
Dina tayi sallama ta shigo tana fadin “tashi, abincin da kike gudu ne na biyo ki da shi. In dai Amiru ya dade da barin gidannan. Ta tashi ta zauna sosai ta karbi farantin ta soma ci. Dina na kallonta, can kuma tace “Mairo me kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita a yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?”.
Ta cira kai daga cin abincin tamkar wadda aka katse wa gudun jini a cikin jikinta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta tace.
“Yana magana ne kan wai yana so na, so kuma na aure, yana burin na zama uwar iyalinsa. Nikuma na gaya masa kai tsaye cewa “bana son sa!”.
Dina tayi murmushi, daga jin kalaman Mairo da yanayin maganarta kasan kuruciya na dawainiya da ita. Cikin sanyin murya tace “sabida me ba kya son nashi Mairo? Gashi kyakkyawa son kowa kin wanda bai samu ba, gashi da dimbin ilmi kamar Yaya Habibun da kike cewa yana burge ki. Yanada matarshi baturiya zallah amma ya tsallakota yazo yace ke Mairo yana son ki. Zai iya rabuwa da ita saboda ya aureki. Gashi da kirki ga addini, ke kuwa Mairo me kike nema a da namiji da ya wuce wannan?”
Sai Mairo tasa kuka, ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, ta shiga kuka mai tsuma zuciya.
“Na kasa mance Uncle Junaidu ne Anty Dina! Na kasa mance dimbin alherin da yayimin a rayuwa. Shine tsanin duk wani matsayi da matakin dana ke kai a yau. Idan na auri wani ba shi ba na ci amanar sa…….!”
Dina ta katseta “akwai hanyoyi da yawa da zaka sakawa mutum Alherin da yayi maka ba dole sai ta hanyar aure ba. Misali shine ki dinga bin shi da kyakkyawar addu’a ba tareda shi din ya sani ba. Wannan addu’ar Ubangiji yayi alkawarin karbar ta Mairo. Kada ki yi mamaki zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wadda yake so ya aura ya manta da ke.
Ni na kasa gane kan wannan soyayya da kike yiwa Junaid maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana son ki ba! Kince ba kuyi alkawarin aure ba! Kince ya san gidan Baffa amma bai nemeki ba! To Mairo gaya min wace hujja gareki da zata tabbatar da cewa yana son ki?
Bakisan akwai masu taimako sabida Allah ba? Ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo, kiyi tunani mana, kiyi amfani da hankalinki, ki so mai son ki a zahiri da badini. Kiyi aure saboda Allah da raya sunnar Ma’aiki amma ba don abinda zuciyarki ta afu a kai ba.
Ina tabbatar miki Amiru in kin nutsu, kin bude zuciyarki a hankali zaki so shi wallahi har ma fiyeda son da kike ma Junaid. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yiwa Junaid, ko baki aure shi ba Allah ya shaida! Yayi alkawarin sanya masoyan gaskiya da suka mutu ba tareda sun auri juna ba a gidan aljannah. Ina tunanin Junaid yayi abin nan ne da hausawa ke cewa ABARI YA HUCE SHI KE KAWO DA RABON WANI!”
Ta dubi Dina da sauri har tsakiyar idanunta tace.
“Idan hakane Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana so na, furtawa ne baiyi ba kamar yadda Inna ta da Nabilah ke cewa???”
Gyada kai Dina ta yi. “EH, yana son ki, amma ya bari YA HUCE! Don kuwa a zahiri babu wata mu’amala ta mutunci da tausayi tsakanin mace da namiji sai ‘SOYAYYAH’. In ma mutuncin ne da farko, to daga baya rikidewa yake ya koma soyayya. …
Ke dinnan Mairo har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yimawa ba soyayya ba. Amirun shi kike so da gaske; na gani a kwayar idon ki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aureki ne don ya tallafi rayuwarki a wancan lokacin da kike neman matallafi ido rufe, amma ba don kinsan hakikanin me aure ya kunsa ba.
Mairo kinaso ki ramawa Junaid halaccin da yayi miki ne ta hanyar ‘aure’ don da shi kika saba, ya sanki, kin san shi, a tunanin ki wannan shine karshen soyayya, to ba shi bane! Soyayyar aure daban take, Allah ke hada ta, kuma bata fassaruwa.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shine tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba! Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne to sai muyi shirin tafiya Kano, unguwar Galadanchi gidansu Uncle Junaidu, mu nemeshi mu kai kudin aure… mu gaya masa yadda kike son shi, har kina duban tsakiyar idanun masu son ki da aure na hakika kina gaya musu ba kya son su. ……sabida kawai kada ki ci amanar soyayyar shi da ya baki a makaranta. ……” .
Ala dole ta murmusa, ta san zambo ne Dina take mata. Duka wannan bata lokacin da yawan bakin da Dina ta share tana bayani, ba duka abinda tace ne Mairo ta yarda dasu ba.
Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga AMEERU! Sabida shi ta sani, shine mai irin tsarin rayuwar su. Bata san komsi game da rayuwarta ta baya ba, batasan wanene Uncle Junaid a rayuwarta ba. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro yake bata balle na Amirun da ta ji suna cewa yana World Bank karewar Barclays . A karkashin inuwarsa rayuwar Habibu ta ginu bakidayanta. Shi ya maida Yaya Habibu ko me yake a yanzu.
Ta yarda ta hakura da Uncle Junaidu sabida hujjoji kwarara da kowa yake gaya mata. Hatta Nabilah tace da ita “lokaci yayi da zata manta da Uncle Junaidu tayi aure”. Ta dubi irin auren da ita tayi, amma daga baya ya zame mata ALHERI. Don yanzu ba abinda take so a duniya sama da Ismael kuma shima hakan har ga albarkar haihuwa.
Ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta bayan fitar Dina. Ta ja bargo har kanta ta kudunduna. Bacci take so ta yi amma ya ki zuwa. Al’amuran na neman tarwatsa mata kwakwalwa tareda wargaza mata tunani bakidaya. Tana so ta yarda da Dina, halaccin dake zuciyarta na karyata Dina. Amma abubuwan da ta zano ai duk haka suke; zata je neman auren Uncle Junaidu ne??? Ko kuwa haka zata kare a zaman jiran tsammanin warabbuka ???
Zata iya cigaba da zaman jiran ranar da uncle Junaid zai nemeta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya bata uzurin da ya hana shi yin hakan a lokacin da ya dace daga nan har gaban abada! Amma bazata iya jure bukatar gangar jiki da zuciyarta ba irin na kowanne lafiyayyen dan Adam. In hakane aure ya zama dole a gareta domin kare kanta daga zina , da sauran ayyukan alfasha, cikar mutunci a idon duniya da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.
Wayarta dake karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text ). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a daidai wannan lokacin karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna. Bata san lambar ba don kuwa bakuwa ce, ga abinda ke rubuce;
“………. When life changes, and we go our separate ways, you will still be in my heart till my dying days…… my world has never meet a person like you!”
(A yayin da rayuwa ta canza ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu) zaki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba).
Haka ta sa sakon a gaba tana ta karantawa har akayi kiran Assalatu. Don ta tabbata ba kowa bane; Amiru ne. Duk da bai saka suna ba ko wata alama mai nuna shi din ne. Allah sarki! Har YA HUCE ne? Tana so ta bashi amsa bata san me zata ce masa ba.
Da safe take nunawa Dina a kitchen, ta karanta tayi dan miskilin murmushin nan nata. Tace “ke kuma kika ce me?”
Ta zumburi baki “ni ko kula sa ma na yi?”
Dina tayi dariya tana kwaikwayon muryar ta tace “Haba Mairo! Yi hakuri ki dan kula sa. Kin ga shi yayi fushin amma ya sauko, sabida ya fahimci Mairo ba sonsa bane bata yi, kawai ita din mai amana da rikon alkawari ce”.
Tayi murmushi har kumatunta ya lotsa. Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami. Tace.
“To me zan rubuta???”
“Ki ce kawai yazo yayi joining dinmu breakfast “.
Mairo ta rubuta ta tura. Amsar da ya bata ta sa ta yin murmushi, domin ya ambato rabin ranta.
“A’ah kirawo JUNAID……”
” He’s far away….!_ ” (Amsar Mairo).