Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
GOJE

GOJE 37 and 38

Ad

_____

37&38
Da yake ta sheda fuskarsa suna shiga ta ganeshi, cike da farin ciki take masa barka da zuwa, ta nuna masa gurin zama da fadin.” Ashe tare kake da yaran naka sannu da zuwa ga guri zo zauna.” Asp ya zauna kusa da ita yana amsawa ya dora da fadin.” Tare muke tafe dasu ai nace su zo su gaisheki sannan kuma ita ZINATU tayi miki bankwana domin gobe idan Allah ya nufa zamuje mu kaita gida da yardar Allah.”

Tace.”Eh ta sheda min hakan har na bada sakon gaisuwata ga manyan nata, ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya kuma dawo daku lafiya.”

Gabad’aya suka amsa da ameeen ya Allah.

Falon yayi shuru na minti biyu kafin tace.”Duk ya iyalin naka ina fatan kowa lafiya.” ? Yace.”Kowa lafiya lou insha Allah gabadaya zasu zo su gaisheki.” Cike da jin dadi tace.”To shikkenan ina nan jina jiran zuwansu.”

Tun shigowarsu shida Asp din yake a tsaye a gefen kujerar da take zaune, be kalleta ba ballantana ya fahimci yanayin da take ciki wanda tsayuwarsa a kanta ya janyo mata, k’amshin turaran jikinsa ne yake fizgarta take jin wani irin azababben feelings! ta rasa wace irin masifa ce wannan duk sanda zai kusanceta hankalinta ya kan tashi, gabadaya jikinta ya mutu ta dinga matse ‘kafafunta wani irin sanyi ta keji a cikin jikinta, cikin zuciyarta take wasu irin tunane-tunane marasa kan gado…………Gyaran murya yayi gabadaya suka kalleshi amma banda ita, Ya dubi Uwale da fadin.” Ina Hamra’u ne.”? Tace.”Yanzu-yanzu ta shiga daki watakila ko tana wani uzuri ne.”

Ya kalli Asp da d’an murmushi a fuskarsa yace.” Yana da kyau kafin ka wuce ku gaisa da matata da yardar Allah.”

Jin abinda yace yasa Asp din yin ‘yar dariya ya bashi hannu suka tafa da fadin” Gaskiya ne abokina hakan yayi ya kamata ta fito mu gaisa.” Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya nufi dakin nata.

Cikin tsantsar fad’uwar gabada gami da jin wani abu mai bala’in d’aci a wuya ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin bude dakin, ba ta janye idonta daga kansa ba har sai daya shiga dakin, sannan ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya wacce ta janyo hankalinsu kanta, sunkuyar da kanta tayi ‘kasa tana ‘kokarin saisaita yanayin da take ciki, halin da ta shiga a lokacin da yake maganar ta kasa fassara shi shin wai me hakan yake nufi?

Cikin yanayi na damuwa ya sameta, ya kira sunanta ta dago kai tana kallonsa , nan ya hango b’acin rai cikin ‘kwayar idonta, cike da kulawa yace.”Menene yake damunki.”? da yake a kusa take kuma kishi yana cin zuciyarta, sai kawai ta fashe da kuka harda shashsheka!

Hankalinsa ya tashi ya zauna kusa da ita yana rarrashinta, da kyar tayi shuru sai ajiyar zuciya take saukewa, ya rike hannunta da fadin.” Waye ya ta’ba min ke.”? shuru tayi ba tace komai ba, yace.” Ba zaki fad’a min ba ko baki da lafiya.”?

Kai ta girgiza alamun a’a. Yace.”Babu daya daga ciki amma kike kuka gaskiya ban yarda ba kada ki boye min abinda ke damunki kinji my dear.”

Zuciyarta ta sake karyewa kawai sai ta tsinci kanta da fadin.” Yanana don Allah Menene tsakaninka da ita.”?

Yayi jim yana kallonta kafin yace.” Wa kenan.”?

Ta kalleshi hawaye na karakaina a saman fuskarta, hannu yasa yana goge mata tare da girgiza kai alamun ta daina.

Cikin shashshekar kuka tace.” Kada ka gujeni na riga na makance akan sonka ba zan iya rayuwa da kowa ba idan ba kai ba, zuciyata tana wasiwahsi cewa zaka maye gurbina da wacce ‘yar sarkin daka taimaka wannan shine dalilin daya sani zubar da hawaye.”

Da murmushi a fuskarsa yake girgiza kansa har yanzu hannunta na cikin nasa yace.” Babu wata alaka da take tsakanina da ita, ki cire faruwar hakan a cikin ranki, bani da matar aure sai ke, domin duk kin tara abunda nake da bukata, insha Allahu kece uwar ‘ya’yana.”

Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, cikin tsantsar farin ciki ta kalleshi da fadin.” Nagode masoyina ina fatan Allah ya tabbatar da alkairin da yake tsakaninmu.” Ya amsa da “ameen ya Allah.”

A ‘kalla ya kai minti ashirin da shiga dakin shiru bai fito ba, shi kansa Asp din ya ‘kosa ballanatana ita da take jin kamar taje ta sha’ko wuyansa ko uwar me yake a dakin oho!

A cunkushe! ta kalli Asp din da fadin ” Ranka ya dade ya kamata mu tashi mu tafi wannan mutumin ya mayar damu shashashai! ya shige daki ya bar mu a zaune zaman jiransa.”

Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin.” Hakane nima nayi mamakin jimawarsa amma bari na kira wayarsa naji.”

Uwale kuwa gyangyadi take bata ma san ma abunda ke faruwa ba.

Yana kokarin kiran wayar tasa, suka fito a tare hannunta na cikin nasa.

Har suka zauna bata kallesu ba, cika kawai take tana batsewa! wani mugun abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya.

Gwiwa a kasa Hamra’u ta gaishe da Asp, ya amsa da fuska a sake yana janta da wasa, murmushi kawai take ta kasa hada ido dashi, gabadaya farin ciki ya mamaye zuciyarta, tayi mamakin yanda akayi ya santa har yake kiranta da amarya hakan ya sanya ta sake gazgata maganarsa.

Tashi tayi kawai ta kama hanyar fita ba tare da ta tankawa kowa ba, Nabilan ta kalli mahaifinta nata da fadin.” Daddy bari muje kawai sai ka shigo.” Ya mike da fadin.” Aa ku jira ni mana saurin me kuke.” duk da taji abunda yace hakan besa ta tsaya ba, ta bude kofa ta fita, ita Nabilan ita ta jira mahaifin nata har sukayi sallama cikin girma da mutunta juna.


Washe gari da wuri suka shirya tafiyar, bahaushe yace sabo turken wawa, ‘yan kwanakin da tayi a tare dasu ya sanya duk jikinsu yayi sanyi har dashi Asp din kawai ya daure ne domin ya san dole watarana yarinyar zata bar hannunsa, Madam dai kasa hakuri tayi sai share hawaye take a fakaice.

Al’amarin ya bata mamaki mutuka! ta rasa wane irin so matar take mata, gabadaya sai jikinta ya mutu ta rungumeta da fadin.” Mommy kiyi hakuri ba mu rabu da juna ba insha Allah zan dinga ziyartar ki, bayan haka kuma zamu dinga gaisawa ta waya ki daina kuka.” tana maganar tana share mata hawaye.

Hannunta ta rike da fadin” Idan kin isa gida lafiya kice ina gaishe da mamanki kuma insha Allah idan an kwana biyu zamu kawo muku ziyara dani da Nabila.”

A sanyaye tace.”To shikkenan in Allah ya yarda zan sheda mata sa’kon ki daga zarar na isa .”

Nabila ta fito daga daki ta same su cikin damuwa, a sanyaye ta zauna kan kujera tana kokarin magana ya k’araso gurin yana duba agogon dake hannunsa, ya kalleta da fadin.” Tashi muje ko.” Ta mike tana gyara mayafin jikinta, Nabila ta kalleshi da fadin.” Dady zan je nima.” kai ya girgiza da fadin.” Ki bari idan an kwana biyu zaku shirya zuwa keda Madam.” Kamar za tayi kuka tace.” Dady ni nafi so naje yau.” be saurareta ba ya kama hanyar fita, itama da sauri tabi bayansa domin bata so ta tsaya dogowar magana zuciyarta ta karye, gabadaya suka bita da kallo cike da alhinin rabuwa da ita.

Wayarsa ya kira ya sheda masa cewa sun fito suna jiransa.

Da yake tuntuni ya shirya tafiya sai kawai ya fito daga gurinsa kai tsaye bangaran su Uwale ya nufa domin yi musu sallama.

Fitowarsa ta dauki hankalinsu daga ita har Asp din……Yana sanye da kayan mu na hausawa shadda milk colour dinkin tazarce har kasa, sai yayi amfani da hula zannar bukar mai duhun zare, kafafunsa sanye da bakin takalimi mai gidan yatsa, agogon dake d’aure a hannunsa ma baki ne, yayi kyau sosai fuskarsa tayi kar! sai fitar da annuri take.

Ad

_____

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button