GOJE

GOJE 35 and 36

Ad

_____

FREE PEGE
33&34
Police barrack nan ne mafi akasarin ma’aikatan tsaro suke zaune da iyalansu, a nan gidan Asp yake, haka zalika ma anan ne mai girma Governor ya mallakawa UMARU gida tazarar su da Asp din babu yawa gida biyar ne a tsakaninsu, tsarin ginin gidan mai kyau ne, plate ne mai dauke da bangare uku, kowanne ‘bangare a shirye yake tsaf da dukkan abinda za’a bukata na yau da gobe, abinda kawai ya rage a gidan mace, don a ranar da ya tare a gidan ma ‘yan uwa da abokan arziki surutun da suke masa kenan, cewa a yanzu Allah yayi masa komai na rayuwa, abinda ya rage masa mace domin duk cikar mutum da kamalarsa mutukar bashi da aure to darajarsa dole tayi ‘kasa……….’Kwarai hakane a yanzu ya san cewa cikar mutumcinsa shine aure, wannan dalilin ya sanya yaji sha’awar auran a cikin zuciyarsa, sai dai kuma babu wanda ya amsawa cewa zai auri ‘yarsa a cikin wa’inda suke kawo masa tallan ‘ya’yansu, da kansa zai duba wacce ta kwanta masa a ransa ya aura.

B’angare d’aya ya dauka Uwale da Hamra’u sai suke amfani da daya, Uwale ganin ba zata iya zama a gidan ita kadai ba yasa tace Hamrau ta ta zauna domin ta taya ta zama, hakan yayi mata dadi mutuka domin dama tana neman hanyar da zata kusanta kanta dashi.

Itace ta d’auki ragamar kula da gidan, ta tsaftacce ko’ina har sashensa idan zai fita take ‘karbar key a gurinsa ta shiga ta gyara masa ko’ina tasa turare idan taga ya cire k’ananun kayanshi a toilet ta wanke masa tas ta shanya idan sun bushe ta ninnke tasa masa a wardrobe, kullum idan ya dawo daga gurin aiki tsaf-tsaf yake samun gurinsa yana kamshin turare na mussaman, kafin yayi wanka ya fito ta shirya masa abinci da duk wani abinda zai bukata, k’wazon yarinyar da yanda take kulawa dashi da kakarsa yana burgeshi! ba tun yau ba ya gane inda ta dosa a kansa, zai iya auranta saboda kyawawan dabi’unta dama wannan shine abin dubawa a cikin lamarin aure.

‘Bangaranta kuwa shawarwari take da zuciyarta kan cewa ta sheda masa tana sonsa ko kuwa ta bari ya furta mata da bakinsa, a ganinta yanzu tunda yayi kudi yafi k’arfinta shiyasa kullum take jin tsoron tunkararsa da maganar gudun wulakanci, sai dai duk sanda masifar sonsa ta isheta daki take shiga taci kukanta ta koshi, kafin ta roki Allah ya za’ba mata abinda yafi alkairi a rayuwarta, amma tayi mamakin yanda akayi Uwale tayi shakulatun ‘bangaro da maganar wanda ada can baya har kayan lefe take tarawa burinta bai wuce tabbatuwar auran ba, amma yanzu kwata-kwata bata maganar, ballanatana ta bashi umarnin auranta kamar yanda tayi alkawari a can baya.

Kamar yanda gwamnati ta mutuntashi ta kuma karramashi, shima haka ya mutunta yaransa ya karramasu yayi musu alheri sosai, domin duk rabin alherin da ya samu ya sadaukar musu, a cewarsa suma suna da hakki duba da irin muhimmiyar rawar da suka taka, hakan ya sake janyo masa kwarjini da farin jini a gurinsu da sauran jama’ar gari.


Yau satin sa guda kenan da fara gudanar da aiki a ofis dinsa na mussaman, Uniform dinshi ma na mussaman ne, amma yayi kamanceceniya dana Asp amma kuma akwai bambanci sosai!

Da yake yana da hikima da nazari babu wani abu da ya shige masa duhu, aikin yake kamar wanda ya shekara yana aikin tsaron lafiyar al’umma!

Wasu takardu yake dubawa kira ya shigo wayarsa dake saman tevur din dake gabansa.

Ya ajiye takardun cikin nutsuwa ya daga wayar da fadin.” Ranka ya dade barka da aiki.”

Daga daya bangaran Asp ya amsa da “Barka dai Jan wuya! da yake sunan da yake kiransa dashi kenan, ya cigaba da cewa.” Gobe ne fa tafiyar nan.”

Ad

Yayi jim! yana tunanin maganar kafin ya dan ja siririn tsaki! ya manta shaf da maganarsu ta zuwa garin kano domin kai marakunyar yarinyar nan gaban iyayenta……..Yace.”Ogah me zai hana ka sata a mota ta tafi ai ita din ba yarinya bace zata kai kanta gida.”

Ya girgiza kai da fadin.” A’a mutumina ba za’ayi haka ba, ni nayi wa mahaifinta alkawarin cewa dani da kai zamu kai masa ita, sannan kuma ba haka dokar aikin take ba, dalilin da yasa ma tuntuni ban shirya tafiyar ba, saboda na fi bukatar yarinyar ta murmure na ‘yan kwanaki hakan zai farantawa iyayenta rai su kuma ji dadin ganinta cikin koshin lafiya, to alhamdullihi yanzu naga tayi kyau sosai babu rama ko wani abu wanda ya danganci haka daga gareta.”

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin.” Ranka ya dade don dai kawai ka shirya tafiyar nan dani ne amma da sai dai nace kaje kai kad’ai kawai dalili bana bukatar abinda zai sake danganta ni da yarinyar nan wallahi.”! Cike da takaici ya ‘karashe maganar.

Asp na ‘yar dariya yace.” UMARU ban san me yasa kai da yarinyar nan bakwai jituwa ba, itama yanda kake jin haushinta haka take jin haushinka kullum bata da magana sai taka.”

Da sauri yace.” Tana zagi! na ko.”? Asp din yasa dariya da fadin.” In kaji zagi! ma d’aya kenan! shin ka san kuwa maganar da mukayi da ita kwanaki a kanka.”?

Kai ya girgiza a k’untace yace.” Sai ka fad’a.” Jim yayi kafin yace.” Na san sharri kawai tayi maka ba zaka aikata hakan ba, duk da dai zuciya bata da ‘kashi kuma a lokacin hakan na iya faruwa saboda kusancinku da juna wanda dama shi shed’an burinsa kenan mace da namiji su kad’aice shi sai ya zama na ukunsu.”

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button