ABAR SO COMPLETE

“Okay,for you besty”tafada
“Thanks dear,kaikuma nasan bazaka ki kaifa bah kodan yayanka”tafada
“Ke nifa kin ishe ni, tukunna mah waye yayanshi?”Hasana yatambaya tana mai zaro big eyes nata
“Soboda shi Zan aura”ta bata amsa atakaice hade da kanne mata ido,dariya kurun Hasana tayi hade da daukan side bag dinta
“Ke kisameni amota,kuma kiyi sauri”yafada cikeda neman tsokana
” Baza’ayin bah”tafada tana murguda baki,kwafa yayi tareda ficewa itakuwa Nadhira dariya tadinga musu
“Dariya mah zaki min koh? shikenan natafi”tafada tareda ficewa wai tayi fushi,itakuma ganin tafice cikin jin haushi,yasata bin bayanta
“Haba besty kiyi hakuri mana, am so sorry”tafada tana mai kama kunne….
“It’s okay dear,saikin jini”Hasana tafada
“Thanks dear and remember no mistake”
“Trust me”Hasana tafada daidai motan yafara tafiya kuma yayi daidai da fitowan mumy, mumy kuwa ganin mutum kamar yar India yasata gyara zaman medicated glass din eyes dinta,juyawa tayi daniyar komawa cikin gida ya hange mumy, karasawa tayi tareda gaishe ta
“Ashe kece,nadau bakuwa mukayi”Mumy tafada tana murmushi
“Ammafa Dana baya son masu Karin gashi fah cos naga har lashes kike karawa”mumy tayi adding,saiyanzu tatina ashe ko dankawali babu akanta,wani irin kunya taji ya lullube ta,wanda tinda bata taba jin irin shi bah
“It’s okay,ki gyara kinji”mumy tafada,gyada kanta tayi tareda shigewa while mumy tabita da kallo tareda sa shakku acikin ranta gameda yarinyar
“Dole nasa abincika minke cos ba yadda dake bah”mumy tafada lokacin tana komawa cikin gida.
Abangaren su Hasana kuwa yana zuwa daidai gidansu ta tsayar dashi,fita tazoyi ya danna lock din motan
“Malam yadai?”tafada frowning her face
“Hmm….. Shadayan ki zaki bani”yafada yana Sosa keyarshi
“Miye shadaya kuma?ta tambayeshi looking so serious,ganin dagaske takeyi batasan abinda yake nufi yasa yayi dariya daidai lokacin da dabara tafado mai, jefa wayarshi yayi tagefen seat dinshi
“Ok barina tambaya miki matar yaya”yafada yana lalube
“Miye kake nema ne wai?”tafada cikeda kosawa da zaman
“Wayata fah nake nema,oh gosh kardai na batareda”yafada kaman dagaske,haka suka dinga neman abinda bai bata bah
“Toh kiban aron wayarki nayi flashing din nawa”yayi requesting,batareda tayi musu bah tabashi wayarta cos itafa ta kosa taji miye shadaya,karbar yayi tareda dannawa nashi Kira kawai saiga waya na ringing agefen seat dinshi
“Oh ashe mah faduwa tayi”Hasana tafada,shikuwa dariyar dayake dannewa ne ya kusan kufcewa , daukar wayan yayi sannan yaduba screen din wayanshi, special numbern ta ne ya bayyana
“Miye wannan?”yatambaya tareda nuna mata screen din wayanshi
“Special number naneh”ta bashi amsa
“Toh ki kirga kigani”yafada yana tabe baki
“Toh miye amfanin kirgawa?”ta tambayeshi
“Just to prove something”yabata amsa,kirgawa tayi dukda tasan amount dinshi
“Shadaya neh”tabashi amsa
“Yauwa toh wannan shine shadayan danace kibani,kinga yanzu basaina tambaya miki matar yaya bah”yafada hade da kanne mata ido daya,tsaki taja tareda fadin
“Budemin kofa nafita”murmushi mara sauti yayi cos dariya tabashi yanda take ta faman hada rai
“Ko baki fada bah daman zanbude tinda motan banaki bane”yafada cikin son tayi magana tareda bude mata kofa
“Sai munyi waya”yafada daidai tafita daga motan,sanda yashige gida kafin yafadi……
A week later……
Acikin sati dayan dasuka wuce abubuwa dayawa sun faru irin shakuwan da Amin da Nadhira sukayi dukda awaya neh, amma har Amin ya gayawa Nadhira sirrin azuciyar shi,itakuwa cemai tayi zatayi tunani akai……
Ga kuma Abdul yayi nisa akogin son Hasana batareda yashirya bah ,gashi kullum saiya mata 100 missed calls amma bata taba dauka bah abin sosai yake mishi ciwo,harya kaiga zuwa gidansu,anan aka fada mai tayi tafiya,daganan yanemi ganin Babanta sannan ya fadamai bukatunshi,Babanta kuwa cewa yayi idan yashirya yaturo iyayen shi,sosai Abdul yaji dadi while dayan bangaren azuciyar shi kuwa cike yake da fargaban kallan masifan da zaisha Hasana yakeyi.
Akwana nabiyu akaje tambaya mishi aurenta kuma anbayar,dayake tinda yatafi akayi bincike akansu kuma aka samu basuda wani aibu.
Su Abba sunso abasu auren Nadhira ma aranar ,amma gudun magana yasa tace zataje tafada wa big Dady cos bazaiyiyu tayanke hukunci dakanta bah,kuma su Abba sunyi na’am da barin .
Hasana kuwa gadan gadan tafara aikin da yakaita ,inda masu gidan kuma suka amince da ita ,duk movement din mutanen gidan babu na wanda ba tayi monitoring bah,atakaice dai aikinta yana tafiya smooth
Back to labari….
“Baby”…..
“Na’am Abba”….
“Why not ki fito da dadynki yasha iska”Abba yafada wa Nadhira dayake yaje wajen Antynsu kuma ta bashi LABARINSU kuma har mumy yafada wa kuma itama ta tausayi musu kuma tabada goyon bayan a aurawa Amin Nadhiran
“Gaskiya Kam baby yakamata kifito dashi”inji mumy dafada
“Toh”ta amsa cikeda jin dadi cos itama taso ace yana fitowa shan iska amma Kuma babu yanda zatayi….
Shiga tayi tareda fitowa dashi akan wheelchair dinshi daidai bakin kofa ta tsayar dashi tareda komawa cikin gida dan dauka ruwa,dadynsu kuwa sake hannunshi yayi daga kan handle din wheelchair din SAKAMAKOn gyangyadin dayafara,aikuwa nan wheelchair yafara tafiya dakanshi,kuma daman gangare ne, wheelchair Kam Sai tafiya yakeyi abinshi,daidai kuma lokacin Nadhira tafito dauke da goran ruwa a hannunta,mamakine yakamata ganin bata ganshi bah, jefar da goran hannunta tayi SAKAMAKOn ihun da taji anyi,aguje tayi inda taji ihun
“Innalillahi…..
Vote
Comment&
Share
????????wurarh????????
????????????????????????
ABAR SO
????????????????????????
WRITTEN by: NAFISAT MA’ARUF SHEHU
????????wurarh????????
*Wattpad: mhizzphydo
????GEORGEOUS WRITERS FORUM????
????G.W.F????
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST
Page 85-86
Barkanmu da sallah,Allah ya maimaita mana. Ameen
“Innalillahi”shine abinda su mumy da Abba ke furtawa sanda suka karasa inda dadynsu yafadi
“Dadynmu kabude idonka babynku ce,wayyo Allah kuyi wani abu mana ga kanshi yafashe “haka tadinga magana ita kadai lokacin da ta isa awajenshi,Abba kuwa phone yadauka yakira doctor,kamin yakira Amin akan yayi gaggawan dawowa gida, baima jira jin abinda Amin ke Shirin fada bah ya yanke wayan.
Bada dadewa bah doctor ya iso ko gama parking baigama yi bah Keke napep yashigo da Amin cos daman alokacin da aka kirashi yana cikin Keke napep din dasauri yakarasa wajen, Abba yasha mamakin ganinshi amma yanzu ba lokacin magana bane
“Akawo ruwa” shine abinda doctor yace,dasauri mumy tadauko bottle water, yayyafa mai akayi inda shikuma ya sauke nauyayiyar ajiyar zuciya
“Yaya kataimake ni kabarni,karka cutar da families dina yanda kake ikrarin cewa,duk abinda kakeso Zan baka”Shine sambatun da yakeyi ,dasuka ga sambatun bamai karewa bane yasa su danna mai Allura,nan da nan bacci yakwashe shi.
Carpet aka shimfida daidai wajen da yake sannan suka mirgina shi. Alokacin kuma Baby na rungume ajikin mumy tana sharban kuka.
“Abbana garin yaya akan tafaru??” Amin ya tambaya yana mai miye da kallonshi wajen Abba, muryan dataji ne yasata dago kanta domin ganin mai magana amma Kuma bayanshi tagani, sake sunkuryar da kanta tayi yayinda Abba yabashi rahoton abinda yafaru……