MUTUM DA DUNIYARSA 49 – 50

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[49➖50]_*
……….Kasancewar yau mafi yawan bak’in suka wuce sai Umma tasamu
damar zaman k’irga y’an kud’ad’en data samu a wajen dangi na gudunmawa ita dasu Aunty Hannatu, bayan sun kammala sukayi d’an lissafin abinda Jiddah bata dashi za’a Kai Mata, walida dake rubutawa ta kalli su Aunty Nafisa cikin kwantar da murya tace, “Auntys dan ALLAH baza’a sayama Yaya Jiddah freight ba wai?”.
Duka Umma takai mata tana fad’in, “Walida ki kiyayeni wlhy, Ubanki yabani kud’in? Yanzu kina gani dai a gabanki aka lissafa kud’in duka nawane ya rage a ciki”.
“Kiyi hak’uri Umma badan ranki ya 6aci na fad’aba, ni dama dan nagafa kishiyarta nadashine, sainaga itama da da hali sai a saya mata ko k’aramine”.
“Humm Walida kenan, bakisan mutuwar mageba sai kinga tana shure-shure, dan kawai abokiyar zamanta nadashi sai akace itama dole sai an saya mata? Tomu bagasa zamuyi da waniba, abinda ALLAH ya hore mana dashi zamuyi amfani”.
Dariya duk sukayi, Aunty Saudah tace, “ALLAH Umma maganar Walida abar dubawace, badan gasa za’a saya mataba, kinga kodai Sana’a tayi da kayanta ai, amu talakawa ajiye firij ai badan gayu muke ajiyewa ba, ina ganin mizai hana acire a sadakin Jiddah sai a saya ko Wanda bai wuce dubu arba’in baneba zuwa hamsin haka”.
A take kowa ya aminta da maganarta, Yaruwaiya tace, “Kumafa gaskiyane wlhy, inaga hakanma shi kawai za’ayi, amma afara sanarma kawunku yahya sanan, saimuji shi mizaice, mace babu sana’a ai akwai matsala, randa miji yatashi baidashi sai kowa yay zuru-zuru, irin wannan ke kawo yawan husuma kuma wlhy, shi yana wuya saboda talauci kaima kana mak’ogwaro, abu kad’an zai hasala kowa ya fusata saikiga anyi sama”.
Umma ce ta d’auki waya ta Kira Uncle yahya, cayay mata gashinan a hanyar gidan ma. Tana ajiye wayar babu jimawa saigashi yazo. Bayan an gaggaisa Yaruwaiya tamasa bayani, 100% ya yarda da shawarar, danshima aljihun nasane yayi k’asa, amma harga ALLAH yayi niyyar siyama Jiddah duk abinda yadace mace ta bud’e ido tagani a d’akinta, musamman abinda za’s iya Mora har a sana’a.
Bayan sun gama tattaunawane yasamo musu motar dazata kwashi sauran kayan Jiddah da akwatinanta da kayan gara dadai sauran tarkace.
Umma kawai aka bari a gidan sai wasu tsoffi uku danginsu Jiddah 6angaren su Abba, su Balu, aunty Zulai, aunty hannatu, Walida, suka wuce gidan Jiddah. Maman Sadiq, Yaruwaiya, aunty Saudah, Aunty Nafisa, sai Zarah suka wuce kasuwa k’arasa sayo abinda ya rage Na Jiddah.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ikon ALLAH ne kawai yakawo Abba kano, ammafa wujiga-wujiga ya Iso saboda 6acin ran da yake a ciki.
Su Hajia Hindu na zaune a Dani itada yara suna dinner ya shigo ko sallama babu, Maneer yatashi da gudu yaje yana masa oyoyo. Rik’e hanunsa yayi kawai amma yakasa magana, saima wata uwar harara daya zubama su hajia Hindu itada yaran, “yanacan yana wahala su sunanan hankalinsu kwance”, dan duk sunwani zubo masa idanune amma babu Wanda yace masa koda sannu.
Tsaki yaja yana sakin hannun Muneer yashige abinsa. Hajia Hindu ta ta6e baki tana d’auke kanta. Shima Hussain bakin yad’an ta6e kafin yace, “Wai Mom mi akaima Dady ne daga dawowarsa?”.
“Ina Zan sani Hussain, ai tare muke daku anan ya shigo”.
Dariya Kalifa yayi yana fad’in, “ku nifa kwana biyunan gani nake kamar Dady a rikice yake, kokuma rud’un tsufane oho”.
Dariya suka sanya gaba d’aya, Hajia Hindu ta mik’e tana, “Kai yaranan ALLAH ya shiryeku, kodai tsohonne ma ai ubankune dai, bara naje naji mike faruwa”.
Kwance ta iske Abba hannunsa dafe da kansa, zama tayi gefen gadon kusa dashi, “Abban kalifa lafiya kuwa?”.
Banza yay mata tamkar baimajiba, saida ta maimaita sau uku kafin ya janye hannunsa ya kalleta da idanunsa dake jajur, sai dai yagaza cemata uffan.
Hakanne yad’an tada hankalinta, takuma maimaita masa tambayar.
Mik’ewa yay zaune yanajan guntun tsaki, “Yanzu nan Hindu na d’auki tsawon kwana shiddah bana gidannan, amma nadawo kuna kallona tamkar wani kashi, wane iron rainine wannan?”.
cikin kwantar da murya ta kallesa, dan zatonta koya samo kud’inne, shiyyasa ta aro sabon ladabi, “Ohni Hindu, yanzunan Abban kalifa wace irin maganace wannan dan ALLAH? To kayi hak’uri, wlhy mamakin yanda kashigone yasanyamu yin hakan, yaya Abuja? Ina fatan dai andace da samun kud’ad’en?”.
Jin yanda ta kwantar da murya sai Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta “Bansan yanda zanyiba Hindu, ina cikin tsaka mai wuya, kud’in danaje nema ban samoba, dolene a darenan naje na turke Y’ar iskar yarinyarcan yaronan ya saketa, nasan inhar Alhaji garba yaga zata dawo gareshi zai hak’ura ya barni”.
“Hummm Alhaji kenan, to ai daga baya kenan wannan, komafa miye ya faru laifinkane, Kaine ka 6ata komai a randa Alhaji garba ya kiraka, sannan nabaka shawarar musanya masa da Zarah, amma sai kak’i saurarena, to ai yanzu bakada hurumin rabama Jiddah aure kuwa balle bashi ita, dan ta tare tunma shekaran jiy…..”
A zabure ya mik’e, “k ban fahimcekiba? Ni da raina za’akai y’ata gidan miji ban saniba?”.
Baki hajia Hindu ta ta6e tana masa wani kallon rainin wayo, balle taji babu kud’in, “Oh kajimin Abban kalifa fa, yo yaune karan farko da aka Fara Kai y’ay’an naka gidan aure bada saninka ba? Naga ko hannatu sai dama tayi wajen wata biyu da aure ka sani, Zulai kuwama saida takusan haihuwa”.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya bangajeta ya wuce zuwa bayi. Bayansa ta raka da harara tana k’ya6e baki, saima ta fice abinta kawai tabar masa d’akin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kamar da wasa k’aramar magana saita zama babba, dan tsawon kwana uku Alhaji garba ya gagari hajia deluwa sakawa a ido, tunda ya shige sashen amarya a randa aka kawota bai sake ko lek’o wajeba, sallama agida yakeyi, abinci kuwa bashida Matsala, dan amarya ke musu daddad’en girki, cikin k’awayenta takira tabada umarnin ayo musu cefane mai yawa, wannan yasa suka kuma yima hajia deluwa nisa, sai dai tajiyo sautin kid’a Na tashi, knocking kuwa tayi har hannunta ya gajiya, tayi wujiga-wijiga da ita, nutsuwa ta gagareta, takira malam Na marwa yafi sau dubu amma wayar yak’i shiga, komai saiya kuma harmutse Mata. Su Kansu su Ashir sunma kasa gane kanta kwata-kwata, gefe kuma su hajia Hindu k’awayenta na kuma tunzurata a waya.
Aiki ya samu mata????
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai wajen sha d’aya Jiddah ta farka, ta tashi kuma bata samu Sheikh Aliy a d’akinba, hakanne ya sata d’anjin dad’i, yunk’urawa tayi zaune da k’yar, dan jikinta duk ciwo yake Mata, ji kawai tayi hawaye suna zirara Mata, yanzu nan wannan abunne har kesa mace yin zina?, miye abin dad’i anan banda bak’ar wahala? Wai a hakanma shi bawani gama shigarta yay gaba d’aya ba kamar yanda yafad’a, tayi kusan zaman minti talatin tana hawayenta, Wanda dalilinsu yafi k’arfi a kewarsu Ummanta, sakkowa tayi a gadon zuwa bayi, tasamu takumayin tsarki da ruwan zafi tayi wanka, lokacin walha ya wuce, hakan Yakuma sakata takaici.
Saida ta shirya sannan ta gyara d’akin tasaka turaren wuta, takardar data gani saman mirror ta d’auka ta karanta.
_Ina fatan tashinki cikin aminci da farinciki Aglan Nisaa (Mafi tsadar mace) amin afuwa na fita saboda wani uziri, ga abinci nan a falo auntynki ta kawo miki, Ku yini cikin aminci da kariyar ubangiji matana._
Guntun murmushi tayi tana had’iye hawayen da suka cika idonta, ta linke takardar ta ajiye sannan tafito. A falo ta iske abincin karin kumallonta daya ce, bata cutama kantaba ta zauna taci dai-dai iyawa tasha maganin daya ajiye Mata. Tanason zuwa ta duba Maimuna amma tanajin kunyar tafiyarta, haka ta zauna shiru harma takai da kwanciya cikin kujera ta fad’a duniyar tunani.
A wannan yanayin su Walida suka iso suka sameta, wani farin ciki Na musamman ya kamata, ta tashi cikin hanzari domin tararsu, sai dai taku biyu tayi tatsaya cak saboda kallon dataga sun tsaya sunama k’afafunta.
Aunty Hannatu dayake tanada hankali saita basar dasu ta hanyar zuwa ta rungume Jiddah.
Jiddah tad’an sauke ajiyar zuciya dan a ganinta k’ila basu fahimci abinda take zarginba.
Kayan hannunsu suka ajiye suma sauran sukazo suka rungumeta, kafin su saketa su kuma fita kwaso sauran kayan.
Maimuna dataji hayaniya ta fito, dan dama tun d’azun take d’an zagayo Jiddah taga kota tashi, Aliyu yace Mata kanta ke ciwo, dukda zuciyarta ta sosu da tunanin wani Abu daban hakan bai hanata lek’owa taga kota tashiba.
Da fara’arta takemusu sannu dazuwa. Suma suna amsawa fuskarsu d’auke da Fara’a, koda tace zata tayasu d’aukar kayan sai Balu ta hanata, dukda haka saida ta amshi agogon dake wajen Aunty Zulai suka k’arasa falon Jiddah.
Jiddah Na ganinta tai k’asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta, dan ita gani take kamar Maimunatun tasan abinda sukayi a daren jiya.
“Ashe kin tashi K’anwata, tun d’azun nake zagayenki amma saina iske kina barci”.
Batare da Jiddah ta kalletaba tace, “eh wlhy aunty, maganin murar Dana Shane yasani barci”.
“Dama yace kanki ke ciwo, yanzu dai ya daina ko?”.
“Eh ya daina Alhmdllh”.
“To ALLAH ya k’ara afuwa, sannu”.
“Yauwa aunty, kema yanaki jikin?”.
“Alhmdllh”.
Su Balu ma duk sukaima Maimuna ya jiki bayan ta zauna sun kuma gaisawa cikin mutunta juna, mik’ewa tayi ta fita itada Walida data kira.
Suna fita aunty Hannatu tace, “Wlhy Jiddah kin more da abokiyar zama ba irin namuba da kullum fitina bata k’arewa, dan ALLAH kema ki kwantar da hankalinki Ku zauna lafiya, nasan kishi abune mai zafi, amma inka had’a da hak’uri sai ALLAH ya sauk’ak’a maka, ita kanta nasan tanajin zafi, amma take dannewa saboda tasan mutuncin kanta”.
Kan Jiddah a k’asa tace, “Insha ALLAHU aunty zan kiyaye, kumani wlhy bana wanijin haushinta, dan tanada kirki”.
Dariya sukayi, Aunty Zulai tace, “Zakijine Jiddah, har yanzu akwai saurankine, bakigama tantance abinda akema kishinbane ba, babu macen da zatace bata kishin mijinta ai”.
Balu zatayi magana su Maimuna sukayi sallama, hakanne ya sakasu barin maganar, ruwane ta kawo musu sai zo6o data dafa d’azun da safe da Aliyu yace yanaso, saita had’a musu shi yanzu takawo musu, akan shid’in saita data masa wani kafin ya dawo.
Sallamar su Yaruwaiya ce ta karad’e gidan, Maimuna talek’a tana amsawa, suma cikin fara’a take musu sannu da zuwa, suma suna amsawa cikin mutuntawa da sakin fuska.
Sun shigo da tarkacen da aka k’arasa sayama Jiddah dakuma freight d’inta madaidaici ruwan toka.
Sannu sukayiyyi musu sannan sukai gaisuwa da Maimuna tafita domin nema musu d’an abinci mai sauk’i.
Zarah da bakinta baya iya shiru ta kalli Jiddah tana fad’in “yaya Jiddah mi akayi miki? Dan dagani kuka kikayi amma? Idonki duksun kumbura fa”.
Rasa amsar da Jiddah zata bata tayi, kafin kuma wani ya bata amsa cikin manyan takuma d’auki kwalin maganin da Jiddah tasha na rage rad’ad’i da ciwon jiki tana dubawa, tad’ago zata kuma jeho wata tambayar Aunty Saudah ta dakatar da ita, “K akku ya isa haka da ALLAH, batajin dad’ine ko dole saikinji mike damun Nata?”.
“Yi hak’uri aunty Saudah, nifa kawai dana ganta wani irine, sainake ganin ko wani abu wani yamata, kinsan mai kishiya, gakuma hardasu maganin ciwon jiki, yaya Jiddahr ce tacika sanyi, naga kuma kishiyar nan tata akwai shegen way…”
Kulli Yaruwaiya tayimata a baya, “Zarah ki iya bakinki, banason maganar banza fa, irinkune dangin dake had’a fitina a gidajan y’an uwanku idan sunada abokiyar zama, wlhy koda wasa karna sakejin wannan banzar maganar akan abokiyar zamanta”.
Kai Zarah ta d’aga tana tura baki da shafa inda Yaruwaiya ta doketa, su aunty Saudah ma duk fad’a sukai Mata akan hakan da nuna Mata rashin k’yautawa.
Walida tace, “Wlhy matarnan tanama da kirki, wace macece za’aima kishiya a wannan zamanin ta iya dannewa ta kwar6i kishiyar da danginta kamar haka?”.
“Wlhy gaskiyarki Walida, aike kinfi Zarah hankali”.
“To maganar ta isa hakanan, a canja da wata kuma”.
Daga nan suka saki maganar suka koma wata daban, sunayi suna bud’e kayan, wasu na gyagygyarasu inda ya dace. Hakanne yasaka Jiddah d’an sakin jikinta, amma tak’i yarda ta tashi ko nan da can.
Kusan awa d’aya saiga Maimuna da kular abinci babba da zata iya d’aukar abincin dazai wadatar dasu, duk sukai Mata sannu da godiya.
Murmushi kawai tayi, dan hankalinta yakwanta dasu, yanda suke girmamata, dukda yawanci duk san girmeta, Zarah ce kawai takula kamar bata sakin jiki da ita sosai, amma hakan bai dametaba dan k’aramar yarinya take kallonta, kuma baizama dole dama kowa ace kamasaba.
Bayan fitarta sukayi haramar sallah, yayinda akabar wasu a kicin suna k’arasa gyarawa.
Aunty Saudah ta kalli Jiddah tana fad’in “Wane d’aki kuke kwana Jiddah?”..
Da hannu ta nuna mata kamar zata nutse dan kunya.
“A to bara muyi amfani da wannan mu kenan, wancan yazama Na k’aninmu ai”. ‘cewar Aunty Nafisa’.
Dariya sukayi irinta shak’iyanci suka shige. Jiddah k’in tashi tayi saida taga sun shige, su Zarah kuma hankalinsu na a kicin sannan ta lalla6a d’ayan d’akin domin yin salla.
Bayan an idar da sallah Aliyu ya shigo gidan, saida yafara shiga sashen Maimunatu sannan, itace take sanar masa zuwan y’an uwan jiddahr.
Hakanne yasashi zuwa dansu gaisa, amma saiya iske falon shiru, sai maganganunsu da yake jiyowa a kicin da d’ayan d’akin, kamar zai koma da baya saikuma ya nufi d’ayan d’akin da Jiddah take, a nufinsa saiya kirata a waya dan zatonsa tana kicin ko d’ayan d’akin da yakejin firarsu.
Jiddah dake canja kaya duk zatonta Zarah ce ko walida, batareda ta juyoba tace, “Zarah zoki jamin zip d’inan sama”.
Murmushi Aliyu dake tsaye yana kallonta yayi, yatako a hankali zuwa gareta…………….✍????
_Naga kuna Neman shiga rud’ani akan buk d’in da kuka gani jiya, wancan sunansa *WUTSIYAR RAK’UMI…* Na kud’ine da zamuyi Na k’ungiya, so dukmai buk’ata zai sayane, guda biyarne muka fitar, pages na jiya kuma d’and’anone????, ciwon Kai ya hanani yimuku typing jiya????????♀_.
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????