Tana cewa kado katsaya
kabani kudina gudu take iya karfinta alameen na kallonta ta
mirror yana dariya dataga bazata iya kamoshibane tace kaci
wuta balbal ban bakaba tadauki dutse tawurga ma motar
dayake surbajo ta iya jifa seda tasamu motor
Alameen Allah ne kawai yakaishi gida Lfy Sabida daya tuno
surbjo dariya yakeyi lalle ya yarda fillo akwai wowta baabinda
kebashi dariya irin nacuceshi nataba ramin wannan Abu
nabashi dariya ahaka har yaiso gida
itako surbajo Allah yaisa tajata yafi kwando dubu sabida
naira gomanta Dan kudin da daddy yabata gona ardo
yasiyamata dasu goman data ba alameen ardone kullum yake
bata goma takashe toshine tayau alameen yagudu da ita har
kuka tayi akan naira goman koda sukaje makarantar dare
kasa karatu tayi sabida gomanta yayinda tasha alwashin duk
randa taga kado seya sani
taku har kullum
Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button