NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 45

*_NO. 45_*
…………Matso da fuskarsa yay daf da tata tamkar zai haɗe bakinsu, sai ya buso mata numfashinsa a kan fuska.
      Zuƙa tai ta haɗiye tana kuma tunzuro baki,  yasa yatsansa
manuniya ya ɗalli bakin kaɗan, yana faɗin “fine girl nagani ai, amma ba zanyi ba, niba ɗan iska bane”. 
      Babu shiri Ummukulsoom ta waro idanu sosai a kansa, tare da azamar maida bakinta da sauri, saboda zafin da taji da kunyar furicin da yay.
      Shikam tuni ya ɗauke kansa tare da basarwa tamkar bashi ya faɗa ba.
     Dole ta sadda kanta ƙasa dan harga ALLAH bata taɓa jin kunyarsa ba irin yau, sosai furucinsa ya kunyata ta, ita sam bada manufar da yake nufi ta turo baki ba wlhy……
       Amaan daya kafeta da ido yana nazartar ta ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta tareda sakin hannunta ya dafe dirowar yanda dai bazata gudu ba, “Karki zurfafa tunani, tunda kinaso zo nai miki matar Usman Ajiwa”. Yay maganar da matso da bakinsa kusa da nata.
    Babu shiri Ummukulsoom ta turashi tanason barin wajen, taga yau salon taɓara da bata kunya yakeji kawai.
        Saka ɗayan hannunsa yay a ɗayan gefen, ta ɗago ta kallesa fuska a ɗaure saiya ɗaga mata gira ɗaya cike da wani salo “K Haka zaki ringa tarbar naki mijin idan ya dawo daga tafiya?”. Yay maganar cikin wata ƴar shagwaɓa da narke murya.
     Janye idanunta tayi tana ƙara mamakinsa, fuskar dai a tamkenta take babu walwala, amma kuma sai iya shege yakema mutane tamkar ba shiba, ta ya mutse fuska cikin salon tura masa haushi tace, “Kanada matsala wlhy malam”. 
     Shiru yay bai amsata ba, ya dai kafeta da mayun idanunsa hannayensa harɗe a ƙirji.
     kallonsa tai Ƙasa-ƙasa ta janye idonta, mamakin yanda maƙogwaronsa daya fito sosai a wuyansa yake motsawa alamar akwai magana a ransa, take jinjinawa, a zuciyarta tace, “Miskilanci baiyiba wlhy”…..
        A fili kuwa saita marairaice masa, dan ta kula buyaginta bazai fiddata ba, ga yunwa na cinta.
       “ALLAH yunwa nakeji” ta faɗa cikin langaɓe kai idanunta na tara ƴan ƙwalla da suka ƙara musu ƙyalli da girma.
    Karon farko da ya sakar mata lallausan murmushi mai cike da ma’anoni masu yawa da tunda take bata taɓa ganinsa a kan kamilalliyar fuskarsa ba.
     “Ya salaam” ta faɗa a hankali saboda wani cikar haiba da kamala daya ƙara mata, sai taga kamar da gayya ma yay murmushin.
      Matsowa yay gabanta kaɗan yakuma ƙara kusanci a tsakaninsu har sunajin saukar numfashin juna. cikin raɗa yace, “Zan tabbatar miki nafi haka matsala ƴammata, amma sai nan gaba kaɗan”.
        Babu shiri Ummukulsoom ta lumshe idanunta saboda wani yarr da taji a jikinta.
    Shima ja yay da baya, yana nuna mata hanya alamar ta wuce.
    Cike da sassarfa tabar wajen tana ambatin Alhmdllh. Tukunyar ta ɗauka ta cigaba da hidimar ɗora noodles ɗinta.
    Shikuma ya jingina da bango tareda da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu.
    Gaba ɗaya Ummu ta takura da zamansa, tare da kallon daya kafeta dashi babu wani risinawa ko basarwa kamar yanda yakeyi a da.
      Kasa jurewa tayi, dan aikin na neman gagarar ta gaba ɗaya, sai yin komai take a ɗan rikice.
    Guntun murmushi yayi yana janye idonsa cikin Basarwa, a ransa yace, “A shema Matsoraciya ce”.
     A fili kuwa saiya maida idanunsa kanta, cike da haushin wannan kallon ƙurulla ta ɗago nata manyan idanun ta kallesa, caraf suka haɗa ido, Ummu ta ɗan hararesa.
       luuu yay da nasa zai lumshe amma saiya buɗe batareda ya rufe ɗinba akanta, itama saita  janye nata ta maida ga girkinta tana ƙunkuni ƙasa-ƙasa yanda bazai jiba.
    Wani murmushin gefen baki yayi ganin yanda takeyi, ko wane motsinta sake tsundumasa a ƙaunarta yakeyi.
      Ummukulsoom data shareshi tana cigaba da aikinta takuma ji a jikinta ido na yawo a kanta, juyowa tai ta sake kallonsa, sai caraf suka sake haɗa idanu.
    Shine ya fara janye nasa, ita kuma ta ƙwaɓe fuska, “Nifa bana son kallo, dan ALLAH ka fita karma wani ya dawo ya ganka”.
     Yanzu kam sosai ya ɗago ido ya kalleta tare da lumshesu da buɗewa lokaci ɗaya, kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsaiwarsa sosai yana mai fuskantarta gaba ɗaya, saɓanin da daya karkata kaɗan, “Idanma na kalleki ai sadakina na kalla ko madam?”.
     Kasa bashi amsa tayi ta ɗauke kanta gaba ɗaya, bata sake kallon inda yakeba harta kammala ta juye a filet, ta ɗakko ƙwai zata fasa. 
     Yace, “Hummm”.
 Juyowa tai ta kallesa amma sai ya basar kamar bada ita yakeba, itama ɗauke idanunta tai taci gaba da abinda takeyi.
      Kiransa da akai a wayane ya sashi fita yana amsawa, Ummukulsoom ta sauke ajiyar zuciya tana harar bayansa, a ranta faɗi take wannan irin takura har ina.

     Ƴar hayaniyar da tajiyo a falo ce tasata jin daɗi, dan kamar maganar Attahir, cike da ƙwarin gwiwa ta fito ɗauke da indomie ɗinta, ta sauke ajiyar zuya ganin Bily ma ta dawo, ga Yaa Attahir ma, Amaan na zaune har yanzu yana waya, ido suka haɗa tai saurin janye nata tana gaida Attahir da basu haɗu da safe ba.
     Ɗakinsu ta nufa dan tasan bily na can.
     Bata sake jin ɗuriyarsa ba dan ƙin fitowa tayi, shi kuma bai nemeta ba, dama akwai abinda ya kawosa gidan ya zauna zaman jiran Attahir ne.

    Kwanaki biyu da faruwar haka ya wuce kd, ita Ummukulsoom ma bata saniba, sai da daddare tana duba masseges a wayarta taga saƙonsa.
       _“Congratulations da gama exams my happiness, Naje KD, zankuma zauna har sai an bani matata sannan na dawo lagos, ki kula min da kanki dan ke ta Usman Mahmud Ajiwa ce shi kaɗai har a aljanna insha ALLAHU”_.
      Karan farko da tai murmushi akan saƙonsa tun bayan gane shine A-Waheed, ta lura indai a rubutu ne akwai zaro magana, ta bakine dai ya zame masa abu mafi wahala. ƙin masa reply tayi, ta cigaba da harkokinta hankali kwance.

★★★★★
         Sosai Maman Ahmad ta dage gyara su Ummu, dan dukkan kayan gyran jiki da kowanne fanni an dage musu, maganin sanyi kam tunda suka dawo dama suke shansa kala-kala, duk sunyi ƙyau da ƙara murjewa, kowa ya gansu yaga amare ƴan gata, su kansu sunaji a jikinsu sun canja.
    Biki ya matso gab dan kwanaki biyar kawai ya rage, dan haka washe garin da zai zama saura ƙwana huɗu su Ummukulsoom ke shirin wucewa kd, duk kuma sai jikinta ya fara yin sanyi, hakama Bily duk ta zama wata shiru-shiru, rawar kan nan duk yanzu babu shi, aiko Ummukulsoom saita samu damarta yanzu, haka zata zauna taita tsokanarta, tun Bily na iya maida murtani har ta bari, ashe haka akeji idan auren ya kusanto?.

  
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         Key ɗin motane ya faɗo mai matukar ƙyau da tsada, dan motar da ake yayice daga wane sai wane, sai ƴar takarda a tare da key ɗin.
      Meenal ta kalli Basiru dake tsaye yana kallonta hankaki kwance, danshi dai a saninsa bai aikata wani laifi ba.
       *_“Happy Valentine day my Handsome, i love you so much har ƙarshen rayuwa, wannan key ɗin motar tukuycin farin cikin da kabani ne jiya, danka shayar dani zumar danasan ko matar nan taka bata taɓa samuba, dolene kasamu tukuyci mafi tsada daga gareni. Ka duba wayarka na turo maka saƙo….”_*
       Kasa ƙarasa karantawa Meenal tayi, ta dage iya ƙarfinta ta zubama Basiru mari tana huci.
    Da sauri yasa hannu ya dafe kuncinsa baki buɗe, “Meenal ni zaki mara? Rainin har yakai ki ɗaga hannu ki mareni?”.
     “An mareka, kai wanene banda banza a banza, baƙin munafuki, to yau ALLAH ya tona asirinka”. Ta ƙare maganarda fisge wayarsa ta shiga bincike.
     Sosai jikinta ke wani irin tsuma da rawa, hawaye masu zafi suka wanke fuskarta, ta nunashi da ɗan yatsa tana ja baya, “Basiru yanzu nan har takai ka dinga ɗaukar jikinka kana turama karuwai? Dama haka kake daƙiƙi ban saniba…..”
     “K dalla banason hauka, ubanwa nake turama wa idan bakeba, naga kullum kece kike cewa na tura miki saboda kina kewat…..”
     Wani marin ta kuma sauke masa, kafin ya dawo hayyacinsa ta sake zuba masa wani,  sosai Basiru ya gigice, babu shiri ya kai mata duka itama, dan ankai bigiren da bazai iya jurewa ba.
       “Kutumelesi, lallai bakada hankali, harni zaka doka ɗan matsiyata” meenal tayi maganar tana ƙwala masa wani ɗan abun kwalliya dake sam center table ɗinsu.
     Kansa ya dafe yana layi, kafin ya fisgota cikin zafin nama shima ya hau jibgarta.
    Iyaka iyawa meenal ke zabga ihu itama tana kai masa duka, baba mai gadi daya iso da gudu saboda jin hayaniyarsu duk saiya ruɗe ya rasa ina zai nufa, fita yay da gudu neman mutane, hakan yay dai-dai da shigowar motar Su’ada yayar Meenal. a ƙofar gida ta faka motar ta fito hankali tashe saboda ganin yanda mai gadi ke tsaidata.
     “Kai lafiya kuwa?”.
 “Hajiya kiyi taimako Alhaji zai kashe hajiya wlhy…..”
    Bangajesa tai ta afka cikin gidan, saboda jiyo ihun meenal da takeyi sama-sama.
    Ɗane-ɗane ta iske Basiru saman Meenal yanata duka tamkar ya samu jakarsa.
    Sai da ta fara yin gajeren bidiyo sannan tasa iya ƙarfinta ta hankaɗashi gefe, lokacin meenal ta gama fita hayyacinta gaba ɗaya saboda shaƙar da Basiru yay mata a wuya. 
      Waya Su’ada tasa ta kira mahaifinsu kafin police, cikin mintuna da basu fi 20 ba saiga police tare da yayan meenal da yay aure kwanan nan.
     Duk yanda Basiru yaso musu bayani sunƙi fahimtarsa, tunma anan suka fara dukansa saboda gaddama da yaso musu, aka cukuykuyesa aka jefa a mota, ita kuma Meenal akai asibiti da ita….

   ⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            Tun isowarsu suka tabbatar da bikifa ya kankama, dan gida ya fara cika da dangi makusanta na nesa, inna laraba ma ta iso ta ɗilau da sauran dangin maman Ummukulsoom, hakama wasu daga dangin Ummi.
        Abokan wasa suka fara tasasu da tsokanar amare-amare, duk sai sukaji abun banbara kwai wai namiji da suna hajara.
     Isowarsu baifi da mintuna 40 ba saiga ƴan kawo lefe daga gidansu Amaan, ita Ummu ma abin ɗaure kanta yay sosai, lefe sai kace wani auren farko? Dan danan gida ya kacame da guɗe-guɗe, kasancewar zuwan ƴan kawo lefen Ummukulsoom babu jimawa sai ga lefen Bily itama, gidafa ya kuma kacamewa, komai sunyi abinsu akan tsari.
   Dole su Ummukulsoom suka fice gidan badan sun soba.

*_WASHE GARI_*.

     Da hantsi aka kai lefen yaya Zaid gidansu Aziza, wannan kam da Ummukulsoom akaje, taji daɗi sosai ganin ƴan uwansu na ɗilau ɓan garen babanta suma sun fara isowa.
    Sai surutu suke mata wai taji ƙyau da jiki, harda masu mata habaici a kaikaice wai shiyyasa ta guji ɗilau dan tafi ƙarfin mazajen can, (adai taƙaice suna mata shaguɓen sun san aurenta ya mutu), sarai ta fahimcesu kasan cewarta lauya, amma saita basar kamar bata fahimta ɗinba.
     Sai kuma akai sa’a Amaan ya kira wayarta dake hannun Bily a dai-dai wannan lokacin.
      Cike da tsokanar magana Bily da sam bata fahimci gugar zanarba tace, “Bestie ga mijinki na kira”.
     Duk kallon bily sukai su masu shaguɓen, Ummu kuma taɗan yatsine fuska kamar bazata amsaba sai kuma ta amsa saboda maida murtani.
   Sakin ranta tai cike da yanga tai sallama bayan ta saka wayar a hans free kowa naji.
      A hankali ya amsa tare da cewa “Inason ganin matata”.
    Murmushin ƙarfin hali Ummukulsoom tayi tana faɗin, “ba yau ba”.
    “Why?” ya faɗa a marairaice.
    Mikewa tai tabar wajen dan tasan wannan amsar kawai ta ishesu. Aiko duk sai jikinsu yay sanyi suka faɗa wasi wasin to kodai ƙarya akeyi dama aurenta bai mutuba?.
    Ita dai tuni ta koma gefe tana cigaba da wayarta da Amaan dake tambayarta kalar kayan da takeso suyi amfani dashi wajen mothers day ɗin da Momcy ta haɗa musu.
    Ita kuma ta dage akan bazata jeba gaskiya.
    Shiru yay mata bai sake tankawa ba, bai kuma yanke wayarba.
    Itama sai tai shirun tunda kuɗinsa akeci. Ƙitt ya yanke kiran ba tare da ya kuma cewa komaiba.
    Itama saita harari wayar ta koma cikin ƴan uwanta.

*WASHE GARI ALHAMIS* akai kamun amare har Ummukulsoom, da safe sukaje wankin kai da ƙunshi su duka ukun har Aziza, sai yamma lis suka dawo aka shiga taron kamu da akai a gidan Hajiya yaya.
    Babu wata hayaniya dan iya dangine na kusa suka zo kasan cewar auren duk tuwona maina ne.
      Abin ya kayatar sosai dan matane kawai a wajen, akaɗan sha kiɗan ƙwarya kowa ya kama gabansa zuwa magriba.
     JUMA’A bayan tasowa massalaci aka ɗaura auren Aziza da Zaid, sai Bilkisu da angonta Muhseen, a masallaci ɗaya aka haɗa dan kar a wahal da mutane, shiyyasa abun ya kayatar matuƙa,anguna sunsha ƙyau abin har ba’a magana.
     Hakama amare su Ummukulsoom dake a cikin gida. Zuwa yamma aka cigaba da shan karasun biki da Ummi ta shirya.
    Gaba ɗaya sai Ummukulsoom ta samu kanta da zubar hawaye, dan taji ana cewa yau ɗin za’a miƙa kowacce ɗakinta.
    Can bayan ɗakunan maman Ahmad sukaje ita da Bily suka haɗa kai sunata kuka ita da Bily, Peace da sukazo bikin da ƴan uwanta da Mom nasu tana zaune tana musu dariya, sai da ta fuskanci da gaske fa sukeyi saita koma lallashinsu, rayuwar hausawa na birgeta, inda sune amarya tata ɓarar da rashin kunya kenan da taɓara ita a dole ana bikinta, amma jiba su Ummukulsoom yanda suka shiga damuwa, sam babu wani rawar kai a tattare dasu kuma.

     Ana fitowa daga sallar magriba akace su shirya, duk sai suka rikice, sai da maman Ahmad taita lallashinsu sannan suka kimtsa, an miƙasu falon Abba inda baban Ummukulsoom da Dad da Hajiya yaya, gwaggo hinde, Inna laraba da yayyen Ummi ke zaune, daga Ummukulsoom har Bily fuskarsu a rufe take suna sharar ƙwalla.
     Bayan an fara saka musu albarka aka ɗora da faɗan bin miji da kiyaye dokonin ALLAH, aka koma kuma nasiha, kowa saida yay musu tashi a taƙaice kafin Abba ya dankama kowaccensu ƙyautar key ɗin mota yana haɗiye ƙwallarsa da ƙyar, bai taɓa aurar da mace ba sai yau, shiyyasa duk sai ya damu, ƙarfin hali kawai yakeyi. Ummi kam kasa dairewa tayi saida ta share hawaye.

      Ana idar da Sallar isha’i aka kwashi amare bayan an caɓa musu kwalliya, za’a fara zuwa wajen Mothers day ɗinne, daga nan kowanne ango ya ɗau amaryarsa.
    Sai dai fa su Ummukulsoom basu san da wannan shirin ba, ganin anmusu kwalliyar zuwa wajen taron sai suka ɗauka ko an fasa kaisu yau, dan haka daɗi ya kamasu sosai………✍????

      *_jiya kun jini shiru, hidimomin mai iyaline basa karewa, yauma ciwon haƙori nake wlhy, amma banason barinku shiru shiyyasa na daure nayi, sai daifa ko editing babu kuyi manage a haka, idan naji dama ko zuwa anjima ko gebe idan ALLAH ya kaimu zaku iya jina da wani page ɗin._*????????‍♀️????????‍♀️????????

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button