Labaran Kannywood

Bayan Auren sa da Ummi Rahab,Lilin Baba ya raba gari da Yayan Ummi Rahab

Bayan Auren fitaccen mawakin Kannywood Lilin Baba da Ummi Rahab,Lili din ya raba gari da dan uwan Ummi Rahab wanda ta sanadiyar sa ne ya auri Ummi din.

Yasir ga duk mai bibiyar Ummi Rahab kafin Auren ta zai sansu tare,haka kuma lokacin rigimar Adam Zango da Ummi din ya fito yayi wani bayani akan cewa “yar uwarsa ce.

Yasir din ya bayyanawa tashar Tsakar Gida dake YouTube cewa,tun bayan Auren nasu ne idan ya bukaci yayi waya da “yar uwar tasa baya samun damar hakan,domin ko ya kira ba’a dagawa,wanda hakan yayi matukar bashi mamaki.

Sannan Yasir din ya bayyana Lilin Baba yayi unfollowing din sa a shafin Instagram,haka kuma a shafin Ummi din da yake a hannun shi a wannan lokacin.

Ba tare da bata lokaci ba, zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa,kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button