ABAR SO COMPLETENOVELS

ABAR SO COMPLETE

“Naga surprise din da kikace zaki nuna min”yafada yana murmushi

“Oops!!!”tafada tana shafa gashin kanta ga ta yamutsa fuskanta, dariya yake mata harda gwalo cos ba haka taso bah

“Catch me if you can baby” yafada yana girgiza mata bumbum dinshi tareda guduwa aiko cikin zafin nama tafara binshi dagudu ,Sai tazo dab dashi zai sulale , Hasana kuwa Sai dariya takeyi harda zama akan daya daga cikin chairs din wajen,nan kuwa ashe su Amin mah suna kallonsu,itakuwa ta dage Sai binshi take yi cos girgiza bum bum din dayayi neh ya tunzirata ga gashin ta Sai tsale yakeyi ta bayanta harta mai gadi kallon baturiya yakeyi sbd alokacin tacire jacket dinta hango maigadi da yake kallonta Amin yayi ai kuwa wani abu yasoki zuciyar shi…

Tsawan da aka dakamata yasasu tsayawa cak nan da nan kuma hawaye yafara sintiri afuskarta…

“Ke jakar ina ce??” Yatambaye ta cikeda bacin rai daidai lokacin da ya isa wajenta

“Baki da hankali ne?” Yasake jefo mata tambaya, juyawa takeyi don tabbatar da muryan wanda yake zaginta ai kuwa taga babu kowa Sai masoyinta

“Ke!!!” Yakara daka mata tsawa, wani kuka mai tsinka zuciyar mai sauraro tasake cos zagin yashigeta amma ainihin bazallan zagin yasata kuka bah,magana take sonyi amma kuka ya hanata nan da nan jikinshi yayi sanyi.

Kukan da Salim yashiga dashi ne yafito dasu daga cikin gida harda Dady acikin wheel chair dinshi cos suna ta tambayanshi amma bai amsa bah Sai nuna musu waje dayake yi azatonsu wani mumunar abu yafaru shiyasa suka garzayo,abinda suka ganin ne yasasu yin turus, ido Hudu dasukayi da Antynsu neh yasata ruguwa wajenta

“Kya uwah?? Anty ta tambaye ta hade da bin jikinta da kallo

“Tell him abinda banaso” tafada tana nuna shi da yatsa

“Nace miki miye faru?” Anty tafada hade da rike ta cos she’s so scared kwata kwata bata son ganin abinda zai bata musu rai balle azo ga zubar hawayen su

“Tsawa yamin Antynmu, kifada mai tinda nake arayuwata ba’a taba min tsawa bah , kifada mai natsani tsawa balle wanda yake yinta ,Zan iya mai rashin mutunci ba bu ruwana da inasonshi ajiye soyayyar zanyi agefe na mishi rashin mutunci which bazaiji dadin shi bah kuma Allah yagani that will be the least thing din da zanyi, gwanda yakiyaye cos bana barin bashi kema kinsani” tafada hade da barin wajen

“Babynmu kiyi hakuri bazan kara bah” Salim yafada ganin wajenshi ta nufo, amma still bata daina nufanshi bah while shikuma naja da baya,hawayen da tagani a idonshi yasata tsayawa cak,aiko yana ganin ta tsaya ya ruga ya rungumeta

“I hate that Salimu nah” tafada hade da goge mishi hawaye

“Am so sorry Babynmu I don’t that it will hurt you”

“Don’t do that again okay?” Gyada kanshi yayi

“Good boy” tafada hade da tashi ta wuce cikin part dinsu, banda na mujiya ba abinda suke dinsu dashi while kowa na mamakin abinda yafaru atsakanin su, Hasana ne kawai tasan abinda yafaru

“Allah sarki” shine abinda tafada azuciyar ta ,shi kam Amin gabadaya ya damu da cos shi baisan bata fushi bah

“AL-AMIN!!”Dadyn su yakira shi bayan sun gama gaisawa da Hasana harma tashige abinta cos kowa yabar wajen Dady ne yace abarshi cos ya Lura da yanayin Amin din. Karasowa cikin sanyin jiki

“Ya akayi baka san abinda bataso bah??” Cikin sanyin murya yake fadin

“Bata taba fadamin bah” murmusa Dadyn yayi

“Tin yanxu jikinka yayi sanyi??, Amma kasan tanada riko??”

“A’a Dady”

“Yadda ta tafinnan yatabbatar bazata sake maka magana ba Sai after a month” arazane yadago yana kallon Dady

” DanAllah Dady katayani rokonta kozatayi hakuri, in tadaina min magana bansan yazanyi da arayuwa na bah” yafada cikin rawar murya

“Ai haka halinta yake, ko kasan yar’uwarta?? Dady yatambaya

” Kaga duk son da take mawa yar’uwarta toh koya suka samu sabani toh ta daina mata magana kenan!!, Soboda haka just let her be for now cos duk abinda zaka fadamata bazai yi tasiri akanta bah soboda bata barin bashi”

“Au daman abinda take nufi da bata barin bashi kenan??”

“Kwarai dagaske”

“Hmmm”

“Ka kwantar da hankalin ka soboda kasan ance mai Hali bai fasa halinshi”

“Ok Dady amma tasani wannan hukunci nata yayi tsauri dayawa”dariya kurun Dady yayi…….

“Besty!!”

“Miye”

“Akan kawai yamiki tsawa kikayi wannan kukan ko kuma there’s more to it??”

“Idan natina da babu hanyan dazanbi inbar gidan nan zuciyata kuna yakeyi sosai amma Kuma kinsan abinda yayi is not fair,miye na mishi daxaimin irin wannan tsawa? ” Ta tambaya cikin sanyin murya

“Nima gaskiya abinda ban gano ba kenan”

“It’s okay”

“Does that means kin hakura??”

“I don’t know cos nasan in yayi gigin min magana I may disgrace him soboda har yanxu inajin karar tsawan dayamin”

“Allah yakawo mana da sauki”

“Ameen”

“Barina mawa Antynmu sallama”tafada hade ficewa….

“Miye zai mata dazaice tazo??”shine abinda Anty ke tambayan Dady cikin sanyin murya ga idonta harya kawo ruwa…

“Toh miye don ya bukaci tazo?? Shima fah amatsayin uba yake awajenta karki manta” Dady yafada

“Yadda Nadhira bata kaunar shi anya zataje kuwa kasanta da taurin kai” antyn tafada tana share hawayen ta

“Why not aji ta bakinta tukunna”mumy tafada

“Hakane kuma fah” Abba yafada,ganin Hasana yasa Dady aikanta Kiran Nadhira,cikeda sanyin jiki takirawo Nadhira….

Ganin su atsatsaye yasata yin turus

“Karaso baby” jin muryar Antyn yasata karasawa wajen ta dasauri , face dinta ta rike

“Miye sameki Antynmu??” Ta tambaye ta cikeda da damuwa soboda itama bakaramin so takewa antyn nasu bah

“Big Dady neh yace yakamata kizo” wani irin dadi taji tindaga tsakiyar kanta amma Sai ta daura fuska tareda fadin maganar dayasa kowa yin tsit awajen….

Naji wasu nacewa miyesa zance Dady ya yafe mah yayanshi bayan duk abinda yamusu…

Kucigaba da bibiyata InshaAllah Zan kawo muku abinda yasa nace hakan

Comment,
Vote&
Share

????????Wurarh????????

????????????????????
ABAR SO
????????????????????

WRITTEN BY: NAFISAT MA’ARUF SHEHU

WATTPAD: MHIZZPHYDO
????GEORGEOUS WRITERS FORUM????

           ????G.W.F????

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 89-90

“Big Dady neh yace yakamata kizo” wani irin dadi taji tindaga tsakiyar kanta amma Sai ta daura fuska tareda fadin maganar dayasa kowa yin tsit awajen

“Nima kashe ni yakeson yayi kenan??” Wani munafikin hawaye tashare harda Jan hanci sannan tacigaba

” Ba damuwa zanje yanda yabukata amma inhar ban dawo da raina bah ina rokon kowanne daga cikin ku ya yafe min!!!” Tana gama fadin hakan Sai tayi cikin gida da gudu

“Kutimelesi gaskiya baby drama queen ce taab”shine Hasana ke fadi acikin ranta

“InshaAllah babu abinda zai mata, Hasana ki bita cikin gidan koh” Dadynsu yafada wa Hasanan,dama kuma abinda take jira kenan amma Sai tace

“Daman fah Zan muku sallama ne cos naga dare nayi kuma ana rasa abin hawa anan”tafada hade da kallon Abdul ta gefen ido Sai akayi sa’a Shima din kallon nata yakeyi

“Ga Abdul Sai ya kaiki in kinshirya tafiya”mumy tafada cikeda jin kunya take fadin toh kafin tabar wajen,daganan babu kuma wanda yasake magana cos kowa da abinda yake sakawa aranshi

“Amma Allah yayi munafika anan”Hasana tafada lokacin da taci karo da Nadhira tana rawa

“Am extremely happy besty, daman yanda za’ayi nafita nake nema gashi da kanshi ya gayyato mutuwar shi”

“Bangane mutuwar shi bah” Hasana tafada afirgice

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button