ABAR SO COMPLETENOVELS

ABAR SO COMPLETE

Ganin kallon da suke mata neh yasata tattara duk nutsuwar ta waje daya takuma aza murmushi asamar fuskarta tareda karasawa wajen Amin cos ita kam mah tadauka wani abin daban zasu gani shiyasa tsoro shiganta .

Karban kwallin Condom din tayi hannunshi, tareda lura da yanayin bakincikin dayake ciki kafin tace

“Akan wannan abin kuke kallo na kaman wata sabuwar hallita,nikam mah har kunsa naji kunya”

Ganin yanda take magana naneh yasashi tsura mata ido for some seconds gani yayi duk wannan tsoron dakuma rashin gaskiyan daya bayyana a fuskarta dazu babu su.

Cikin sanyin murya yace”miye kikeyi dashi??”

“Toh miye zatayi dashi ai kowa yasan amfanin wannan abun guda daya neh tal” wannan police din yafada cos bakaramin bata mai rai Amin yayi da wannan tambayan bah.

“Lah???????? waye cemuku amfanin shi daya neh??” Ta tambaye su cikeda mamaki.

Shuru dakin yadauka suka sake Baki da hanci suna mai neman dayan amfanin Condom cause gabadaya ta jefa su aduhu.

“Ke karki raina mana hankali fah” wannan police din yasake fada a kaushashe cos gabadaya tafara bashi haushi ,shidayake son neman hanyan daza su hadu soboda gaskiya ran shi yabiya(Niko nace kwalelenka)

“Yadai kana min magana saikace yar ka??” Tafada tareda maka mai harara.

Zaro ido yayi ganin abinda tayi mishi amma ba damuwa zaijira insun hadu yafada mata shi baya daukan raini( lallai kam)

“Just say what kikeyi da wannan” yafada cikeda zakuwa

“Packing din gashi na nakeyi dashi” tafada sounding relieved

“What a bullshit” Amin yafada afusace cos gani yake raina musu hankali kawai takeson yi

Itadin mah bai tsira bah sanda ta banka mai nashi hararan, rolling eyes dinta tayi sannan tacire dankawalin kanta.

Nan kuwa doguwar gashin ta ya bayyana wanda aka tufke atsakiya.

Zaro abinda ta tufke gashin tayi tareda mika mishi abin wanda shi bah roba Lin bah。

Karba yayi yana juyawa ahannu shi amma har lokacin bai dago miye bah, shima police din karba(inaga shi yayi leading dinsu) yayi yana dubawa.

Duka dakin sanda suka rike abin suna kallo daga karshe suka miyarda duban su gareta.

“Baku gane miye bah koh??” Batareda ta bari sun yi magana bah ta ciro Condom daya daga cikin kwali.

Fatima kam harda rufe ido wai batason gani, dariya kawai tayi sannan tayi wajen drawer.

Razor blade tadauko sannan ta ijiye Condom din akan dressing mirror.

Yanka daidai wajen band din rike …???????? tayi Sannan ta dago shi.

Toilet tashiga ta wanke yanda maikon zai bar jikin abin bayan nan tafito.

Na mujiya suka zuba mata suna kallon ikon Allah.

Mika musu tayi suna kallo Sai sukaga iri daya neh da wanda tacire akanta.

Murmushi tasakar musu tareda fadin” akan nayi amfani da roba Lin ya tsinka min gashi toh gwanda nasa wannan, in takaice muku nafi jin dadin amfani da ”’CONDOM BAND”’ akan kowani band”

Mamaki neh yacika su jin abinda takeyi da Condom cos basu taba zargin haka abin yakeba sun dai San ana amfani da Condom neh wajen kariya

while Amin ya dinga blaming kanshi akan zarginta dayake yi, sosai zuciyan shi yasamu relief jin ba abinda yake tunani bane

Dariya da ita kadai tasan ma’anar shi tafashe dashi sannan tace” I knew you will all be shocked, shiyasa ma dafari tsoro tashigeni dana tina da na fito da kwallin kuma dafari I thought bazaku tsaya ku fahimce ni bah”

Ta karashe maganar da murmushi, dukkansu mah murmushi sukayi amma banda wannan police din cos gabadaya shirin shi ya wargaje.

Fita sukayi daga dakin, cewa sukayi zasu duba compound din ba bata lokaci aka musu izinin dubawa.

Har suka gama dube duben basu ga komai bah, haka suka koma akan in Maimuna tafarfado zasuji komai…

Zaune take agaban mirror acikin daki banda murmushi babu abinda yake fitowa daga Samar labbanta.

Daman tin randa taje tasiyi Condom ta lura wasu na binta amma dayake shu’umace saitayi kaman bata gansu bah.

Abin mamaki kuma saitaga abokin Amin neh yashiga nan tasan tareda Amin sukazo kuma sawunta suka biyo.

Washe gari takoma chemist din tareda tambayansu wanda yazo immediately lokacin da tafita ,basu tsaya bata lokaci bah suka zayyana mata abinda ya tambaya dayake bakin su baida rufi.

Nan tamusu godiya tareda ficewa, tana komawa gida tadinga sakawa da warware akan yanda zatayi da Amin cos tasan yanzu yadaura Ayar shakku akanta kuma mai yiyuwa mah yafara zarginta.

Daman tinda taga doctors sunyi confirming substance din Cocaine acikin abin da tasha tasan dole Sai anzo yin bincike shiyasa tinda wuri tasan inda dare yamata.

Amma agarin kwashewa Sai akayi rashin sa’a Condom yafadi,amma batasan takamen men abinda yafadi bah irin bari tagama saita dauka Sai Allah yasa tamanta shi awajen.

Sai alokacin da akace za’a duba dakinta ta tina ashe bata dauki abinda ya fadi bah shiyasa tsoro ya shigata.

Tana ganin Condom neh ranta yayi fari fatt tsantsan murna cos tasan in akan Condom neh zata iya kare kanta…

Numfawa tayi tareda sakin wani murmushi tinawa datayi yanda tayi da cocaine.

Jan drawern jikin dressing mirror din tayi tareda daukan hands glove sannan ta tashi, dayake dare neh kuma anriga da an rufe kofa kuma tana kyautata zaton kowa yayi bacci.

Ahankali tayi jikin window tayaye labule, sliding glass din tahau cirewa ahankali gudun karyayi kara.

Tana gama cirewa tasauke ajiyar zuciya mai karfi, zura kafafun ta tayi sannan ta dira ahankali.

Wajen bolan gidan tanufa sannan ta sanya gloves din ahannunta, sanda ta daddaga wasu abubuwa kafin tazura hannunta chan kasa.

Torch din wayan ta tukunna daidai tafito da wani bakin leda. Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna…(nace master planner bah…)

Vote,comment&share

Mhizzphydo
????????????????????
ABAR SO
????????????????????

WRITTEN BY: NAFISAT MA’ARUF SHEHU

WATTPAD: MHIZZPHYDO
????GEORGEOUS WRITERS FORUM????

           ????G.W.F????

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 98

Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna…(nace master planner bah…).

Straight kitchen tanufa sannan ta dauko container din gishiri tazazzage gishiri acikin buhun gishirin cikin store kafin ta zuba cocaine din acikin container din.

Ajiyar zuciya tasauke sannan tasake wannan murmushin muguntan ta kafin ta koma dakinta…

Washe gari ita tafara tashi tashiga kitchen ta dafa musu lafiya yiyar breakfast.

Kafin su fito ma har tagama komai ta feso wankan ta as usual cikin short gown yau kam ko dankwali batasa bah.

Ta zauna da 10mins yen gidan suka fara fitowa, sosai suka sha mamakin ganin abinci asamar dining table.

“Babynmu kece kika bawa kanki wahala haka??”mumy tafada cikin farinciki cos Nadhira bakaramin burge ta tayi bah

“Ai bawani wahala bane” tafada cikin sune kai kaman da gasket

“Madalla Allah ya biya”

“Ameen mumy”

Tashi tayi tareda karasawa wajen dining table din cos su kam har sun zauna sun fara serving Kansu.

Lura datayi Nadhira batacin abinci yasa mumy cewan” ya naga baki cin abinci”

“Inajiran Big dady tinda naga baku jira shi bah” Tafada cikin murmushin daya zame mata jiki

“Kin kyauta Babynmu “suka ji muryan Big dady daga bayansu.

Tashi tayi taje ta taroshi tareda mai Ina kwana amsawa yayi cikin Jin dadi tareda kawar da duka zargin dayake mata acikin zuciyarshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button