BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 12

Seven days later…

FARUQ POV.

A gabanta ya dire kofin dake dauke da koko ya dora mata suga a saman murfin.

“Ga abun da muka samu”

Wani banzan kallo tai ma kofin ta dauke ido tana turo baki gaba.

“Koko kuma? Ni bana son shan koko gaskiya”

Kallonta kawai yai ya dauke kai ya shiga dakin ya cire tufafin jikinsa ya daura wani tsohon tawul ya fito ya nufi inda ya jona ruwan zafi a electric a juye a karamin bokitin wanka ya fita waje ya sirka ruwan sannan ya dawo falon.

“Ni fa bana son koko”

“Wani yana can yana nema be samu ba”

“Wallahi babu, ba dai sa’ata ba, sai dai tsofafi sa’o’ina kyawawa kam suna can suna neman arziki”

Uffan be sake ce mata ba ya nufi hanyar dakin.

“Ni fa ba zan sha koko ba, waina nake so da nama”

Juyowa yai ya kalleta.

“Idan ina da halin siya miki ita kin sani, kuma babu abun da zai hana na siya miki, idan kuma babu sai ki yi hakuri har Allah ya kawo”

Sai ta mike tsaye.

“Tsakani da Allah Faruq kana cutar da ni, yanzu haka zan yi ta zama cikin matsi? Kamar mu muka fi kowa? Duk wani abun da nake so baka iya siya min sai idan na siyawa kaina ko kuma an aiko min daga gidanmu, ni gaskiya na gaji kana cutar nan kuma na san Allah zai saka min domin baya son zalinci”

“Gaskiya ne, Rafi’a baki da tunani ko kadan, kan mu farau talauci? Ko kuma mutum yana yi ma kansa arziki ne? Halin nan naki ya ishe ni..!”

“Da ya isheka da ka sauwake min, da ya isheka da ka samawa kanka mafita, tsakani da Allah Faruq idan ba kaddarar aure ba babu abun da zai hada ni aurenka, daman can na dauka zaka samu aiki rayuwa ta tafi mana da kyau, ashe hauka nake, gashi na gagara samun abun da zan ci ma”

“Saki kike so?”

“Eh saki nake so, ka sake ni Faruq ka sake ni idan ka haihu”

“Zan nuna miki na haihu”

Yana fadar hakan ya wuce cikin dakin da bokitin ruwan ya shiga bandaki ya watsa ruwan ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya dauki makullin shagonsa ya saka aljihu, dayan aljihun kuma ya saka wayarsa, ko da ya fito tana zaune falon tana jiran ya mika mata takardar sakinta, tana ganinshi gabanta yai mugun faduwa.
Be kulata ya nufi kofar fita daga falon yai ficewarsa rai a bace.
Sai da ya fita sannan ta tashi ta fita ta rufe gidan ta dawo falo ta zauna, can kuma ta tashi ta fita ta dauko ludayi ta zo ta zauna ta bude kokon ta mutsa.

“Ba zan saka sugan ba”

Ta fada tana wurgar da kullin sugan ta fara shan kokon lami ba suga, ludayi biyu tai sai gata ta tashi ta nufi inda kullin sugan ya fashe ta kwaso a hannun ta nufo kokon ta zuba, ta zauna ta fara sha. Rabi ta sha ta bar ba Sultan dake bachi rabi, domin ta san bayan ya sha yanzu da rana ma zai iya nema.
Tashi tai ta koma saman kujera ta zauna, ta mika hannu ta dauki keypad din da Umma ta siya mata kamin ta siya mata smartphone, tsaki tai bayan ta shiga contact dinta ta fito ta shiga inbox dinta, nan babu komai domin sabun line ne da tai welcome back, hakan yasa ta ji babu dadi domin wanda ya saba rika babbar waya yana chatting idan ya rasata zai ji kamar ya koma a wata karamar duniya.

“Allah tsinewa Aljanin nan, ya dauke ni ya kai ni Kano kuma gashi nan ya rasa wayata da atm dina da yan kudina, Allah kasa min, Wallahi Faruq be da kashin arziki gashi nan na rasa komai”

Ta fashe da kuka. Kamar jira ake ta fara kukan sai ga kiran Ramlee ya shigo wayarta, share hawayenta tai sannan tai picking call din ba dan ta gane mai kiran ba domin number babu suna.

“Hello”

“Baturiya ya kike?”

“Lafiya kalau Ramlee ce?”

“Ni ce fa baki gane ni ba?”

“Number ba suna wayata ta bata ne na yi welcome back kuma numbers din ba su dawo ba”

“Garin ya? No wonder na yi ta kirankin number ki ban samu ba, na yi mamaki domin na san baki kashe waya”

A nan Baturiya ta labarta mata abun da ya faru, sai Ramlee ta saka mata dariya.

“Farin jininki yayi yawa Baturiya abun har da su Malam aljani? Shiyasa na ji muryarki wani iri kuka kike ne?”

“Ba dole ba Ramlee ina cikin matsala, ina son na ci da dadi na saka mai kyau amman abu ya garara, yanzu ko wayar nan tawa da ta bata ai daidai ne ya siya sabuwa amman sai da Umma ta siya min karama”

“Fee’at kenan, wannan fa duk kika so, da kin yarda da yanzu kin dangwali arziki har ma ki raba mijinki ciki, Wallahi Baturiya da zaki sake jiki yadda kike da kyau nan da har kyautar gida sai kin yi ma wasu”

“Ramlee ina fa da aure har da”

“Mace nawa ce mai yaya uku hudu har biyar take biyawa kanta bukatar da jikinta? Ke ko a unguwarku idan aka ce za a bude wasu matan auren ki ga sirrinsu zaki sha mamaki Wallahi, ba ki san cewa aure yana rufa miki asiri ba? Ko da kin samu wani abu ba za a zargeki ba? Yadda kike da kyau nan Baturiya ba ke ba ko ni da maza suke ganin hotunanki a wayata suna hauka sai na samu arziki, wai kin san ma dalilin daya saka na kira ki?”

“Sai kin fada”

“Wallahi wani ne ya sake ganin hoton ki yace kina cikin irin matan da yake so, na fada masa ke ba irin mu bace amman ya saka ni gaba wai na lallaba masa ke dan Allah, kuma babbar mutum ne dan siyasa, yanzu haka haka 100k ya bani wai na baki na wankan hoton da kika yi”

Baturiya ta mike tsaye tana dokan kirji idonta kamar za su fito.

“Dubu dari fa kika ce Ramlee”

“Wallahi ga su nan, tun shekaran jiya ya bani su jiya ma daker ya bar ni na yi bachi sai damuna yake da maganarki a waya kamar zai min kuka, shiyasa ma na kira ki da safen nan, Allah yasa ma mijinki baya nan”

“Baya nan ya aje min wani shegen koko ya fita”

“Kin gani yanzu da kina da kudi sai abun da ranki yake so zaki ci, idan kina free anjima zan zo na dauke ki a motata muje na siya miki sabuwar waya”

“Da kudin?”

“Aa da kudina dai, wacan kudin a cewa yai a baki kuma zan danka miki abun ki a hannu, amman ki yi tunani idan kika bada kai me kike ganin zaki samu? Bayan shi ma akwai maza da yawa musamman ace kina samun sakewa ana zuwa da ke hutu abuja ko kasar waje? Hmmmm Hajiyata ai kin take”

“To zunubin fa?”

“Allah gafurun raheem ne, kuma ban ce zaki dauwama a haka ba idan kin yi kin samu dan abun da kike so, sai ki daina amman ki yi tunanin future dinki dana yaronki koma nace yayanki na nan gaba Baturiya”

“Shikenan zan yi tunani”

“Yauwa Tawan haka nake son ji, ki yi tunanin kamin na zo kin ji? Yau ko wayar 500k kike so zan siya miki ita da yardar Allah”

Baturiya ta yi murmushin jindadi.

“Na gode kawata Allah ya bar min ke”

“Ameen Allah ya bar mu tare”

“Ameen”

Ta sauke wayar tana ta murna.

“Bari na yi sauri na gyara gidan kamin ta zo”

Ta dauki zane ta fara kabe kujerun, sai ta ji an kwankwasa kofar gidan, saurin saving number Ramlee tai sannan ta goge kiran da tai mata domin a tunaninta Faruq ne ya dawo. Sannan ta nufi kofar gidan ta bude sai tai arba da Malam Musa dilalin, cikin mutunci suka gaisa duk da kasancewar babu mayafi a jikinta sai hullar dake kanta.

“Mai gidan yana nan kuwa?”

“Aa ya fita”

“Oh dan Allah idan ya dawo ki ce masa na zo maganar kudin hayar nan, masu gida sun matsa, ko jiya da dare masifa yake ta min domin ganin yake kamar an bani kudin na kashe ne”

“Idan ya dawo zan fada masa, dazun ma yake cewa da ya ganka da ka saka masa number mai gidan domin yana son yai magana da shi”

“Indai maganar haya ne kar ma yayi domin Alhaji Sule be da mutunci ko kadan”

“Aa karka ce haka Malam Musa, bari na dauko wayar”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button