
Mairo wajen Hajiyar su Dina ta koma tana goga goro a magoginsu na tsoffi, da gani ka ga ‘yar gatan tsohuwa da da ya hucewa takaicin duniya. Ga wasu mulmulallun awarwarayen zinari a hannunta guda uku, sai walwali suke, tufafin jikinta kadai, sun ishi karamin talaka jari. Ta zauna gefenta ta ce “Hajiya kawo goron in goga miki”.
Ta mika mata dankwalelen goron fari sol da magogin ta soma gogawa, in ya taru ta mika mata ta hambuda a baki. Tana bai wa Mairo labarin Dina.
Ta ce “Kin ganta nan, duk cikin jikoki na ashirin da biyar na fi sonta. Sabida halayenta na kwarai da rashin daukar rayuwa da fadi. Babanta shine da na biyar cikin ‘ya’ya biyar da na haifa suna mutuwa, shi kadai ya tsaya. Kuma daga shi Allah bai kara ba ni da namiji ba, sai kannensa mata guda biyar.
Ita ce ‘yarsa ta fari, sai tarin kanne guda bakwai. Ta kawo Yayanki dalibi da ba shi da komai ta ce ita shi ta ke so ta aura. Da fari ba mu yarda ba, tunda ba mu ga iyayenshi ba, shi kuma ya ce, ba zai koma gida a wancan lokacin ba.
Ya fito neman ilmi da arziki ne sai Allah Ya yi mishi zai koma, don haka muka saduda muka yi musu aure. Da ya ke abokiyar arzikinshi ce ga shi Allah Ya azurta su, da ‘ya’ya da dukiya. Allah Sarki, ashe iyayen da ya nema don su huta, kamar yadda nake hutawa a tsufana, Allah bai yi za su mori arzikinsa ba.
Ki saki jikinki, ki kwantar da hankalinki da Dina, zata zame miki uwa, abokiya, kuma Yayar kwarai, kin ji Maryamu?”
Ta girgiza kai, ta ce “Na ji Hajiya, Yaya Habibu ma ya gaya mini”.
Dina da Habibu suka shigo, sun jero, tsawonsu daya, takunsu iri daya, sai annuri ke fita daga fuskokinsu, ga dukkan alamu an ci soyayya an koshi. Ta dubi Hajiya da Mairo da ta takarkare sai nika goro ta ke yi, ta yi dariya ta ce “kawa da kawa, hirar me ake yi?”
Hajiya ta ce “Ina ruwanki da hirarmu? Ko mu mun tambaye ki hirar me kika je taya mijinki?”
Habibu ya nitse cikin leather yana amsa waya da thuraya dinsa, cikin wani dan bantan uban Turanci kamar Karl Mad sabida yadda Turancinshi ke fita tar-tar irin wanda Mairo ba ta taba ji ba. A da, tana tsammanin a duniya babu wanda ya iya Turanci irin Uncle Junaidu, ashe Junaid rarrafe yake yi, ga wadanda suka mike suke dabo, suka tsaya da kafafunsu.
Kwanansu uku a Dutsinma suka tattaro suka yo Kano, Mairo dai kamar ba zata tafi ba sabida jin dadin zama da Hajiya, har hawaye ta ke da suka fito za su tafi, Habibu da Dina na mata dariya.
Hajiya ta cika mata Bacco fal da atamfofin edclusibes irin wadanda ‘ya’yanta ke kawo mata, don ta dinka, amma ta tattara ta bai wa Mairo. Wannan a jinin Mairon yake, FARIN JINI da shiga zucci. Idan ka zauna da ita yini guda, zaka so ka kwana da ita. Idan ka kwana da ita, zaka so kayi wata tare da ita, idan ka yi wata tare da ita zaka so ka yi zaman shekara da ita, haka idan ka yi shekara da ita, zaka so ka zauna da ita har zuwa karshen rayuwarka.
Karfe uku dai-dai na rana suna cikin Kano, Habibu ya karya kan mota suka shigo Yakasai. Tun daga nesa wani dankareren European Billa (Bungalour) ya dauki hankalinta, ya karkada mata ‘ya’yan hanji. Abin mamaki a get din gidan Habibu ya sanya hancin motarsa kirar Porsche. Zuciyarta na gaya mata, wai wannan gidan Baffa ne? Amma wani sashen na karyatawa. To idan ba shi ba ne, wanne ne? A nan dai gidan Baffa ya ke, ga makotansu nan ba su motsa daga inda suke ba, su ma sun samu arzikin sabon fenti irin na gidan. Dama dai gidan Baffan babba ne, ga kuma bene an daura, ko ina gilashi da tile ke zagin idonka.
An fidda sashen baki daga gaban gidan, a cikin gidan kuma sashe biyu ne na matan gidan, sashe guda na yara, Baffan yana sama, sai dakin ‘yammata. Kowanne daki an kafe plasma a sama tana ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam, ga dindima-dindiman kujeru masu nishi ‘yan Italy da labulaye masu garai-garai da gani tafiyayyu ne tun daga China. Abin dai ba a cewa komai sai a gaida Habibu, a gaida ma’aikatan Julius Berger. A gaida Habibu da aikin ZUMUNCI, da rama hairan da hairan.
Suna tsayuwa su Rahma suka diba yuuu! Suka yi cikin gida suna ta ihu, “turawan sun dawo da Mairo, ba su sace ta ba. Baba ga Mairon nan sun dawo da ita”.
Baffa dai baki ya ki rufo, ya fito ya taro su, Abbas ya gane shi, ya je ya kama hannunsa, Hajara da Habiba kowacce ta fito daga bangarenta bakin nan kamar gonar auduga, har rige-rigen daukar Mairo karama su ke. Mairo fa ta fara jin tsoron al’amarin Habibu. Allah dai Ya sa ba kungiyoyin nan na matsafa da sassan jikin mutum ya shiga ba. Allah Sarki! Da tasan Barclays da ba ta ce haka ba.
Hankalinta na kan ‘yar uwarta Ladidi da halin da ta tafi ta barta a ciki. Don haka suna shigowa ta tambayi Habiba “Ina Ladidi?”
Habiba wadda ke jin kamar ta suri Mairo ta goya don ta samu fada wajen Baffa wanda ya daure musu fuska tam ya ki kula su don yasan duk borin kunya suke yi. Ta nuna mata dakin da Ladidi ta ke, ta ce “Halan Mairo a inji matar Habibu ta sakaki ta wanke?”
Mairo ta yi murmushi ta ce “A’ah, a lagireto ne”.
Ta wuce ta barta nan, tana ta sosa keya don kunya.
A dakin ta cimma Ladidi, an yi dai-dai cikin Italian bed, ana shan lemon Safari ana kallon tashar Zee-Aflam, ba tasan sanda dariya ta kubuce mata ba, don kwata-kwata ba ta yi matching da gadon ba da dakin gaba daya, ta fi dacewa da mai aikin dakin ba mamallakiyarshi ba.
Tana ganin Mairo ji kake kat, ta kware. Ta dinga tari ba kakkautawa. Mairo ta zauna a bakin gadon tana yi mata sannu. Ta mutsittsike ido ta ce “Mairo ke ce kuwa?”
Ta ce “A’ah, ba ni ba ce, Ladidi ce”.
Ladidi ta soma kuka ta ce “Don Allah Mairo ki yafe mini. Ga shi dai tun a gidan duniya mun ga ishara, dan uwa duk lalacewarshi ba abun wasa ba ne, sai dai nasan kome zan fada miki a yanzu ba zaki yarda ba, za ki ce don na ga Habibu ne, ko don abin da ya yi mana, amma wallahi ba haka ba ne. Yadda kuma kika rufa min asiri a duniya, Allah Ya rufa naki duniya da lahira”. Ta sa habar zaninta ta share ido.
Mairo ta ce “Duk ba wannan ba Ladidi. Ki tuba ga Allah, ki sani cewa, Yana kallonki, idan su Baffa ba sa kallonki. Yau idan Baffa ya samu labarin kin cire ciki har sau biyu a wane yanayi kike tunanin zai tsinci kansa? Idan ba kya tsoron Allah, ai kya ji wa kanki tsoron cututtukan zamanin nan da ba su da magani. Idan aure kike so ki fidda daya daga cikin manemanki ki aura mana?”
Ladidi ta ce “Na tuba, na bi Allah na bi ki. Wallahi daga yau bazan sake ba…”
“……Ki ma sake din mana don ubanki”.
Suka juya a razane, Habiba ce tsaye a kansu, ashe ta dade da shigowa ba su ankara da ita ba. Ta kwance dankwalinta ta yi damara, ta yo kan ladidi ta hau ruwan cikinta ta soma kirba mata naushi tana ihu tana “Na tuba Mama, wallahi bazan sake ba”.
Wannan bai ishi Habiba ba, sauka ta yi ta nufi kicin ta dauko tabarya ta yo kanta tana fadin, “Gara na kashe ki kafin kanjamau ta kashe ki, kibar mana abin fadi cikin zuri’armu”.
Ganin ta yo kanta da tabaryar Ladidi ta yo waje da gudu don tserar da rayuwarta, wannan ya janyo hankalin kafatanin jama’ar gidan yara da manya, suka fito tsakar gida har Dina da Habibu da Baffa. Ganin Ladidin zata yi waje da rigar bacci, kafarta ko takalmi babu, kanta ko dankwali, Habibu ma ya rufa da gudu ya kamota tana ta kuka, tana “Na tuba wallahi ba zan sake ba……..”
Habiba ta fito tana sharar hawaye, ta ce, “Ni fa ince, wannan aman da wannan kwanciyar nakin na Ladidi, ba na lafiya ba ne, na zama shashashar Uwa, yanzu Mairo da kunnawana ba su jiye min ba, haka zaki biye mata ku binne mu?”
Mairo na kukan tausayin Ladidi ba ta ce komai ba.
Baffa ya ce “Mai Ladidin ta yi ne?” Ya tambaya yana kallon Mairo.
Ta yi tsuru-tsuru ba ta yi magana ba. Ya sake tambayarta, ta ki magana. Habiba cikin kuka ta ce “Ciki suka je aka cire mata, wai wannan shi ne na biyu, na ji su tana yi wa Mairon godiyar ta rufa mata asiri”.
Baffa ya ce “Mairon? Da ita aka je aka cire cikin?”
Mairo ta girgiza kai cikin kuka ta ce “Wallahi ba ni na rakata ba, ita kadai ta je abunta. Ni asibiti na kaita ta ga likita”.
Dariya ta kama Habibu, wai asibiti ta kaita, sai ka ce wata uwarta? Habibu ya ce “Ke ma sai mu je a duba ki, don abokin barawo ai barowo ne”.
Ya hankada Ladidi da ke hannunsa ya tankado keyar Mairon, ya ce, “Oya! Lets go, har gwajin kanjamau duk za a yi muku tunda kun zama karuwai”.
Mairo ta soma rantsuwar, wallahi babu ruwanta, ba ta da saurayi, ba ta taba yin zance da namiji ba. Babu wanda ba ta baiwa dariya a wajen ba. Baffa ya kamo hannunta ya ce
“Share hawayenki Mairo. Babu inda za ki, kanwarshi ce karuwa ba ke ba”.
8/1/21, 9:30 PM – Kawata: Mairo
Little Mairo tana ta murnar ganin mamarta da ta kwana biyu ba ta gani ba. Shi kanshi Yaya Habibun idan ka lura zaka ga annurin fuskarshi ya karu sosai. Oh! Ashe haka auren so yake? Mairo ta ce a zuciyarta. Kai ka ce sun shekara ba su ga juna ba.
A otel din da Amiru ya sauka (Best Western) suka ajiye shi, da alkawarin sai ya shigo da daddare yin dinner. Kuma Mairo yake so ta yi mishi girki. Dina ta yi murmushi ta ce “Ban fa gane ba, kada ka sa Harrit ta bindige min kanwa”.
Ya yi murmushi ya ce, “Allah babu wasa cikin maganata Aunty Dina, don ni yanzu kin zama Auntyna, alfarma nake nema ku yi min ke da mijinki, kokon bara na yana gidanku, duk da mijinki is not hundred percently agreed (bai yarda gabadaya ba) sabida wasu hujjojinshi marasa makama. Nasan ke za ki dube ni da idon rahma. Zan ba ku mamaki, zan nemi soyayyar Mairo ba campaign nake so ku yi min ba”.