Lu’u Lu’u 13

*13*

 

A k’ofar babban b’angaren motocin suka tsaya, da sauri suka firfito suka jeru suna jiran fitowarshi inda d’aya a ciki ya bud’e mishi k’ofa, k’afarsa d’aya ya fara zurowa mai sanye da takalmi kalar maroon k’irar turkey amma ba k’afa ciki ba, karasa fita yayi gaba d’aya cikin sauri ya tunkari shiga ciki suka rufa masa baya, saida suka kai daf da falon suka tsaya sai biyu da suka bi shi zuwa ciki, tunkarar matakalar da yayi yasa shi d’aga musu hannu alamar su dakata kafin ya shiga takawa da sassarfa kamar zai yi gudu.

D’aki na biyu a jerin corridor ya k’wank’wasa, bai jira izini ba ya bud’e ya shige dan yasan wacce ke d’akin ba zata iya bashi izinin ba, cak ya tsaya yana kallon sanyin idaniyar tashi, wani annuri ne ya ziyarci fuskarshi sanda ya d’ora idonshi akan kyakyawar fuskar dattijantakarta, a hankali kuma har sanyayyan murmushi ya bayyana a fuskar shi ba tare da sanin shi duk dan shauk’in ganin *mahaifiyarsa*.

Bai yi k’asa a gwiwa ba tunda yasan ba zata iya motsa ko da k’afarta ba yasa shi saurin k’arasawa gareta, saida ya zagaya b’angaren hagunta sannan ya durk’usa kan gwiwarshi d’aya, hannunshi na hagu yasa yana shafa gashin kan ta yana mayar mata da shi baya, tattausan murmushi yake sakar mata hannun dayan shi kuma ya sak’alashi cikin na ta, a sanyaye ya furta “Fy Mam (mahaifiya ta, a yaren Gallois).”

Farin cikin ganin mahaifiyarshi da kuma tsananin tausayin halin da take ciki yasa shi jin wata k’walla na taruwa masa a gefen idon shi, cike da k’arfin halin son kawar da ita yace ” Fy Mam kina lafiya ko?”

Idonta dake rufe ya kalla wanda yasan ba dan bacci take ba da ta amsa masa da ido, k’urawa fuskarta ido yayi cikin muryar jimami da alhini ya sake fad’in “Komai ya kusa zuwa k’arshe fy Mam, na samota dana tafi, kuma zan tabbatar na kawo miki ita har nan, bansan ko nayi kuskure ba, amma dai dole ne sarki Musail ya d’and’ani hukunci, dole ya ji rad’ad’in rashinta yayin da zai hangeta a cikin gidan nan, amma kuma babu yanda zai yi, ko ta zama ajalinsa, ko ta zama silar rugujewar duk wani iko na shi, wannan bai dameni ba, zafi da tashin hankalin da zai shiga na rashinta ma kawai ya isheni.”

Sake damk’ar hannunta yayi tare da sako hawayen daya gagara tsayar da su cikin k’unar zuci yace” Sai na d’aukar miki fansa fy Mam, a dalilinshi ne kike kwance ba kya motsa ko da yatsanki, a sanadiyarshi ne mahaifina ya rasa duk wani farin cikinshi, a sanadin shi ne na rasa d’an uwa na…”

D’ora goshin shi yayi a hannunta yana zubar da hawaye, wannan d’umi hawayen dake sauka hannunta ne ya farkar da ita, saidai ido kawai ta zuba masa tana kallon sumar kan shi, saida ya ci kuka mai isarshi ya d’ago kan shi ya zuba idonshi a fuskarta, suna had’a ido ya saki murmushi yana share k’wallan shi yace “Fy Mam, kin tashi ne?”

Ido kawai ta zuba mishi ba tace k’ala ba, murmushi shi dai kawai yake sakar mata, hannunshi na cikin na ta yana ta mammatsawa, banko k’ofar d’akin da aka yi aka shigo yasa shi d’aga idonshi ya kalli k’ofar, kan farin gemun mahaifinshi ya fara sauke idonshi kafin gaba d’aya farar fuskarsa, wani bayyanannan murmushi ya saki ya mik’e tsaye da hanzari ya tunkareshi, shi ma sarki Wudar da farin cikin ganin gudaliyarsa kuma magajinshi yasa shi bud’e hannayenshi yana fad’in “Fyddai (d’ana).”

Da fara’a shi ma ya rumgumi mahaifin na sa yace “Fy nhd (mahaifina).”

Sosai suka rumgume juna kowa na shak’ar k’amshin junansu, cike da so da k’auna sarki Wudar ya d’an bubbuga bayanshi hakan yasa suka d’ago suka kalli junansu, da farin cikin sake had’uwa da sukayi Wudar yace “Yaro na ya kake?”

Da fara’a ya sunkuyar da kai yace “Ina lafiya mahaifina, kamar yanda kake gani.”

Jinjina kai yayi yace “Ya akayi ka zo baka sanar dani ba? Baka so na san da zuwanka ne?”

Kallon fuskarshi yayi yace “Amma yanzu ya akayi ka sani?”

Da fara’a ya amsa masa da “Abokinka ne ya sanar da ni, Haman.”

D’an girgiza kai yayi tare da k’yabta idonshi alamar sam bai ji dad’i ba, nuna masa mahaifiyarshi yayi yace “Ka ga jikin na ta ko? Har hanzu Umad k’ok’ari nake akan rashin lafiyar mahaifiyarka, izuwa yanzu abun ya daina bani mamaki sai ma tsoro.”

Jinjina kai yyi yace “Mam ta kusa samun lafiya Ba, insha’Allah.”

Da mamaki sarki Wudar ya kalleshi yace “Me ka fad’a a k’arshen?”

Girgiza kai yayi alamar ba komai, sai kuma ya sunkuyar da kai yace “Ka gafarce ni mahaifi na, ni zan je b’angare na.”

Da alamar mamaki a fuskar sarki Wudar ya kalleshi yace “Sosai nake mamakin sababbin halayanka Umad, wai me yake damunka ne?”

Kallon fuskar mahaifin na shi yayi, irin kallon nan na tsaneke kallo na basira, a take kuma ya d’auke idonshi ya mayar k’asa yace “Sarki na, zan sanar da kai komai da zaran mun zauna.”

Bubbuga kafad’arshi yayi ya jinjina kai alamar gamsuwa, cikin nutsuwa yace “Ka huta da kyau, zuwa dare zamuyi tafiya.”

D’an kallonshi yayi da mamaki sai kuma ya sunkuyar da kai yace “To Ba.” Da ido ya masa izini da zai iya tafiya, a ladabce ya rab’ashi ya fita a d’akin, hadiman dake bakin k’ofar ne suka rusuna masa alamar gaisuwa, bai kula da su ba sai wucewa inda zai sadashi da na shi b’angaren.

A kasalance ya k’arasa had’add’en b’angaren shi, cike da gajiyar tafiya ya shige b’alle mab’allansa amma kuma idonshi a lumshe yana tunanin _”Ina take? Shin zai iya samunta a cikin gidan nan kuwa?”_

Ajiyar zuciya ya sauke ya bud’e idonshi tare da jefa rigarshi kan gado ya nufi ban d’akin shi yana tunanin tabbas idan suka zauna zai fad’awa mahaifinshi ya fa jima da canza addininshi.

Tunda ya fita sarki Wudar ma ya k’arasa kusa da uwar d’akinshi, sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta ya kalli fuskarta yace “Ina son ki, anjima zanyi tafiya ki min addu’a, zan je cinikayyar lu’u lu’uta, ba zan dawo gidan nan ba sai da ita.”

Sake sumbatarta yayi sannan ya fita a d’akin cikin rakiyar hadiman shi biyu dake take masa baya.

*Egypt*

Irin yanda ta ga suna d’aukaka lamarinta da kuma yi mata komai daban yasa ta jefawa kan ta tambayar *wacece ita*? Dan yanda ta ga hatta da ruwan wankanta kalarsu daban, wata irin kalar pink mai duhu ga kuma wasu furannin flowers da aka zuba a ciki, uw uba k’amshin da ruwan ke fitarwa, yanda suka tsaya a kan ta bayan ta fito suka dinga shiryata kamar yar tsana, wata doguwar riga kalar ja suka wacce kamar da tattausan leshe aka d’inka ta har jan k’asa take, kamar yanda ta nuna bata so haka suka barta da fuskarta babu kwalliya, saidai farar hodar ruwan da aka shafa mata wacce ta dace da kalar fatarta, jan bakin da suka shafa mata a leb’enta kalar ja, duk da gashinta gajere sosai haka suka shafe mata shk da mayuka suka mishi gyara mai kyau sannan suka d’ora mata kambu mai kalar ruwan zaiba kuma kamar hasken lu’u lu’u, hakan sai yasa ta fito kamar wata sarauniya tayi kyau kamar ba gobe, bandejin kanta kam wani sabo suka nad’a mata kafin su shiga take masa baya su fito.

Ta siririn corridor suka bi da ita, ko da suka kai bakin k’ofar b’angaren na shi suka tsaya, d’aya a cikinsu ce ta bud’e mata k’ofa alamar ta shiga, kallonsu tayi kafin ta tattare rigarta ta shiga takawa a hankali, kamar yar k’auye haka ta shiga k’arewa babban falon kallo, amma abun mamaki duk kyau da had’uwarshi bai kai na falon da waccen garjejen k’aton ya ce falonta ne ba a cewarta fa, tana cikin juyowa ta inda kujerun zama na alfarma kirar Italy suke kawai ta zabura tare da sakin yar k’ara tace “Ahhhhhh!”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button