ABAR SO COMPLETENOVELS

ABAR SO COMPLETE

“Yan’nan baxa’yayi haka bah….”itama antyn katseshi tayi dacewan

“Baba DanAllah abar maganan kudin nan kadaisan kadan daxata samu zaifi kudi koh?”

“Tabbass ladan zaifi kudin bari insame Alhaji  in fada mai yadda mukayi daku amman zaku iyashiga …..”yafada masu

“Toh baba”suka amsa in chorus

“Daman akwai Wanda suke tunanin lada akan kudi kuwa?gaskiya Sun burge ni “baba maigadi yafada tareda sallama akofar main entry din gidan…….

      
             Suna shiga dakin anty tayi tozali da uban danta,masoyinta dakuma abin kaunarta

“Allah sarki!!! Haka yamayarmin da kai “tafada tareda fara sabuwar kuka …..

             Yana  isa yakorawa Alhaji bayani

“Gaskiya nima Sun burge ni Sun nunamin cewan kudi bai damesu bah, Kuma zanso na hada zuri’a dasu”

“Alhaji bangane mai kake nufi bah,ba dai wa mai sunan babana za’akara wa aure bah?”

“Tabbass shidinne cos yana da bukatan hakan”

“Gaskiya sbd matan nashinnan sai addua”……

        Sanda sukayi kuka mai isarsu  kafin suka tashi tsaf suka gyarashi sbd alokacin bacci yakeyi sakamakon maganin baccin da aka bashi . Sunagamawa antyn t ashirya tafiya

“Antynmu ki kawo min kayana dakuma tablet dinna  Kuma kisa min SIM aciki” tafada wa antyn

“Toh babynmu” antyn ta amsa  tareda ficewa daga dakin ……. tana zuwa bakin gate tamawa mai gadisallama tareda cemai zata kawo kayanta …….inda yamata sai tadawo . Tana isa gida tahadu da Hasana

“Antynmu Ina babynmu?” Ta tambaya

“Tadanyi tafiyan kwana biyu kiyi hakuri bata fada miki bah,it’s urgent shiyasa”

“Lah babu damuwa fah Antynmu”

” yakamata kibani numbern Ku saina bata”

“Hakane Antynmu” tafada hade da karanto mata tana gamawa tamatasai anjima.


“Love” kursum takirashi juyawa yayi dakanshi   yana kallonta

“Daman inason na  rokeka wani alfarma neh “

“Inajinki”yafada

“Yawwa daman inason naje Turkey neh nextweek “

“Miye xakiyi?”yatambaya ta yana kafetada eyes

“Wai akwai wani fashion runway dinda nayi applying Kuma an zabeni acikin models din shine nakeson naje”

“Babu inda zakije”yafada in a serious tune ,ai nan da nan ta hasala

“Bangane babu inda zanje bah,naga dai  ni Ban hanaka zuwa inda kake so ,Kama samu natambayeka ni wlhy kana takurawa life dinna daba Dan inasonka bah  dana dade dah tambayar takardatah” afusace yafara mata magana

“Me wai ance inason ki neh  kawai sai inamawa mahaifiyata biyayya neh , Kuma karki damu  da takurawan danake miki da zarar na hadu da ABAR SOna  San hutasheki amma karki dauka yawon gantalinki xakina zuwa min da igiyoyin aurena akanki Kuma karki manta Nike aurenki ba ke ke aurena bah “

yafada tareda hayewa sama,  abinda tacene yasa shi tsayawa cak ……..

Don’t forget to vote

????????wurarh????????

????????????????????????
                  ABAR SO
                            ????????????????????????

WRITTEN BY:NAFISAT MA’ARUF SHEHU
                        ????????WURARH ????????

????GORGEOUS WRITTERS FORUM????
              
                ????G.W.F????

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS,WE ARE THE BEST AMONG THE REST

PAGE 60-62

Abinda tacene yasa shi tsayawa cak wato inba gizo kunnenshi kemishi bah tana nufin inta hadu dah ABAR SOnshi  kasheta zatayi, ai baisan sanda hannunshi ya isa jikinta bah wani muguwar naushi yasake mata a fuska,dukanta yakeyi koh ta Ina idanun nan sunyi jawur tsantsan bacin rai

“wlhy ko scratch ABAR SOna tasamu saina kusan hallakaki” itakuwa babu abinda takeyi sai bada hakuri

“DanAllah natuba kayi hakuri ban karawa” haka yadinga maimaitawa sanda yamata lilis tukunna yabarta yahaura stairs. Ajiyarzuciya taketa saukewa akai akai soboda  tunda aka haifeta  ba’a taba mata irin wannan dukan bah

“Wlhy kinshiga uku ABAR SO” shine abinda tace itama tana hayewa sama,straight dakinta tawuce agaban mirrow ta tsaya tana karewa new face nata kallo

“Oh gosh…. my model face” tafada tana daukar handbag nata tareda ficewa straight tasha tanufa fuskanta Kaman an mawa barawo duka Amma ita ko ajikinta cos ita so take mumy taga yanda danta ya mayarda mata da kamaninta.


Bangaren Nadhira  kuwa kwannanta biyu tana Kula da dadynsu Kuma Alhmdllh yanxu yadaina jifanta amma haryanxu alamu Sun nuna bashida cikakiyar  lafiyar kwakwalwa .

               Tarinda yakeyi neh yadakatar da ita daga hadamai abincinda takeyi,tana juyawa taga Wani bakin abunafita daga bakinshi ai batayi wata wata bah tayi waje da gudu inda adaidai lokacin KURSUM ke kokarin  shiga main palourn gidan  itakuwa Nadhira batama san da mutum awajen kofan bah tabangaje tah itama batayi kasa agwiwa bah ta fincikota hade da bata hot slap inda yayi daidai da fitowan Alhaji Kuma sarai yaga Marin, Nadhira dataji azabar Mari daga sama tafashe da kuka cos ita azatonta gamo tayi cos Kaman guduma taji akumatunta ,muryan Alhaji neh yadawo da ita daga duniyan kwankwanton da tashiga Kuma yasa zafin Marin gushewa lokaci guda

“A’a miyeke faruwa?” 

“Abba kataimakani  karya mutu aman bakin abu yakeyi”tafada cikin kuka

Jin hakan yasashi yin hanyan boys quarters din itakuma tabishi abaya.

KURSUM kuwa suna shigewa ta harare bayansu tareda jan doguwar tsuka  sannan tafashe da kuka Mai tsuma rai , mami kuwa jin muryar yarta yasata fitowa da sauri daga kitchen

“Lafiya dai koh da irin wannan kukan…. miye sameki afuska ?”ta tambaya lokacinda taga face dinta  akumbure ga Kuma jinin dayabushe a gefen bakinta (saikace lokacinda aka mawa HUA SHIANGU hukunci a film JOURNEY OF FLOWER  …lol)

“Wlhy mami nasha bakar wahala yau awajen Amin Kuma wlhy baxan yadda bah sainaje Human Right anbimin  hakkina  akan kawai nafadi ra’ayina akan maganin planning dinda yake duramin  shine yace shi bazai iya haihuwa Dani bah saida ABAR SONshi” tayi shiru tanajan magina sannan tacigaba

“Danacemai yabarni koda kuwa da insamu cos nima inason haihuwa Kuma daman zaman gidan ya gudureni ni kadai  ko kuma xanfara aiki shine fah yafara zagina ta uwar ta uba don kawai nace zanzo nafada miki shine  yamin wannan dukan”

Tafada tana Kara fashewa da kuka mai tsuma rai saikace dagaske neh abinda take fada  cos mamy hartafi tah daukan zafi  salati kawai mami keyi  kafin tace

“Yaushe Amin yazama mara tausayi …?” Katse mami tayi da cewa  waifah kishiya zaimin kwanan nan ,Kuma fah wai daman basona yakeyi bah Kuma inyagadama yana iya sakina daman nj matsala ce agareshi”

“Haka yace miki koh?”

“Eh mami “tabada amsa tana Jan hanci

“Zaizo yasameni tunda ban isa dashi bah  Mara mutuncin yaro”hakadai mami tadinga surutu batareda taji ta bakinshi bah, ita dai Dadi yagama kasheta cos tasan tajefi tsuntsaye biyu da Dutse daya

“Tashi ki gasa jikinki ” mami tafada

      Sukuwa Suna shiga yatarar da halinda yake ciki , ciro wayarshi yayi hade da danna mai kira , ringing biyu kuwa yadauka tareda yin sallama amsawa yayi yanacewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button