LabaraiYan bindiga

Macizai Na Saran Fasinjojin Jirgin Kasan Da Ke Hannun ’Yan Bindiga’

Bayanai na nuni da cewa macizai sun fara saran wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kadunan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Mawallafin nan mazaunin Kaduna da ya jagoranci tattaunawa da ’yan ta’addan har suka sako mutum 11 daga cikinsu, Tukur Mamu ya tabbatar da hakan ranar Litinin.

Ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce akwai tarin macizai a dajin da ’yan bindigar ke rike da wadanda suka sace din, kuma sukan bayyana idan dare ya tsala.

“Ina mai tabbatar muku cewa akwai macizai sosai a dajin nan, kuma sun sari wasu daga cikin wadanda aka sace saboda da daddare suke fitowa. Ga shi ba magani sai na gargajiya ake ba su,” inji shi.

Ya kuma ce, “Sanin kowa ne saran maciji na kisa, don haka ya kamata gwamnati ta yi wani abu don kubutar da mutanen nan, domin ita ke da iko idan ta bi hanyar da ta dace, kowa ya ga yadda muka karbo mutanen 11, ina kira ga gwamnati da ta yi abin da ya dace.”

Ya ci gaba da cewa bayan saran macijin ma akwai rashin abinci mai inganci, da rashin tsaftataccen muhalli da jiki ma kadai da suka isa su tagayyara mutanen.

A karshe Mamu ya tabbatar wa iyalan wadanda ke hannun ’yan bindigar cewa ba duka ba zagi tsakanin ‘yan ta’addan da wadanda suka sacen, sai dai rashin kyawun muhalli da yanayi da suke Fama da shi

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button