
PAGE 1&5
BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM
????Ƙauyen Lafani wani ƙauye ne a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Illela local govment yamma da ƙauyen ciwake,sanaan mutanan garin noma,mazan garin kusan mafi aka sarin su suna fita hausa(lagos ibadan etc) shi ake nufi da hausa.
_WANNAN KENAN
“Jiddah-Jidda,wai Jiddah dan uwarki bakiji ina kiran kine,ko so kike muryata ta dashe?,shegiya dangin mayu masu ƙashin tsiya,yanda uban naki yake kwance ba cas sai an juyar tayaya in baki fita kinyo talla ba zan ciyar dake dashi,su Atiƙha dai da Sa’ina wa ƴanda suka kawo dukiyar auran su,sun hana su tallah,ke ko basu hana su bama baza suyi b,tunda gaki ƙatuwar banza duk kin tsofe musu shekara sha huɗu ba mashin shini duk ƙauyen nan babu sa’ar ki,ni wallahi da babban budurwa gwamma ƙaraman bazawara”.
Wata ƴar matashiyar dattijuwa,bazama akirata dattijuwa ba ,kasancewar ƴaƴan ƙauye ana musu auran wuri,ga wahala da rashin gyara ke sa su su tsofe,fara ce gajera mai faɗeɗen baki da gajeran hanci,daja-daja take da ƙazanta.
Daga wani ɗan ɗaki Jidda share hawayen da ya zubo mata gyara ma mahaifinta kwanciya tayi bayan ta goge masa jiki ta cire masa kayan da yayi fitsari ta aje a gefe,”Gwaggo ina zuwa,na gyara ma Abba jikine bari in ɗauko hijjabi”.
Fyace majina tayi da saleɓen zanin ta daga bisani tace,”dan uwarki ma karki fito,in rana tayi kyasan yanda zakiyi da kayan nan nide kuɗi nake buƙata”.
Fitowa tayi da sanye da hijjab ɗinta duƙun-duƙun ta cukuykuye shi don matuƙar kunya takeji yanda take fita,yau inshaAllahu sai taje ƙauyen ɗan boka wajan yayar mahaifiyarta ta samo ɗan sabulu na wanka dana wanki tazo har kayan kashi da fitsarin Abbanta ta wanke,don duk tallan nan da take ma Gwaggo iyakan ta ta bata abinci ba suturan balle tokan wanka dana wanki.
Ɗaukan bokitin wainar tayi ta ɗaura akai ta fita,bayan gwaggo ta gaya mata na nawa tayi.
Zahra kenan ,bata aje komi ba face gulma,ba ruwan ta da sallah tun ƙarfe uku na dare take tashi ta hasa wutan ta ɗaura masa,ba ruwan ta da sallah ko wanke ido,neman kuɗi ne kawai a gaban ta.
“Zarah ki wanke min kayana gaskiya duk sunyi dauɗa”.
Faɗan wata ƴar yarinya ɓai kama da zarah kallo ɗaya zakai mata zaka tabbatar da ƴarta ce ,yarinyar bazata gaza shekara sha ɗaya ba,ɗaure take da ɗaurin ƙirji kan nan daga-daga ba kitso hamma take tana miƙa.
“Kajimin ƴar kaza-kazan uwa,in ankai ki gidan Hallirun hakanan ubanki zai rinƙa zuwa miki aiki”.
“Wallahi Zarah kwasowa zanyi in rinƙa kawo miki,ai baki koya min ba”.
“Gafaran kudai mai kuke tattaunawa ne hayani har killa tunda safen nan?
Wata yarinya ƴar kimanin shekara sha uku tana sanye da riga da zani, ta ɗauke da baƙar leda.
“Ke kuma daga gidan uban wa kika kwana?.
Ya tsina fuska tayi tace,”ke zarah ansa wannan Alhaji Sa’idu ne ya ce inkawo miki kaji ne ki goge wiya”.
Lokaci ɗaya Zarah ta washe hauru ta amshi ledan tana dubawa.
“Alhaji Sa’idu ɗan albarka,kinsan de gidam sarkin aska sun kawo kayan auren ki koh?,tou ki iya takun ki a hankali,karki bari ki kawo min ciki gida”.
“Kinga Zarah innayi cikin ma uban shi yafi kowa kuɗi a wannan ƙauyen namu,ko zubar wa bazan yi ba don inci gado”.
????????????????????????OHH NI JIKAN HAJJA TALA,WA YA GAYA MA BALLAGAZAN GA ƊAN SHEGE NA GADO???
WANNAN WATA IRIN UWACE,MAI KASHE ƳAƳANTA???
Jidda ko tana fita tayi sa’an saida masar ta,daganan ta wuce ɗan boka inda yar mahaifiyata ta amso sabulu da omo,a gaggauce bata zauna ba ta juyo don tana tsoro kar Gwaggo ta casa ta,don don yau tana da cin kasuwar gada kuma tana so ta tsamtsame kayan su.
“Assalamualaikum gwaggo n dawo”.
Tana aje bokitin.
“Tou ina ruwa na,da dwowar ki,bani kuɗina in biyar ya ɓace wallahi sai na naɗa miki na jaki”.
Cike da masifa take maganan.
Miƙa mata tayi daidai lokacin ledan sabulun ya faɗo.
Da kallo Zarah tabi leda kafin ta ɗago,tace,”kuɗina kike ɓoye wa ki kashe,shegiyar ɓarauniya”.
Girgiza kai tayi jikin ta ma rawa tace,”………..!
SAI NAGA COMMENTS ƊIN KU
DEDICATED TO ALL MY FANS,luv u oll kamar saman alala????????
typing????️
????JEEDDATOU????
NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)
(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE
SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU
PaGe 6&10
BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM
_????Girgiza kai tayi jikin ta na ɓari yana rawa tace,”Gwaggo ban taɓa miki kuɗi ba wallahi”.
Ahasale tace,”in baki taɓa min kuɗi ba kanti sani kikaje kikai sata koko yawon ta zubar ɗin da kike zuwa yi anan kika samo,dole ma yau in duba ki,don karki kwaso min abin kunya duniya ta zageni baccin ina iyakan ƙoƙarina akan ki”.
“Gwaggo wallahi Inna Mairamu ta tabbani,naje ɗan boka ne kayana duk sunyi dauɗa”.
Cikin muryan kuka take maganan,yayinda hawaye ya saukko kan farar fatan fuskan ta da ta koɗe da datti.
Gwafar uban can,har can kika je don kija min zagi,in banda kin rainani,in ɗaura miki talla ki wuce ɗan boka wajan munafukar Inna ki,tou uban mai kika ce mata, wani sharri kika laƙaba min,ko kinje tabaki sabon maitan ne?.
Cike da masifa take maganan,ta ƙarashe maganan da sigar tambaya.
Girgiza kai take yayinda hawaye ke cigaba da wanke mata fuska.
Sa hannu Zahra tayi ta wufce ledan sabulun.
“Bazaki wanki da wankan ba,saide ki mutu cikin dauɗa,harni zaki gaya ma kayanki sunyi dauɗa”.
Tana magana tana dukan ƙirjinta.
Gwagg……!
“Zanci uwarki kika ƙara kiran sunana kurwata kur la’ilafi ƙafa dubu,in wani sidda barun maitan aka ƙara baki tou namana ɗaci”.
“Zarah wai miyasa baki karkashe ƴar iska da mari,bata san ban bancin ɗiyar bora da ɗiyan mowa ba,da kin bari ta fara wanka da wanki,wannan mai ƙwalaƙwalan idanuwan sai tace tafi ƙarfin miki talla”.
Faɗar Atiƙa dake zaune kan gadon kara ƙarƙashin bishiyar dalbejiya tana kallo a wayarta sha kiɗanka baƙauye.
“Ke Atiƙa ina zanyi sake ,ai wallahi a ƙauyen nan na lafani JIDDAH sai ta zama abin kwatance ba boka ba mallam,amma sai ta zama mafi ƙatuwar budurwan da ta tsufa ba aure,inko kinga tafara tsafta ta samu wanda zai aureta sai bayan raina”.
????????????????????????NIKO DA NAKE GEFE NACE TA ALLAH BATAKI BA ZARAH DAKE DA ƳAƳANKI
Sum-sum Jiddah ta wuce tana sharan ƙwalla ta nufi ɗakin da mahaifin ta yake kwance,da sallama ta shiga ɗakin duk da tasan bazai iya amsawa ba.
Ƙarasawa tayi kan gadon karan da ko tabarma babu akai da yake kwance.
Hawaye tagani nabin fuskan shi,jikin ta na rawa ta duƙa daidai kan fuskan shi duk tabi ta ruɗe jikinta har yafi ɗazun rawa,don sam bataso taga mahaifinta cikin damuwa,da da dama ta ɗauke mai ciwon da ta cire mai ajikin shi tace,”subuhanallah Abba hawayen kuma na miye?,dan Allah Abba kadena damuwa cuta aiba mutuwa bace,zaka warke inshaAllahu kaji Abba”.
Cikin muryan lallashi take maganan,tana haɗiye kukan dake ƙoƙarin ƙwace mata.