
BURGEWA da SHA’AWA ba tubala ne na kwarai da za a gina aure a kansu ba. Idan aka yi hakan, ba da jimawa ba ginin zai rushe tamkar ba a taba ginawa ba.
Don haka gara ta hakura da rudin zuciya don shaidaniya ce, ta fuskanci gaskiya. Ta yi aure don Allah, ba don kyale-kyalen Amiru da rayuwa bakidaya ba. Ta ci gaba da jiran Uncle ya gaya mata da bakinsa cewa ba sonta yake ba, sannan ne zata hakura, ta yi addu’ar Allah Ya kawo mata mijin da zata so da gaskiya, ta kaunata saboda Allah, kamar yadda ta ke yi wa Junaidu.
Ta daga kai a hankali ta dubi Amiru, wanda har zuwa wannan lokacin bai dauke kyawawan idanunshi daga kanta ba, binta yake da ido, da zuciya. Idan Mairo ta ce ba ta sonshi, bai san inda zai sa kanshi ba.
Ta ce (cikin kaskantacciyar murya) “Don Allah ka ba ni hanya in wuce”.
Ya ce “Ai ba ki ba ni amsa ba, ko na yi miki tsufa ne Mairo?”
“Ni ban ce ba”.
“To mai kika ce?”
“Cewa na yi ni ba sonka nake yi ba!”.
Wannan ita ce kalma mafi muni da wani ya taba gaya mishi a rayuwarshi. Ji ya yi kamar ta soka mishi mashi a kahon zucci. Hajijiya ta kamashi. Ta wani fannin kuma sai ta BURGE shi, sabida kai tsaye ta gaya mishi kalmar da babu wata diya mace da ta taba gaya mishi. Wannan ya tabbatar mishi da cewa, ita ta daban ce.
Sai dai yadda ta yi maganar da yanayinta kadai zai nuna maka tsabar kuruciyarta karara. Don haka bai yi fushi ba, ance wai, ‘Mai nema yana tare da samu’. Ya lumshe ido ya bude su dukka a kanta “Amma mai yasa Mairo?
Komi yana da dalili, kamar ni, na so ki ne sabida wasu abubuwa guda uku, wadanda bazan iya gaya miki ba. To ke mene ne naki dalilin?”
Ta so ta ce da shi “Sabida ina da wanda nake so”. Sai ta tuno alkawarin da ta daukarwa Yaya Habibu, na barin soyayyar Junaid da mantawa da al’amarinshi. Don haka sai ta ce.
“Sabida wasu dalilan nima, da bazan iya gaya maka ba!!”.
Sun dauki mintina uku shiru, babu wanda ya sake cewa da dan uwansa uffan. Kamin ya dauke ido daga kanta, ya ce.
“Ni kuma na yarda ki aure ni ko da ba kya sona…!!!”.
Ta ce “Ba zan yi hakan ba, idan na yi hakan na yaudare ka, na ci amanar kaunar da nake yi wa Uncle Junaidu……….!!!”
Ta yi saurin kai hannu ta toshe bakinta da karfi, ba ta san yaushe furucin ya subuto daga zuciyarta ba, ga shi an ce ‘magana zarar bunu’ ta riga ta fita.
Sai ya kauce da zafin nama ya ba ta hanya sabida wani masifaffen KISHI da ya taho ya tokare masa a kirji. Ai tana samun hanya ta arce. Da kyar ya iya dago matattun kafafunsa bayan mintina goma sha biyar, ya nufo falon inda ya tarar da Raymond da Habibu akan tebur suna cin abinci, Dina na tsakiyar falon tana canza channel a talabijin. Abincin da bai ci ba ke nan, ya zauna cikin doguwar kujera fuskarshi babu walwala, ya ce.
“Raymond idan ka gama sai mu wuce”.
Habibu ya juyo ya dube shi yana nazarinsa, ya ce “Ba zaka ci abincin ba? Mairo ce ta girka maka………..”
Ya dago idanuwanshi da suka canza launi luuuu! Yana kallon Habibu a kankance, ya ce “Ba zan iya ba!!”.
Dina ta ce “Haba don Allah Amiru? Ba ka ga wahalar da ta sha wajen girkin nan ba? Idan ba ka ci ba bazata ji dadi ba”.
Bai san lokacin da ya ce “Ba don ni ta girka ba, don Yayanta ne”.
Daga haka ya mike ba tare da ya iya hada ido da kowa ba. Ya sake ce da Raymond, “If you finish, meet me outside….”.
Shima Habibu sai ya ajiye cokalin don jikinshi ya yi sanyi, don bai taba ganin Amirun cikin kwatankwacin irin wannan halin ba.
Don haka ya mike ya bi shi wajen ya dafa kafadunshi da ya juya baya. Ya ce.
“Mai ya faru ne?”
Ya kalle shi kawai bai amsa ba, tambayar duniyar nan Habibu ya yi, amma ya ce “Babu komai”. Don ba burinshi ba ne a takurawa Mairo ta aure shi. So na hakika ya ke nema, ba da tallafin wani ba.
Mairo da ta koma daki kwanciya ta yi, rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon mutum mai kima kamar Amiru da ya ce yana sonka, ka ce ba ka son shi, ya zama wulakanci da cin fuska. To amma ita a ganinta dai-dai ta yi, don ba ta iya karya da yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san ba ta kyauta ba, sai dai a ganinta gara hakan, da ta yi irin auren da zuciyarta ta raya mata.
Dina ta yi sallama ta shigo, dauke da faranti tana cewa “Kin yi barci ne?”
Ta girgiza mata kai, alamar “A’ah”.
Ta ce “To tashi, abincin da kike gudu ne na biyoki da shi”.
Ta tashi ta zauna sosai, ta karbi farantin ta soma ci, Dinan na kallonta. Can kuma ta ce “Mairo mai kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita cikin yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?”
Ta cira kai ta dube ta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta, ta ce “Yana magana ne akan wai yana sona, ni kuma na gaya mishi cewa, bana son shi!”
Dina ta yi murmushi. Daga jin kalaman Mairo, da yanayin maganarta kasan kuruciya ke dawainiya da ita. Ta ce “Sabida mai ba kya sonshi Mairo?
Ga shi kyakkyawa, son kowa, kin wanda ya rasa. Ga shi da ilimi kamar Yaya Habibun da kike cewa yana burge ki. Yana da mata Baturiya, amma ya tsallakota ya zo ya ce yana sonki. Zai iya rabuwa da ita sabida ya aure ki. Ga shi da kirki, ga addini. Ke kuwa mai kike nema a da namiji da ya wuce wannan?”
Sai Mairo ta sa kuka. Ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, tana kuka mai tsuma zuciya.
“Na kasa mance Uncle Junaidu ne Aunty Dina. Na kasa mance dumbin alherin da ya yi min a rayuwa. Shi ne tsanin duk wani matsayi da matakin da nake kai a yau. Idan na auri wani ba shi ba, na ci amanarsa…….”
Dina ta katse ta “Akwai hanyoyi da yawa da zaka saka wa mutum alherin da ya yi maka ba dole sai ta hanyar aure ba. Misali shi ne, ka dinga binshi da kyakkyawar addu’a ba tare da shi din ya sani ba. Wannan addu’ar Allah Ya yi alkawarin karbarta. Kada ki yi mamakin zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wata da yake so ya aura.
Ni na kasa gane kan wannan soyayyar da kike yi wa Junaid, maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana sonki ba. Kin ce ba ku yi alkawarin aure ba, kin ce yasan gidan Baffa, amma bai neme ki ba. To ki gaya min wacce hujja gare ki da zata tabbatar da cewa yana sonki?
Ba ki san akwai masu taimako sabida Allah ba, ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo, ki yi tunani mana? Ki yi aiki da hankalinki. Ki so mai sonki a zahiri da badini. Ki yi aure saboda Allah da raya sunnar ma’aiki, amma ba don abin da zuciyarki ta afu akai ba.
Mai yiwuwa ne shi wannan abun da kika kwallafawa ran ba alheri ba ne a gare ki, wanda ba kya so din shi ne alherin. Idan kika fauwalawa Allah a hankali za ki so abun, tunda shi ma Junaid ba lokaci daya kika fara sonshi ba, so na soyayya, kin ce sai da tafiya ta yi tafiya kika mallaki hankalin kanki, sabida fahimtar halayenshi da kika yi.
Shi ma Amiru a hankali za ki fahimce shi, kuma ki so shi wallahi fiye da son da kike wa Junaid ma. Ba ki ci amanar Junaid ba, ba ki yaudare shi ba tunda ba alkawari kuka yi ba. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yi wa Junaidu, ko ba ki aure shi ba Allah Ya shaida ya yi alkawarin sanya masoyan gaskiyan da suka mutu ba tare da sun auri juna ba a aljanna. Ina tunanin Junaid ya yi abin nan ne da Hausawa ke cewa, “A BARI YA HUCE… SHI KE KAWO DA RABON WANI”.
Ta dubi Dina sosai, ta ce “Idan haka ne Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana sona? Furtawa ce bai yi ba, kamar yadda Inna da Nabilah ke cewa?”
Gyada kai Dina ta yi, ta ce “Eh, yana sonki, amma ya bari YA HUCE… Don babu wata mu’amala ta mutumci da tausayi tsakanin mace da namiji sai SOYAYYAH!
Idan ma mutumcin ne da farko, to daga baya rikidewa ya ke ya koma soyayya. Kuma dama ita irin wannan dadaddiyar soyayyar ba a fiya auren juna ba. Wasu ma har su mutu, ba sa kara ganin juna.
Wasu kuma daya ne yake mutuwa ya bar dayan cikin soyayyar, kuma babu yadda dayan zai yi, a karshe dole zai hakura ya auri wani, wasu kuma hakura suke da auren har zuwa sanda nasu ajalin zai riske su.
Amma Ubangiji ba ya son hakan, don haka bana son ki zamo daga cikin wadanda za su kyamaci sunnar Ma’aiki sabida soyayya. Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi “Ku yi aure don ku hayayyafa… Bai ce ku yi aure don soyayya ba. Karewama, duka matan ma’aiki da dalilin da ya yi sanadin da ya aure su, ba soyayya ba.
Soyayyarsu tana kafuwa ne a hankali cikin gidan aurensu. Ki yi koyi da Nana Khadijah wadda halayen amana na Ma’aiki ya kwadaitar da ita ga son aurensa, shi ma kuma ya aure ta don dukiyarta, addininta da nasabarta. Ki auri Amiru don yana da nasaba, addini, ilmi da arzikin ma, ku raya sunnah ku haifi ‘ya’ya ku yi musu tarbiyyar musulunci in gaya miki karshen soyayya ke nan.
Ke nan har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yi mawa ba SOYAYYA ba. Amirun shi kike so da gaske, na gani a kwayar idonki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aure ki ne don ya tallafi rayuwarki a lokacin da kike neman matallafi, amma ba don kin san hakikanin me aure ya kunsa ba.
Kina so ki ramawa Junaid halaccin da ya yi miki ne ta hanyar ‘aure’ don da shi kika saba, ya sanki, kin sanshi, a tunaninki wannan shi ne karshen soyayya, to ba shi ba ne, soyayyar aure daban ta ke, Allah ke hadata, kuma bata fassaruwa.
Haka ita ma kauna daban ta ke, sai kin auri Junaidun za ki ji kamar kin auri Babanki. A sa ma shi din ya ce yana son naki, balle bai ce ba. Tsayin shekara biyun nan wallahi da duk inda kike ya neme ki, da fa ya damu da ke.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shi ne tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba. Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne, to sai mu je gidansu mu neme shi mu kai kudin aure, mu gaya mishi yadda kike sonshi har kina gayawa masu sonki da auren, ke ba kya sonsu, sabida kar ki ci amanar soyayyar sa da ya ba ki……”
8/2/21, 10:31 PM – Kawata: G
Ala dole ta murmusa, don tasan zambo ne take mata. Duka wannan bata lokacin da Dina ta yi tana bayani, ba duka abin da ta ce ne ta yarda da su ba.
Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga Amiru, sabida shi ta sani, shi ne mai irin tsarinm rayuwarsu. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro ya ke bata, balle na Amirun da ta sha jin suna cewa yana world bank, karewar Barclays.
Ta yarda ta hakura da Junaid sabida kwararan hujjoji masu karfi da kowa yake gaya mata, hatta Nabilah. Ta ce da ita lokaci ya yi da ya kamata ta manta da soyayyar da ta ke wa Uncle Junaid ta yi aure. Ta dubi irin auren da ita ta yi, amma ga shi ya zame mata ALHERI, don yanzu ba abin da ta ke so a duniya sama da mijinta, kuma shi ma hakan har ga albarkar haihuwa.
Ta sauke ajiyar zuciya, ta koma ta kwanta a gadonta, ta ja bargo har kanta. Barci ta ke so ya zo ya dauke ta, amma ya ki zuwa. Al’amarin na neman tarwatsa mata kwakwalwa, tareda wargaza mata tunani. Tana son ta yarda da Dina, halaccin da ke zuciyarta na karyatawa. Amma abubuwan da ta zana ai duk haka suke, zata je neman auren Uncle Junaid ne? Ko haka zata kare da zaman jiran tsammanin warabbuka?
Zata iya ci gaba da zaman jiran ranar da Junaid zai neme ta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya ba ta uzurin da ya hana shi yin hakan har nan gaba da abada. Amma ba zata iya jure bukatar gangar jikinta da zuciyarta ba, kamar kowanne lafiyayyen dan Adam. Idan haka ne tana bukatar aure, domin kare kanta daga ZINA, da sauran ayyukan ALFASHA, cikar mutunci a idon duniya, da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.