ABAR SO COMPLETE

“Ke kinsan miye ake Kira da kisa kuwa,kinsan hunkuncin wanda yayi kisa amusulunci kuwa toh let me tell you in baki sani bah duk wanda yakashe wani tabbas Shima kashe shi Za’ayi, koh kina son akashe ki kema??”
“Toh shima ai naga har rayuka biyu yakashe arana daya ba’a mishi komai, koh hakan na nufin yaci bulus kenan??”
“Sakkayyar Allah fah wani Babban abu ne in bai gani aduniya ba ai in ya hantaya lahira zai gani,amma pls karki ce zaki kashe narokeki cos bazamu so jini yahau kanki bah please” Hasana tafada cikin sanyin murya
“It’s okay bazan kashe shi bah amma gaskiya bazan kyaleshi bah,zan bashi live to remember”
“Ohk ,nizan tafi”
“Jirani nakwashe kayana saimu tafi tare”haka ta tsaya har tagama kwashe kayyayakin ta sannan suka fita.
Ganin dasukayi Nadhira tafito da kayyayaki yasasu sauke ajiyar zuciya cos har Big Dady yasake Kira akan lallai taje ranan.
“Zantafi “Nadhira tafada
“Allah yataimaka and behave your own self there” Dady yafada
“InshaAllah” sannan tarungume Antynsu harda Sumba tabawa Antyn a cheeks dinta
“I will miss you Antynmu” tafada tana mai share guntun hawayen ta all the same time tana share hawayen antynsu,sanda kowa agurin yaji tausayin su dakuma jinjina irin soyayyar dake tsakanin su biyu cos in ba’a fada bah you will think she’s her sister nan kuwa amatsayin uwa Antyn take awajen Nadhira
“Allah yabiya ki da gidan Aljanna amaryata” Dady yafada acikin aranshi cos yasan dawata daban ne amaryan nashi to ba makawa yarshi tashiga gari amma ji yanda take nuna tsantsan so ga gudan jini Nargis dinshi daya rage
“Take care of yourself Baby” Antyn tafada
“InshaAllah” Salim tagani yakura mata ido, Sai asannan mah ta ganshi ahankali takarasa inda yake ga idonshi yayi raurau ,tsungunawa tayi agaban shi
“Hey why do you look sober??” Ta tambaye shi (yafi jin turanci akan Hausa)”
“I’m gonna miss you our baby”yafada hade da rungumeta
“Calm down I will be back it’s a matter of my troby Salim and I will also miss you dear” tafada tana breaking hug dinsu sannan ta tashi, juyawan ta keda wiya taga Amin yanufi gurin mota da trolley dinta alaman shi zai kaita
” Antynmu!!! I love you so much”tafada da dan karfi cikin sweet slim voice dinta daidai ta isa wajen motan Abdul
“I love you more dear”Antyn ta amsa ga murmushi kwance asamar fuskarta cos itama Nadhiran murmushi takeyi,
(Toh gareku matan da suke kishi da yaran miji,wasu kam ma a idon miji zasuyi behaving normal Wato mai two face kenan wasu kuma they don’t care… Toh bari Kiji daga lokacin dakika fara hantaran yaran kina nuna kishin ki karara akan yaran agaban shi toh in yana miki 100% So toh ki tabbatar zai dawo 40% cos bada yaran yakamata kiyi kishi ba da uwansu yakamata kiyi idan kuma bata raye kuma saiki ajiye kishin ki agefe ki Kula marayu. Ke kuma mai two face kina nuna musu so agaban miji dazarar ya fita Zaki fara musguna musu toh billahi lazi in yazo yagane toh in son dayake miki
100% ki tabbatar ko 15% sonki azuciyarshi baizai sake haurawa kuma kinyi loosing kimarki darajarki da kuma mutuncin ki a idon cos koda kin daina mawa yaran abinda kike musu still zai dauka as pretending kikeyi. In anzo kuma kice kinason mijinki ko kin manta Suma daga jikin mijinki suka fito neh hala?? In kikaso su tsakanin da Allah zai daukaka kimarki ,mutuncinki da soyayyarki acikin zuciyar mijinki bama shi kadai bah harda yaran nashi cos bazasuyi kukan uwa bah. In bakiso su bah kuma kinason babansu me kikayi kenan ??wannan shi ake Kira da naughty work.Wlhy yaran ma bazasu na kallonki da daraja bah kuma daga karshe suyi sanadiyar mutuwar aurenki da baban su!!! DanAllah mata akiyaye cos yana daga cikin matsalolin da ake fuskanta ayanzu)
Mamakine yakamashi ganin motan Abdul tanufa bacin kayanta na motan shi
“Jeka fito mi da kayana acikin wancan motan kafin raina yabaci” tafada lokacin data shiga bayan motan
“Ohk ma” Abdul yafada cikeda da tsokana
“Kai miye zakayi??” Amin yatambayi Abdul dake kokarin bude boot din motan shi
“Spare me Aika nazo dauka” yafada yana fitowa da ido waje,haka yagama daukan trolley din sannan ya rufe boot kafin ya bar wajen, haushi kuma kaman ya kashe shi ganin irin abinda tamishi agaban jama’a.
“Ba laifin ki bane”yafada underneath his breath.
“Arrange my meeting with those guys,i will be in your area in no time”shine message din daya shigo wayanshi cikin gaggawa yayi dialing din wata number
“Ya akayi ne??” Shine abinda aka fada cikin wata katuwar murya daga dayan side din wayan
“Cewa akayi kuzo yanxu”
“Ohk gamu nan zuwa” shine abinda mai katuwar murya yafada.
Cikin motar dasuke babu wanda yayi magana, Nadhira ne ta katse shirun dacewa
“Kafara dire Hasana cos zanmawa ummi sallama”
“Toh matar yaya” Abdul ya amsa mata,suna isa daidai kofar gidan Nadhira ta sauka daga motan Sai ya rage daga Hasana Sai Abdul amotan,instead of tayi cikin gida sai tabiye wani hanya daban
” Aturo gidanmu sbd susan kafasa auren yarsu” Hasana tafada kaman bata damu bah at the same time tana kokarin bude motan domin fita.
Cak ta tsaya dalilin rike hannunta dayayi
“Haba Hasynah!!!”
“Nibah Hasynka bace” tabashi amsa a hasale
“Ohk Hasyn matar yaya”
“Better”
“Am so sorry,i never mean my words, kin ban haushi ne shiyasa am sorry,taya ma kike tunanin Zan iya rayuwa babu ke acikin?? Ki yafe min kinji” yafada yana girgiza hannunta jin bata juyo bah
“It’s okay” tafada still bata juya bah
“If you know it’s okay pls atleast look at me and smile” daman kuma abinda take jira kenan, ahankali tajuyo sannan ta mishi murmushi
“Wow pretty, one hug for this” yafada batareda tunanin komai bah ta rungumeshi, kankameta yayi Yan mai sauke ajiyar zuciya, breaking hug din tayi sannan tamishi Saida safe
“Baza’ayi haka bah barina rakaki”
“Ok”sannan suka fita
Bangaren Nadhira tana fita daga motan tayi hanyar baya, mika mata abu akayi acikin…..
Vote,
Comment&
Share
???????? wurarh????????
????????????????????
ABAR SO
????????????????????
WRITTEN BY: NAFISAT MA’ARUF SHEHU
WATTPAD: MHIZZPHYDO
????GEORGEOUS WRITERS FORUM????
????G.W.F????
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST
Page 91-92
Bangaren Nadhira tana fita daga motan tayi hanyar baya, mika mata abu akayi acikin bakin leda sannan tamusu godiya kafinnan tashige gidansu Hasana. Tana shigewa toilet yin Alwala Hasana tashigo
“Kice mai yaje yayi Sallah”
“Toh Tasallah”
“Whatever lover girl” dariya kawai Hasana tayi sannan taje ta fada mai. Tana idar da sallah tamawa ummi sallama akan zata tafi gidan big dady , Addua ummi tamata sannan tafice daidai nan kuma yadawo daga masallaci,rungumeta Hasana tayi
“Take care and don’t do anything foolish over there,and be a good girl cos matar gidan bata da matsala and am very sure heart naki zaiyi melting because of her behaviors”
“InshaAllah Hasynah amma batun heart dina zaiyi melting bai taso bah”
“We shall see to it then”
“Whatever” sannan tashige cikin mota,shidai bai gane akan me suke magana akai bah
“Darling bae saina zo hira koh??” Yatambaye ta
“Yauwa sweetest boo saika zo” tabashi amsa
“Ohk bye and take care of yourself”
“I will and you also”
“InshaAllah” yafada sannan tashige mota,sanda tadaina ganin motan tashige cikin gida.