ABAR SO COMPLETE

Sallaman da akayi neh yasa su miyar da dubansu inda suka jiyo sallaman
“Antynmu!!!” Tafada cikin kuka tareda barin jikin mumy, dagudu takarasa wajen Antynsu tareda rungumeta ta kuka, itama Antyn kuka takeyi sosai…..
Mamaki ne yakama Amin dalilin ganin wanda baiyi expecting ba
“Miye sukeyi anan??”Amin yatambaya
“Kasansu neh??” Mumy ta tambayeshi batareda ta amsa mishi bah
” Erh mana ABAR SO na da Antynsu” yabawa mumy amsa
“Allahu Akbar, daman itace ABAR SO din?? ai itace mukace zamu aura maka”mumy tafada mai
“Tsuntsu daga sama gashasshe”yafada azuciyar shi amma afili cewa yayi
” Amma kince bazan kara aure bah??”
” Yanzu ba lokacin magana bane” tabashi amsa
Some hours later…
Ahankali yake bude idonshi ,dishi dishi yafara gani kafin idon yabudu tas… Nadhira neh tafara lura dashi ,aikuwa dasauri suka matsa wajenshi
” Dadynmu!!!” Tafada cikeda jindadi, muryan wanda yajine yasashi runtsa idonshi abubuwan da suka faru yafara dawowa mai…..
” Nakashe duka iyalanka , kaida su kuma yanxu Sai amafarki kokuma a lahira” yayanshi yafada
” Innalillahi wa’inna illahir rajioun…..” Dadynsu yafada dakarfi hade da bude idanunshi,still bata bace ba juyar da kanshi yayi wajensu Abba yana sake fadin
” Ya kashe su, he killed those innocent souls , he killed all of my happiness , why didn’t he killed me too?? He knows that I lived for them, they are my second half…..
“Dadynmu!!!” Nadhira ta Katse shi cikin cracking voice, dasauri ya juya jin ankira shi tareda taba shi
” DanAllah ku mintsi ne ni ko zantashi da mafarkin danake yi ” yafada yana me kallon kwayar idonta
“Dadynsu!!! Antyn takira shi tana me taba fuskarshi ( cos haka take kiranshi)
Ahankali yake juya fuskanshi gabadaya awajenta sannan ya sauke ajiyar zuciya mai karfin
” Daman nasan yayana bazai iya kashe min iyali bah , nasan wasa yakeyi amma those jokes where so expensive, amaryata ina habibity na take sannan kuma ina Nafhira dakuma cikin jikinki??” Yafada yana mai taba cikin ta
” Dadynmu!!!” Nadhira takira shi , miyarda duban shi yayi wajen ta
” Babynmu!!! Ina yar uwarki dakuma Mommanku ??” Yatambaye ta tareda riko hannunta
” That monster killed them, he gave them the worst death ever” ba bata lokaci ta zayyano mishi abinda yamusu saidai abu daya bata fada mishi ba shine alluran da aka mata
” Ya Salam!!!” Dadynsu yafada hawaye na zuba daga idonshi likewise kowa na wajen
” How could he be so cruel?? Hmmm Nayafe mishi duniya da lahira!!!” Arazane Nadhira tadago ga eyes nata sun gama rinewa tsantsan tashin hankali, su Abba kuwa mamaki ne Yakama su
” Bangane ka yafe mishi bah??” Abba yatambaya
” In ban yafe mishi bah kuma miye zanyi mishi?? Ku Tina fah sakkayya a wajen Allah yake,kuma Allah yanason masu yafiya muma fah muna mawa Allah laifi kuma yana yafe mana nikuma asuwaye da bazan yafe wa wanda ya mana laifi bah?karku manta fah ciki daya muka fito dashi dan’uwa na ne najini in shi ya kini wlhy ni haryanzu inason shi , tinkan ayi daran akayi kwandi, kunga babu abinda Zan iyayi akai” Dadynsu yafada cikeda da kwarin gwiwa
” Tabbas haka yake, Allah ya yafe mana gabadaya” Abba yafada
“Ameen” aka amsa in chorus amma banda Nadhira cos ance na ciki na ciki
” Nagode sosai Allah yabiya ku” dadynsu yafada wa su Abba cikin hawaye
” Babu komai ai yiwa kaine” Abba yafada
” Zaku iya dawowa nan da zama tinda akwai parts dayawa cos nasan zai iya zamowa matsala idan yaganka da rai” Abba yafada
” Gaskiya neh wannan shawaran yayi” mumy tayi adding
” Bazamu daina yimuku godiya bah” Antynsu tafada
” Ai babu komai yar uwa mugode wa Allah ” mumy tafada da murmushi asaman fuskarta ,while Nadhira tana zaune kaman an dasata ga tunani kala kala kai kawo sukeyi azuciyar ta shikuwa Amin banda nazarinta babu abinda yakeyi ga wani dadin da yaji Yana huda kahon azuciyar shi.
” Ina Saleem din??” Dadynsu yatambaya
“Yana school amma sun kusa tashi” Antynsu tabashi amsa
“Baby, kishirya muje dauko shi cos bansan makarantan bah” Amin yafada cikin nutsuwa yana mai kallon Nadhira
“Yauwa ka kyauta “inji Antynsu dafada , murmushi kawai dadynsu yayi yana mai raya wani abu azuciyar shi gameda Amin din.
Itakuwa tashi tayi cikin sanyin jiki sannan tawuce cikin gida while kowa ya bita da kallo….
“Ina… Taab wlhy bazanyi hakuri bah bayan Alkawarin dana dauka wa Yar uwata…” Haka Nadhira tadinga magana kaman wata sabuwar Kamu , toilet tashiga tasan watsa ruwa , tana fitowa wayar ta yafara ringing karasawa tayi tadauka , tana ganin sunanda ya bayyana acikin screen din tayi wata sanyayar murmushi sannan tayi receiving
“Am done besty” Hasana tafada daga dayan bangaren
” You’re so sweet dear, nagode sosai”
“Mention not besty, yaushe Zan shigo??” Hasana ta tambaya
“No Zan shigo and kuma dadynmu yafarka” tafada tana mai murmushi
“Wow Alhmdllh, naji dadi wlhy” Hasana tafada har anajin sautin dariyar ta
” Kuma yace shi ya yafe shiyasa banason muyi maganan awajen mu cos nasan maybe Antynmu tayi hearing conservation dinmu and I won’t want that to happen” tafada cikin sanyin murya
” Ayyerh amma why not mubari tinda yace ya yafe??” Hasana ta tambaya
“I can’t let it go wlhy” itama tafada
“It’s okay, yanxu yaushe zakizo??
“Inaga zuwa da yamma zanzo kokuma gobe “
“Okay Allah yakaimu”
“Ameen” tafada sannan tayi dropping, shap shap tashirya cikin wata armless short ready-made white gown as usual cos tafi ganewa da irinsu, agaban mirror tatsaya kafin taja tsaki sannan tabude wardrobe tadauko black American jacket mara nauyi tadaura akai, kamar kullum ta shafa Kohl , sannan tadauki nude lipstick tashafa wanda ba karamin kyau ya mata bah, katuwar black khimar ta dauko sannan ta sanya shi, flat black cover shoe tadauko sannan tafita haryanzu suna nan ainda tabarsu
” Masha Allah” Kalmar dayafurta neh yasa dukkansu suka juyawa saitin inda yake kallo, dukkansu sakin baki sukayi suna kallonta kaman sunga sabuwar hallita cos bakinta bakaramin karawa fuskanta kyau yayi bah
“Sai mun dawo” tafada batareda ta Lura da kallon da suke mata bah,tashi yayi Shima yamusu sai sun dawo
” Sunshine!!!” Yakira sunan ta bayan yatada mota
” Moonlight” itama tafada
” Ya akayi kina gidanmu kuma bamu taba haduwa bah??”
“Nima dai bansanibah”
“Miracle”yafada underneath his breath
“Indeed” tayi adding, daga nan kuma babu wanda yasake yin magana acikin su har suka isa makarantan su Saleem din
” Why are mute??” Yatambaye ta
” Kaima haka” tabashi amsa
” Daman kana da aure shine baka taba fadamin bah??” Tafada cikin sanyin murya
” Am so sorry , bana son Kiji babu dadi ne shiyasa banfada miki bah” yabata amsa
” But At least you should have told me koda zanji babu dadi, akan miye zanji babu dadi don kayi aure ?? You need it shiyasa kayi auren and I can’t question you for that” tafada hawaye nasintiri a idonta cos ita kadai tasan irin zafin da zuciyarta yakeyi
“Stop crying sunshine am really sorry for keeping the truth away from you ki gafarce ni” yafada tareda rungumo ta , dukan shi tafara yi at the same time tana tureshi daga jikinta, ahankali yashiga Jan jikinshi daga nata cos yasan kishi ne kawai yake cinta, tana ganin yasake ta ta rungumeshi gam gam kaman za’a kwace mata shi , ajiyar zuciya yasauke sannan ya saka hannunshi tabayanta yana shafawa a hankali daga bisani kuma suka breaking hug din