NOVELSUncategorized

DIYAM 49

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Nine : The Utterance

Inna taga ta kanta a gurin jama’a jiya. Duk inda na shiga kowa kokawa yake yi da abinda Inna tayi. But to me, laifin Inna a yanzu guda daya ne, rashin sauraron Diyam kafin ta yanke
hukunci bawai hada Diyam da tayi da Sadauki ba. Wannan kuma shine halin kusan 70% na northern mothers. Kullum su dai burinsu shine yarsu ta zauna a gidan mijinta kar ta kashe auren ta dawo gida ta zauna a gabansu. But what if the marriage is not working? What if she is buying her ticket to hell fire instead of paradise a cikin auren?

And Saghir, Saghir yayi laifuffuka da dama a baya but a yanzu laifinsa shine dukan Diyam. Nothing, nothing gives a husband the right to hit his wife. Duk kuma namijin da yake dukan matarsa to ba mijin aure bane ba, ballantana mata mai ciki? Hmmm

Then Sadauki. Na lura Sadauki ya zama shafaffe da mai a gurin readers, sam basa ganin laifinsa komai yayi daidai ne dan ina jin few mutane ne naga sunyi comment akan laifin Sadauki. Sadauki is rather rude and very authoritative. Ba shi da right din da zai sa a rufe Saghir, yes Saghir yazo gurin aiki drunk kuma ya fadi maganganu wadanda babu wanda ya gane in banda shi Sadauki da ake magana a kansa. Abinda ya kamata Sadauki yayi shine yasa ka security su fitar dashi waje, in ya ga dama ya hada masa da takardar kora daga aiki. But bashi da right din kaishi station a rufe shi kuma wai without bail, saboda yana da kudi?

Let’s continue

Na rufe fuskata ina girgiza kaina da sauri. “Inna kar kiyi min haka dan Allah. Inna ki tsaya ki saurare ni ki fahimce ni kar ki mayar dani gidan Saghir in na koma wallahi mutuwa zanyi” tace “da baki mutu ba shekara da shekaru sai yanzu da Sadauki zaiyi aure shine zaki mutu?” Sai ta mike zata shige daki nima na mike da sauri na rike hannunta da hannu na daya dayan kuma na daga mara ta da shi nace “Inna nayi bari jiya” sai ta juyo tana kallo na ido a bude, ta taba fuskata da hannunta tace “bari Diyam? Ya akayi kika san bari ne kinje asibiti?” Na gyada kaina nace “naje Inna, su suka tabbatar min da cikin jikina ya fita Inna. Saghir ya fitar min dashi” ta dan bata rai cikin rashin fahimta tace “Saghir? Ta yaya Saghir zai fitar miki da ciki?” Nace “dukana yayi Inna, dukana Saghir yayi ya buga ni da jikin bene ya kashe min baby na, kamar yadda shaye shayensa ya jawo mutuwar yan biyu”.

Sai ta kama hannuna muka zauna tace “Diyam, kin tabbatar abinda kike gaya min gaskiya ne? Me ya hada ki da Saghir har ya dake ki haka?” Na shafa fuskata sai itama ta saka hannu ta taba fuskar tawa, side din da Saghir ya mare ni, na dan yamutsa fuska alamar zafi sai naga idonta ya kawo kwalla amma sai tayi sauri ta mayar da ita. Tace “me ya haɗa ku nace” sai na bata labarin messages din Sadauki. Tana girgiza kai tace “me yasa? Me yasa zaki ajiye sakon Sadauki a wayar ki har mijinki ya gani bayan kuma kinsan yasan tsakanin ki da Sadaukin” nace “inna na fada miki menene a cikin sakon nan, babu wata kalma ko daya data kauce hanya a ciki kuma in na goge su ai kamar bani da gaskiya kenan. Ina son Sadauki na sani, amma Allah ne shaidata cewa ko sau daya ban taba tunanin yin sabon Allah da Sadauki ba. Kuma ke kece shaida, Sadaukin nan tamkar dodanniya haka nake a gurinsa, ko kallon inda nake baya yi. Shi dai ya zarge ni ne saboda shi din yasan shi mai laifi ne, abinda yake cikin tasa wayar idanuwa ma ba zasu iya gani ballantana hankali ya dauka” Inna tace “akan wannan maganar ne Sadauki ya sa aka kama shi?” Nace “ni ban sani ba, amma ina jin akanta din ne. Ya dai fita a fusace yace sai ya wulakanta Sadauki, tun daga nan kuma bai dawo ba sai da safe Kabiru abokinsa yazo yace mana yana hannun yan sanda” Inna tayi shiru tana tunani sannan tace “yace za’a sake shi gobe, Allah ya kaimu goben, ya fito sai yazo yayi bayanin dalilin da yasa ya dake ki. Kar ki goge messages din ki barsu saboda shaida a gani cewa babu abin duka a cikin su”.

Sai naji raina yayi min wani irin dadi, babu abinda yafi dadi irin a fahimce ka babu kuma abinda yafi ciwo irin ace kana da gaskiya amma a hana ka tsarawa ballantana a fahimce ka. Ina ma dai iyaye zasu ke bawa yayansu wannan damar? A fahimci kowa sai a hada both parties ayi wa kowa fada dai dai da laifinsa? Ba wai ace da mace ki komaki cigaba da hakuri ba tare da ko murya an daga wa shi namijin da yake maltreating dinta ba, wannan tamkar ana ce masa ka cigaba da maltreating dinta ne.

Amma dana fara tunanin abinda zai iya faruwa gobe sai naji duk hankali na ya kuma tashi. Nasan halin Saghir sosai nasan zai iya jujjuya maganar gabaki daya ta koma laifina kuma na tabbatar iyayen mu musamman mazan bayansa zasu bi, musamman in nayi la’akari da irin kiyayyar su ga Sadauki, da kuma soyayyar da suka san ina yiwa Sadauki, tabbas komai Saghir ya gaya musu yarda zasuyi. Ni kuma ba yardar su ko rashin yardar su ce problem dina ba a’a tirsasani in koma gidan Saghir shine problem dina. Na gama auren Saghir, ba zan koma gidan Saghir ba. Wannan is my decision. Ni a yanzu auren Sadauki ko rashin auren Sadauki ko shi kansa Sadaukin basa gabana. Abinda yake gabana shine rabuwa da Saghir.

Inna tace inje in kwanta in huta a daki. Na tashi na shiga ina jin Asma’u tane cewa “Inna amma ba za’a mayar da Adda gidan can ba ko?” Inna tayi shiru bata ce komai ba. Na kwanta kawai sai hawaye ya fara zubo min ina lissafin abin da zanyi in akace sai na koma. A ciki har da guduwa na lissafa amma inna gudu inje ina? Yan uwan uwata dai sune yan uwan ubana sune kuma yan uwan mijina. Sai kawai na yanke shawarar in aka matsa min akan in koma gidan Saghir to zan gudu gurin Sadauki, inje in tuna masa da amanar da Baffa ya bar masa ta kula damu, sannan in tuna masa cewa ni ma fa yar Baffa ce ba wai Asma’u ce kadai yarsa ba. In kuma roke shi daya shige min gaba in kai karar Saghir court alkali ya raba auren mu. Yes, wannan shine abinda zanyi. 

Ina kwance Subay’a ta shigo ta kwanta a kusa dani. Sai naji tana sheshshekar kuka, na jiyo nace “Subay’a? Lafiya kike kuka? Wani gurin ne yake yi miki ciwo?” Sai tace “Mommy ki daina kuka kema” na jawo ta jikina nace “ba kuka nake ba Subay’a ido nane yake min ciwo” tace “kuka kike yi ai na sani, naji kuma aunty Fauziyya dazu da tana shirya ni zan tafi school tana waya tana cewa kunyi faɗa da Daddy shine ya dake ki kike kuka, kuma naji dazu kina fada wa Inna Daddy ya dake ki” sai na kasa ce mata komai, lallai yara duk abinda ake yi a gabansu suna sane. Ta goge min fuskata tace “kiyi hakuri Mommy, in Daddy ya dawo zance masa kar ya kara dukan ki”.

Sai na dage da addu’a sosai ina rokon Allah ya shiga lamari na ya kawo min agaji. Dan nasan in na koma gidan Saghir to ba rayuwata ta duniya ba har ta lahirar ma tangadi take yi, two zero kenan. Saboda ni dai nasan a rayuwar auren da nayi da Saghir a baya ba karamin zunubi na lodar wa kaina ba ballantana in na koma nasan bazan iya yi masa koda rabin biyayyar da nayi masa ada ba. In kuma haka ta faru to nice a ruwa dan Ubangiji babu ruwansa, laifina daban a gurinsa laifin Saghir shima daban. Kowa littafin sa daban. Dan haka sai na kwana ina kaiwa Allah kuka na.

Washegari tun safe nake saka ran wani abu ya faru amma shiru, ko ya naji anyi motsi sai in tsorata in dauka Saghir ne zai shigo gidan. In naji wayar Inna tayi kara kuwa dai inji kamar zan saki fitsari a wando saboda tsoron ko kira ne a kaina amma shiru. Da safe Inna tayi min farfesun hanta mai romo tace in cinye, na cuccusa da kyar naci dan bani da appetite sam, sai kuma ta fita da kanta taje kasuwa sai naga tayo cefanen green vegetables kala-kala tazo ta hada min miyar ganye mai naman rago ta sani naci da tuwon shinkafa tace zai kara min jini. Daga ni har ita babu wanda yayi zancen Saghir amma dai nasan duk maganar tana ran mu.

Shiru shiru har dare. Har gayi ya waye wani daren ya sake yi. Har aka kwana biyu sannan aka kwana uku, hudu, biyar, sai akayi sati daya. A ranar ne Inna tace “to ni ko Alhaji Babba zan kira ne akan maganar Saghir din nan ne? Kar dai ba’a sake shi ba har yau. Ni kuma bana son in sake kiran Sadauki kar yaga kamar ina damunsa akan sirikina yaji babu dadi” Asma’u tace “dan Allah Inna ki rabu dasu, yayi ta zama mana a cell din wa ya damu ne wai? Itama yanzu ba gashi ta samu kina kulawa da ita ba da yana nan kuwa ba vari zaiyi kije gidan ki kula da ita ba kuma ba lallai bane ya barta tazo nan” Inna tace “Asma’u kenan, ke yarinya ce ba zaki gane ba. Maganar nan fa tana kara jimawa ne tana kara karfi. Dole ya kamata in bincika inji halin da ake ciki” sai ta dauko waya ta kira Hajiya Yalwati, suka gaisa sai take tamayarta ko taga Saghir kuwa? Nan take Hajiya Yalwati tace “dama yanzu nake niyyar in saka kati in kira ki. Me ya hada Saghir da Diyam da tsohon saurayin ta kuma? Tun jiya naji ana ta maganar a gidan nan ni dai ba’a yi min cikakken bayani ba amma na fahimci kamar ko sunyi rigima ne harda su yan sanda” inna tace “Saghir din yazo gidan kenan” Hajiya Yalwati tace “yazo gidan fa, jiya nan ya kusan wuni sai dare ya tafi”.

Tunda suka gama wayar Inna ta zauna ta zabga tagumi, sai ajima tayi ajjiyar zuciya ta sake wani ragumin duk tabi ta damu kanta. Nima kuma na damu din amma ba kamar inna ba, ni damuwata shine bansan zurfin sharrin da Saghir yake shirya min ba. Muna zaune kuwa, Asma’u ta kawo mana lunch kenan sai gasu sunyi sallama. Na ajiye spoon din abincin kawai na fara ambaton Allah dan ji nayi zuciyata kamar ta dawo wuyana.

Daya bayan daya suka shigo palo, Alhaji Babba, Kawu Isa, sai kuma Saghir. Inna ta tashi tana musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa ta suka zauna. Ta gaishe su babu wanda ya amsa mata, dan haka sai naja bakina naji shiru ban gaishe su ba kaina a kasa. Kawu Isa ne yayi magana “gamu munzo Amina, mun sauke girman mu mu da muke manya munzo mun same ki tunda haka kike so. Kin bamu kunya Amina, Allah yaji kan hardo da inno, Allah yaso ba zasu ga wannan rana ba ba zasu ga wannan bakin ciki ba na abinda suka raina suka rike kamar abinda suka haifa kuma yazo yana yi musu bita da kulli. Amina yanzu ke wato duniya ta bude miki ido ko? Yanzu wato kudi sunfi miki yan uwanki ko?” Nace “Kawu….” Inna ta daga min hannu tace “kar ki sake inji bakin ki” sai ta juya tace “hamma kudi ba komai bane ba akan zumunci da halacci. Amma yanzu ni me nayi da har kake cewa na zabi kudi?” Alhaji Babba yace “me kika yi?” Ya nuna ni yace “wannan bata gaya miki abinda ya faru ba?” Inna tace “ta gaya min, ta gaya min komai har dukan da Saghir yayi mata da barin da tayi ta gaya min” Kawu yace “kuma ta gaya miki labarin cin amanar Saghir din da take yi tare da wannan tsinannen yaron? Ko kuma dama kin riga kinsan wannan labarin?” Inna ta girgiza kai tace “shi Saghir din ne yace Diyam tana cin amanar sa da Sadauki? Zai iya rantsewa da Allah cewa ya gansu suna cin amanar sa? Ko kuma zai iya rantsewa cewa sakon daya gani a wayarta ya nuna wata alama na cewa suna cin amanar sa” Alhaji Babba ya dubi Kawu Isa yace “kaji ba? Na gaya maka dama ta sani sarai. Da hadin bakinta ne akeyi komai. Ba dai yaron yayi kudi ba? Ni kuma na talauce” Inna tace “in kuka ce haka baku kyauta min ba. Yaron nan, duk cikin ku babu wanda ya kuntata rayuwarsa kamar ni. Tun yana cikin zanin goyonsa bana binsa da komai sai harara da muguwar magana amma me? Shine ya dauke ni a lokacin da Saghir ya watsar dani. Ya baku labari? Naje gidansa duba Diyam ya kore mu ni da Asma’u cikin dare ana ruwan sama. Badan Allah ya bude mu ba badan Allah ya kawo mana Sadauki ya taimake mu ba da yanzu babu Asma’u a duniya. Sadauki ne ya taimaka mana. Tun daga ranar kuma nayi nadama mai tsanani na kuma yi alkawarin yin rikonsa tamkar yadda zanyi rikon dana. Wannan ne yasa tun ranar da Diyam tazo min da maganar na kira shi nace ya sa a saki Saghir, sannan kuma na zauna ina jiran shi Saghir din yazo yayi min nasa bayanin inji” Kawu Isa yace “to mu yaje yayi mana bayani, ya gaya mana komai har yadda shekara da shekaru Diyam take tare da tsohon saurayinta, ta saka ya bashi aiki dan suji dadin cin amanar sa, yanzu kuma mun kuma tabbatar cewa duk abinda ake yi da sanin ki Amina. Wato ke naki salon sakayyar kenan a bisa dukkan alkhairan mu a gareki ke da yayanki. To gasu nan mun bar miki su, gaki nan ga duniyar nan ga kuma Sadauki nan. Ba dai kudi ba? Kamar yadda nawa ya kare haka nasa shima zasu kare sai kuma muga wanne sarkin za’a bi. Saghir dai kam ya gama auren Diyam. Dama tursashi muka yi ya aure ta ba’ason ransa ba saboda muna son mu karfafa zumunci da iyalin dan uwanmu kuma muna so mu rufa muku asiri. Taje ta auri Sadaukin mu gani, ba dai mune masu daurin auren ba?” 

Na dago kai na kalli Saghir wanda tunda suka shigo yake tsaye a bakin kofa ya rungume hannayensa ya zuba min ido, ina jin idonsa a kaina amma ban kalle shi ba har saida Alhaji ya gama maganar sa sannan na kalle shi.

Sai ya tako yazo gabana ya durkusa yana kallon cikin idona yace “tunda nake a rayuwa ta ba’a taba yi min wulakanci irin wanda akayi min akan ki ba Diyam. Zan rabu dake, amma ba wai dan na hakura na yafewa Sadauki abinda yayi min ba sai dan wadanda suka ce in aure ki sun ce in sake ki. Na sake ki saki daya.” 

Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya mike da sauri. Har yakai bakin kofa kuma sai ya dawo yasa hannu ya dauke Subay’a da take kwance kan kujera tana bacci ya dora a kafadarsa ya yi waje. Na mike da sauri kamar wadda aka mintsina nace “Saghir ka bani yata” ya juyo yace “in da ita kika je gidan ba sai ki karbeta ba in gani?” Na bi bayansa da sauri. “Ka bani yata Saghir, Subay’a! Subay’a!” Sai ta farka firgigit a hannunsa ta sauke idonta a kaina. Ganin ina kuka yasa itama ta saka kuka tana miko min hannu “Mommy! Mommy” yana fita waje ya saka ta a mota ya rufe ya shiga da sauri yaja ya bar gidan tun kafin su Alhaji su karasa fitowa”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button