KISSA KO MAKIRCI Page 21 to 30

Tun farkon aurensu salma take fuskantan matsala wajan dangin mahmud, gashi baban abun tashin hankali shine yau shekaran salma uku da aure amma shuru babu haiyuwa, nan hjy binta tace Sam bazai yiwu ba, mahmud ya zama dole ya kara aure domin tana son ganin jikoki, bazai yiwu kaita zama da juya ba, badan ranshi yaso ba ya amince dan yabi umarnin mahaifiyarshi dan baya so ya saba mata, Amma shi a nashi ra’ayin baya sha’awan tara mata shi salman shi ta isheshi kawai,amma babu yanda ya iya matsalanshi kawai yanda zai gayama salma zai kara aure yake damunshi dan baya San bacin ranta, kaman yanda bata san nashi, duk wani abu da zaisa shi farin ciki shi take so, bata san bacin ranshi sai yasa shima yake gujema abun da zaisa ta bacin rai ko zargi duk da yasan ba halinta bane tana da hakuri,amma babu yanda zaiyi dole ya fad’a mata dan yafi so taji abakinshi akan taji a wajan wasu, ya yanke yau Zai fada mata.
MUN DAWO KAN LABARIN
yau aka daura aure, Mutane sun taru domin hjy binta tayi gayya sosai, ango dai kwata2 baya cikin nishad’i, zai iya cewa yau itace ranan bakin cika a rayuwanshi domin an daura mishi mara tarbiya shi yama rasa mai yasa mama ta yarda ta bashi fauziya ba,
Ita kuma gefen amarya tana cikin farin ciki, yau itace matar mahmud abun da take ta burin samu shekara da shekaru yau ya zama nata, ta lumshe ido tare da fadin yau zan nuna maka nawa fagen soyayyar, yau zaka sha zumata, ji take kaman azo a tafi da ita yanzu, ta tashi ta dauko maganin da boka ya bata tayi matsi dashi, tayi murmushi tare da tuna abun da bokan ya fada mata indai ki kai amfani da wannan maganin ya sadu dake toh daka ranan sai yanda kikayi da mahmud, domin duk macen daya sadu da ita zai jita kaman dusa, tace salma saina rabaki da mahmud har abada domin nawa neshi.
Salma anci kwalliya sosai tayi kyau, tasa wani tsadaddan material wanda mahmud ya kuma siyo mata tasa da bikin, gefen ta kuma kanwarta ce hauwa, wanda tazo taya ta zama har a kawo amarya ta wuce, suna dan fira jefi2 hauwa tace niko salma mai yasa kika bar mahmud ya kara aure bayan nasan ba zaki barta ta zauna ba, salma tace hauwa mai kike nufi? Tace naga duk wanda mahmud ya aura kin koresu itama nasan wannan ba barinta za kiyi ba, salma tayi murmushin takaici tace hauwa kenan, kina bani mamaki wlh, tace name ai gaskiya ne abun da yake a zahiri mahmud fah akan ki zai iya komai inba wani abu kika mai ba toh mai yasa zai dinga miki haka, salma tace bana tsafi bana shirka, bana makirci, hauwa tayi dariya tare da fadin toh sai me? Tace KISSA hauwa ta kafeta da ido tare da kuma nanata kalman da salma ta fada kissa, tace ya ake ita kissan hala naki na daban ne, tace a’a kaman na kowa ne, hauwa tace toh koya min mana nima inji ko zan gamsu ita kikeyi, salma tace zan fada miki nan gaba hauwa tace dan Allah ki fadamin yanzu dan na matsu inji, tace na miki alkawari dakai na zanzo gidan ki in fada miki, hauwa tace toh shi kenan, nasan bakya karya alkawari ai, sukayi dariya a dai2 nan mahmud ya shigo salma ta tashi da sauri tare da fadin wlcm my dear dana iya guda da nama, yayi dan murmushi yace toh Ina binki bashi tayi dariya dan ta fahimci abun da yake nufi yayi gefenshi itama ta bishi anan suka bar hauwa tana shs’awar irin rayuwar su, sai dai salma taki fada mata sirrin yayin da ita nata mijin suke yawan samun matsala wannan kenan
Anzo daukan amarya an jera motoci masu tsadan gaske, nan fauziya ta tashi cikin murna da zumudi, aka fita, kai tsaye aka wuce da ita gidan ta, suna shiga suka fara guda da habaice2 suna fadin an kawo wacce zata haifa mana y’ay’a Allah ya rabamu da juya sai ci ana zubarwa, salma dai tana d’aki bata fito ba,.
Hjy binta ta kira mahmud taja mishi kunne akan idan ya saki fauziya toh wlh saiya saki salma itama, dan wannan karan bazan dauka ba, gwara ma ka dawo hankalinka tun wuri yace insha Allah hakan ma bazai faru ba, tace toh saika tashi kaje dan fauziya tana jiranka dare kuma yana yi ya amsa da to, ya wuce.
Yan kawo amarya sun wuce aka bar amarya ta tashi ta fad’a bayi tayi wanka tasa wata rigan bacci wanda dashi ma gwara babu, ta zauna tana jiran mahmud ya dawo, lokacin daya dawo taji shigowanshi nan ta koma ta zauna, shi kuma kai tsaye dakin salma ya wuce, nan ya zauna yana ta faman yi mata kalaman soyayya, tace ka tashi kaje d’akin lanwata tana can tana jiranka, yace korata kikeyi salma? Tace a’a inaso ka zama mai adalci ne kuma kasan yau ranan tane ranan dako wace mace take buri kaga bai kamata mu shiga hakkin taba, fauziya jin ya dade bai shigo bah ta fusata tare da fadin yama raina min wayau ta tashi ta fita tana huci tayi d’akin salma….
Maryam Obam????
????????????KISSA KO MAKIRCI????????????
NA
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Mrs nura kuriga)
35to40
A dai2 lokacin ya fito daka dakin, nan sukai Karo, salma na bayan shi, kallo daya ya mata cikin tsana yace ke wace irin mara hankali ce, zaki fito haka bayan kin san bake daya bace a gidan, salma gaba daya ji tayi ta dauke wuta dan wani azabban kishi ne ya dauketa, wanda yasa idonta ya canza amma saita daure tace dear sai da safe ta rufe kofarta, dan bazata iya ganin wannan takaicin ba, kuka ta sake mai karfi, gaba daya xuciyarta tafarfasa yake, daka ta rufe idonta sai taga fauziya da mahmud ranan barci gagaranta yayi duk yanda taso ta dake ta cire abun amma ta kasa, da dai taga haka ta tashi ta dauko al’qur’an, tana fara karantawa nan ta danji dama2.
Mahmud tunda sukai d’aki shida fauziya ya kasa sukuni dan bai yarda da yanayin salma ba, dan yaga kaman ta dan shiga damuwa, yayin da amarya ta kame a gefe ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa amma abun mamaki shi gogan ko kallo bata isheshi ba, ta saki tsaki tare da fadin wannan fah inna biye tashi babu abunda zai faru yau, zai sa inyi asaran magani gashi boka yace sau daya yake bama mutum shi, ta tashi ta nufi mahmud din wanda yake zaune kan kujera yana danna laptop, ta zauna ta gefen kujeran tare da rufe laptop din, ta fara magana tana kashe mai ido haba mahmud dare fah yayi kasan kuma Ina jiranka ya kamata kazo mu kwanta, gaba daya mamaki ya hanashi magana dan bai taba xaton haka ba, tasa hannunta cikin riganshi, yayi sauri ya tashi tare da fadin tir da halinki duk wata mace mai mutunci indai tayi aure aka kawo ta duk rashin kunyanta bata neman namiji sai dai shi ya nemeta, amma ke dubeki wai amarya kenan babu kunya babu komai, ta tabe baki tare da fadin toh miye aciki kuma miye abun jin kunya,ina bukatar ka, dan me bazan nuna ba, kallon tsana da mamaki yake mata, yace lallai sai yanzu na yarda da baki da kunya kuma baki santa ba, inba karuwa ba babu wacce za tayi abun da kikayi a daren farkon ta, dan haka yanzu ni kin samin tantama sai anyi miki test kafin in kulaki, cikin fushi tace mai kake nufi kana nufin ni yar iska ce? Yace waya sani abu a duhu, zama tayi tana hawaye ta rasa abunyi tana tunanin shirinta zai rushe lokaci daya ta kuma tashi tace toh naji na kuma yarda in kace baka yarda dani ba, zaka iya amfani da condom, dan ina bukatar ka, yace fauziya am sorry bazan taba kiba har sai anyi test ya tashi ya koma kan gadon ya kwanta abinshi, ranan tayi kukan bakin ciki tare da daukan alwashi sai ta rama duk abun da mahmud ya mata tare da fadin kai da kanka zaka nemeni, a lokacin zan wulakanta ka zan nuna maka aikin boka, itama dai ranan juyi tayi2 bacci yaki zuwa,