
Nabilah ta yi shiru cikin mamaki, yau Allah Ya nuna mata ranar da Mairo ta bude bakinta da kanta ta fada mata cewar tana son Uncle Junaidu.
Ina ma ace shi ma hakan ne a zuciyarshi? Duk duniya ba ta taba ganin mijin da ya dace da Mairo ba, irin Uncle, wanda yasan zahirinta da badininta, jinin jikinsu ke gauraye guri guda yana circulating. Amma ba zata taba yarda cewa wai Junaidu ba son Mairo yake ba.
Babu wanda zaka bai wa jinin jikinka sai wanda kake matukar so.
Ta dago a hankali ta dubi Mairo ido cikin ido, ta ce “Wallahi Mairo yadda kike son Uncle, shi ma haka yake sonki. Zan yi rantsuwa in dafa Alkur’ani akan hakan. Sai dai ban san dalilinshi na janye kafa a ranar da zaku rabu ba. Zan yi mishi uzuri da wani abu mai muhimmanci a gare shi, amma haka kawai Uncle ba zai ki yi miki sallama ba, sai ko sakamakon wani muhimmin abu da ya faru gare shi.
Rashin haduwarku ya zama rahma ke nan ga mutumcinki da martabarki a idanunsa…….”
Ta yi saurin duban Nabilah, tana mai daga gira ta ce, “Yes, gara da Allah bai baki ikon ki furta masa ba, wai ya aure ki koda ba ya sonki. Duk inda yake, Mairo ni na gaya miki ko ba dade ko bajima WATARANA zai neme ki, ki rike wannan a zuciyarki ki ce, ni na gaya miki”.
Ta mike ta fada bandaki tana cewa, “Bara na shirya mu tafi, ni har ma na warke da ganinki Mairo”.
Ta yi dariya, cikin samun nutsuwa a zuciyarta da kalaman Nabilah, ta ce “Dama ba wani ciwo ke damunki ba, sai shagwaba da gata, da suka taru suka lullube ki”.
7/30/21, 1:01 PM – Kawata: B
Sun isa Minjibir ana sallar azahar, zuwan da ya tuna musu da dabdalar kuruciyarsu. Shekaru shida cur, cikin dalibtaka da al’amura masu dama, da suka faru cikin rayuwarsu, suka tuno Kausar suka yi mata addu’a. Suka karasa Edam office suka amso sakamakonsu. Ba abin da suka fadi, sun cinye sun lashe 9 credits ris. Ina ma Uncle na nan, ya zo ya ga girbin abin da ya shuka?
Nabilah ta kasa daurewa ta tambayi Mr. Kayode malamin lissafinsu, ko ina Uncle Junaidu? Cike da alhini ya ke sanar da ita cewa, “Yau watanninsa uku kenan da tafiya karo karatu (in-serbice) zuwa kasar Russia (Ukhrain). Yana daga cikin malaman da federal ta dauki nauyin karo karatunsu a kasashen duniya talatin da biyar”.
Mairo ta samu wani kututturen bishiya ta zauna ta yi kukanta mai isarta, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a rayuwarta, ko a rashin iyayenta kuwa. Ta tabbatar wani bigiren nata ya kuma faduwa. Ta dubi takardunta, wahalar shekaru shidda da Uncle ya yi, yau ga shi Allah Ya cika mishi burinsa, amma ashe ba zai gani ba.
Kuka ta ke kukan sabo, soyayya da kewa. Ta tabbatar ta rabu da Junaidu ke nan har abada! Ya yi mata nisan da ba zata taba kamo shi ba. ALHERINSA da kyautayinsa masu yawa ne a gareta da ba zata taba mantawa ba. Soyayyarsa da kaunarsa wani abu ne da ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Shi kadai ta fara so, kuma shi kadai zata ci gaba da so har zuwa karshen rayuwarta, yana sonta ko ba ya sonta. Ta tabbatar ita ke son Uncle, amma shi ba hakan ba ne a zuciyarsa ba, ai yasan inda zai same ta, da yana sonta da ya neme ta.
Ciwon kana so ba a sonka, matukar ciwo ne da shi. Ya san ba ta da kowa a duniya a halin yanzu, daga Baffa sai shi, amma ya yi mata haka, ya ki tallafar rayuwarta a dai-dai lokacin da ta fi bukatar tallafinsa. Ta kullaci Uncle Junaidu kullata mai tsanani, irin kullatar da ta yi wa Habibu tare da alkawarta wa ranta yin kokari ta yakice shi daga zuciyarta, ta fuskanci rayuwa ta karbeta a duk yadda ta zo mata…..!!!
*** ***
B
ikin Nabilah bai yi armashi ba, sabida amaryar da angon duk sun ki ba da hadin kai, sai iyaye da ‘yan uwa ke ta sha’aninsu cikin farin ciki. Ko yaushe Mairo na tare da Nabilah, don ita kadai ce zata yi mata magana ta ji. Abinci ma sai Mairo ta lallashe ta sannan za ta ci, don wai fushi ta ke da Momi da Daddy. Ranar lahadi aka kai amarya gidanta da ke Nassarawa GRA. Tana kuka, Mairo na yi suka rabu, don wata irin kauna ce shakikiya Allah Ya hada a tsakaninsu.
Mairo ta dawo gida, ta kwanta a yagulalliyar katifarsu. Ta runtse idonta tana tunanin al’amuran rayuwa. Yau dai ga Nabilah ta yi aure ta barta, ita kuma ko sai yaushe ne Allah Zai kawo mata nata Mr. Right din? Tunda Uncle ba ya sonta? A zahiri aure ta ke so, ba kuma da kowa ba da UNCLE JUNAIDU. Karatun ya fice mata a rai, tunda babu Junaidu mai karfafawa. Tana daga cikin halittattun mata masu tsananin bukatar da namiji, amma ba da kowa ba, da wanda ruhi, zuciya da gangar jikin su ke so. Haka kawai tunanin unguwar GALADANCHI ta fado mata a rai. Idan har ba kuskure ta yi a tunaninta ba, Uncle ya taba gaya mata shi dan unguwar Galadanchi ne, da ke cikin birnin Kano. To idan ta je Galadanchi ta ce tana neman waye? Alhalin ma an ce Uncle Junaidu yana Russia? Zata je ta nemi gidan su Uncle, iyayenshi da ‘yan uwanshi musamman Ilham, wai an ce Gaida mai gaisheka…!’
Zumbur ta mike, ta jona ruwa a heater tana jiran ya yi dumi ta yi wanka, sabida sanyin da ake cikin watan Junairu.
Daga can gefe Ladidi ta tashi tana yatsina fuska, ba a jima ba kuma ta soma kelaya amai a tsakar dakin. Mairo na yi mata sannu amma ko kallonta ba ta yi ba. Ta gama aman ko kurkure baki babu ta koma ta kwanta. Mairo ta dauko tsintsiya da abin kwashe shara ta soma gyara wajen don tasan idan ta Ladidi ne, to a bar wajen a haka,. Ta dauko tsumma da omo klin ta goge dakin tas! Ta kunna turaren wuta na tsinke.
Idan ba ta manta ba wannan aman Ladidi na shidda ke nan cikin kwana uku, amma ko tunanin ta je asibiti ba ta yi. Ta matsa jikinta a hankali, abinki da dan uwa, ta ce, “Ladidi ki shirya na rakaki asibiti mana, ko magani ne a baki, wannan aman ya tsaya?”
Ta yi shiru ba ta ce uffan ba, kuma ba ta kalle ta ba, can kuma ko mai ta tuna? Ta ce “Mu je”.
A gurguje ta yi wankan ta fito, Ladidi ko wanka babu suka fito. Habiba na tsakar gida ta daga ido ta dube su. Wani irin kishi da bakin-ciki ya tushe mata a kahon zucci, ganin irin kyau da kwarjini na musamman a fuskar Mairo tamkar diyar larabawan Turkiya. Ladidi kuwa kamar a rufe ido don muni da rashin tsafta.
Ta ce “Ke Ladidi, ina zaki je da wannan mai kama da kabewar?”
Ta kyabe baki kamar yadda ya ke a al’adarta, ta ce “Asibiti wai zata kai ni”.
“Ciwon me kike da za a kai ki asibiti?”
Ta sake kyabe bakin ta ce “Wai don ina amai, ko ta gaji da kwashewa ne? Oho!”.
Ta gallowa Mairo harara ta ce “Kin ga ni bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai idan ya ci abin da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin zuciyar zai lafa”.
Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa tabbacin ya dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin abinci ga Hajara da autarta Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce “Yaya dai Mairo, babu wata matsala ince ko?”
Kanta a kasa ta ce “Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne”.
Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce “Ga shi ayi kudin mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje”.
Ta ce “Insha Allahu Baffa”.