Labarai

Najeriya na buƙatar shugabanni masu matsanancin hauka – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Najeriya tana buƙatar shugaba dan gada-gada, wanda kuma yake da hauka, domin ya saisaita wa kasar zama tare da dora ta a saiti.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Obasanjo, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗan takarar Shugabancin kasa, a karkashin jami’yyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen, a gidan sa dake Abeokuta, a jihar Ogun. Obasanjo yace, shi kansa wasu abubuwan da suka shafi Najeriya, sai da yayi su kamar a haukace, kuma baya neman afuwa akan hakan.

Halin da Najeriya ke ciki a yanzu na sosawa Obasanjo rai matuƙa

Yana da na sanin cewa, yanayin da kasar take ciki a yanzu haka, ba shi kadai yake sosawa rai ba, har ma da ‘yan Najeriya wadanda su ke buƙatar ganin Kyautatuwar kasar.

Tsohon shugaban ƙasar, ya kafe akan cewa Najeriya zata iya magance matsalar tsaro da take fuskanta a cikin shekara biyu kacal, idan aka sami nagartaccen shugaba, wanda yake a shirye domin ɗaukar kwakkwarar matsaya.

Yayi wani muhimmin kira ga ‘yan Najeriya

Daga nan kuma, sai Obasanjo yayi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi, su jajirce domin sadaukarwa wajen dawo da kasar kan turba.

Ga kalaman na sa:

Wadansu mutanen suna cewa, tunanin mutum ragagge ne, mai yiwuwa gaskiya suke fada, domin idan da ace tunanin mutum ba ragagge bane, to da bamu yi wasu kura-kuran da muke yi ba.

Wadansu mutanen suna cewa, tunanin mutum ragagge ne, mai yiwuwa gaskiya suke fada, domin idan da ace tunanin mutum ba ragagge bane, to da bamu yi wasu kura-kuran da muke yi ba.

Eh, muna da tanadi, wanda wadansu mutanen bazasu so jin sa ba, amma duk abin da mutane ke son suji, kamar dai kai (Hayatu-Deen ) kayi magana mai kyau, inda kake cewa, wannan lokacin ba irin kowanne lokaci bane a tarihin Najeriya, sannan sai kayi amfani da wasu kalmomi biyu, rarrabuwa da daidaicewa. Bazan iya samun kalma daya wadda zanyi amfani da ita ba, wajen bayyana yanayin da muka tsinci kanmu a ciki.

Abune wanda baya yiwa kowa dadi tsakanin ni da kai. Ina so in kara jaddawa, cewa ‘yan Najeriya sune zasu shige gaba wajen gyara yanayin Najeriya, duk da tabarbarewar sa.

Saboda haka yan Najeriya sune zasu jajirce su tashi tsaye wajen dawo da Najeriya kan turba.

Sannan daidai ne abin da kake fada cewa, duk inda ka je, zaka ji ana cewa, Najeriya bata kan ka’idar tattaunawa , saboda me baza’a dora Najeriya akan ka’idar tattaunawa ba? Me Najeriya ke bukata domin zama kan kaidar tattaunawa?

Anan sai in ce muku abu hudu ne, wadanda aka tunatar da ni, a safiyar yau. Abu na farko shine ilimi. Idan Najeriya bata kan ka’idar tattaunawa, mai yiwuwa ilimin da zamu samu dangane da sanin kanmu, na halin da muke ciki, na nahiyar da muke zaune, kai har ma da duniyar, da bai ishemu ba, idan kuwa ilimi ya iahemu to zamu dinga yin abubuwa da ya dace, lokacin da ya dace, ta yadda ya dace.

Na biyu shine hange, wanne hange muke da shi? Koda baka da hange ai kana da idanu, amma kuma kai makaho ne, na tabbata irin wannan yana daga cikin yanayin da muke ciki.

Na uku shine, gada-gada, idan kace kai wannan ka dauka, kamar yadda nake gayawa wadansu a safiyar yau, cewa, gada-gada yana nufin hauka, cewa ka zama ka haukace akan Najeriya ita ce a gabanka, nima haka nake, kuma bana neman yafiya akan haka, saboda bani da wata kasa da zan kira tawa, saboda babu wata kasa da zanje Ince yawwa nazo nan ne domin in zauna in yi rayuwa ta

Gada-gada na nufin, ka zama ka haukace akan Najeriya, hauka mai karfi, kuma na lura, kai Hayatu-Deen, ka haukace akan Najeriya kai ma.

A jawabin da ya gabatar, tun farko Hayatu-Deen ya bayyana Najeriya da cewa tana “rarrabuwa da ɗaiɗaicewa cikin hanzari.”

Hayatu-Deen din wanda shine tsohon Manajan daraktan bankin kasa da kasa na FSB, ya gana ne da deliget ɗin jami’yyar ta PDP a Abeokuta.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button