GUGUWAR ZALUNCI BOOK 1

PAGE 1 & 2
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
NA
*ZAINAB HABIB (MOM ISLAM)*
Free page
*Gargaɗi! Gargadi!!! Ban yarda wani ko wata su juyamin littafi ba ta kowace siga ba haƙƙin mallakarsa nawa ne abi doka a zauna lafiya*!
Bismillahir rahmanir rahim da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai .
Ina godiya ga Allah daya bani aron rai da lafiya da kwanciyar hankali har nakai ga fara rubuta wanan littafi mai suna GUGUWAR ZALUNCI ya Allah ina roƙonka ka tsaremin hankali na da basirata gurin rubuta alkairi ya Allah ka tsaremin alƙalamina da rubuta abinda zai tarwatsa rayuwar jama’a ya Allah ka ƙara mana lafiya ka nuna mana ƙarshe littafinnan lafiya kamar inda ka bani ikon farashi cikin ƙoshin lpy amen y Allah.
Wattpad momislam2020
Facbook mom islam mon islam
Email:
Zainabhabibu@gmail.com
Whtsapp: 08141799224
*BIRNIN TARAIYYA ABUJA WUSE TWO.*
Anguwa ce mai cike da manyan masu kuɗi ga kuma tsararun gidaje kamar a ƙasar turai .
A cikin anguwar akwai wani ƙeraren gida mai kyan gaske gidane daya sami ƙwararun magina masu aiki da ilimi , tun daga wajen gidan zaka gane mai gidan hamshaƙi ne wato Alhaji Sani ana kiransa da Alherin Allah , babban ɗan kasuwa ne sananne a kowace ƙasa kuma kowane fanni yanada kamfanoni da dama dakuma motoci wanan kenan.
daga gefe ɗakin mai gadi ne can kuma gefen kudu da arewa shuke shuke ne na wasu kyawawan flowers gwanin sha’awa , ga wasu ɗawisu da suke kaiwa suna komowa guwanin birgewa .
Iyalan gidan ne zaune a palon da za’a iya kiransa da aljannar duniya iya tsaruwa ya tsaru nera tayi kuka musamman ma danƙara danƙaran kujerun da suka mamaye palon ,wata farar mata ce zaune a ɗaya daga cikin jerin kujeru sai wasu ƴan mata su biyu masu kama da ita amma sun fita haske matashiyar matar ce ta dubi ɗaya daga cikin ƴan matan tace “Diyana zakuyi dare fa kinga har yanzu dadynku bai fito ba ,
Wace aka kira da Diyana ce ta taɓe baki tare da lumshe fararen idanunta masu ɗauke da zara zaran gashin gira tace “mom ni dama bason zuwa ƙauyen nan nakeyi ba dady ne ya matsa mini wai nice banison zuwa duk cikinmu ,
Budurwar dake gefe ce ta dubi momy fuskarta da alamun ɓacin rai tace ” mom village ɗinnan ya cika sauro gakuma rashin tsafta ,
Diyana ce tace ” good Afreeda ashe kin gane ,jin maganar tasu zatayi yawa ne momy tace ” shiii alamar suyi shiru dan tajiyo takun mai gidan nata ,
ƙarasowa yayi da shiga ta alfarma a jikinsa shadda ce gezna fara wace tasha aiki , momy ce take ƙare masa kallo da murmishi a fuskarta shima mayar mata yayi tare da kallon su Diyana da Afreeda da hankalinsu ke kan wayar dake hanunsu ,
Dady ne yace ” to nagama so ke nake jira rau rau Diyana tayi da ido tana kallon mom ganin batace mata komai ba yasata miƙewa tana bubuga ƙafa Afreeda na dariya ƙasa ƙasa ,
Dan tasan ita zata iya jure wuyar ƙauyennan amma Diyana kam tana tausaya mata, dady waje yayi dan shima ba mai son yawan magana bane kamar mom ,
Hand bag ɗinta Afreeda ta ɗauko mata tare da wata jaka mai kyau da alamu itace jakar kayan nata ,
mom ce ta miƙe ta nufi step ɗin dake tsakiyar palon bata ɗau lokaci ba sai gata ta fito da wato leda fara ƴar baba ta miƙawa Diyana , buɗewa Diyana tayi taga su man shafawa ne masu tsada dakuma takalma harda atamfa itama mai tsada kana ga turaruka , taɓe baki Diyana tayi tace “mom wanan kayan wa za’a kaiwa granny ɗinku taɓɓ hmm Diyana tasa kai ba tare da takuma cewa komai ba ,
Jerowa sukayi tare da Afreeda idan kaga yanayin tafiyarsu kai kace ƴaƴan sarakuna ,
Fuskar Diyana babu fara’a kasancewar dady na cikin mota yana waya hakan ya basu damar yin magana , Afreeda ce tace “Anty Diyana saifa kin daure da mutanen village ɗinnan dan lokacin da mukaje wlh cemin sukeyi anyi jar fata tashigo ƙauye kokuma sudinga bina suna kallo na ,
Dafe kai Diyana tayi kana tace ” nashiga uku nikam nima haka zasuyimin ? har Afreeda zata yimata magana dady ‘ ya katsesu zo mu tafi ,
dady na back side ita kuma ta shige gaba dan batason zama kusa dashi kasancewar ba tun yanzu ba ya hanasu chart eyepice tasa a kunnen ta kana ta jingina kanta da kujera ta lumshe ido driver na shiga suka ɗauki hanyar ƙauye .
*KANO. ƘAUYEN SHAFA*
Ƙauye ne mai gidaje jifa jifa dakuma mutane iri iri yawancin gidaje nasu duk rufin ɗakin anyishi ne da jinka basu damu dayin katangu ba wasu kuma sunayi kana babu ginin siminti sai a wani gida dake gefe shi kaɗai .
Bacci mai daɗi ne ya ɗauki Diyana dady kam hankalinshi na hanya dan sun shiga kano a halin yanzu ma hanyar ƙauyen suka dosa , wata irin gargada suka shiga wace tayi nasarar farkawar Diyana a tsorace ihu ne kawai bata kurma ba ga mumunan faɗuwar gaba ,
Ƙarewa ƙauyakun kallo tashiga yi tana salati badai nan ne kauyen ba taɓɓ gashi dady yace ” 5 days zanyi ina bazan iya ba , duk cikin zuciyarta take wanan maganar jin anyi parking yasata ɗago kai tare da juyawa ta kalli dady dake tattara wayoyinsa a kan siddin motar dady har mun iso ne ?” yes daughter yau zakiga granny ɗinki , yana maganar da murmishi a fuskarsa,
driver ne ya fito ya buɗewa dady mota kana ya buɗewa Diyana , a tare suka fito daga motar hanunta riƙe da wayoyinta guda biyu tabi bayan dadyn ,
Daga bakin ƙofa dady yai sallama jin muryar wata tsohuwa yasa Diyana waro ido dan ganin wacce mata ce zata fito ?”.
Wata tsohuwar mata ce fuskarta taɗan tamushe haƙoranta sunji jiki tsabar cin goro tasa riga da zani dakuma ɗankwalin yadi barka da zuwa Alhaji tanata faɗaɗa fara’arta ywwa Hajiya , Hajiya ce tace ” to kuzo mushiga jikalle ansha hanya ta dubi Diyana ,
Yamutsa fuska Diyana tayi batare da tace ” komai ba suka shige ciki .
Tsakar gidan da yaji siminti fess yake a share ko tsinke babu amma hakan bai sa Diyana dena yatsina fuska ba tana tattare kayanta wai karsu ja ƙasa , shiga cikin ɗakin sukayi da yake malale da leda babu kujera sai ƴar tuguno Hajiya ta miƙawa Diyana batare da tayi magana ba ta karɓa ,Hajiya ce tace ” Alhaji a ina ka samo wanan ƴar gwallin ?”dan naga kamar ba wannan bace da ta taɓa zuwa shekarun baya ?.
Kawar da zancen dady yayi ta hanyar durƙusawa yace ” Hajiya bamu gaisa ba ina wuni washe baki Hajiya tayi tace” lafiya lao Alhaji ya aiki ya hidima yakuma Faɗimatun buɗe baki Diyana tayi cikin zuciyarta tace ” waye Faɗimatun komai sai an ɓatawa mutum suna mom ce Faɗimatu taɓɓ ,
Dady ne yace ” tana gaisheki Diyana ce ta kalli driver tace ” kaje motor ka ɗauko wata farar leda ka kawo min , to driver yace ” cikin rawar jiki ya fice Hajiya ce ta miƙe ta fita sai gatanan da kwanon fura da nono a wani baban kwanon silba da suga a leda dakuma ludayi ,
Tunda Hajiya ta shigo da nonon Diyana take keɓe baki dan inba na kanti ba batashan wanan , driver ne ya dawo hanunshi riƙe da ledar ya durƙusa yace ” ranki shi daɗe gashi karɓa tayi ta ajiyesu gaban Hajiya batayi magana ba , kallonta kawai Hajiya takeyi dan a bisa dukka halamu jininsu bai haɗu da Diyana ba , dady ma ya lura da rashin sakewarta dama yasan halin abarsa ko anyi abinci a gida bataci inba tayi ra’ayi ba drinks sune kayan shanta sai cake da shauransu .