Ta tabbata Ado Gwanja ne kadai a Mawakan Kannywood baya temakawa “yan uwan sa! Ga dalilan nan:
TUN bayan labarin kyautar N50,000 da Dauda Rarara ya bai wa Sa’idu Isa Gwanja a watan azumin da ya gabata, wanda shi Gwanja ya mayar tare da martanin ba ya so saboda an shiga kafafen yaɗa labarai an yayata shi, jama’a sun yi ta sharhi kan lamarin. Wasu su na ganin abin an yi shi ne da wata manufa, don a nuna wa duniya cewa duk da shaharar da Ado Gwanja ya yi a fagen waƙa, amma sai da ya bari aka yi wa ɗan’uwan sa kyauta ta cin mutunci.
Masu wannan maganar su na ganin cewa karan Ado Gwanja ya kai tsaikon da ya kamata a gani a jikin na kusa da shi ko kuma ‘yan’uwa da dangin sa kamar yadda ake ganin arziƙin waƙar sauran mawaƙan da ke tashe a yanzu, irin su Naziru Sarkin Waƙa, Rarara, Ali Jita da Aminu Ala a jikin na kusa da su da ma dangin su.
Kamar Ali Jita, duk wasu abubuwa nasa za ka ga ƙannen da yayyen sa ne a kai, kuma an sha ji ya na yi masu kyautar gidaje da motoci. Haka ma Naziru da ‘yan’uwan sa.
Duk da yake wasu na ganin kyautar Rarara cike ta ke da siyasa, amma dai na kusa da shi su na amfana. Ko Tijjani Gandu da ake ganin bai shiga cikin manyan mawaƙa ba sosai, ana ganin na kusa da shi a tare da su.
To amma me ya sa Ado Gwanja ya fita daban? Domin idan ka ɗauki yayan sa, Sa’idu Gwanja, ai an nuna duniya ya na buƙatar taimako daga Ado, musamman a yanzu ma da ko motar hawa ba shi da ita, bayan ga tsala-tsalan motoci Adon ya na hawa. Lallai ya kamata a ce ko bai ba shi a cikin su ba, to ya saya masa ta ƙasa da su don shi ma ya samu ya yi “warr”, a daina ganin sa ya na yawo a ƙasa ko cikin A Daidaita Sahu.
Ganin yadda surutan su ka yi yawa, kuma sun ƙi ƙarewa, mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Ado Gwanja ɗin, amma duk lokacin da mu ka kira wayar sa ba ya ɗagawa, kuma mun je ofishin sa da ke Titin Gidan Zu a Kano har sau biyu ba mu samu ganin sa ba.
Amma dai mun samu zantawa da yayan nasa, Sa’idu Isa Gwanja, wanda a kan sa maganar ta taso, inda ya ce: “To, ka san shi abu na rayuwa kowa da yadda ya ke kallon sa. Kamar yadda ake ganin sauran mawaƙa su na yi wa ‘yan’uwa da dangin su hidima, to mu ma dai ba za mu ce ko kaɗan ba a yi mana ba, don ana yi mana ɗan abin da ya sauwaƙa.
“Kuma ka san kowa da yadda nasa tsarin ya ke. Don haka ko da an ga bai yi ba, ta yiwu nasa tsarin kenan.”
Da mu ka tambaye shi ko gaskiya ne a yanzu ba shi da motar hawa, sai ya ce, “To idan ka lura tsawon lokaci motoci kala nawa na yi? Don a yanzu ba ni da mota ko abin zai dame ni zan ɗauka cewa yanayi ne na rayuwa. Amma dai idan zan samu a yanzu, ina so!”