Labarai

Nan Gaba Zaʼa Rubuta Sunayen Mu Da Alƙalamin Zinari – Inji Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da matsaloli da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, ya na da yaƙinin cewa nan gaba za a yaba masa dangane da irin ayyukan da ya samar, ta yadda a cewar sa za a rubuta “sunayen mu da alƙalamin zinari.”

Cikin jawabin wanda ya fitar a ranar Juma’a daga Fadar Shugaban Ƙasa, Buhari ce ya na yi wa sabuwar shekarar 2022 marhabin, cike da fatan cewa wannan shekara za ta ɗara ta 2021 wajen samar da ci gaba, tsaro da inganta tattalin arziki.

“Duk da cewa mun fuskanci ƙalubale masu yawa cikin 2021, to an yi ayyukan raya ƙasa, an samar da ababen inganta rayuwar talakawa da kuma ayyukan inganta tattalin arzikin ƙasa.

“Mun maida hankali sosai wajen ganin mun cika alƙawarin nan uku na samar da tsaro, inganta tattalin arziki da kuma yaƙi da rashawa da zambar kuɗaɗe.

“Tabbas mun ci karo da matsaloli da ƙalubale, musamman ɓarkewar cutar korona, wadda ta dakushe kaifin tattalin arzikin Najeriya. Amma dai gwamnatin mu ta yi rawar gani wajen tabbatar da cewa tattalin arziki da inganta rayuwa ba su ƙara samun tawaya ba, tun bayan tawayar farko da su ka samu bayan ɓarkewar cutar korona.”

“A yanzu dai gaba ta wuce kenan, saura jiran abin da zai biyo baya. Kuma ina da yaƙinin cewa bayan za ta yi kyau, ta yadda za a rubuta sunayen mu da alƙalamin zinari.” Inji Buhari.

Dangane da matsalolin tsaro, Buhari ya ce a kullum ya na kwana da tashin jimamin waɗanda rayukan su ke salwanta. Sannan kuma ya jinjina wa ƙoƙarin da Sojojin Najeriya da ‘Yan Sandan Najeriya da sauran ɓangarorin tsaron ƙasar nan ke kan yi.

Sannan kuma ya miƙa saƙon ta’aziyyar waɗanda suka mutu ko aka kashe a hare-hare da waɗanda su ka sadaukar ka kan su wajen kare ƙasar su.

Da ya koma kan Najeriya baki ɗaya, Buhari ya nemi ‘yan Najeriya su haɗa kai domin a yi kishin kare ƙasa ta tabbatar da an ci gaba da kasancewa a dunƙulalliyar ƙasa ɗaya, al’umma ɗaya.

“Mu tashi mu haɗa kan mu domin mu yi kishin ƙasar mu, tare da kasancewa mun riƙe Najeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasar da mu ke kishin ta.”

Buhari ya yi wannan jawabi a ranar da ya sa hannu kan Kasafin 2022.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button