NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 33

*_NO. 33_*


     ………“Yaya kin ɓata ɓat, baba yasa anyi   nemanki daga baya har an gaji, wani yaro Sallau har danfarar sa yay ya saida ƙaramar gonarsa ta bakin fadama ya bashi kuɗin akan wai ya
ganki a Legas zai je ya kawo ki gida, amma yaron nan tunda ya tafi bai sake dawowa ɗilau ba sai da baba ya rasu”. ‘Gwaggo hinde ta ƙare maganar da fashewa da kuka’.
     Itama Hajiya yaya kukan takeyi jin Baba ya rasu, “Hindatu kina nufin ALLAH yay ma baba rasuwa?”.
    “Eh yaya baba yarasu tun bayan Auren wannan ƴar (Inna Laraba, bata faɗar sunanta saboda ƴar fari ce), bayan tafiyar ki a zuwan da kukayi baba ya ɗau zafi sosai, ashe Iyami ce ta tunzuro shi, sai da inna haule ta dawo daga tafiyar da tayi katsina, kinsan sanda kukaje baku isketa ba, to bayan dawowarta taji abinda ke faruwa tazo har gida ta sake tambayata, ban ɓoye mata komaiba na sanar mata, itace taje ta samu baba ta warware masa komai har yanda kuka gudu, aiko baba yayta kuka yana dana sanin korarku da yayi, tunda ga nan yashiga nemanki, itakuma iyami ya saketa, amma sam sai ba’a daceba harya kwanta ciwo, kusan shekararsa ɗaya yana jiyya ALLAH yay masa rasuwa, sai dai yace ko bayan ransa aka ganki a shaida miki ya yafe miki duniya da lahira, kema ki gafarcesa keda mijinki”. Kuka sosai Hajiya yaya da Gwaggo hinde sukeyi, sai da ƙyar suka tsagaita, Gwaggo hinde ta nuna Ummukulsoom da itama ke kuka tana faɗin, “Wannan jikarmu ce, ɗiyar Hassana ce data bari, sunanki aka saka mata”.
      Hajiya Yaya ta kalli Ummukulsoom tana murmushi da zirar da hawaye a lokaci ɗaya, “ALLAH sarki, ashe Hassana rabuwar har abada mukayi da ita daga ita har baba, na gwada zuwa ɗilau yafi a ƙirga, amma kalaman baba ke hanani, ALLAH ya gafarta musu, Ummukulsoom zonan kinji”.
     Matsowa Ummu tayi ta shige jikin Hajiya yaya dake hawaye har yanzu, ji take tamkar tana tare da ɗiyarta Hassana.
    Bayan an sake samun nutsuwa Abba yay gyaran murya tareda jaddada godiyarsa ga ubangiji da ban haƙuri ga iyayen nasa, ya ɗora da faɗin, “Ubangiji sarkin hikima, ashe ni ƴata nake riƙo ban saniba, nayi murna da hakan sosai nakuma ji daɗi, a ƙiyasi mahaifinmu ya riga ƴar uwata rasuwa, dan haka tana da gadonsa kenan, dukiyar daya bari yazama ni kaɗaine magajinsa a yanzu hakan ya canja, dole za’a fiddama Hassana haƙinta a damƙasa ga ɗiyata mai sunan Hajiya tunda itace magajiyarta”.
     Ummu na hawaye tace, “Ni dai A’a Abba na yafe maka, ganinku ya fiyemin komai”.
     Murmushi Abba yay yana faɗin, “Mai sunan Hajiya ai haƙƙine, dolene kuma a fitar, ke dai ALLAH yay miki albarka, a yanzu saimu fahimci kuma duk abinda ALLAH ya jarabci bawa dashi badan baya sonsa baneba, na tabbata kinshiga ƙunci mai yawa sanadin matsalarki da Fodio, to ashe wani babban mabuɗin alkairinne ke bibiyar ki, ƙila da hakan bata faruba da wannan sirrin bazai taɓa buɗuwaba, har sai mu bar duniya da tabon a ranmu”.
    “Wannan gaskiyane Abubakar, dolene mu ƙara nuna godiyar mu ga ALLAH, kaima Attahiru ALLAH ya saka maka da alkairi, domin girman da ALLAH ya baka ka riƙe shi, ALLAH ya sake baka wuyan ɗauka”.
     Da amin kowa ya amsa, daga nanfa aka ɓarke hira, zuciyar kowa ƙal da farin ciki.
     Abba kam ai neman Dad yay a waya ya zayyane masa abin farin cikin daya faru.
       Rasama mi Dad zai faɗa yayi saboda al’ajab da farin ciki, a lokacin ya baro gidansa zuwa gidan hajiya yaya.
      Hajiya yaya sai ƙara zuba masa albarka takeyi, domin ƙyautatawar sa akan na ƙasa dashine da ƙyaƙykyawar zuciyarsa ta zama sanadi, da ace bai haɗa Ummukulsoom da Fodio aure ba da duk hakan bata kasanceba. Hajiya yaya sai kuma ƙarfafa musu gwiwa take akan su cigaba da zama masu adalar zuciya, domin hakan basusan alkairin da zai janyoma rayuwarsu ba.
    A dai ta ƙaice ranar saita zama anyi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan, dan sai dare su Abba suka koma gida, aka bar Gwaggo Hinde da Hajiya yaya suna cigaba da hirar zuminci.
      
      Musalta muku farin cikin da Ummukulsoom ta tsinci kanta a cikima ɓata lokacine, amma kowa ya ganta yasan yau ɗin ta musamman ce, ga albishir da Dad yay mata na komawarta makaranta nanda sati ɗaya, zataje Law school, ta birnin ikko (Lagos) ta ƙarasa shekara ɗayanta da zai tabbatar da ita a matsayin cikakkiyar Barrister..

         Sai daren ranar Attahir yasan Amaan baya ma garin ya koma Lagos, murmushi ƙeta yayi dan kuwa abinda ya gudar mawa zaije ya iskeshi, da Ummukulsoom zasu tafi Lagos, kuma a gidansu zata zauna harta kammala. 


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

               Su baseer ansha shagalin bikin rantsarwa, yaci gayu yanata basarwa sai kace shine ɗan gwamna ɗin, danma Meenal ta kafa ta tsare saboda kar yayma wata mace magana….

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         Zaune suke a katafaren falon gidansu, ta canja tamkar ba Suhailat matar baseer ba, ta kuma cika da girma dan batafi sati uku da dawowa ƙasarba ma, tana Germany karatu, waya take latsawa hankalinta kwance, yayi da su Mom ɗinta ke kallon labarai.
    Kamar ance ta ɗago sai ta kalli TV jin Daddynta tana kwarzanta bikin rantsarwar dayake shima yaje saboda mahaifin Meenal abokin sane.
    Ƴar zabura tayi tana kuma ware idanunta akan tv n, “Kam bala’i, Baseer!!”.
      Atare Mom da Daddyn ta suka kalleta tareda cewa, “Baseer kuma?”.
       “Ƙwarai kuwa Daddy, wannan Baseer ne ya gama magana a matsayin surukin gwamna, Daddy yaran Alhaji Ɗalha nawane mata?”.
     “Eh to, kamar guda biyu ne, ɗaya ce kuma tai aure shekara kusan biyar data shige, kinsan anyi bikin lokacin bana nan shiyyasa ban jeba sai Salman na wakilta”. 
        “To aiko lallai Abba shegen nan ne Baseer mijin”.
       “Ya zakice haka Suhailat? Tayaya kika san haka?”.
     “Mom ko shekara nawa nayi banga Baseer ba na gansa saina ganesa, Daddy kana da
Invitation ɗin bikin?”.
      “Za’a iya samu Suhailat, amma fa kinsan kusan shekara biyar kenan, ganesa sai ansha wahala”.
     “Daddy bazanji wannan wahalar ba, zanje na duba inda kake tara invitation card ɗinka yanzu nan, dan rayuwar yarinyar tana cikin haɗari, na tabbata itama ba sonta yake ba, kamar yanda yay min zai mata ya gudu”.
     “Gaskiyarki kuma Suhailat, kiyi dukkan binciken daya dace, inhar shine kam ya kamata mu fargar dasu”.
    “Insha ALLAHU kuwa Daddy na, nagode da goyen bayanka a gareni”.

        “Amma Alhaji inaga ya kamata kasan mi Suhailat zata aikata ma yaronnan, kar tunanin ɗaukar fansa ta sakata aikata abinda zamu dawo muna dana sani, kaga dai bikinta kwana kaɗan ya rage, ni dama za’abi ta taune da an barsa kawai duniya ai makaranta ce, zai haɗu da daidai shine a cikinta”.
     Murmushi Daddy yayi yana kallonta, “Karki damu a duk motsinta zan saka idanu, amma batun a barsa ma bai tasoba, dan kingansa fa yanzu a matsayin sirikin gwamna, zuwa nan gaba ina kike tunanin zai kutsa? Sannan bamusan su kuma da wace fuska yaje musu ba, irin waɗanan idan ba’a daƙilesu ba,  suke zamewa al’umma wata babbar fitina yayinda ALLAH ya basu wata dama ta mulkin ƙasa”.
     “Eh to hakane kuma Alhaji, ALLAH dai ya shiga tsakanin nagari da mugu, dankuwa yaron nan ya bar mana tabo mai girma, danma ALLAH ya taƙaita babu rabon ƴaƴa a tsakani”.
      “Wlhy kuwa Hajiya”.

       Yayinda suketa tattaunawa Suhailat nacan tana bincike, ganin zata wahala kafin ta gani saita ƙyale komai ta fito.
       Daddy dake kallonta yace, “Kin gansa?”.
     “A’a daddy, wannan zai zama mai wahala, ga shawara mana”.
      “Ina saurarenki auta”.
    “Daddy muje musu gaisuwar taya murna ta musamman dukkan iyalanka, ta wannan hanyarne kawai zan samu haɗa ƙawance da ita”.
      “Eh to kinzo da shawara, ki bari komai ya lafa zanyi tunani”.
       “Yauwa my sweet Daddy na, ALLAH ya ƙara yawancin kwana”.
     Dariya sukayi shida Mom.
    Itako ta fice zuciyarta fes, lallai Baseer yanzu ne za’ai karon, munafiki kenan mai fuskar zalunci,  mai ƙyan ɗan maciji. dolene ta nemo abokansa su Najeeb, ta hanyarsu tasan zata samu bayanai na musamman insha ALLAH.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            Wannan karon kam baba har gidan Alhaji Abubakar yazo shida inna harira, daga can suka ɗunguma zuwa gidan hajiya yaya, inda akaita haba-haba dashi, domin kuwa surukine.
     Ya girgiza shima dajin labarin nan, duk da dai yaɗanji wani abun tun da ƙuruciya gameda hajiya yaya, amma kasan tuwar bata garin sai yazam komai an manta dashi, har ƙwalla yay daya tuna da matarsa abar alfaharinsa Ɗahara, wadda ashe sunanta na asali Hassana. 
         Kwana biyu da zuwan baba suka ɗunguma zuwa ɗilau su duka gidan, har hajiya yaya.
     Kuka dai ta shashi, ƙalilanne waɗanda ta sani suka rage a raye, sai waɗanda tabari suna ƙanana, suma yanzu duk sun tsufa da yawansu, dan danan ƙauyen ɗilau ya ɗauki sabon salon labari, su Ummukulsoom kam ansha yawo, dama tana kewar garin sosai, ta daɗe batayi kwanakin nanba.
        
        Komai na tafiyar Ummukulsoom ya gama kammala, dan haka suka baro ɗilau aka bar hajiya yaya acan akan itafa saita more zata dawo. sosai take ɗoki akan ganinta garin haihuwarta, wanda ada aka haramta mata shigarsa a shekarun baya.
     Su dai su Ummukulsoom kd suka dawo sukai shirin tafiya legas.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button