BuhariLabaraiYan bindiga

Za Mu Kubutar Da Fasinjojin Jirgin Kasan Da Ke Hannun ’Yan Bindiga A Raye – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin yin amfani da hanyoyin karfi da wadanda ba na karfi ba wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kadunan daga hannun ’yan bindiga.

Aminiya ta  tattaro cewa Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu, ne ya sanar da umarnin ranar Talata a cikin wata sanarwa mai taken: “Buhari ya ba da umarnin gaggawa na kubutar da fasinjojin jirgin kasa”.

An dai yi garkuwa da fasinjojin ne a ranar 28 ga watan Maris din 2022. lokacin da jirgin da suke kai ya taka bam din da ’yan ta’addan suka dasa masa.

Amma a cikin sanarwar, Shugaba Buhari ya ce yana iya bakin kokarinsa wajen ganin anceto dukkan fasinjojin da ke hannun ’yan ta’addan.

Garba Shehu ya ce, “Umarnin Shugaban Kasa a bayyane yake karara, wanda shi ne dole a kubutar da su a raye, kuma tuni aa umarci sojoji da ragowar jami’an tsaro su tabbatar da cika umarnin shugaban da gaggawa.

“’Yan ta’addan sun zo da bukatarsu, wacce ita ce ta a sakar musu ’ya’yansu, inda har suka saki mutum 11, kuma ana sa ran sakin karin wasu nan gaba.

“Amma duk da haka, gwamnati na iyakar kokarinta wajen ganin babu wani wanda ba a kubutar ba. Muna kuma sane da dukkan gudunmawar da wasu muhimman mutane suke bayarwa wajen ganin an sami maslaha a lamarin,” inji Garba Shehu.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button