ABAR SO COMPLETENOVELS

ABAR SO COMPLETE

Zaunar dashi tayi tareda serving dinshi nashi abincin, lokacin har su Fatima sun gama cin abinci.

Gaishe shi sukayi sannan ya amsa cos in suna cin abinci ya hana su magana tashi sukayi suka bar wajen…

“In hado maka coffee neh??”tayi requesting

“Gyada mata kai yayi tareda sakar mata murmushi

Itama murmushin tamiyar mishi tareda wucewa kitchen.

Tea cup tadauko tareda fara zuba cocaine din akasa sannan tasa garin coffee din.

Ruwan zafi tadauko ta sheka akai sannan ta dauka spoon ta gauraya su hasaida aka daina ganin garin cocaine din sannan ta fice.

Ta kaiwa ta dauki cube din sugar sannan tasa aciki..

“Allah yamiki Albarka” dady yafada cikin mouthful

“Ameen” tafada tareda Zama akan kujera tukun tayi serving din kanta mah.

Ganin yakai cup din bakinshi neh yasata cikin boyayyen murmushi…

Dayake baiyi changing taste bah shiyasa Big dady bai fahimce komai bah.

Tass ya shanye coffee din harda gyatsa.

Ya na mikewa itama ta Mike dayake tagama cos bata cin abinci dayawa.

Car key dinshi ya dauka sannan ya mawa mumy magana wacce taje shirin zuwa asibiti.

Chan saigata ta sauko daga sama cikin takunta na matan attajirai…

Da murmushi ta tareta itama tareda taka musu zuwa waje

“Ke bazaki zoh dubiyan bane??”mumy ta tambaye ta cikin kulawa.

Murmushi tasake sannan tace” ni bana zuwa dubiya hannu zalla ma’ana so nake na hada koda kunu neh in case inta tashi tasamu abin sawa abaki”

Sosai suka sha mamaki cos ko kadan wannan tunanin baizo musu bah.

“Madalla Babynmu Allah ya biya ki in kin tashi tahowa driver yakawo ki” dady yafada.

Toh tafada still akwai wannan murmushin afuskarta, bye bye tayi musu sannan ta shige cikin gida.

Straight kitchen takara nufa agagauce ta daura ruwan akan gas tareda kara sa cocaine acikin ruwan..

Sharp sharp tagama hada kunun sannan ta juye acikin flask..

Dakinta tawuce ta Kira wani number,dagawa akayi daga dayan bangaren akace

“Ranki shi dade baki da sauki fah” yafada cikin muryanshi irin na mashaya

Wata karamar tsaki taja sannan tace”ya ake ciki??”

“Gaskiya aikan ki yanzu ya kara kudi soboda da kyar ake samu amma dai Alhmdllh ansama miki “

“Nawa neh ??”ta tambaya atakaice

“Dubu goma zaki ciko”

“Toh inason mu hadu nan da minti 10 zan taho maka da cikon kudin”

“Toh Hajiya muhadu a inda kika ce zamu hadu??”

Sanda tayi Jim sannan tace “tsari ya chanza”

“Toh yanzu miye tsarin” yatambayeta

“Akwai wani mai shago a anguwan danake ta bakin titi, inkaje saika bashi kace za’a zo akarba nikuma kafin ka karaso zan bashi aika ya ajiye maka, yanajin kace aika kazo karba zai baka kudin amma kayi wrapping dinshi yanda babu wanda zai gane wani Abu neh aciki” tana gama magana ta katse kiran tareda deleting din numbern”

Dariya yayi yana jinjina irin kwakwalwar Hajiyan( bai taba ganinta bah daman) afili yace”komin kwakwalwar ki yau kam saina san wace ce ke”

Tana ajiye wayar tasauke wata ajiyar zuciya kafin tabar cikin dakin da leather a hannunta.

Waje tafita dashi sannan ta gaisar da baba mai gadi.

Yana ganinta yafara wangale baki musamman mah daya hangota da leather.

“Wa’inan yaran fah??”ta tambaye shi

“Ai basu nan amma sun kusa dawowa daga makaranta”

“Ohk in sun dawo amin magana” tafada tareda juyawa”

Yace”toh” yana mai yin adduan Allah yabashi y’a kaman ta.

”’5mins later…”’

Fitowa tayi amma yanzu leathers biyu neh a hannunta.

Yaran suna ganinta suka fara murna cos sosai suke sonta.

Wanda tasan tana da nutsuwa kuma wanda bata fiye magana bah takira acikin su sannan ta jata gefe daya.

Bata leather daya tayi sannan tace “ki kaiwa mai shagon bakin hanyan nan,kina bashi kice za’a zo akarba sannan kijuyo”

Gyada kai yarinyar tayi sannan ta wuce wajen mai shago din.

Kaman yanda tace haka yarinyar tayi, tana dawowa tabawa yarinyar nata alawan cos daman kullum saita raba musu shi sadaka

”’5mins later…”’

Hango wani huge guy nayi wanda kallo daya xaka mai kagane bashida mutunci shagon ya shiga tareda bashi aikan sannan aka bashi kudin.

“Waye neh yakawo kudin??”ya tambaye mai shago

Mai shago kuwa ganin babu rahama afuskarshi yasa shi fada mishi wata ce ta kawo,

“Ya take??”

Nan kuwa ya zayyana mai kallan kayan yarinyar dayake akwai niqab afuskarta(daga islamiya suka taso amma babu uniform ajikinta)

Gyada kai yayi tareda ficewa daga shagon, yaje ya zauna a inuwa yana jiran dawowarta.

Hango shi tayi tacikin mota awajen inuwa,wata murmushi tasake ganin zaton ta yazama gaskiya.

Sanda suka danyi nisa tace mai ya tsaya sannan tace”in bazaka damu bah aika zaka karbo min??”

“Haba miye kuma abin damuwa anan,kifadi komiye ni mai iya miki neh”yafada cikin sanyin murya

Murmushi tasake akaro na biyu sannan tace “shagon bakin titi dinnan zakaje kasiyo min flour mudu 5, sai kaga yafara auna flour din ma’ana in yajuya baya saika dan duba min karamin leathern da aka mai kyakyawan package. Wannan leathern zaka dauko amma fah karka bari yagani. Ga wannan saika ijiye shi awajen da kadauki leathern”

Yace toh tareda karban kudi da wata farar envelope daga hannun ta.

Fita yayi daga cikin motan tareda wucewa shagon ,kaman yanda tace haka yayi ,yana karba ya faki idon mai shago sannan ya tusa leathern acikin flour din kafin yafito.

Yana komawa ya Mika mata leathern flour din karba tayi tareda ajiye wa cos batason ya bata mata hannunta.

“Wajen matan ka zaka fara kaini kafin muwuce asibiti din”tafada mai

“Toh”amsa tareda nufar daita anguwan Mahaukata(karku ce fah Mahaukata neh a anguwan a’a sunan anguwa neh kawai)

Anguwan talakawa neh sosai wanda kowa harkan gabanshi yakeyi ga yen talla sai fitowa sukeyi yasu wajen cin kasuwan su.

Adaidai wani gida mai labulen buhu yayi parking itama fitowa tayi tana jinjina ma masu Zama a anguwan.

Iso yamata zuwa cikin gidan inda ya tayata rike leathers din flour din samun matarshi sukayi inda take cilla dan wake acikin ruwa.

Gaisheta takeyi amma abin mamaki Maimakon matar ta miyarda hankalin ta kan bakuwa sai takara miyarwa kan danwaken ta.

Duban agogon hannunta takeyi inda yanzu taci minti uku azaune cos tintini driver yafita.

Gyaran muryan da tayi neh yasa matar Dan juyowa”gashi ni natafi”tafada tana tashi tsaye

Cikin dan Jin kunyan abinda tayi matan tashi tsaye tareda gaishar da Nadhira.

“Gashi akwai wani leather acikin wannan kidan cire min sai ki karkada min flourn jiki”tafada cikin nutsuwa

Cikin rawan jiki matan tasa hannu ta cire sannan ta karkada harda gogewa da zanin jikinta.

Karba tayi sannan tace”ni natafi sai watarana in Allah yayi zamu sake haduwa tinda na Lura kinfi bawa kasuwan cin ki muhimanci fiye da mutane” tana gama fadin hakan tayi gaba tareda boye leathern acikin side bag dinta.

Sosai matar driver taji kunyan abinda ta aikata cikin sanyin jiki takarasa gurin tukunyan sana’arta…

Suna Isa asibiti tabar side bag nata acikin jaka sannan tafito da flask din kunu.

Shiganta dakin yayi daidai da farfadowan Maimuna kuma alokacin akwai doctors aciki, ciki kuwa harda Amin.

Gaishe su tayi cikin sanyin murya sannan ta karasa wajen gadon Maimuna din.

“Ya jikin ki??” Tafada a hankali,itakuwa Maimuna banda binta da ido babu abinda takeyi.

In akwai liquid abinci abata soboda taji karfin jikin ta”Amin yafada

Mumy neh ta dauki flask din tareda zuba kunun ciki acikin cup.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button