NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 34

*_NO. 34_*

……….Fuska ta kuma haɗewa tana janye idanunta daga cikin nasa, ta fara takowa a hankali zuwa inda suke da nufin kama Ahmad su tafi. Amaan kam sam yakasa ɗauke manyan
idanunsa a kanta, sai binta da kallo yake ƙasa-ƙasa da mamakin ina zata je? Sam ya kula bata da tsoro yarinyar nan.
    Mayen ƙamshin turarenta ne ya fargar dashi kusancin da suka samu, ya sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya yana kuma tamke fuska.
   Ko kallon inda yake Ummukulsoom ba tai ba, ta kamo hannun Ahmad dake laɓe a bayansa zata jawoshi, shima saiya riƙe ɗayan hannun Ahmad ɗin.
     Kallan kallo suka sakema juna kowa fuska babu ɗigon walwa, har ƙasan zuciya Ummu haushinsa takeji.
     “Zamu wuce”. Ta faɗa a kausashe.
       Banza yay mata kamar bai jiba, saida ya shaƙi iska ya fesar sannan yace, “Dani na kawo ki?”.
          Ƙin tankawa tai itama, ta ja hannun Ahmad kawai.
     Ahmad da yake tirjewa yace, “Aunty ni kibarni zan zauna a wajen big daddy”.
     Hannu ta ɗaga tamkar zata makesa, harda cije baki. Ahmad daya tsorata ya ƙankame hannun Yaa Amaan sosai.
    Ba ƙaramin dariya abin yabama Amaan ba, amma saiya fuske ya haɗiye abarsa yana kafeta ta idanunsa, ”Miyasa kika fasa? Ki dakesa mana”.
     Baki ta murguɗa masa  tana wani wulkita idanu da kaɗan ya rage ta wulkice da zuciyar sa, dan gaba ɗaya ƙofofin gashin jikinsa sai da suka buɗe, ya haɗiye yawu da sauri yana janye idanunsa a kanta.
     Ita kam bama tasan yanaiba, sai ƙoƙarin ɗaukar Ahmad ɗinma da take hannu biyu.
     Sam bazai iya jurewa kusancinsu ba, dan haka ya sakar matashi kawai, amma sai Ahmad ya fasa kukan shifa anan zai zauna.
    Bata saurari kukansa ba ta fice abinta.
     Idanunsa ya lumshe tareda kai hannu ya shafi girarsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, lallai indai wannan shine so to sam bai masa adalciba, dan shikam bazai juraba. Gaba ɗayama jiyay aikin nasa ya fita kansa, dan haka ya tattare kayan ya koma ciki.

      Ummukulsoom kam tana fitowa taci karo da Bily a ƙofar gidan sunan ita da wani saurayi.
      Cikin mamaki tace, “Bestie daga ina haka?”.
    Tsaki Ummu tayi tana dire Ahmad da har yanzu yake kuka a ƙasa, “Ki bari kawai Bestie, wai dan wulaƙanci fa Ahmad ya kama kaimu wannan gidan a matsayin gidan sunan”.
       Bily ta ɗan waro idanu waje tana dariya, “Amma Ahmad ALLAH ya shiryeka, gidan Yaa Amaan ɗinne ya zama gidan su Sulaiman?”.
     “Ai ki barni dashi, yau ba sai gobe ba sai na zanesa, da wani kansa tun na haihuwa”.
      Sosai saurayin da ke tare da Bily yake dariya, shi mamaki ma take bashi, ta dage ita a dole faɗa takeyi, amma kuma muryarta na fitane a nutse kuma cikin amo mai daɗi.
     Sam Ummu ko kallonsa bata yiba itakam tai gaba ta bar wajen, Bily ma dai sai da ta dara, tana binta da kallo, dan ita tunda taji alaƙar dake tsakanin Ummukulsoom da Yaa Amaan tasan sun dace, fatanta kuma komai ya zama normal ta koma ɗakinta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

              Sosai Suhailat ke bincike akan Baseeru, ba dare babu rana, ta haka ne ta samu ganawa da abokansa su Abdul, da yake duk sunsan da zancen rabuwarta da Baseeru basuyi mamakin komaiba, sai dai canjawar da tai musu.
      Itama sun canja mata ƙwarai da gaske, dan gaba ɗayansu sunyi aure zuwa yanzu.
         Najeeb ne ya fara faɗin, “Mudai a bayan rabuwarku mukejin ƙishin-ƙinshi akan aure yayi, badai mu tabbatar ba dan sam yaƙi yarda mu haɗu dashi, sai bayan aurensa da ƴar gwamnan katsina ta yanzune mukabi diddiginsa har mukasan ashema bayan ya auri Lubnar da muka taɓa ganinsu tare sannan kina amarya amma yace mana ƙawarkice ya kuma auren wata yarinya Fannah, a tare ma ya sakesu da Lubna lokacin aurensa da Meenal ɗin”.
     Mamaki ya kuma danne Suhailat, lallai lamarin Basiru ya gawurta, amma ta ɗauki alwashin nuna masa *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA*.
       “To yanzu ta yaya kuke ganin zamu sami Lubna da Fannah?”.
       Abdul yace, “Lubna dai samunta zaifi sauƙi, tunda mahaifinta ba ɓoyayyen mutum baneba, Fannah ɗince dai matsalar”.
        “Hakane, amma inhar mun haɗu da Lubna itama Fannahr zamu sameta insha ALLAH”.
      A tare sukace hakane.

  *Washe gari*

       A washe garin ranar Suhailat tai shirinta na alfarma ta doshi kanon dabo, batasha wata wahalar samun gidansu Lubna da aka bata address ba, hakama bata sha wahala ba wajen masu gadin gidan, kasancewar tace itaɗin ƙawar Lubna ce. Tai kuma sa’a Lubna na gida bata fita ko inaba.
      Tana tsaye jikin motarta Lubna ta fito tare da mai bama fulawar gidan ruwa da yaje ya sanar mata, kallan kallo kawai sukema juna, dan babu wanda yasan wani a cikinsu, sai dai kasantuwarsu wayayyu duk sai suka basar wajen yima juna murmushi.
       Suhailat tace, “Sorry dear, baƙuwa babu sanarwa, baki kuma sannni ba”.
     Murmushi itama Lubna tayi mata, “Babu damuwa, koma dai minene mu shiga daga ciki”.
      “Thanks”. Suhailat ta faɗa a hankali.

         Tunda suka shigo gidan Suhailat ke jinjina tsarinsa, dama tasan ai Basiru bazai taɓa aurar macen da babu manda a gidansu ba, dan shi kaska ne raɓu mai jini.
     Sai da aka gama ajiye mata kayan motsa baki sannan Lubna ta zauna suka sake gaisawa, Suhailat da ke shan lemo ta kalli Lubna da fararen idanunta, “Nasan zakiyi mamakin ganina, gashi baki sanniba, Sunana Suhailat, tun daga kd nayo takakkiya zuwa gareki. Ta sanadin alaƙar da wani banza ya haɗamune nazo nan”.
      “Wake nan?” lubna ta tambaya tana tsare Suhailat da idanu.
    Murmushi Suhailat tayi na takaici, kafin ta ajiye kofin hannunta tana gyara zama, tace,
    “Ba kowa bane face Basiru”.
    Tuni murmushin dake kan fuskar Lubna ya gushe gaba ɗaya, ta yunkura zata miƙe Suhailat ta dakatar da ita ta hanyar faɗin,
      “Ni ya cancanta na fara irin wannan fushin Lubna, amma dana zauna nai tunani sai naga bazai amfaneni da komaiba, domin kuwa zan ƙare rayuwatane inayinsa batare da wanda nakeyi dan shiba ya sani balle yasan na tsanesa, zuwa yanzu ba zuciyar fushi bace a ƙirjina Lubna, ta ɗaukar fansace, wannan dalilinne yasani zuwa gareki domin mu haɗa hannu wajen maida murtanin bashin gaba. Badan Basiru zai gagareni bane ba, sai dan nasan irin tabon daya barmin kema shine ya barmiki, kenan ya dace mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tabbatar masa da mata ba hularsa bace da zai ɗauka a sanda yaso yakuma aje a lokacin da yaso, amma in babu ra’ayin hakan a tare dake karki damu zan koma, na ida cikar burina, na gode da tarbar mutunci da kikaimin sosai, sai gani na biyu…….”
        “Indai wannan shine burinki nima shine nawa, dan nayi alƙawarin sai Baseeru ya ƙwankwaɗi madarar baƙinciki fiye da wadda ya bani na ɗanɗana, na tsani cin amana, hakama yaudara”. Lubna ce mai maganar a fusace.
    hakan ya saka Suhailat dakatawa daga shirin fitar da takeyi, ta juyo gaba ɗayanta tana kallon Lubna fuskarta shinfiɗe da murmushi, ƙaramin ɗan yatsanta ta miƙa mata, Lubna ta tako har gabanta suka ƙulla tareda sakarma juna murmushi.
      Komawa sukai suka sake dasa hiran basiru da rayuwar da kowa tayi dashi, anan ma Lubna ke sanarma Suhailat ta haihu da Basiru ita, yarinyar tana nan Amal.
       Sosai Suhailat ta tausayama Lubna da yarinyar kanta da batai dacen mahaifiba.
     Sun yanke hukuncin yanda zasu samo Fannah itama, dan daga baya bayan rabuwar Lubna dashi itama takejin ya auri Fannah, a tarema ya sakesu.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           Tunda ta fito daga lecture ta hangesa tsaye jikin motarsa, sai dai ta yauma ba irin ta shekaran jiya bace, sanye yake cikin suit kalar sararin samaniya, ƙyaƙykyawane ajin farko, sannan ɗan gayu, yau kwanaki huɗu kenan daya fara bibiyarta, sai dai sam taki saurarensa, amma bawan ALLAH yaƙi yin zuciya.
       Ta ɗan sauke numfashi tareda cigaba da takowa inda yake, dan yau taji a ranta zata sauraresa taji da wacce yazo shikuma.
     Sanye take cikin atanfa ruwan fauda siket da riga, sai hijjab ɗinta da kaɗan ya wuce cinyarta mai hannu shikuma ruwan madara, tayi ƙyau sosai dukda kamar kullum babu kwalliya a fuskarta.
    Tunda ta dososhi murmushi ya faɗaɗu akan fuskarsa, yarinyar ta haɗu ta ko ina, kallo ɗaya ta wuce da dukkan tunaninsa, gata da jan aji, dan itace mace ta farko a rayuwarsa da zaice yanata bi tana yarfashi amma yakasa yin fushi……
     “Assalamu alaika” zazzaƙar muryarta ta rangaɗa masa sallama.
      Eyeglasess ɗin fuskarsa ya zare yana murmushi, “Wa’alaikissalam gimbiyar mata, Wannan juma’a tazo min da babban alkairi, ga farin wata gab da ni yana haska min hanya”.
     Basarwa Ummukulsoom tai tamkar bata fahimcesaba, sai ma cewa da tai, “Wai kai bakayin zuciyane?”.
     “Zuciya kuma Babie? Ai akanki ki ɗauka banida zuciya irinta fushi”.
      Murmushi Ummukulsoom tayi ba tare da ta shirya ba, ta ɗauke kanta gefe kawai tana faɗin, “Nifa bana zama inuwa ɗaya da maza”.
    “Babie aini kece inuwa ta, dan ALLAH a tausaya mini abarni na shiga daga ciki, zafin rana na gasani, sanyin kuma da ya kasance ba na inuwarkiba cutarwace a gareni, aji dani raɓar ƙankara tana neman daskarar da jinina”.
      Ɗan kallonsa tayi kafin ta ɗauke idanunta, “Zan duba naga idan ka cancanta”.
     “Yeeees!” yafaɗa yana dunkule hannusa.
    Hakan sai ya bama Ummukulsoom dariya, tai murmushi mai kayatarwa da har ya bayyana jerarrun haƙoranta farare tas.

    Duk yanda taso ƙin binsa saida ya kalameta da daɗin baki ta amince ta shiga motarsa.
     Suna tafiya yana janta da hira game da kanta, a taƙaice taita bashi amsa, yayinda shikuma yake sanar da ita wanene shi kai tsaye.
       A gate ɗin farko tace ya ajiyeta, dan tasan baza’a barsa ya shiga Barrack ɗinba.
     Fitowa yay da kansa ya buɗe mata ta fito, harda wani ɗan sunkuya mata irin na girmamawa, hakan ya sata sakin ƴar siririyar dariya……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button