KYAWUNA JARAFTA TA 1-END

KYAWUNA JARAFTA TA Page 11 to 20

Dakinshi yawuce, bude kofa yayi yashiga dakin Mum na zaune kan kujera itakuma Nana tana zaune akasa tana share hawaye danhar lokacin kuka take ganin Abba yashigo yasa gabanta yacigaba da faduwa dan gabaki dayansu suna tsoron mahaifinsu danko kadan baida wasa sanan yanada zafi. Maida kofan yayi yarufe sanan yashigo ciki har lokacin kanta nakasa sanan yawuce yazauna kan kujeranshi yana facing bata, cikin kakkausan murya yace “maiya hadaki da kanwarki Du’a Nana”?Hawayenta tashare cikin sheshekan kuka tace “Abba dazu Muhsin yazo na shimfida mai dadduma a garden shine nakoma nadauko zobo ina zuwa naganshi tareda Du’a…..” yanketa Mum tayi tace “fadama Babanku komi kina bobboyemai kikaga dai Du’a ajikinshi” wani irin kallo yama Mum sanan yace “kika kara magana batare danabaki izinin kiyiba wlh saikinyi mamakin abinda zan miki” yajuya yakalli Nana yace “ina jinki” sake share hawaye tayi tace “Abba tarena ganshi da Du’a babuma dan kwali akanta yarikemata hannu yana kokarin tabamata gashi, shine Du’a na ganina tahau kuka wainace yasaken mata hannu, sakinta yayi ta tafi shine yacemin waishi bazai aureni ba wai Du’a yakeso ita zai aura yanzu bayasona waizaije yagayama babanshi” shiru tayi takai bayan hannunta ta goge wasu sababbin hawayen dasuka zubomata. 

Gyara zama Abba yayi ranshi amugun bace yana kallonta yace “dago fuskanki ki kalleni nan” girgixa mai kai tayi takasa, hakan yasa yadaka mata tsawa yace “I said look at me” dasauri tadago kanta takalleshi jikinta har bari yake tsabagen tsoro da shakkan Abban ta yace “so sabida namiji ne kike neman kashe blood sister ki, da Allah bai kawoni gidan nanba dayau kinyi kisan kai eh!” yasake dakamata tsawa kana ganin yanda yake maganan kasan ranshi abace yake, yace “to the extend kina ciremata riga exposing your fellow sister body kannenku su ganta, Nana is that how I train you eh answer me” fashewa tayi da kuka sosai tace “Abba kayakuri bazan karaba” girgixa mata kai yayi yace “kece y’ata mace tafarko yau idan namutu I believe kece zaki kula dasauran kannenki u will be their mother but look at what you did today, sabida namiji eh? sabida yace bazai aureki ba and so what zaki kashe yar uwarki ur blood sabida wani eh? Saina hukuntaki sosai Nana, stand up jeki kawomin wayanki, your laptop ki kawomin ATM card dina danabaki” fashewa tayi dakuka sosai dan babu abinda yafi tadamata da hankali irin wayan dawani wayazata kira Muhsin su shirya, ita karan kanta Mum saida ta girgixa amman takasa magana dan taga ranshi inyay dubu yabaci. cikin kuka Nana tace “Abba dan Allah kayakuri nayi kuskure amman namaka alkawari bazan karaba” wani kallo yamata yace “you know my principle bana dukan yara, but kika bari natashi daga wajen nan batare dakinje kin kawo what I asked for ba sainamiki jina jina” wani kallo Mum tamata na alamun taje takawo hakan yasata tashi tafita bata bata lokaci ba tadawo takawo komai kujera yanuna mata yace “keep them there and leave this room, sanan dagayau!” yajuya yakalli Mum yace”ki sallami Uwani duk wani aikin Uwani ita zata dingayi bazatabar gidan nanba saita gama kodako zatai lattin lectures get out” dasauri tajuya tafita tarufo musu kofan.

Wani kallo yabi Mum dashi yace “I am so disappointed in you Hajara, halinki nabani mamaki and ki sauraren kiji bazan zauna inaji ina gani ki rabamin kan yarana ba, wlh duk randa kika kara attempting abinda kikayi yau kinasa anacirema yarana mata kaya kina kiran yara suyi ihu wlh wlh saina rabu dake take this as a warning” cikin kwantar da murya tace “kayakuri Alhaji na yarda nasan nai kuskure I know I took everything far, but raina abace ne maganan da Kaka keyawan fadi duk yadawomin kai, wlh Alhaji da gaske Du’a yar aljanu ce to inba hakaba ya za’ayi Muhsin dake tareda Nana kusan sjekaru biyu kenan yau kawai daga ganin Du’a yace ita yakeso yafasa auren wacce yasani for years, dududu bikinsu saura wata daya, tuntuni Kaka tace ka tattara yarinyar nan ke korata chan duniya inba hakaba bala’i da masifu iri iri sundinga samunta gidan nan kenan, yanzu maganan Muhsin baiwani dadani da kasaba amman what if dagaske yake eh? da gasken gaske yake shi yafasa auren Nana Du’a yakeso bahakan ya tabbatar mana itadin yar Aljanu bace ba kenan, wlh indai aka fasa auren nan saina kira Kaka na sanar da ita komi gwara tun yanzu nagaya maka sabida kar bayan kaji nayi kaga kaman na yaudareka ne” “tashi kifita daga dakin nan” Abba yay maganan cikeda fada, tashi tayi tace “narasa me kakeyi da yarinyar dakai karan kanka kasan bataka bace agidan nanba saisama baka ambato sunanta cikin y’ayan ka, hakanan wlh koma mezai faru saidai yafaru I am a mother bazan zauna inada zankada zankadanyanmata ba sukasa aure ba sabida yar aljanun da aka haifa maka agidan nan, gaskiya nake fadi I can go to any limit dannai protecting yarana, grounding nata adaki doesn’t solve anything dan gashinan fita take causing trouble, the best thing is tabar family mu takoma chan family su na aljanu” tai maganan tana bude kofa tafice abinta, gabaki daya duka abinda tafadi yajisu.

Ajiyan zuciya yasauke ahankali tareda fuzarda iska daga bakinshi yadade ahaka zaune sanan yatashi kaman an tsikareshi, bude kofa yayi yafice, hanyar dakin Mami yayi, ahankali yasa hannu yabude dakinta wani kamshi ne yamai sallama, shiga ciki yayi tareda maida kofan yarufe, tashi tayi tsaye daga kan gadon datake zaune idanunta sunyi jajir takakalo murmushi tace “sorry Dadyn Hamad bankawo maka abincinka ba” tazo da sauri zatabi ta gefenshi tawuce hannunta yakamo sanan yajawota jikinshi fuskanta ya tallabe yace “you’ve been crying ko jibi yanda idanunki suka kukkumbura” girgizamai kai tayi zatai magana saiga wani kukan kuma hakan yasa dasauri yasata ajikinshi yana bubbuga bayanta batare dayayi magana ba, tadade ahaka sanan tadago ta kalleshi tace “Abban Hamad kafin muyi aure ai kokai saida aka tabbatar maka dana warke ko naji sauki, babu any form of jinn ajikina, bana wasa da azkar safe rana da dare, yau shekara nawa muna tare ba kara having any form of attack ko mafarki ba, but yau nafara tunanin kodai sune baban Du’a di…….” hannu yadaura mata akan baki yace “shiiiiii banson maganan nan, kintaba ganin jinn sun haifi mutum? nine mahaifin Du’a, kawai Allah yabamu y’ace daban damu nothing more nothing less” girgizamai kai tayi tace “what if Muhsin da gasken yafasa auren Nana Yaya zamuyi? how are we going to explain this to the family Yaya zamuyi” saiga wasu sababbin hawayen, yatsanshi yakai yasharemata hawayen daya zubomata yace “when we get to the bridge we will know ta yanda zamu tsallaka shi karki damu kanki kinji” gyadamaikai tayi ahankali wasu hawayen na zubo mata tace “Dadyn Hamad Du’a batajin magana, we’ve grounded her for years now tundaga JSS3 har zuwa yau, amman kwanan nan tasoma sneaking tana fitowa, hakanan inaji araina something is about to happen, what if tasake samin attem………” hannunshi yadaura kan lips dinta yace “stop talking, and stop thinking negative, idan tafarka nida ita we will have some serious talk, yanzu all abinda nake bukata is natsuwa dan banda ita ko kadan, ina bukatan natsuwa sanan nasamu nayi tunani, bari nasami natsuwa dake” yana maganan yadauketa zuwa gado bashi yafito daga dakinba sai wuraren 5 ya chanza kaya zuwa jallabiya fuskanshi tayi wani annuri alamun akwai full natsuwa taredashi yasauka zuwa falo, Mum na zaune a falo tadauke kai kaman bata ganshi ba.

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button