

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja Kwankwaso ya ce kimanin watanni 11 da suka wuce aka bijiro da maganar kujerun shugabannin shiyyoyi a jam’iyya.
Tsohon Sanatan ya ce an warewa kowace jihar Arewa maso yamma kujerar da za ta rike, amma sai aka hana mutanensa wannan dama a jiharsa ta Kano.
Rahoton ya ce wannan ya sa Kwankwaso ya ga tamkar bai da amfani a PDP. Bayan shafe tsawon lokaci ba tare da an yi sulhu ba, ya ce sai ya sauya-sheka domin share hawayen jama’arsa.
“An samu wani yanayi a Afrilun bara inda aka raba mukamai na shiyyoyi tsakanin jihohi shida, inda aka ba mu damar mu kawo ‘yan takara.” “Amma a jihar Kano sai wasu suka ga cewa ba ni da muhimmanci, sai suka yi abin da suka yi.” “Wannan ne ya jawo wannan lamarin (na sauya-sheka), kuma sai da na shafe shekara kusan daya kenan ina jiran jam’iyyar PDP ta zauna da ni.”
“Har aka nada sababbin shugabannin jam’iyya, amma ba su da sha’awar su yi zama da ni.” “A kan wannan dalili, na ga akwai sabanin da ba za a iya shawo kan shi ba tsakanin ni da sauran shugabannin da ake da su saboda bambancin akida.”
“Yanzu na karbi katin zama ‘dan sabuwar jam’iyyar NNPP, babu shakka akai ina matukar farin ciki da na zama ‘dan NNPP a Kano.”
[ad_2]