LabaraiMatar GidaYar aiki

Daga zuwa aikin gida na zama matar gida’, cewar wata budurwa yayin da ta wallafa bidiyonta

Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya yayin da ta yi murnar samun yanci daga mai aiki zuwa matar gida

Sabuwar amaryar wacce ta cika da farin ciki ta je dandalin TikTok don wallafa bidiyonta yayin da take taka rawa

Sai dai ta yi na’am da wani sharhi da wata tayi don kare ta cewa tun farko bata ambaci cewa ubangidan nata na da aure ba

Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan ta wallafa wani bidiyo a dandalin sadarwa ta TikTok dauke da rubutun, “daga mai aikin gida zuwa matar gida.”

A bidiyon da ta wallafa, an gano matashiyar matar dauke da murmushi a fuskarta yayin da take zaune a bayan mota tana rawar wata waka mai suna ‘Competition’ wato ‘gasa’ wanda Mayorkun ya rera.

Wata mai amfani da shafin soshiyal midiya mai suna @confirmibadanbabe ta tambaya a bangaren sharhi,

“Da fatan ba mijin uwar dakinki kika aura ba dai.”

“Shine fa,” matar ta mayar da martani.

Shafin @lindaikejiblogofficial ta dauko hoton tambayar da amsar da ta bayar sannan ta wallafa shi a Instagram.

A wani yanayi mai ban mamaki, matar ta kuma yi na’am da sharhin da wata tayi tana mai kare ta.

Sharhin wanda wata mai suna @cinderella ademu ta yi ya ce:

“Ji mana amma ba ta ambata cewa yana da aure bah aka kuma bata ambata cewa ta auri wanda take yiwa aiki ba.”

Kalli bidiyon a kasa:

Ga bidiyo da martanin nata:

Asali Hausa Legit 

 

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button