Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 47-48

🅿️ 47&48

……tunda baffa idi yafara mgn Aysha batace komaiba”gabanta nata wata iriyar fad’uwa”tana tunani aranta wannan lokacin bazata hak’ura ba” tabari azalinceta ba”guduwa zatayi kawai gun ummanta”sbd bazata lamunci amata auren dole ba….bakijine?”

Inaji baffa”amma waye zaka auramun?”

Kinsanshi Alh nura ne”ina tausayinki kina marainiya”da fiddausi yakeso nace garadai ke “kinga kin huta nima na huta ko?”

fashewa da kuka Aysha tayi tace”.wlh banisonsa bana k’aunar sa”sbd ba mutumin kirki bane”kuma kasani kaima”mena maka haka baffa?”wlh Inda fiddausi ce Agidanmu nasan Abbanah bazai tab’a yimata haka ba….

Lallai wuyanki yayi k’wari”tunda ina mgn kinayi”kina maidamun murtani ko?”sbd ke kinzama y’ar iska”, to bari kiji aure dole saina miki”kuma fita keda yinta saidai idan za’a fito dake akaiki gidan mijin ki….

wlh banason sa…..wata iriyar haura yakaiwa Aysha da k’afa”yacire takalminsa yafara dukanta dashi”ya fisge baby nokia d’inta yasaka aljihu.”ta dinga ihu da kururuwa”sulemanu yashigo d’akin”aikuwa baffa idi yace”.yazane Aysha da belt”

babu tausayi aransa yafice”sulemanu yasameta da belt”tun tana kare kanta”har bata iyawa”duk yafasa mata jiki”saida goggo sa’a ta shigo tace”yak’yale ta tukum yabarta…

duk mai tausayi yakalli Aysha dole ya tausaya mata”gaba d’aya takasa motsi”kuka takeyi Ahankali na tausayin kanta da rayuwarta”

Jikinta sai radad’i da zugi yakeyi”ta juyo muryar baffa idi na cewa kar abarta ta fita ko ina”kasancewar ba gida yake kwana”

sulemanu yace”.tazo ga hanya ta gwada fitar jikinta yagaya mata”

duk Aysha naji ta kasa tashi”dandanan zazzab’i da ciwon kai yarufeta”

sai kusan 1na dare tasamu zazzab’in yasauka”taje tayi alwalah tarama sallar isha’i”ta had’a da nafilfili”tana sallah tana kuka”gwanin ban tausayi”

Idanuwanta sunyi jajir sun kumbura sbd kuka”
yadda taga rana haka taga dare” duk damuwar dake ranta amma dr sadeeq nanan aranta tana tuna fishin dayakeyi da ita….

Da misalin k’arfe 2 na dare”tsatstsaye suke acikin wani d’aki dogo”da bak’ak’en kaya ajikinsu” su kusan 12 duk maza”suna sanye da yadi baki k’irin da jar hula”sun shafe fuskarsu da wani abu kamar jar powder”

Alh nura shine a farko sai honorable lawal”agefensa baffa idi ne dasauran y’an k’ungiyarsu”

wata k’waryace a hannun honorable lawal”yakafa kai yasha jinin dake ciki”kafin yamik’awa Alh nura”bayan yasha yabawa baffa idi shima yasha…..

Bayan kowa yasha suka zuba magani acikin garwashin wuta dake d’akin ajiye”

atake d’akin ya gauraye da hayak’i”atake wani abu babba yabayyana atsakkiyar su
“Anan kuma dodon tsafinsu yafito acikin abun da yayi tsaga”bayan yafito abun yab’ace”

Duk’awa sukayi su duka 12″cikin muryar sa ta dodanni yace”.idi mutumin daka bani” jininsa baya shawuwa(ma’ana wanda aka badan yana addu’ar neman tsarin Allah)

sbd haka nabaka sati 1 xuwa 2 ka kamun wani ko waye”sbd dole kabayar da jini tunda kana acikin k’ungiyya”ko kuwa acikin iyalanka “d’an ka ,matarka,ko y’ar ka” zan d’auki guda acikinsu”saidai ka wayi gari d’aya ya mutu kaga gawarsa”

Cikin zaro ido baffa idi yace “.kamun rai karka tab’a iyalaina”zan kawo wata yarinya”shikuma wanda nakawo inaso kasaka aljannu su kasheshi kawai….

Hahahahahahahaha hahahahahahahaha”dodon yayi wata iriyar dariya”atake yab’ace bat”

Cikin tashin hankali da damuwa baffa idi yafito daga d’akin “yaja honorable lawal da Alh nura agefe sbd sune suka sakashi a k’ungiyyar”yyinda wasu mutane ukku dasuka kama ke zaune ad’aure….

Cikin tsoro da razana baffa idi yace”.gsky honorable kucireni dg k’ungiyyar nan taku bazan iyaba…

Wani kallo Alh nura yamasa yace”.karka manta anyi yarjejeniya dakai Inka shiga bbu fita”idan kuwa ka zurfafa dodo zai kasheka.

zaro ido baffa idi yayi yace”.meye mafita yanxun?”

Alh nura yace”.mai zai hana ka kawo masa yarinyar dazaka auramun”amma kabani kwana 1 na huta da ita”tunda sati d’aya ko 2 aka baka ka kawota”

Ai bama wannan ba”yaya zanyi kar agane?”kunsan halin jama’a da saka ido”

Honorable lawal yace”.yau naga shegiyar yarinyar nan gidan Alh Aliyu”bansan kuma miye alak’arta dasuba?”ina zaton dai ko sadeeq yana sontane” wlh taso ta tonamun asiri data ganni gidan d’azun”

gashi kud’in danaso karb’a gun nakashashshiyar matarsa ban amsaba”gara ka kawota kawai agama da y’ar iska”saika d’auki gawarta ku bani”nikuma zan kai gawar d’akin sadeeq d’an matata”muturo police da zancen anyi kisan kai”sai anuna raping nata yyi yakasheta sbd kar asirinsa yatonu”

kunga sai akamashi koba’a kasheshiba zaiyi zaman gidan yari”nikuma dg nan burina zai cika na kwashe komai nasu”sannan nasaki hjy Aysha….dama nariga naci alwashin ganin bayan Alh Aliyu da iyalansa”sbd banida mak’iyin daya wucesa aduniya”naga bayansa zan kuma ga bayan iyalansa.

Ajiyar zuciya baffa idi yasaki kafin yace”.da safe idan nakoma gida”zan nuna mata najanye auren”sbd nasan tanacan tana kuka”

Dg nan aka kwana 2 zanzo da motarka da zancen muje batsari da ita gun ummanta”sai kawai idan tashiga motar na hura mata powder ta suma”nakaita gunka”dg nan akawota gun dodo kawai…. yafad’a yana kallon Alh nura”tabbas hakan shiyafi”amma kaima honorable saikace ba tashinmu”katsaya yaro na neman yagaka”

Sadeeq d’in me kuma?”cewar Alh nura yana kallon honorable”

Hmmm wani irin matsiyacin yaro ne wlh”idan naganshi gabana har fad’uwa yakeyi wlh”

Amma yanzun tabbas haka za’a yi idi ka akaita kawai”saika kamun ita”zansan yadda nayi yau akamun key d’in d’akin sadeeq”asakata boot na mota na shigo da ita gidan”sai idan baya nan naje na bud’e d’akin sa na azata saman bed nasa…..

Insha Allahu ubangiji bazai baku nassara akan wannan abunba”

Atare suka juya bayansu ,sbd suga waye?????✍️

Yau insha Allah ake gama book 1kuyi k’ok’arin biyan kud’in book 2 akwai chakwakiya agaba guys😳😳

Mom fareesa🖊️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button