GOJE

GOJE 9 and 10

       FREE PEGE

Ina mika sa’kon ta’aziyya ta ga al’ummar musulman duniya baki daya, Na babban rashin da mukayi, hakika ba zuri’ar Malam kadai ne sukayi rashi ba duk duniya ne, muna rokon Allah ya jikin Malam Ahamad B.u.k (Bamba) Ya sanyashi cikin Aljanna madawwamiya Allah ya kyauta namu zuwan bayan tasu馃檹

9&10
Ya jima yana kokarin kawar da yanayin daya yake ciki amma abun ya gagara! yakan zama sakarai mara dubara a duk sanda irin wannan yanayin zai shiga jikinsa, gabadaya wayo da dubararsa nemarsu yake ya rasa, jikinsa ya takure guri daya, yana jin wani irin sanyi tare da tashin tsigar jiki. Ba da son rasa ba ya juya kanta, yaga tana wanke fuskarta da ruwan daya ajiye,
Asuwaki ya mika mata tabi asuwakin da kallon banza kafin tasa hannu a wulakance ta karba, duk da asuwakin sabo ne sai da ta wankeshi sannan tasa a bakinta, dauke kansa yayi yana girgiza kai ya lura da yarinyar kyankyaminsa take, a tunaninta ko yasa asuwakin a bakinsa.

Wani buhu ya janyo ya dauko wasu mangwaro masu nuna manya guda uku, ya wanke tas karamar wuka ya zaro daga jikinsa ya mika mata mangwaron da hade da wukar.
Hannu na rawa ta kar’ba yawunta na tsinkewa, bala’in yunwa takeji dama.

Kafin tayi amfani da wukar sai data tasa ruwa ta wanke duk da tana ganin acikin gidanta ya fito da ita amma bata yarda da tsabtar duk wani abu da zai fito daga jikinsa ba.

Inda Allah ya taimkashi, kayan dake jikinsa masu kauri ne wannan dalilin ya hana girmanshi fitowa amma a zahiri gabanshi yana tsaye kyam! sama da awa daya da rabi yaki kwanciya duk da ‘yan dabarun da yayi abun yaci tura, sa’i da lokaci yana shiga irin halin amma na yau yafi muni.

Itacuwa ya had’a ya kunna wuta ya zauna yana gasa jikinsa duk a kokarinsa na ganin ya kawar da abunda ke damunsa.

Ita da take zaune ba tsirara ba ba kuma mai suttura ba, ta yun’kura ta mike da kyar take tafiya har ta cimma inda yake jin zaune.

Zata zauna ya daga mata hannu, ba tare da ya kalleta ba yace.”Ki koma ki zauna a inda kike ko kina bukatar wani abu ne.”?
Hararsa tayi tana murguda baki kafin tace.”Naga kana shan dumi kai kadai shiyasa nazo nima ina bukata.
Tana maganar tana kokarin zama kusa dashi.

Tun daga sama har kasa yake bin ta da kallo, har ta samu guri ta zauna tana kara hannuwanta a jikin wutar, yanayin zaman da tayi yayi masifar jefashi cikin tashin hankali, inda ita kuma a wautar ta bata kawo komai ba tana ganin ai da tun farko yayi niyyar lalata da ita to da yayi amma ta lura sam ba wannan ne a gabanshi ba.

Ya dinga kokarin dauke kansa da kanta amma Shaidan yana kara ‘kawata masa suffarta, gaza dauke idanuwansa yayi daga kanta, ya cigaba da satar kallon wasu guraran da suka bashi sha’awa a jikinta, amma be yarda ta fahimci halin da yake ciki ba.

Sun jima a haka babu wanda yayi magana a cikinsu, kafin suji bushe-bushe na kusanto inda suke da alama yaranshi ne suka dawo daga farauta.

Ta kalleshi a lokacin da ya tsirawa shara’ban kafarta ido. Tayi saurin gyara kafafunta tana watsa masa harara.

Ya sauke ajiyar zuciya tare da sake tamke fuskarsa cike da bada umarni yace.”Ki tashi ki bar gurin nan.”
Yanda yayi maganar babu wasa yasa ta tashi tsaye, yayi saurin dauke kansa, kawai sai taja masa tsaki ta wuce!
Abin ya bashi mamaki mutuka! ya girgiza kai tare da nazari da tunanin matakin da zai dauka a kanta

Gurin gabad’aya ya rikice da gangi da bushe-bushe duk a sakamakon dawowarsu, hannu tasa ta toshe kunnuwanta takaici kamar ya kasheta, da yake da akwai hasken wutar daya kunna tana kallo suka dinga firfito da matattun macizai da mesa tare da sauran dabbobin da suka farauto,
Abun ya dinga bata mamaki ganin sun daga wani lafcecan maciji sun sanya wuka mai kaifi sun rabashi gida biyu, suka tsire shi a jikin wani itace kafin su barbada masa gishiri da wani abu ja da alamar manja ne sannan suka sanyashi a wuta suna gasawa.

Hankalinta yayi bala’in tashi, karni da wari duk ya cika gurin zuciyarta ta dinga hantsilawa saboda tsabar kyankyamin abunda suke.

Tana nan zaune tana kallon ikon Allah suka gama gasa maciji nan wanda bai sani ba sai yace bushashshan kifi ne suka fara yankarsa da wuka suna ci hankalinsu a kwance.

A gurin ta dinga kyalaya amai duk sai da ta amayo mangwaron data sha, taja gefe guda tare da toshe hancinta.

Sai da dare ya tsala sosai sannan kowa ya nemi makwanci, yana sanya kafarsa yaji ya taka abu cabal! yayi saurin kunna fitilar hannunsa yana dubawa, aman da tayi ne duk ya bata kan shimfidar, tana rakube a gefe guda bacci ya dauketa.

Yaji takaicin bata mai shinfida da tayi yaja tsaki tare da samun ruwa ya wanke kafarsa ya dawo yana tunanin inda zai sanya hakarkarinsa ya kwanta ba don bacci ba.

Kusa da ita ne kadai babu kazanta kuma baya so ya kusanceta gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, domin har yanzu yanayin be bar jikinsa ba.

Kawai sai ya yanke shawarar zuwa gurin yaranshi domin samun matsuguni, tsakaninsu babu wata tazara mai tsayi kuma yana da tabbacin babu abunda zai sameta, rigar jikinsa ya cire ya rufa mata a jikinta sannan ya bar gurin.

Da yake baccin ya dauketa a cikin tsoro da fargaba yasa ta dinga munanan mafarkai da namun daji sun biyo ta zasu cinyeta sai ta farka a gigice! tana kwalla ihu! da fadin.” Kura ce! kana inaaaa! GOJE!! zata cinyeni.”!
Gabadaya suka tashi tsaye da shirin ko ta kwana, amma ba subi bayansa ba, shine ya cimma inda take tsaye sai rawar dari take a tsaye.

Yana zuwa ta rungumeshi, tsam! tsam! tana wani irin kuka da fadin.” Kura ce ta biyo ni.”!!!

Ya dinga nanata mata addua a kunnuwanta har ta samu nutsuwa, ya zaunar da ita, amma fafur taki zama wai dole sai sun zauna tare. ta rike masa hannu katamau!

Shi kam taushin hannunta da dumin da yake shine yayi masifar sanyayyar masa da jiki,

Babu zato babu tsammani ta janyoshi duk karfinsa, sai ya tsinci kansa a zaune a kusa da ita, yayi mamakin hakan mutuka

A maimakon ta saki hannunsa, tunda yana kusa da ita, sai ma ta sake shigewa jikinsa, tana boye fuskarta a kirjinsa dake waje babu riga sai singlet.

Tsigar jikinsa ta tashi gabadaya ya rasa nutsuwarsa, so yake yafi karfin zuciyarsa amma ta kanainaiyeshi, ta hana shi tsira da mutuncinsa.

Haka suka wanzu har asubah! tana makale a jikinsa, ta hanashi sakat daga yayi motsi zata zabura! ta matseshi, tana goga masa sassan jikinta.

Da kyar ya iya furta magana.” Sai ki sakeni haka asubah tayi babu wata dabba da zata zo ta cutar dake.”

Kanta ta cire daga kafardarsa tana kallonsa da jajayen idanuwanta tace.”Kayi wa Allah da Annabi ka hada tawagarka mu bar dajin nan! duk abunda kuke bukata mahaifina zai baku kada ka cutar dani ko kuma wata dabbar tayi sanadiyar rayuwata.

Ya jima yana mamakin furucinta ashe tana da hankali irin haka.

Sai shi ma yayi mata magana irin ta samu hankali yace.”Bana bukatar komai a gurin mahaifinki, kuma ki daina dora zarginki akaina ni ba ‘barawo bane Allah ya nufeni ne da na taimaka miki.”
Yana kare maganarsa ya nufi bakin kogi da asuwaki a hannunsa, kallo ta bishi dashi har kurewa ganinta kafin ta girgiza kai tana tunanin wani abu akansa.

Sai da gari yayi haske sosai sannan ya dawo gurin dunga nesa yake hangota a kwance rigingine, ta dogare kafafunta a kasa cinyoyinta a waje amma ta suturta gabanta, saurin dauke kansa yayi har ya karasa gurin be sake kuskuran kallonta

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button