HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

TYPING????

???????? HASSANA ????????

              *DA*

❣???? HUSSAINA????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

LABARI AKAN WASU Y’AN BIYU ,LABARI NE ME TAB’A ZUCIYAR ME KARATU

DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN K’AI ,SARKI MABUWAYI ME GIRMA ,INA ROK’ON KA ALLAH KASA NAFARA LITTAFINNAN LAFIYA NA GAMA LAFIYA ,KUMA ALLAH KABAWA DUBUN DUBATAR MUTANE DAMAR KARANTA SHI DOMIN SU K’ARU DA ABINDA YAKE CIKINSA

MASOYA NA NADAWO GAREKU BAYAN HUTAWAR DA NAYI LOKACIN DA NA KAMMALA SANADIN HOTO ,DAFATAN WANNAN LITTAFIN ZAI KARB’U FIYE DA SANADIN HOTON ,SAI KU BINI DAN JIN WANNAN KARON WANE SAK’O NAKE D’AUKE DASHI

SADAUKARWA

KYAN ALK’AWARI CIKAWA ,GAREKI FATEEMA SARDAUNA MARUBUCIYAR (SHU’UMIN NAMIJI) ,FEJIN FARKO NA WANNAN LITTAFI NAKINE FATEEMA ,NAGODE DA K’AUNARKI GARENI ,HASSANA D’AN LARABAWA NA MATUK’AR K’AUNARKI ,KUMA INA GODIYA DA GUDUMMAWAR DA KIKA BANI ,ALLAH YA BARKI DA SARDAUNAN KI????????????

page 1⃣to 2⃣

***Kamar kullum k’arfe 5:30 pm suka taso daga makarantar islamiyya dake can nesa da layinsu ,tafe suke a jere sanye da unifoam kalar green me haske Riga da wando da zumbulelen hijabi har k’asa ,sai nik’ab da suka sanyawa fuskarsu suka rufeta ruf ,k’afarsu sanye da safa bak’a da takalmi sau ciki irin na mata ,kafad’arsu rataye da jakunkunan su wadda ke d’auke da alk’ur’ani me girma da sauran litattafai na addini da tajweed.

     A nutse suke tafiya cikin takun natsuwa da hankali duk da suna saurin isa gida ganin yamma tayi sosai magriba ta kusa ,ta cikin nik'ab d'in fuskarsu suke magana da juna hannunsu sark'e da na juna kafad'arsu na gogar juna ,tsawonsu d'aya ,yanayin jikinsu d'aya ,sun kasance wad'anda basu cikin halittar mata masu tsananin k'iba ko tsananin sirantaka ,su d'in matsakaita ne da Allah yayi musu halitta me kyau da tsarin jiki me kyau duk da basu kasance da kyawu matsananci ba ,sai dai sunada kyawunsu dai dai misali.



 Hassana ce tak'ara damk'ar hannun hussaina ,sannan a hankali ta furta cewa .


  "My sister muyi hanzarin isa gida banason muna waje ayi kiran sallah ,yau Malam huzaifa ya tsayar damu wallahi ,nasan yanzu Baba yana gida yana tsumayin dawowar mu shida su Hamma.



Ta cikin nik'ab d'in Hussaina tayi murmushi sannan tace "to ai rabin jikina kece bakida sauri wallahi ,jibifa yanda kike tafiya kamar bakyason taka k'asa ,amma tunda mun kusa k'arasawa karki damu kinji "



  Hassana tayi murmushi kawai ba tace komai ba, saboda batada yawan magana ,in kaga tana magana sosai to da Hussainar tane ko y'an gidansu .



       Dai dai wannan lokacin suka iso cikin layinsu ,mutane jefi jefi a gurare da dama nata haramar d'aura alwala domin isa masallaci Dan sallatar magariba .




  Zaune yake kamar kullum akan wani dakali na farkon shigowa layinsu ,sanye yake da k'ananan kaya bak'ak'e  da hula hana sallah , kasancewar sa fari tas sai kayan suka amsheshi yayi matuk'ar kyawu naban mamaki ..........yau ma taba ce sigari a hannunsa yana faman zuk'arta yana fesar da hayak'in cikin gwaninta da k'warewa,MUHAMMAD SAGEER KENAN.

Karyowar su cikin layin su yayi dai dai da sanda SAGEER yagama shan tabarsa sai wata Y’ar guntuwa a hannunsa ,a maimakon ya yarda ita a k’asa ya take ta sai yayi cilli da ita ,bata sauka a ko’ina ba sai akan hijabin Hassana da suke shigowa layin a dai dai wannan lokacin.

Firgita sukayi gabad’ayansu sukayi baya da sauri ,sauran kad’an Hassana ta fad’i sai Hussaina tayi saurin tareta tanayi mata sannu tare da karkad’e mata hijabin inda sigarin ta tab’a ,Dan ragowar wutar jikin sigarin har ta d’an tab’a hijabin gurin ya d’anyi duhu .

   A matuk'ar fusace Hussaina ta juyo tana duban SAGEER da yake niyyar mik'ewa tsaye ,alamunsa sun nuna ko ajikinsa abinda yayi ,sai ma wani mugun d'auke kansa da yayi daga garesu yana faman cin mur da yatsina fuska tamkar yaga kashi .....

D’age nik’ab d’in fuskarta tayi tanai masa kallon banza ,duk da mugun kwarjinin da yayi mata hakan baisa tayi shiru ba ,a fusace tafara magana tana b’alla masa harara da k’ank’antar da idanu …….

  "Bakasan abinda kayi bane .......?!bakasan abinda ka aikata bane ........?!Dan wulak'anci karasa inda zaka jefo k'azantar sigarinka sai akan jikin da nafiso  a duniya fiyeda nawa ........?!karka kuskura kasake gangancin haka kaji ko ......wallahi da ka tab'an ita gara ka tab'ani ........bani k'aunar abinda zai tab'amin Y'ar uwa Dan haka ka kiyaye .......!




 Baiyi niyyar duban inda suke ba ,amma masifa da shouting d'in da yaji anai masa shiyasa ya juyo ya dubesu a sanyaye ..........mutum biyu ya gani tsaye sanye da uniform d'aya da nik'ab a fuskarta ,sai d'ayar da ta d'age nik'ab d'in tanai masa kallon banza ..........gabansa ya yanke ya fad'i ,k'irjinsa yayi wani tsananin bugawa bai San dalilin haka ba .




  Ya kalli me nik'ab d'in sai yaga ta sunkuyar da kai ,ya kalli wadda ya tabbatar itace take masa wannan bala'in ,ilai kuwa wata uwar harara ta banka masa ta bud'e baki da niyyar fad'a masa wata bak'ar maganar .

Lura da hakan da HASSANA tayi shine yabata damar damk’ar hannun Hussaina cikin sanyin muryar da bata fitowa sosai tace .

   "Sisina  rabu dashi ,kimasa uzuri k'ila ba da Sani ya aikata ba ,zo mu wuce gida muna k'ara b'ata lokaci da yawa ,kiyi hak'uri komai ya wuce kinji sisi na "




            Taja hannun Hussaina sukayi gaba ,yayinda Hussaina tayi k'wafa tana k'ara banka masa harara da Jan tsaki .



     Runtse idanunsa yayi da k'arfi yanajin k'una cikin zuciyarsa ,agabansa wata mitsitsiyar yarinya ke masa tsaki ......?!ya bud'e idanunsa da sukayi jajir yana jin matsanancin damuwa da b'acin rai ........baiji abinda me nik'ab d'in tace ba ,amma ya tabbatar k'ila itama zaginsa tayi ........in kuwa hakane ya tabbatar da zarginsa KENAN.

A hankali ya furta cewar “

      "Haka kuke dukanku bakuda uzuri ........!kuma bakuda kirki .......halayenku d'aya ne MATA ........yaushe ne mata zasu gyara halayen sune ......?! Yaushe ne MATA zasu dinga ganin k'imar MAZA .......?!



        Wani Abu me k'arfi ya tab'a zuciyar sa ,zuciyarsa ta tuna masa da abinda bayason tunawa ,Wanda shi yajefa shi a halin da yake ciki yanzu ........k'ara rumtse idanunsa yayi sai zuciyarsa tayi rauni hawaye ya malala a kan kyakkyawar fuskarsa me tsananin haske da annuri ,ya cije  lips d'insa da suka d'anyi duhu alamar shan sigari ,kafin yafara sha kuwa lips d'insa pink colour ne masu taushi da k'yalli .




    Kiran sallar da aka fara shiyasa yafara takawa a wahalce yabar gurin......yana jin tsanar yarinyar da yayi mata lak'abi da fitsararriya a ransa .

***Daf da zasu shiga soron gidansu ,mahaifinsu Malam Abubakar da sauran jama’ar gidansu suka fito da niyyar tafiya masallaci don bin jam’in sallah ,daga gefe suka rakub’e sukabawa baban su hanya ya wuce ,sai da suka wuce dukansu sannan Hassana tace ” Baba adawo lafiya ,don Allah asamu acikin addu ‘a Baba “.

      Saboda saurin da sukeyi shiyasa baban bai tsaya ba, illah d'aga musu hannu da yayi yana fad'in " insha Allah kyautar Allah kuna cikin addu'ata "Hussaina ta Shafa kan Usman dake d'auke da dadduma akan kafad'arsa tace " autan Umma kaima kayi mana addu'a kaji .......!

Da hanzari ya k’ara sauri yana bin bayansu Baba ganin sunyi gaba ,yana cewa “toh adda Hussaina zan miki addu’a kirage fad’a kikoma kamar adda Hassana ” ya fyalla da gudu yana dariya ya cimma su Baba .

Dariya maganar Usman tabawa Hassana ,Hussaina kuwa k’wafa tayi tana cewa “zaka dawo ka sameni ne yaro ,wato ka maiidani mafad’aciya ma ……..ta kuma yin wata k’wafar tana girgiza kai dacewar ” aini bawai inada yawan fad’a bane raini ne kurum banaso ……

Hassana tayi dariya aranta tana cewa “duk duniya bataga me son girma irin sisinta ba .

Shigar su gida suka tarar Umman su na d’aura alwala ,sallamarsu tayi dai dai da kammalawarta ,amsa sallamar tayi kawai batace musu komai ba ,tayi hanzarin shigewa d’aki saboda sallar da taji an tayar ,itama ta tada sallar .

  A tsakar gidan suka ajiye jakunkunansu suma ,Hassana tafara shiga band'aki tayi tsarki ,sannan tafito ta d'aura cikakkiyar alwala ,yadda tayi haka Hussaina ma tayi ,sannan suka nufi d'akin su basu tsaya cire uniform ba sukayi sallar su .

Bayan sun idar ne suka sauya kayansu zuwa kayan gida ,kaya kala d’aya suka saka saboda ba’a bambanta su a komai ,komai nasu iri d’aya ne ,in kaga ansamu bambanci kuwa to sai dai kad’an shima kuma saina colour.

Bayan idar da sallah a masallaci ne su Baba suka dawo gida ,Hassana ta shimfid’a tabarma a tsakar gidansu inda kullum mahaifinsu da yayyensu suke zama, musamman bayan magriba ko isha’i domin cin tuwon Umma me rai da lafiya ,mutum biyu a cikin yayyen su sunada aure ,amma duk da haka kullum sai sunzo sunci tuwon Umma saboda mugun sabon da sukayi dashi .

Hassana &Hussaina sunata hidimar jera kwanukan tuwo da miya ,sannan kuma suka kawo ruwan wanke hannu da ruwan sha ,tuwan dawa ne da yaji kanwa yayi mul mul dashi yayi sulb'i da laushi ,sai miyar kuka da taji tantak'washi da manshanu ga yajin daddawa a gefe ,a kwano d'aya suka sanya hannu sukaci bayan sun wanke hannu tare da bismillah ,Baba yafara saka hannunsa  sannan Hamma sulaiman yasaka nasa hannun ,Hamma  Aminu shima yasaka nasa ,sai ya safwan Wanda su Hassana kebi ,sai kuma Abubakar me sunan mahaifinsu da suke kira Baban gida ,sai k'aramin k'aninsu usmanu (autan Umma ),a nutse suke cin abincinsu babu wata hauma hauma ,yayinda su Hassana suke gefe kan wata tabarmar,bayan sunci masu abincin , ummansu nayi musu k'arin karatunsu na ahalari .


     Bayan sun kammala kowa yayi hamdala ga sarki Allah ,Hussaina tazo ta kwashe kwanukan da sukaci abincin ,sannan tadawo ta zauna ana d'an tab'a hira tsakanin ahalin gaba d'aya ,babbar yayarsu ce kurum(Adda Nabeela) bata cikinsu tana gidan aurenta inda take auren wani babban attajiri a garin ,Baba ne ke tambayarmu dalilin dad'ewar mu a Makaranta yau ,Hassana tace "Baba Malam huzaifa ne ya tsayar damu akan batun musabak'ar da zamuyi ta gasa da wasu makarantu ,shine yake fad'amana ni da Hussaina Makaranta ta tsayar amatsayin Wanda zasu wakilci Makaranta "

Fuskar baba ta washe da fara’a ,a hankali yake furta “alhamdulillah ,nayi farinciki da hakan ,kucigaba da dagewa tare da k’ok’arin mahaifiyarku da kullum take tsaye akan karatunku ,hak’ik’a kunyi dacen uwa tagari me d’ora yaranta akan turba tagari ,Allah yayi muku albarka dukanku tareda sauran yaran musulmi .

Gaba d’aya muka amsa da ameen ,Umma tana murmushin yabon da baba yayi mata ,kuma inda sabo tasaba kullum babanmu cikin yabonta yake saboda halayenta nagari da kyautatawar da take masa ,Hamma Aminu kecewa idan muka dage mukaci wannan gasar zaimana kyauta me muhimmanci wadda zamu yaba sosai ,Hussaina harda matsawa takama hannunsa tana dariyar murna fad’i take ” yawwa hamman mu shiyasa nake sonka fa Dan kuwa ka iya kyautar girma ,insha Allahu zamu dage mu d’auko nasarar ,atayamu da addu’a dai ,Allah yabarka da adda Amsad d’inka Hamma “ta k’arasa tana kallon fuskar sa da dariya …….shima dariyar yake yana runtse hannunta a nasa hannun yana girgizawa .

Baba yace ” kyautar Allah menene kuma Amsad ?naji kinacewa Allah yabar Aminullahi da Amsad d’insa ……!?

Ya Safwan yana tasa dariyar yace “baba waifa aunty Sadiya ce Amsad .

To, to ,to Halimatun ce takoma Amsad kuma ?wane irin sunane kuma wannan ?inji Umma kenan da take kama hab’a tana furta kalamin.

Kan kowa yayi magana Hussaina takuma yin caraf cikin dariyarta dake k’ara haskaka fuskarta tace” Umma sunan soyayya nefa ,ai Amsad yana nufin sunan hamma Aminu da aunty Sadiya aka had’a yabada haka ,nima a bakin aunty sadiyar naji tana fad’e.

 Kowa agun saida ya dara ,amma banda Hamma sulaiman da murmushi kurum yayi shida Hassana ,aganinsa shirme Hussaina kurum takeyi ,shiyasa ya tab'e baki ya mik'e tsaye ya nufi gurin baba ya tsuguna yace "Baba zan k'arasa gida ,akwai dai maganar da naso muyi baba amma naga lokaci ya k'ure gobe insha Allahu sai muyi maganar ".

Baba ya kalli d’an nasa shine babba a cikin mazan gidan ,mutum ne me tsananin kamala da kamun kai ,duk wani Abu na shirme bazaka sameshi cikiba ,hakanan komai da zaifita a bakinsa me amfani ne ,kyakkyawa ne me kyawun halayya ,baba yace ” babu komai sulaiman Allah yasa munada rabon ganin goben lafiya ,Allah kuma yasa alkairi ce maganar taka, duk da nasan komai zai fito daga bakinka alkairi ne ,tashi jeka gurin iyalinka ,Allah yayi albarka .

Hamma sulaiman kansa a duk’e yanajin dad’in maganar baba har ya kammala ,sannan yak’ara rusunar da kansa k’asa yace “nagode baba Allah yak’ara lafiya da Nisan kwana me amfani ,sannan ya mik’e yaje gaban Umma ya tsuguna yace ” ummanmu zan k’arasa gida kiyimin addu’ar da kika sabayimin nida y’an uwana “

Umma tadubeshi tace “addu’a tazama dole ai ,Allah ya kareku ya tsaremin Ku gabanku da bayanku ,Allah yacigaba da dafa muku adukkan lamarinku ,Allah ya had’amin kanku cikin zumunci da k’aunar junanku ,agaishemin da sakeenan da maigida saddik’u na .

Hamma yayi murmushi yace ” Amin Umma ,amma sadauki da mominsa kawai za’a gaisar ??ragowar yaran kuma fa ??

Kan Umma tayi magana Hassana ta rigata cewa “ni ina gaishesu duka Hamma ,duk kashafamin Kansu kafin muzo ,sulaiman yace ” kinkuwa San sakeena tace ran juma’a kuje zaku tayata wani aiki ,sai yanzu na tuna wallahi .

“Insha Allahu zamuje Hamma, Allah ya kaimu ,cewar Hassana.

   Sallama Hamma sulaiman da Hamma Aminu sukayi musu ,sannan kowa yaje ya d'auki mashin d'insa dake soro ,Babangida yabi Hamma yana tuna masa litattafai da zai siya masa na school ,Hamma sulaiman yace babu damuwa zai siya masa gobe, kowa ya hau mashin d'insa ,suka tayar kowa yanufi gidansa .



Sai misalin goma na dare su Hassana suka kwanta barci saboda karatun da suka tsaya yi ,bayan sun kammala suka kwanta tuni Hussaina tayi barci ,yayinda Hassana tarufe idonta tana karanto addu'ar barci sai hoton fuskar sageer ya bayyana a idanuwanta .

comment’s and share pls

Hassana d’an larabawa✍✍✍

1/1/2020

TYPING????

???????? HASSANA????????

           *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 3⃣to4⃣

SADAUKARWA

GAREKI MAMAN MAMY (SHALELE MASOYIYAR ASALI????????)marubuciyar (RAGON MIJI)NABAKI KYAUTAR WANNAN FEGI KIYI YADDA KIKESO DASHI ,INA YINKI SHALELE KAMAR YADDA KIKE YINA????????????

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button