BAKAR WASIKA 9

Page -9️⃣
If you’re not living around these people, you will never know what they are going through, fiye da haka ma yana faruwa, kawai dai Allah ya tsare mu su kuma yai musu mafita.
Tun daga jin sunan Labarin kun san abun da ya kunsa. Ban san abun da readers suke so ba, idan an saka kudi da luxury life sai ace writers suna bude idon mutane, and when we’re talking about reality kuma ba mu tsira ba, anyway if you don’t like the story you can quit it.
*** *** ***
Har past 12am Talba yana zaune bangaren Momy doing nothing, haka nan kawai yake jin yanayinsa sai a hankali. Idan zaka tambaye shi damuwarsa ba zai ce maka ga matsalarsa ba. Mikewa yai tsaye ya isa gaban plasma ya kashe sannan ya wuce kitchen domin samu abun da zai sakawa cikinsa, rabonsa da abinci tun da rana, ko lunch din Momy ta hada be ci ba. Tea ya fara hadawa kansa sannan ya bude freezer dake kashe ya dauko cake ya kunna oven ya saka shi a ciki, sannan ya dauki tea ya rike a hannunsa yana ta kallon harabar gidan ta windows kitchen din, ko ina haske ne kamar rana.
Juyowa yai a hankali jin kamar shesshekar kuka a falo, aje cup din dake hannunsa yai ya tako a hankali zuwa bakin kofar kitchen din ya tsaya. Sai ya hango Leila zaune a bakin stairs din sanye da kayan bachi riga da wando sai kuma safar dake kafarta, kanta ba dankwali sai hawaye take tana kallon wani bangare na falon, sam bata lura da shi ba har sai da ta juyo tana cigaba da rera kukan a hankali. Suna hada ido sai tai sauri share hawayenta ta dauke kai sannan ta mike tsaye ta juya a hankali zata hau stairs din.
Har tai rabi ban da kallon mamaki babu abun da Talba yake mata.
“Leila…”
Ya kira sunanta kamar wanda baya son magana, tsayawa tai cak gabanta na mugun faduwa, domin har ga Allah bata dauka yana zaune a falon har lokacin ba, da b zata fito daga dakinta ba, juyowa tai a hankali sai dai bata yarda ta kalleshi, sanin kanta ne ba zai tambaye ta me take yi ma kuka ba, kiran sunanta kawai da yai ya isa ya sanar da ita cewar tambayar damuwarta yake.
“Na yi mafarkin tsoro ne…”
Ta fada tana wasa da yatsun hannunta, bata tsaya jiran abun da zai ce mata ba ta juya da sauri ta haura sama. Da kallo ya bita har ta bace masa sannan ya juyo ya dawo cikin kitchen din, mamaki karara a fuskarsa.
‘Mafarki tsoro?’
Ya maimaita aransa, idan mafarkin tsoro tai me zai saka ta fito a nan ta zauna ita kadai?
“Ko dai saboda ni ne?”
Ya tambayi kansa yana kokarin kai hannunsa ya dauki tea, domin ya san abun da zai tashi hankalin Leila ba karami ba ne, and bayan shi ba ya ji akwai wani abu da zai saka Leila ta yi kuka ko ta shiga damuwa. Kamar wanda baya son bude baki haka ya kai cup din a bakinsa ya soma sha a hankali, dayan hannunsa ya saka a aljihu yana kallon oven din sai dai gaba daya tunaninsa ba a nan yake ba.
Sai da ya sha rabin tea sannan ya kashe oven din ya ciro cake din daya dumama ya aje, ya dauki tissue ya saka a hannunsa sannan ya fara daukar cake din yana ci. Bayan ya gama ya kashe wutar kitchen din ya fito falo ya kashe wutar sannan ya wuce bangarensa. Shirt din jikinsa ya fara cirewa wanda hakan ya bawa kyakkyawar surarsa da murdaden kirjinsa bayyana, a kafadarsa ya dora rigar sannan ya nufi wani madaidaicin daki dake hannunsa na dama, a hankali ya murda kofar ya bude ya shiga, kai tsaye ya nufi teburinsa ya ja kujera ya zauna ya bude system dinsa yana duba sakon da Jahid ya turo masa na adadin kudin da za a kashe wannan watan na gidan marayu.
“Okay”
Ya furta sannan ya rufe system din ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kunna data ya shiga WhatsApp.
‘Zan rubuta maka cheque gobe, after that, ka bincika abun da yan gudun hijira suka fi bukata ka kirga ko nawa za akashe na mutun 300’
Bayan ya gama rubuta masaya kashe data ba tare da ya duba sako ko daya da yake shigo masa ba, balle har ya amsa. Fitowa yai daga dakin ya nufi Bedroom dinsa yana shiga ya aje rigar dake kafardarsa a muhallinta ya cire jean din jikinsa ya nufi bathroom ya jika jikinsa da ruwa ba tare da ya saka sabulu ba yai alwala ya fito, sai da ya tsane jikinsa sannan ya nufi closet din ya dauko kayansa na bachi.
Wando kawai ya saka domin abu ne mai wahala ya kwana da riga komai tsananin sanyi, sai dai ya rufa da bargo, riga na cikin abun da ke takura shi ta hana shi sakewa idan zai yi bachin dare.
BATURIYA POV.
“Wallahi tun da nake a rayuwata ban taba zuwa Kano ba, ni fa ban taba barin Zamfara ba”
Ta fada tana fyace hancinta daya cika da majina tsabar kukan data sha.
“To ya akai kika zo nan?”
“Agwagwa da buje na shiga nace ya kai ni tsohuwar kasuwa sai na ga kansa yan rawa kamar dan tsuntsu, bayansa kuma da gashi shine nace ya sauke ni yana sauke ni na fito da sauri, sai wannan mahaukacin ya biyo ni”
“Minene kuma Agwagwa da buje?”
Ta kalli wanda tai tambayar da idanuwanta da sukai ja abun ka da farar mace.
“Keke Napep”
“Oh Allah na wata kila aljanine ya dauke ki, kin san fa ance suma suna yin Napep din”
“Ga zahiri na gani, wata kila da bance ya tsaya ba da yanzu na tsinci kaina a Russia ko Iraq”
“Lallai kuwa abun na su ba wuya, to yanzu kina da waya a tare da ke?”
Sai a lokacin ma ta tuna da jakarta, domin wayarta da kudinta har da makullin gidanta suna cikin jakar.
“Na shiga uku Wallahi jakata na cikin napep din aljani nan kuma ya tafi da ita”
A take ta fashe da sabon kuka, domin ta san samun wata wayar ma agareta yanzu abu ne mai wahala.
“Subhanallahi, to kina da number wani akai ko mijinki ko Baba?”
“Babana ya mutu sai dai mijina kuma shi ma ya siyar da wayarsa, yau ina cikin ukuba”
Ta kara fashewa da kuka.
“Baki da number kowa akanki”
“Akwai ta yayata da Mamana”
Sai da ta share hawayenta sannan ta karbi wayar ta saka number Mama tana shiga aka dauka.
“Hello Sallamu Alaikum”
“Mama ina cikin matsala Mama gani a Kano”
“Kano kuma Rafi’a? Gurin me?”
A nan ta labarta mata abun da ya faru, cikin labarin tafi nanatawa Mama cewar wayarta na cikin jakarta kuma ya tafi jakar, da alama ma batan wayarta yafi mata zafi fiye da ganin kanta da tai a Kanon cikin kankanen lokaci, yan kudinta ma duk suna ciki. Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka Baturiya ta zama har wani yamutsar kai take.
“Wallahi Takauci be yi ba, daman ance idan mutum ya kwana arba’in be ci nama ba idan yai maka baki zai ya kama ka, gashi nan ai laifin Faruq ne”
“Wanene kuma haka?”
Sai tai shiru bata fada ba, domin bata son tace mijinta ace bata jin magana tun da har ya hanata fita kuma ta fita duk kuwa da kasancewar ba wannan ne karo na farko da ya hanata kuma ta fita ba.
Account din mai POS din unguwar aka karba aka turawa Mama ta turo mata kudin mota, aka ciro mata sai dai tafiyar ba zata yi a yau ba domin yamma ta yi gashi kuma hanyoyin nigeria babu kyau a dole ta hakura sai gobe da safe ta kama hanyar dawowa Zamfara.
Kamar kullum sai bayan sallah isha’i Faruq ya dawo gida. A bakin kofar gidan ya tsaya ya kwankwasa yana sauraren ta bude masa amman shiru bata bude masa ba, ya sake kwankwasa nan ma ba a bude masa ba, yayi haka kusan sau hudu sai a na biyar ya saka makullin hannunsa ya murda ya bude kofar daman can a tunaninsa ko ta rufe kofar ne daga ciki kamar yadda ta saba, sai dai tun a yanayin yadda ya tararda gidan ya tabbatar masa da matarsa bata nan. Yayi sa’a akwai wutar nepa sai ya kunna gulob din waje dana falo ya shiga daki ma ya kunna, tsaye yai yana karewa dakin kallo komai a watse kamar yadda ya fita ya bar shi, daman yana fita ta shirya ta fita bata tsaya gyaran komai ba. Gashi kuma be tararda ita ba, ajiyar zuciya ya sauke.