ABAR SO COMPLETENOVELS

ABAR SO COMPLETE

Suna Isa kofar gidan taji wani sanyin dadi naziyartar ta ahankali ta furta

“Yar’uwarta nakusa cika miki Alkawarin dana dauka miki”

“Ya kikayi shiru kuma matar yaya??” Abdul ya katse ta da tambaya

“Nothing much wlhy” ta bashi amsa tareda bude kofar motan sannan ta wuce wurin booth,b babu bata lokaci ta fito da trolley dinta sannan tamai Sai anjima kafinnan ta yi wajen gate din tareda kwankwasa wa , alokacin kuma har ya bawa motan Wuta yayi gaba abinshi.

“Ina wuni baba” tagaisar da baba mai gadi

“Lfy yen nan,daman kuna nan?”yatambaye ta cikeda mamaki

“Erh wlhy muna nan”tafada tana kutsawa gaban cikin gate din

“DanAllah baba akwai chemist neh kusa??”

“Eh akwai amma saikin dan fita ta bakin hanya”

“Toh ga kayana nan barina siyo magani nadawo”

“Toh adawo lfy”

“Allah yasa”tafada hade da ficewa, tafiya tadanyi kadan kafin ta iso chemist din babu bata lokaci aka bata abinda take bukata kafinnan ta yi gaba abinta.

“Assalamualaikum”shine abinda wani yafada daidai lokacin daya shigo chemist din

“Wa’alaika Salam” suka amsa mai

“DanAllah ina tambaya neh”

“Allah yasa mun sani”

“DanAllah yarinyar chan data fita miye tasiya neh??”

Sanda suka kalle juna tukunna kafin daya yace

“Oh kana nufin wancan yar hannun kake tambaya??”

“Eh ita dai wanda tabarnan yanzu”

“Dinger tasiya” yafada cikin ko in Kula

“Dinger kuma!!!” Sadiq Ya maimaita cikeda mamaki

“Eh mana ko baka gane bane”

“Nagane, nagode sosai” yafada hade da ficewa har lokacin bai daina mamaki bah, ahankali takarasa wajen motan su sannan yashiga

“What’s up dude?? Ina fatan ba ciwo mai tsanani bane yake damunshi??” Amin yatambaya cikeda tsoro , tsaki kawai Sadiq yaja sannan yace

“In fada maka abinda taje siya zaka yarda??”

“Erh mana”

“Dinger taje siya”

“Dinger kuma!!??”yatambaya afirgice

“Kasan miye ake Kira da Dinger kuwa??”yafada har wani zufa ke keto mishi

“Toh da bansaniba ne toh bari na maka dalla dalla, CONDOM tasiya”

“Innalillahi, miye zatayi da Condom kuma??” Yatambayi Sadiq cikeda damuwa

“Waye San mata” Sadiq yabashi amsa

Haka suka bar wajen tareda jimami dakuma tambayoyi aranshi.

“Sannu baba nadawo”

“Yauwa sannu da dawowa” baban yabata amsa sannu takarasa wajen da ta bar trolley dinta sannan tashige cikin gida da sallama sauke abakin ta

“Abin mamaki!!! Waye nake gani kaman enbiyu(haka take kiransu)”

“Nice”

“Ai ba’a fada mana kinji sauki bah(dayake daman basusan tafara magana bah)

“Ai kuwa inaga banyi wata 2 dajin sauki bah”

“Ayyerh Allah yakara sauki”

“Ameen ya Allah”

“Kardai ke Alhaji yace zakizo mana kwana biyu?”

“Eh wlhy “

“Ok sannu da zuwa,bari yaran nan suzo su nu…..

Kuyi manage da wannan babu yawa, naso nayi dayawa amma ban jin dadi sosai…..

Comment,
Vote&
Share

???????? wurarh????????
????????????????????
ABAR SO
????????????????????

WRITTEN BY: NAFISAT MA’ARUF SHEHU

WATTPAD: MHIZZPHYDO
????GEORGEOUS WRITERS FORUM????

           ????G.W.F????

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Dedicated to
Hasynah

Page 93-94

Alhmdllh Hasynah tayi waya,toh Allah yasa ki mora kuma ki kashe lfy, namiki murna besty wannan page din naki ne kedai…”

“Ok sannu da zuwa,bari yaran nan suzo su nuna miki dakin da zaki zauna”

“Toh mumy” nan mumy ta Kira Maimuna sabuwar yar aikin ta wanda tayi bayan tafiyan Hasana. Nan tafada mata akan tanuna mata dakin da ta gyara dazu..

“Muje” Maimuna ta fada, batareda Nadhira tayi magana bah tabi bayanta…

Hadadiyar daki aka nuna mata amma baikai dakinta na asalin gidansu bah, kasan mattress tadaga sannan tacire ledar da aka bata ta ajiye likewise Condom dinda tasiya chemist,ta ajiyewa tagyara wajen yayi smooth kaman ba’a sa komai bah ,kai tsaye wajen sif din dakin tanufa ahankali take jera kayanta aciki wanda duk cikin kayayyakin babu atamfa ko daya ,tana gamawa tazare towel dinta sannan tashiga toilet da nufin yin wanka.

Daidai ta fito daga wanka Maimuna tayi sallama sannan tashigo sannan tace” wai inji mumy kizo kuyi dinner kuma Alhaji yadawo”

“Ohk kice sallah zanyi sufara ci ,in na idar Zan fito”

“Toh” tafada tana hararan bayan Nadhira cos tinda taganta taji Nadhira bata mara bah

A Palour tasamesu sannan tafada musu aiken Nadhira din. Daidai kowa yazauna a dinning din Nadhira ta fito, comfy sleeping dress ne ajikinta kasancewan ana sanyi agari ga wani shegiyar kamshin dake tashi ajikinta. Kura mata ido sukayi suna kallon ta,cikin tsarguwa da irin kallon da Nadhira ke jefan shi dashi yasashi tashi yanufe ta

“Babynmu ce tagirma haka, lallai kice sauran kawai muji anzo tambayar aurenki” yafada tareda rungumeta ajikinshi, murmushin karfin Hali ta daura a saman fuskarta, rabe runguman tayi tareda shagwabe fuska da fadin

“Haba big dady wani irin za’a zo tambayar aurena bayan ga wa’incan hajiyoyi azaune , su ba’a yi musu aure bah Sai ni??”

“Ai su karatu sukeyi shiyasa” yafada hade da Jan hannunta zuwa dinning table,azuciyarta cewa take

“Wato nine ban karatu soboda banda gata, dan iskan mutum harda goga mun kirji da wayo,wlhy da badan ubanka da ubana daya bane dana auna mai zagi..” zaunar daita akan kujeran dayayi ne yasata dawowa daga tunanin data fada

“Sannunku” tafada batareda ta kalle su Fatiman bah

“Yauwa” suka amsa cikin shan kamshi,cikeda nutsuwa suke cin abinci har suka gama, suna gamawa Maimuna tazo kwashe plates,da gangan ta fadar mata da cup din juice ajikinta

“Wayyo momma!!?”Nadhira tafada da karfi Sai asannan hankalin kowa yadawo kansu dasauri Maimuna take bada hakuri cos bata zaci zata chanchara ihu bah, kallon ta Nadhira takeyi sai alokacin talura ashe da gangan ne cos inba da gangan bah ai tin kafin tayi magana yakamata ta bada hakuri amma saita share

“Wlhy Sai na rama” tafada azuciyar ta

“Miye kike kallo har Kika zuba mata abu baki sani bah” big dady yafada cikin ihu irin alamun ranshi yabacin nan

“It’s okay big dady,bada sanninta bane” Nadhira tafada hade da tashi daga kujeran

“I need to use the wash room” yafada hade da barin wajen, dukda tabar wajen big dady bai daina surfa ruwan masifa bah,mumy kam hakuri tadinga bashi while su Fatima sunyi kaman ba’a wajen suke ba.

Maimuna nashigewa kitchen tafara tunanin waye yarinyar da har Alhaji zai dinga mata masifa haka ahankali tafurta”zamu hadu da kaine “(nace towww…)

Kai tsaye toilet tanufa tana mamakin halin Maimuna cos she she sees no reason dazata zuba mata abu ajiki itada yaune kawai zuwanta gidan,dazuma da ta harareta tagani ta mirror,tsaki taja hade da fadin ” zakiyi bayani “…

Sanda tasake wanka sannan tafito a palour tasame su ga tea cup agaban big dady,ahankali takai idonta kan agogo taga exact time din Hasana tafada mata ne acikin zuciyarta tace

“Aikin ki yayi kyau Hasynah..” Big Dady neh yakatse ta da fadin

“Karaso mana Babynmu” cikin sanyin jiki taiso wajen su as usual wannan munafikin murmushin na face dinta

“Ahado miki tea neh??”yatambaye ta cikin kullawa

“Munafiki kawai”tafada azuciyar ta while azahiri tace

“A hadomin kuma bayan nasan hanyan kitchen,karka damu daga gobe nizan na hada mana tea din cos na tabbata Zan fita iyawa”

“Ai Dole kifita iyawa ko kin manta da Mommanku ba indiya ce, kuma sune dagin shayi”mumy tafada, dariya sukasa gabadayan su

“Toh indai hakane Babynmu ce zatana mana tea kullum” big dady yafada

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button