SUBHANALLAHI: An Haukatar Da Shi Saboda Ya Karɓi Addinin Musulunci


Sun musulunta shi da ƴan uwansa mata su biyu, Musa yakasance tun ranar da ya musulunta ya fara neman karatun addinin musulunci wanda yayi zurfi gurin karatun addini har sauke Alqur’ani yayi, kuma mutum ne mai ibada da neman kusanci ga Allah.
Wata rana aka wayi gari Musa da ƴan uwansa mata duka sun haukace wanda tunani mafi rinjaye ƴan uwansa ne wanda basu musulunta ba suka haukatar da su sama da shekaru goma sha biyar wanda babu magani babu abinci, saboda rashin kulawa har yunwa tayi tasiri akan ɗaya daga cikin matan da rashin lafiya ta kamata har Allah yayi mata rasuwa wanda suma ragowar a cikin irin wannan halin suke, domin duk sanda ya ji yunwa sai dai yayi amfani da mushe a matsayin abinda zaici da kuma kwata a matsayin ruwan shan sa.
Bashida wani matsuguni duk sanda ake ruwan sama haka yake ƙarewa akan wannan bawan Allah.
Saboda haka muke buƙatar a sanya shi cikin addu’oinmu musamman a wannan wata mai albarka, sannan duk wanda yake da damar yi masa magani da daukar nauyin abincinsa ƙofa a bude take.
Muna roƙon Ubangiji Maɗaukakin Sarki mai yaye cututtuka ya yaye wa wannan bawa nasa sannan ya sanya wannan lalura a matsayin kaffara a gare shi.
Ga mai buƙatar ƙarin bayani sai ya tuntuɓi wannan lambar: 07080806350
Daga Idon Mikiya
[ad_2]