Ahmed MusaLabarai

Yanzu haka an kawo kudin aure na amma hankali na yana kan Ahmed Musa, Wata budurwa ‘yar Kano

Wata budurwa ‘yar asalin Jihar Kano ta bayyana sirrin zuciyar ta ga wani shafin Instagram, Diary of Northern Woman.

Kamar yadda ta shaida ta hanyar tura wani sako mai tsayi mai kama da wasika inda tace ta kwashe shekaru 6 tana fama da son fitaccen dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa, sai dai bai san tana yi ba.

A cewarta, kullum soyayyar ta gare shi kara karuwa take yi duk da an sanya mata rana a watan Mayu zata yi aure amma har yanzu bata hakura ba.

Ta ce a rashin samun Ahmed Musa yasa ta yanke shawarar yin auren amma tana fatan Ubangiji ya hada fuskokin su.

Kamar yadda ta tura wasikar wacce ta fara da sallama tare da sanar da mai shafin, wacce ita kanta sai da ta yi mamakin irin wannan soyayyar.

Kamar yadda ta bayyana:

“Malama na rasa ta inda zan fara, nidai Allah ya jarabce ni da son Ahmed Musa dan wasan Kwallon kafa, tun ina da shekara 18, bana kula kowa.

“Duk wanda ya ce yana so na tsanar sa nake, saboda ni hankali na yana kan Ahmed Musa, son maso wani koshin wahala.

“In takaice miki zancen dai malama, yanzu haka shekaru na 24, kuma son nasa sai abinda ya karu daga Sarki Allah, yanzu haka an kawo kudin aure na, InshaAllah watan Mayu ne bikin.”

Ta ci gaba da bayyana cewa har wanda za ta aura ya san tana son Ahmed Musa.

“Amma wallahi a rashin Ahmed Musa zan yi auren nan, saboda wanda zan aura ma ya san kaunar da nake wa Ahmed Musa.

“Wallahi malama har kuka nake ina tausaya wa kaina. Abinda yafi ban mamaki bai sanni ba, amma kullum kara shiga raina yake. Ina mai tabbatar miki da cewa, wallahi dason bawan Allah nan zan mutu wallahi Allah.”

Ta bukaci a taya ta addu’a kuma idan har akwai wanda ya san dan wasan kwallon ya taimaka ya sanar masa ceqa akwai masoyiyarsa a Kano wacce take son sa fiye da komai.

Daga LabarunHausa

 

 

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button