MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 51 to 60

          Fitowan Jalila daga Toilet idanun ta suka sauka a kan mijin ta. Ɗan kallon sa tayi na ɗan soconni zuciyar ta cike da tausayin sa, har zurmawa yayi tsaban zullumi da tashin hankali na rashin MEEMA, gaba ɗaya ya kasa kwantar da hankalin sa kullum a tafiye yake wajen ganin an samu inda take. Sai da ta share hannayen ta da ƙaramin towel kafin ta isa bakin gadon a inda yake zaune ta zaunaHakan yasa ya ɗan ƙyafta idanun sa yana mayar da su kanta, kana kuma ya gyara sosai yana zama

“Abban Habeeb don Allah ka rage damuwar nan, kwata-kwata ba na jin daɗin ganin ka a haka, yanzu tunda ka shigo nake tambayar ka in kawo maka abinci? but kayi shiru.”

“Jalila ba na jin yunwa ne ko kaɗan, ki bari zuwa anjima zan ci.”

“Ok to in haɗa maka ruwan wankan ne?”

Girgiza mata kai yayi da cewa, “no bar shi.”

Numfashi ta ja kawai tana ɗauke kai daga kallon sa

“Ina ganin gobe ya kamata ku koma gida saboda makarantar Habeeb, ki haɗa kayan ki ku bi jirgin safe.”

“To.” Tafaɗa tana kallon sa, sai kuma tace, “amma Abban Habeeb don Allah ka cire damuwar nan haka insha Allahu za’a ganta in Allah ya yarda, idan har kidnappers ne suka ɗauke ta da yardan Allah zasu nemo mu, Ni dai fata na ka cire damuwar nan a ranka.”

Kallon ta yayi fuskar sa babu walwala yace, “muddin na samu waɗanda suka ɗauki daughter wlh tallahi bazan bar su ba, duk sai na kashe ƴan iska.” Ya ƙare maganar da irin fushin nan nashi

Hakan yasa ta ɗaura hannayen ta a kan nashi, ba dai tace uffan ba sai kallon sa da take yi

“Ki haɗa min ruwan wankan zan sake fita in koma wajen ƴan sandan can, ƴan iska su ma har yanzu sun kasa taɓuka komi, ban ga amfanin su ba, zan tashi tsaye in Yi da kaina tunda baza su iya ba.” Ya ƙare maganar yana tashi da hanzari ya soma cire rigan jikin sa

Jalila ita kuma tashi tayi ta wuce Toilet ɗin zuciyar ta duk babu daɗi, suna cikin matsala gaskiya musamman ma ita tunda mijin ta ya fi kowa tashin hankali, ko lokacin kansa yanzu be samu kullum yana tafe zuwa Ofishin ƴan sanda, damuwa tayi masa yawa wanda har ya shafi zamantakewar su dole itama ta shiga damuwar, fatan ta da burin ta yanzu a samu ganin MEEMA domin sauwaƙewan wasu al’amuran. Bayan ta gama haɗa masa ruwan ta fito ta sanar mishi sannan ta wuce ta fita ta sauka ƙasa.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

          “Wai yanzu Luwaira me kike jira ne har yanzu da baza ki sake tura masa wani saƙon ba? Allah Ni kin fara bani haushi.” Sai ta ja dogon tsaki tana ƙarawa da faɗin, “ki zauna kwaɗo zai miki ƙafa, yanzu damar ki ne kika samu tunda har kika ce yarinyar da yake so an neme ta an rasa, wlh wlh kisan inda kika kwana tun kafin ki rasa chance ɗin ki.”

“To Abida ya kike so inyi? Na fa tura mishi saƙon he’s still haven’t received a reply.”

“To nace miki ki sake tura masa wai me kike jira? Baki yi masa bayani gamsashshe ta yanda dole zai gane abin da kike nufi ba taya zai yi tunanin ba mistake ne kika yi ba?”

“Kuma fa haka ne ko?” Tafaɗa tana ware ido a kan Abidan. “Allah kuma sai yanzu tunani na ya je a kan hakan domin kwata-kwata be sanja min fuska ba, ko kaɗan be nuna min wani yanayin da zai saka in gane ya ga saƙo na ba. But bari in sake tura wa.” Wayan ta ta ɗauka ta soma yinƙurin rubuta saƙon domin ta tura masa

Abida tace, “and apparently you want to miss him wlh, ki zauna kina sakin leɓe zaki ji a salansa al’ƙur’an.”

Hannu ta kai Luwairan ta duke ta a cinya tana cewa, “ke dai baki da dama wlh.”

“Ato Ni gaskiya nake faɗa miki kar ki ɗauki magana ta a wasa wlh.”

Luwairan bata ce komi ba sai da ta gama rubuta text ɗin kafin ta ɗago wayan tana nuna mata da cewa, “kin gani yayi?”

Amsa tayi ta karanta tace, “yauwa ko ke fa, wannan ai dole ya san da shi kike yi, bari in tura masa.” Sai ta tura tana kallon Luwairan da cewa, “sai mu jira amsar shi kuma.

              Daga nan suka sanja hiran nasu duk a kan yarinyar da yake so ɗin wato MEEMA, duk da har yanzu Luwairan bata san wace ce ba. Har suka gaji suka tashi daga wajen shaƙatawan da ke cikin school ɗin suka koma class babu reply ɗin Umar Faruk, duk Luwaira ta gama damuwa domin a tunanin ta, “kar dai ace ya sake gani ne bazai ce mata komi ba?” Shirun sa shi ne babban tashin hankali a wajen ta, gwara ya faɗa mata halin da take ciki ko zata san madafa

Abida ce me kwantar mata da hankali a haka har suka gama lecture ɗayan da ya rage musu. Sannan suka fito zasu tafi. Abidan tace, “su wuce gidan su domin ta yiwa Auntyn ta barka.” Kasancewar ta haihu yau. Shiyasa suka tafi a motan gidan su Abidan

Yayinda Luwaira ta cewa nata drever’n, “ya je zata kira sa ya ɗauke ta idan zata dawo”.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

               Umar Farouk yana tsaka da meeting ne a lokacin da Luwaira ta tura masa text, shiyasa be duba ba sai da suka fito ya koma katafaren Office ɗin sa wanda ya gaji da haɗuwa don kyau. Bayan ya zauna a luntsumemen kujerun da aka jera a Office ɗin domin huta wa ya ɗauki wayan yana duba wa da zummar kiran Hashim. Sai dai cin karo da saƙon Luwaira ya matuƙar firgita masa lissafi domin yanda tayi amfani da kalamai me nuni da tabbas da shi take yi, wanda har sunan sa sai da tayi amfani da shi, shiyasa lokaci ɗaya ya ɗauke wuta yana lumshe idanun sa, shiru yayi kawai yana faman tunani a ransa, ba komi ke dawo masa a rai ba sai mu’amalar su tare, a haƙiƙanin gaskiya a yanda ya nutsu yana tunanin ta sai yanzu ya gane wasu halaye nata wanda take yawan nuna masa da zai tabbatar da cewa tabbas tana ƙaunar sa, sai dai shi be taɓa kallon hakan da wani manufa ba domin ya ɗauke ta tamkar ƴar uwan sa na jini wacce suka fito ciki ɗaya, ba ya tunanin akwai irin wannan alaƙar da zai shiga tsakanin su shiyasa ko kusa be taɓa kawo wai zai iya son ta ba. Idan ko haka ne akwai matsala dole ne ya ja mata birki domin gudun ɓacin rana, shi kwata-kwata ma be taɓa mata kallo me kama da soyayya ba, kuma ba ya jin a ransa zai iya auran ta tunda ita ɗin ƙanwar sa ce, but me zai faru idan Momy ta ji zancen nan? Ace ɗiyar ta tana son shi kuma ya kasa amsar tayin ta? Nan da nan sai kansa ya hau zafi sakamakon wani irin damuwa da ya tabaibaye shi a yanzu-yanzu, kasancewar sa wanda be iya saka abu a rai ba yanzu sai ya cutar da shi, zancen soyayyar Luwaira ya tsaya mishi a rai wanda yake jin shi nan da nan ya rasa walwalan sa da jin daɗin sa, dama ba a cikin mood ɗin shi yake ba, daƙyar ya iya kawar da zancen nata zuciyar sa na masa zafi ya danna wa Hashim kira. Ring ɗaya ya ɗauka sai suka soma waya yana tambayar sa inda yake? Daga nan kuma suka yi sallama bayan ya sanar masa, “idan ya koma gida zai zo ya same sa.”

Har ya ƙarisa zaman sa a Office ɗin ya rasa madafa. Daga ƙarshe a haka ya koma gida, sai dai ya kasa zuwa Part ɗin Momy kamar yanda ya saba illa wuce wa nashi Part ɗin da yayi

Yau su Hafsah suna Part ɗin a zaune suna wasa. Kasancewar tunda suka dawo school da suka je Part ɗin Momy Talatu me aikin ta ta cire musu kaya ta basu abinci suka ci, sai suka dawo nan tunda Momy ko bi ta kansu bata yi ba, tana ɗaki ta ƙule ta bar su nan, shiyasa da suka gaji suka dawo nasu Part ɗin. Suna ganin Dadyn nasu sai suka nufe shi suna mishi Oyoyo

Dauriya ya aza wa kansa yana yalwata fuskar sa da murmushi, kana ya soma jan su da hira yana tambayar su school? Daga ƙarshe kuma sai ya zame jikin sa ya bar su a nan ya wuce ɗakin sa, wanka ya fara yi sabida huce gajiya kafin ya saka farar Singlet da dogon wando Robber coffee color da fatsi-fatsi kaɗan na kalan ruwan ƙasa a jiki. Sannan ya sauko ƙasa ya nufi dainning inda aka jera mishi abinci. Kasancewar yanzu babu kukun shi shiyasa Talatu take mishi abinci ta zo ta jera masa a nan Part ɗin tunda ba ya cin abinci a can wajen Momy, sai dai ko yaran sa wani lokacin. Yanzun ma yana zama suka biyo sa suka hau mishi surutu, dayake jikin sa babu daɗi shiyasa kaɗan-kaɗan yake iya biye musu yana tusa abincin a baki kamar ba ya son ci. Sai kuma can ya dubi Hafsah yace, “ta je ta kira mishi Luwaira idan ta dawo school.”

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button