ABAR SO COMPLETENOVELS

ABAR SO COMPLETE

“NAFHIRA kuma?ai inaga duka anguwan nan babu mai irin wannan sunan ” ta bashi amsa, wani rass yaji azuciyarshi sai kuma ya tsinkayo muryarta tana fadin

“Nandai gidansu Babynmu neh”

“ABAR SO” Yafurta dasauri

“Eh” ta amsa mai , wani murmushi neh ya subuce mai

“Pls kimin iso zuwa ciki zan gaishe da mommansu”

“Momma kuma?kodayake bari dai in fadawa antynmu “

“Ok ” yafada asanyaye , shiga tayi tasanar da antyn yanda sukayi da shi cike da mamaki antyn tace tamai iso, tana fita tasame shi yana danna waya

“Wai ka shigo” wani dadi neh ya lulube shi. Suna shiga yasame antyn acikin compound,  gaisawa sukayi ta amsa

“Saidai fah bangane kabah” tafada mai

“Eh antynmu,  momma Nafhi da ABAR SO fah? Yatambaye tah

“Aina kasansu ” antyn tafada da mamaki

“Eh daman mun hadu neh shekaru hudu da suka wuce acikin plane daganan kuma bamu sake haduwa bah , kingama hoton da mukayi dasu ” tabbass tagane hoton cos wannan karon neh last tafiyansu a flight, katse zancen zucinta yayj dacewan

‘Aina suke cos nakosa nasasu a idanuna , kuma daman…..”maganar neh ya makale cos lura dayayi da yanayin antyn cos hawaye take sharewa atake kuwa jikinshi yayi sanyi 

“Miye faru antynmu?” Yatambayeta, kukan datake rikewa neh yayi nasarar kwace mata tin Hasana batasan miye antyn take mawa kuka bah itama tafara shikuwa zulumi yashiga , toh miye sukewa kuka shine abinda ya raya a zuciyarshi ganin bashida amsa yasashi fara basu baki , shiru sukayi sannan tafara bashi labarin abubuwan dayasame su amman bata fada mishi sunsan wanda yayi aikin bah dakuma nakasa rayuwar Nadhiran da akayi bah, hawaye ne kawai baiyi nasarar sauko mishi bah amma maganan sun tabashi ga idonshi yayi jawur itakuma Hasana tagama jikewa da hawaye cos kuka sosai takeyi , antyn ne tajawota tarungume tah hade dah shafa mata baya , dakyar yadaure yace

“Toh kidan bani numbern ta”

“No kabari gobe zatazo inyaso tabaka numbern dakanta”

“Ok Allah yakaimu”

“Ameen” tace , saidasafe yamata sannan yafita, yana fita yaga sadiq ajikin motansu a hankali yashiga  seat din mai zaman banza  batareda yacewa Sadiq din uffan bah , shima Sadiq din shiga yayi ga mamakin shj saiyaga abokinshi nakuka , daman kuma tindazu daurewa yakeyi acikin gidan

“Miye faru dude” Sadiq yatambayeshi, fadamishi yayi sanan yakarasa da Allah yaisa, shima Sadiq din hawaye yaji a cheeks dinshi

“Gaskiya mutane basuda imani kuma wlhy sai Allah yasaka musu” Sadiq yafada

“Ameen” shime shine abinda Amin yafada daganan kuma suka tafi , gabadaya duk guzarinshi yatafi ahaka ya kwana a ranar.

     Abangaren su Anty kuwa…….

Don’t forget to vote

????????wurarh????????

????????????????????????  
                       ABAR SO
                                    ????????????????????????

WRITTEN by: NAFISAT  MA’ARUF  SHEHU
                       ????????WURARH ????????
????GEORGEOUS WRITERS FORUM????

               ????G.W.F????

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 71-72

Abangaren su anty kuwa kiran wayan Nadhira tayi tafada mata wanda yaxo, murna tayi sosai

“Amma miyesa baki bashi number na bah” Nadhira tafada hade dah pouting da bakin ta saikace antyn nagabanta

“Am so sorry babynmu” anty tafada

“OK Antynmu,  gobe by 11 zanzo ki ajiye min kayan dadi” tafada wa antyn

“Kamar miye xan ajiye miki?” Antyn ta tambayeta

“Coke and Fanta masala dakuma Hot milk cake”

“Toh babynmu , saikin zo saida safe ” sannan takashe wayan tana kallon Hasana

“Yakamata kije gida cos dare yanatayi ” inji anty

“Ok Antynmu” har kofar gida Antyn taraka tah sannan tajuya 

Ranar acikin farinciki takwana har Allah Allah takeyi  gari wayaye.

       Washe gari da safe da wurwuri tagama shirya shi dukda da yanzu da kallo kawai yake binta, Abinci tabashi sannan tagyara inda ya baci kafin tabashi maganin shi nan da nan yayi bacci , Addua ta tofa mishi kaman kullum sannan ta tube tashiga wanka , tana fitowa tashirya tanagama shiri ta shafa kohl a idonta tafesa turarukanta, tana gamawa tafice zuwa bangaren mumy.

Lokacin da take shigewa shikuma yafito duba patient nashi, da sallama yashiga saiyaga kaman babu kowa cikeda rashin damuwa yashiga cikin bedroom din kai tsaye , kamshinda ya buge hancin shine yasa shi lumshe idanunshi

“Wlhy irin kamshin ABAR SOna” yafada lokacinda yake bude black sexy eyes nashi……..

     Tana zuwa daidai kofar palour din tatina da slap dinda akamata ai da sauri ta dafa  cheek dinta

“Wlhy saina rama, zakisan kin mareni zan nuna miki cewan in kin saba mawa wasu suna kyaleki toh ni bana kyalewa balle nayi yafiya” tafada lokacin tana shiga cikin palourn. Har kasa ta durkusa ta gaishe su, dadi sosai sukaji cos Kursum bata taba durkusawa tagaishe su haka bah, amsawa sukayi cikin fara’a

“Nadhira koh?” Abba yatamabye ta

“Eh” tabada amsa

“Zoki zauna muyi break fast din tare mana” Abba yafada idonshi acikin nata , ji tayi bazata iya kin tayinshi bah

“Toh Abba” tafada cikeda nutsuwa dakuma kunya , haka taja kujera tazauna daman kuma ba’ayi serving dinsu bah

“Saffiya!!!” Mumy ta kwala wa yar aikinta kira

“Na’am” ta amsa cikin rawar jiki

“Wakike jira yayi serving dinmu?” Mumy ta tambaye ta

“Kiyi hakuri hajiya” yar aikin tafada

“Kibarshi zanyi” Nadhira tafada , tashi tayi tafara serving dinsu cike da kwarewa cos su sukeyi agida, mumy kuwa Nadhira bakaramin birgeta tayi bah haka tadinga jin son yarinyar har cikin bargonta , Abba kuwa kafe mumy yayi da ido yana nazarinta ,Addua yadingayi akan Allah yasa mumy mah taji sha’awar aurawa Al-amin ita. Tana kammala zubamusu itama ta zuba nata daidai wanda zata iya cinyewa

“Anya wannan zai ishe ki kuwa?”mumy ta tambayeta

“Eh mumy, innaci dayawa zanyi rashin lafiya” tafada tana shwagabe fuska hade da rola Anime eyes nata , dariya tabasu sosai ai kuwa suka dara. Suna gamawa tafada musu uzurinta nazuwa ganin gida

“Toh shikenan kuma karki dade” mumy tafada

“Insha Allah mumy” tafada sannan ta tattara dining din gabadaya, tana kaiwa kitchen tafara wanke na wankewa acikinsu, tana cikin kitchen din Amin yashigo gaida iyayenshi sannan yafita cos shima break nashi najiranshi a part dinshi.

    Ta gama wanke plates din kenan Kursum tashigo sanye da nighty gowm dinta

“Wata yar matsiyacin neh yakwashe dining ban karya bah” Kursum tafada tana zazare ido, atake kuwa Nadhira tagane ita ta mareta ranan. Cike da raini tajuya domin taga fuskar wacce ta mareta, suna hada ido Kursum taji wani dum

“Ba laifi” Nadhira tafada tana juyawa ,awajen  Kursum kuwa yarinya tamata kama da wata amma tamanta waye

“Ke bakya jin ina magana neh koh ke kurma ce” Kursum takara fada hade da karewa Nadhiran kallo .

“Anty ga abincinki na ajiye akan dining” Saffiya tafada mata cikeda ladabi , tsaki Kursum taja hade da barin kitchen din

“Nace bah” Nadhira tafada

“Na’am” inji saffiya

“WACECE ITA?” Nadhira ta tambayeta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button