WUTSIYAR RAKUMI 35
*_NO. 35_*
………..Tun daga wannan ranar abubuwa suka nemi rikicema Yaa Amaan, yay bala’in sakama Ummukulsoom ido, yayinda ita kuma ta samu hanyar muzgunama zuciyarsa da salo kala-kala, ita duk tana yine
saboda fahimtar kamar ya ganeta, duk dama yana yawan tafiye-tafiye shida Attahir, amma dukda haka kowanne motsinta ana sanar masa ba tare da ita tasan ana bibiyar rayuwar taba.
Karatu kam ta maida hankalinta sosai, fatanta ta samu dukkan nasara, ƙawayenta kam basa wuce abokan karatun ta, duk wanda kuma ya tareta da kalmar so takan nuna masa karatune ya kawota. Ita da Umar kam, kamar wasa sai soyayya da shaƙuwa ta shige tsakaninsu, ita Ummu ma tun tana masa komai da wasa har lamarin yafara shiga jikinta, sai dai wanda ya nutsune kawai zai fahimci shaƙuwace a ranta ba soyayya ba.
Sai wani lecturer ɗinsu Abdul-wahed shima fa ya kafa ya tsare, Bahaushe ne amma girman lagos, kuma saurayi da dukkan mace tagani saita ƙyasa, sam shima mutum ne da baya harkar mata, ko a makarantar ƴammata suna shakkar kaimasa wargi harma da mazan, amma tunda ya ƙyallara idonsa akan Ummukulsoom sai labarin ya canja salo, tun ana ƴar kallo hardai ranar yasa aka kira masa ita taje ta samesa har office.
Ita kanta sai da abin ya bata mamaki, dan shi mutum ne da mafi yawan ɗaliban kance yanada shegen girman kai, ita kanta ta jefesa da wannan sunan, amma a yau sai gashi a gabanta yana fara’a da jaddada mata kalmar wai yanason ta zama wata sashe ta rayuwarsa, gaba ɗaya kuma ya ɗaureta da jijiyar wuyanta akan zai jirata har sai ta kammala, sannan kuma bazasu ringa wani mu’amula a cikin makarantar ba, idan yana buƙatar ganinta zaizo har gida ya sameta, shima zuwa gidan ba yanzu ba, sai sun gama sabawa ta waya tukunna.
kasa koda motsi tayi, harya ɗauki wayarta ya saka Number sa ya kira tasa shima yaga tata.
Har Ummukulsoom ta dawo gida abin na dama mata lissafi, guy ɗin yakai dukkan yanda mace bata zato, dan harga ALLAH itadai anata tsarin ya haɗu, kuma sai akai sa’a zuciyarta take kai kawo akan lamarinsa.
Bily dai kasa daurewa tayi saida ta takura mata ta sanar mata damuwarta.
“Ummukulsoom kuma ke kina sonshi kenan?”.
Ajiyar zuciya Ummukulsoom tayi, “To ni Bily mizan ce, danfa haɗuwa bawan ALLAHn nan ya haɗu……”
“Mtsoww, duk haɗuwarsa yakai Yaa Amaan ne, ke nifa ko wannan Umar ɗin haushinsa nakeji, nifa kullum fatana ki koma gidan Yaa Amaan, dan shine yafi dacewa dake ƴar lukutar Ummi”.
Duka Ummukulsoom ta zubama Bily a cinya, “Kefa banza ce, Amaan ɗin mi, wlhy Abdull ya fisa komai ni a wajena. aini yanzu na wuce da saninsa wlhy, kuma kibar kushemin Umari na, inason kayana, ni saurayi nakeso yanzu ba bazawari ba”.
Bily ta taɓe baki tana barin wajen, “gwara da kikace a wajenki, Umar wannan kuma matsalarki ce, insha ALLAHU babu wani mai kai kamar kwakwa dazai mallakeki sai Yaa Amaan, da kike ce masa bazawari kema ai itace”.
Haushi kamar zai kar zuciyar Ummukulsoom, da bily tasan ko sunan mutumin nan batason ji da wlhy bata sake ambatarsa a gabanta ba, sam ta tsanesa fiye da zaton kowa, ganin bily zata fice sai tai saurin maida murtani, “Koda nake bazawara duk wanda ya aura zai tabbatar da sabuwace dal a kwali, shiko ko aure yayi sai matar tace ya taɓa aure, babu kuma wani jawabin da zai mata ta fahimcesa”.
Haɓa bily ta riƙe tana bin Ummukulsoom da kallo, “Oh ni wai Bestie yaushe kika fetsare har irin hakane?”.
“Zo na faɗa miki”. Ummukulsoom ta faɗa tana shigewa bathroom.
“A’a nikam kinfi ƙarfina, bazaki iskantani ba wlhy”.
Murmushi Ummu tayi daga cikin bayi saboda jiyo maganar Bily.
★★★★
Da daddare duk suna falo suna kallo, Ahmad na gefe yana Homework saƙo ya shigo wayar Ummukulsoom, wayar bily ta miƙa mata, dan tana hannunta tana tura mata wasu apps.
“K cigaba kawai, maybe ma mara amfani ne”.
“A’a kedai karɓa, dan A-Waheed ne, inba hakaba na goge wlhy”.
Warce wayar Ummu tayi da sauri tana faɗin, “ƴar baƙin ciki ashe rabin numfashi nane”.
Maman Ahmad tai dariya itada Bily, sungafa wannan Abdul ɗin kamar yazo da ƙarfinsa, maman Ahmad batason shiga rayuwarta ne kawai, amma idan san samune kar Ummu tayi soyayya da kowa, fatanta takoma gidan Amaan, amma basuda hurumin cemata hakan, dan yanzu dai tanada ƴancin zaɓama kanta miji ko a addinance.
Ummu kam tashi tai ta bar falon sannan ta buɗe saƙon.
_Duniya babban wajene mai yawan al’umma da wasu halittu, sai dai zuciya ta fita faɗi, soyyayya kuma itace al’ummar zuciya, to ni tawa babu kowa a cikinta sai ke kaɗai gimbiyar mata_
*Naki UMA*.
Ummu ta maimaita saƙon yafi sau goma, sai murmushi take zabgawa, tai kissing wayar tana lumshe idanu, hundred percent A-waheed yayi.
Bata maida reply ba ta share kawai.
★★
Washe gari da taje makaranta koda ya shigo musu class ko a fuska bai nuna yama santa ba balle saƙonsa daya tura, hakan yasa itama ta basar tamkar batama gansa ba, ya gama ya fita abinsa.
Tun daga sannan Abdul-wahed yazama abokin hirar Ummukulsoom ta hanyar turo mata saƙo a kowane dare, ko fashin hakan bayayi, kullum kuwa akwai salon da massege nashi ke zuwa dashi, kafin aja wani lokaci yagama saye dukkan zuciyarta, sai dai sam maganar fatar baki bata haɗasu idan taje school, kuma bai sake kiranta Office ɗinsa ba, hakama a waya bai taɓa kiranta ba sai dai masseges da kullum baya gajiyawa.
Da farko abin ya fara damun Ummukulsoom, amma daga baya saita zauna ta nutsu, tareda da yimasa uzuri akan shikuma nasa salon soyayyar kenan, to aiko zata tabbatar masa ta fisa ƙwarewa.
Duk yawan masseges ɗin da yake mata bata taɓa masa reply ko sau ɗaya ba, hakan kuma baisa ya gajiya ba. Tsakaninta da Umar kuwa suna tare abinsu.
★★★★
Ɓangaren Amaan kuwa zuwa yanzu ko haɗuwa sukai da Ummukulsoom ko kallon inda take ba yayi, dan yakula raini na neman shiga a tsakaninsu, ya maida hankalinsa gaba ɗaya ga aikinsa, bama sa haɗuwa sai lokaci-lokaci, dan makaranta kan hanata yini a Barrack ɗin itama.
Yau ta kasance litinin, kamar yanda ya saba bakinsa ɗauke da azumi, tun 4pm ya baro office ya koma gida.
Sanin da Desmond yayi duk mafi yawan irin waɗanan ranakun yakanyi azumi sai yake tambayarsa miza’a masa na shan ruwa.
Yana falo kwance tunda ya dawo daga sallar la’ar, ba barci yakeba amma idanunsa na lumshe, desmond da tun ɗazu ya ke tsaye yana masa magana ya sake maimaitawa,
“Boss miza’a girka maka na buɗa baki?”. Yay maganar a ɗarare, dan ya lura a kwanakinnan abu kaɗan ke tunzura zuciyarsa ya hau faɗa.
Shiru kamar bai jisaba, sai kuma ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya tare da furzar da numfashi ya ɗago manyan idanunsa da suka canja launi daga farare zuwa sirkin jaa alamar gajiya na tattare da shi da barci, “Yau kunu nakeso, kaikuma gashi har yanzu ka kasa iyawa, barsa kawai zanje gidan Attahir ”.
“Ok Boss”. ‘Desmond ya faɗa yana barin falon, zuciyarsa cike da mamakin mike damun boss? A gaba ɗaya kwanakinnan yakuma zama shiru-shiru, rashin son maganarsa ya ƙaru, ga faɗa abu kaɗan zai fara juyema mutum masifa.
Waya ya ɗauka ya kira Attahir akan yau zaizo nan yasha ruwa, amasa kunun shinkafa da ƙosai na wake.
Attahir yay murmushi, cike da neman tsokana yace, “ALLAH sarki, wlhy harka bani tausayi, matsalar gwauro kenan ai”.
Tsaki Amaan yayi yana fadin, “Banza kawai magananne”.
Attahir ya kwashe da dariya, “Gwarani a magana na tsaya, wanda ya haɗa abubuwan da sukafi nawa fa? Shi minene sunansa?”..
“Kasa micrephone mana saika tambaya”. Yay maganar yana yanke wayar tareda jan tsaki.
Dariya Attahir ya kuma sanyawa yana janye wayar a kunnensa, ya kira maman Ahmad ya shaida mata danshi yana office bai koma gidaba.
Yamma lis Ummukulsoom ta dawo daga makaranta, lokacin su Bily na kicin suna haɗa abinci buɗa bakin Amaan da itama kanta Ummu ɗin, dan tana azuminne itama, amma na ramadan ne da bata rama ba sai yanzu takeyi.
Bata nemi kowa ba ta shige ɗakinsu itada bily, ruwa ta fara watsawa sannan ta fito, bata wani zaman kwalliya ba, sai mansu mai ƙamshi taɗan shafa sama-sama da ƴar khumra tasa wando da riga masu taushi marasa nauyi, sam kayan basu kama ta ba, dan Ummi ta hanasu saka ƙananun kaya masu bayyana jiki, sai akai sa’a ra’ayin Ummi dana Attahir yazo ɗaya.
Tana shirin fitowa Yaa Zaid ya kirata, murmushi kawai tai tareda ɗagawa suka gaisa, har tazo falo ta zauna suna wayane, dama ƙa’idane kullum saiya kirata suyi hira, wani lokacin hirar tai tsawo wataran kuma Ummu ta gajarta ta da cewar zatai karatu.
Ahmad ne da yadawo daga islmiyya ya shigo yana kuka, Ummukulsoom ta yanke wayar tana kallonsa, “Oga Amadi lafiya shigowa gida da kuka kuma?”.
Zuwa yay jikinta ya zauna, “Aunty”.
Ta amsa da “Na’am Amadi angon Ummi”.
“Kinga dai Chizober ce ta dakeni, wai danna bi takan wasansu”.
“To banda neman rigima Amadi inakai ina taka musu wasa? Kaida ka dawo daga islamiyya maimakon kai maza kazo gida ka kawo ladanka saika tsaya ƙofar gidan su chizober, hakan babu ƙyau kajiko, karka sake, ita kuma zanje na kaima Momynta kashedi idan ALLAH ya kaimu gobe kaji”.
Cike da murna Ahmad yace, “Eh auntyna, ALLAH ya kaiki maka sau 100”.
Dariya Ummukulsoom tayi tana faɗin “Amin Ahmadi na”.
Maman Ahmad dake bayansu tace, “Wai dama kin shigo?”.
“Wlhy na shigo aunty, tiɓis nake, banason shigowa kicin ɗinnna naga abinci yunwata ta ƙaru shiyyasa”.
“Hhhh anya wannan azumin zai kai labari kuwa?”.
“ALLAH aunty zai kai insha ALLAHU saina gamashi, saura biyu fa ya rage yau idan nakai uku”.
“To ALLAH ya taimaka, shiyyasa nayi nawa da wuri na huta”.
Miƙewa Ummu tai ta nufi kicin ɗin itama, “Ai kinyi dabara wlhy Aunty, nima a time ɗin muna tsaka da exams ne wlhy, shiyyasa bana ko sittar shawwal banyiba fa, ALLAH dai ya bamu ladan niyya”.
“Amin” Bily ta karbe tare da ma Ummu sannu da dawowa.
Suna a kicin ɗin har aka kira sallar magriba, Ummu sai tambayarsu take wai wannan uban abincin da akayi duk wa zai cisa? Ko suma duk shi zasuci matsayin abincin dare?”.
maman Ahmad tace, “Kusan hakan za’ai, dan bazamu bari kici dadi ki fimu kibaba”.
Murmushi Ummukulsoom dakecin Dabino tayi, ta ɗauki kofin ruwa tasha sannan ta fice zuwa ɗaki yin sallah.
★★★★
Ana idar da sallar magrib suka nufo gida shi da Attahir, Bily kawai suka iske a falon dan tana fashin salla, tai musu sannu da zuwa a zuciyarta tanama Ummukulsoom dariya, ashe Yaa Amaan ne baƙon da Maman Ahmad tace zaizo shan ruwan, lallai yau akwai kallo.
Shidai Amaan kai tsayema dani ya nufa, dan ba yaune ya fara zuwa shan ruwa gidanba idan yay azumin litinin da alhamis, ba komai ke kawosa ba kuma sai abinci irin namu na hausa, dan desmond ba iyawa yayiba, koya kamanta yi bayayi masa daɗi, shiyyasa inhar yana bukata baya cutar kansa saiya ce maman Ahmad tai masa, itako bata taɓa gajiyawa ba da yimasan.
Matsowa Attahir yay kusa dashi yana faɗin, “Ajiwa nikam dai bara na watsa ruwa”.
Kansa kawai ya ɗaga masa ba tare da yayi magana ba, sai ƙoƙarin buɗe kwanikan saman dani din yakeyi hankalinsa kwance tamkar a gidansa.
Yana ƙokarin zuba kunu a kofi Ummukulsoom ta fito daga dakin tana waya da Umar dake mata barka da shan ruwa, sam bata lura da shiba, sai dai tabbas taji ƙamshin turarensa, hakan kuma baisa ta kawo a ranta yana kusa ba, kujera ta ja ta zauna sunayin sallama da Umar.
Tunda ta fito shikam idonsa ya sauka a kanta, harta ƙaraso yana mata kallon ƙasa-ƙasa, amma sam babu wanda zai fahimci hakan sai shi da yakeyi, kusan gagararsa zuba kunun yaso yi, sai dai ya dake harta karaso wajen, yanda take magana ƙasa-ƙasa a wayarne yasa baiji mi take faɗaba, amma hakan ya soki zuciyarsa sosai.
Ajiye wayar Ummu tayi tana murmushi mai sauti, sai dai tana ɗagowa da nufin ɗaukar kunu ta zuba idonta ya sauka a kansa, ya wani basar yana motsa kunun da ya zubama sukari tamkar bai gantaba.
Tuni fara’ar fuskarta ta ɗauke, a ranta tana mamaki shikuma miyazo yi? Harda yima mutane ɗare-ɗare a dani, aiko ta ɗau alwashin bazata tashiba, dan haka itama ta basar tamkar bata gansaba, ta ɗauki kunun dake gabansa ta zuba tana kuma wani ciccije fuska ita a dole kar a kawo mata raini.
Duk motsinta yana kallonsa ta ƙasan ido, jira yake yaga zata gaisheshi.
Kununta ta gama zubawa ta ɗiba ƙosai tare da farfesun kifi ta fuske abinta tanaci hankali kwance, harda ma yanga ta neman magana, babu wanda ya kula ɗan uwansa a cikinsu, sai dai kowanne yana satar kallon ɗan uwan nasa ta gefen ido.
Saƙo ya shigo wayar Ummukulsoom, hakanne ya sata ɗaukar wayar dan tana ƙyautata zaton A-Waheed ne. Ilai kuwa shine, ta buɗe saƙon kamar haka,
_Safiya ta shuɗe, rana ta gushe, yammaci ya wanzu, alkairin ALLAH yakai gareki ma’abociyar kamewa, barka da shan ruwa._
*Naki UMA*
Lallausan murmushi Ummukulsoom ta saki, wanda yakusa sumar da Amaan dake satar kallonta, ya lumshe idanu ya buɗe akanta a hankali.
Ummu kam da batasan yana yiba reply take ƙokarin maidawa A-Waheed, dan yau taji a ranta zata fara kulashi, jan ajin ya isa haka.
*Kaima Abincin ALLAH ya tabbata a gareka, tare da alkairin da baya yankewa har ƙarshen numfashi.*
_Kulsoom_
Tana gama turawa takuma sakin wani murmushin, jitai kawai an take mata ƙafa da ƙarfi, ta matse fuska saboda zafin daya ratsa har cikin ƙashinta tare da kallonsa, dan tasan sarai shine, kuma yaki ɗaga ƙafar, saima kara murzawa yake tsabar mugunta, ya kuma basar tamkar baya aikata komai.
Filas ɗin kunu ta ɗauka ta diba kaɗan mai azabar zafi, ba tare da ya kula da abinda ta keba dan waya yake dannawa da hannu ɗaya, ɗaya kuma yana rike da cokalin da yake shan farfesu, ta zuba masa kunun a kan hannun dake riƙe da cokalin.
Da sauri ya saki cokalin tare da wayar yana janye ƙafarsa akan tata tare da yarfe hannu saboda azabar zafin kunun data shigesa.
Tuni Ummukulsoom ta mike tabar wajen, ko waiwayensa batayiba ta koma falo dariya nacinta.
Da kallo kawai ya iya binta yana cigaba da yarfa hannun, wajen har yayi jajur abinka da fari……
“Ajiwa lafiya?”. ‘Attahir daya karaso wajen ya faɗa yana kallonsa’.
Sam fuskarsa babu walwala matuƙa, alamar yaji zafin abinda tai masa har cikin ransa, murya a dakile yace ma Attahir ƙonewa yay.
Hannun Attahir ya kama yana kallo da mamaki, “Ƙonewa kuma Ajiwa? Garin yaya haka? ga wajen haryay ja kamar zai tashi”.
Baice ma Attahir komaiba, sai zuciyarsa dake ƙara wani kumbura saboda takaici.
Kira Attahir ya kwalama Ummukulsoom dake zaune a falo, ta amsa tana tasowa tamkar ba ita ta aikata tsiyar ba.
“Samo ƙankara a kicin”.
“To” ta faɗa tana harar Amaan da shi bama ita yake kalloba.
Saida tasha dariyarta a kicin sannan ta kawo ƙanƙarar, ta iske maman Ahmad da Bily ma sun fito, Handkherchief ɗin da Bily ta kawo wanda na Ummukulsoom ɗinne Attahir yace ta amsa ta zuba ƙanƙarar a ciki.
Saida ta harari Bily sannan ta amsa tayi yanda Attahir yace, Amaan dai duk yana jinsu, amma baiko tankaba, ko sannu dasu maman Ahmad suketa jera masa kai kawai ya ɗaga musu.
Attahir na shirin amsar ƙanƙarar yay masa sai kawai sukaga ya mikama Ummukulsoom hannun.
Da wani uban haushi Ummu ta kalli hannun sannan ta kalli Attahir, amma sai yace mata “zauna ki saka masa to”.
Fuska ta ƙwaɓe tamkar zatayi kuka dan takaici amma sai Attahir ya ɗauke kansa, danshi yaji a ransa akwai abinda ya faru, ba hakanan Ajiwa ya ƙoneba, kuma tunda ya nuna Ummu zata saka masa ƙankarar ya tabbatar akwai dalili, dan yasan halinsa sarai.
Ganin babu wanda ya goyi bayantane yasata zama idonta cike da ƙwallar takaici, da mugunta ta danna handkherchief ɗin dake ɗigar da raɓar ƙankarar akan hannunsa, amma ko motsi baiyiba dukda yaji zafi kuwa, haka taita danna masa cike da mugunta har ƙanƙarar ta kusan gama narkewa, hannunsa ya janye, batareda kowa ya lura ba ya ɓara mata kunun gaban Ahmad da aka zuba mawa yanzu a hannu itama.
Tana ƙwalla ƙara yana mikewa cike da basarwa, babu wanda zaice shiɗinne ya aikata.
Duk kanta sukai suna tambayar lafiya, hawayenta ta goge ta ɗago ta kalli Amaan dake shirin wucewa, kallon ido cikin ido sukaima juna wanda babu wanda bai jisaba har cikin jininsa ita da shi.
“Maman Ahmad na gode sosai, ALLAH ya raya Ahmad ya kawo ƙannensa masu albarka, Attahir na wuce”.
Kallonsa sukai, yayinda hankalinsu ke kan Ummukulsoom, bai jira amsar kowa ba ya fice abinsa, hakanne ya saka Ummukulsoom saurin faɗin, “ALLAH ya saka min kuma”.
Wani murmushin da bai shiryama zuwansa bane ya subuce masa, ba tareda ya juyoba ya karasa ficewarsa.
Ita da yake ma kunun ya huce nata bai tashi ba, sai dai zafi da yake mata.
“Ummukulsoom wannan ya tabbatar min da kece kika ƙona Ajiwa ko?”. Attahir ya faɗa yana tsareta da idanu.
Baki ta ɗan tura gaba tana share ƙwalla, “Yaya shinefa ya fara takani”.
“Ke kuma sai kika ƙonashi ko? maganinki ai, na kula sam baki gama sanin halin Ajiwa ba, idan har kikace ta wannan hanyar zakibi ki ringa masa abu wlhy wahala zakiyita sha, dan ba raga miki zaiyiba”.
Ita dai batace komaiba, sai maman Ahmad daketa mata sannu, bily kam tanajin tushen zancen saita hau dariya, dama tayi zargin hakan.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Da ƙyar Baseeru ya samu Meenal ta barsa ya tafi ɗilau gaida su baba, yaso suje tare tace, bazataje ƙauye ba wlhy, shidai daya zamarma tilas yaje, sati ɗaya kuma ta bashi kacal.
Babu tunanin komai ya amince, sai kace itace mijin shine matar.
Tsananin son da yake matane yasa ko kaɗan baya iya ƙetare maganarta, ga kuma daula daya samu kansa a ciki wadda baya fatan ko a mafarki ta yanke masa.
Yauma dai kamar ko yaushe yara bin motar sukeyi tamkar yanda suka saba aduk lokacin da bakuwar mota ta shigo ƙauyen, da murnarsa ya shiga cikin gidansu da yagama lalacewa, katangar gaban gidanma ta faɗi sai danni akayi na itacen geza, sai dai kuma jikinsa yay sanyi ƙalau tunda yay sallama a cikin gidan, dan ya iske tashin hankalin baba kwance babu lafiya sosai, dan haka ya rikice, baiko zauna hutawa ba suka ɗakkoshi zuwa zaria asibiti………..✍????
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
*_ƴan Niger kuma_*
_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*
*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*
_TA NUMBER;_
*+22795166177*
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????