ABAR SO COMPLETE

Ganin yanda ta dage neh yasashi fadin”nikam bazan sha sugar bah ko sokike diabetes dina ya tashi neh”
Bata fuska tayi tace”Oops am sorry”
Azuciyarshi fadi yake”Shegiya an gaya miki zan barki ki Kashe ni da raina neh?? Ai ina dawowa zanyi maganin ki shashasha kawai”
Cikin kwanciya hankali ta fara kurban coffee dinta acikin zuciyar ta kuwa ita kanta bazata iya fadin irin farincikin datake ciki bah…
Ita dakanta ta dauka mai office bag nashi zuwa mota,
Allah yakiyaye hanya suka mishi sannan suka koma cikin gida…
30 minutes later...
Zaune suke dukkansu acikin palour suna kallon wani Indian film mai suna Sanam Teri kasam sosai suka nutsu cos film din sosai yake kayatar dasu kuma suna jin dadin shi dukda su emmatan wajen sai share kwalla sukeyi(????nima ko yaushe na kalli film sai nayi kuka????)
Daidai sun gama kallon wayan mumy yayi kara sanda tayi Jim tukunna kafin ta dauka soboda bakon number datagani
Sallama tayi sannan aka amsa daga dayan bangaren
“danAllah waye neh”tafada asanyaye cos haka kawai taji jikin ta yayi sanyi
“Kina magana da inspector Nasir neh”
Wani irin miyau mai daci ta hadiye tace” lafiya dai koh??”
“Erh akwai wani patients naki a teaching hospital”
Ajiyar zuciya tasauke tace to gani nan zuwa bata jira cewan shi bah ta katse Kiran…
Sosai inspector Nasir yasha mamakin ta amma sai ya basar…
“Miye faru mumy??”
“Ashe yau bamu leka Maimuna bah har an fara neman mu a asibiti so you guys should go and pick up ur khimars”
“OK ” suka fada in chorus sannan fice…
Teaching hospital Bauchi
Suna isa wayan mumy yadau kara
“Ku taho emergency in kun iso”
“Ohk” tafada sukayi hanyan emergency din
“Yana ga munyi tanan??” Nadhira ta tambaya
“Erh inaga condition dinta yayi worse neh” mumy ta bada amsa
Basu kara magana bah har suka isa
“Kune aka Kira??” Wani yafada
Mumy tace”Erh”
“Ohk ni neh wanda kuka yi magana dashi wato inspector Nasir”
“Ohk nagane ” Tafada tareda gaishe shi shima ya amsa
“Ku biyo ni” binshi sukayi kaman jela har suka iso casualty room…
Gurun gado ya nufa dasu inda suka cika da mamaki ganin Maimuna ba ciwo taji bah amma da sunyi la’akarin kwakwalwar ta yadan samu matsala sai hankalin su yadan kwanta …
Cakk suka ja suka tsaya dalilin hango wanda basu yi tsammanin gani bah akan gado…
Nadhira batayi la’akari da cewan hospital sukeyi bah ta kurma wata iriyan wawaiyan ihu ai basu hankara bah suka jita ak…
Vote,comment&share
Mhizzphydo