
Wayarta da ke karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a dai-dai wannan lokacin, karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can. Ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna, ba tasan lambar ba, don bakuwa ce. Ga abin da ke rubuce.
‘… When life change, and we go our separate ways, U will still be in my heart till my dying days… My world has never meet a person like U………!
(A yayin da rayuwa ta canza , ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu), za ki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba).
Haka ta sa sakon a gaba, tana ta karantawa. Har aka yi kiran assalatu. Don ta tabbatar ba kowa ba ne, Amiru ne, duk da bai sa suna ba. Allah sarki ko YA HUCE ne? Ta fada a fili. Tana so ta ba shi amsa, ba ta san me zata ce masa ba.
Da safe ta ke nunawa Dina, ta karanta, ta yi dan miskilin murmushinnan nata, ta ce.
“Ke kuma kika ce mene?”
Ta zumburi baki. “Ni ko kulasa ma na yi?”
Ta yi dariya, ta na kwaikwayon ‘yar muryar ta tace, “Haba Mairo? Yi hakuri ki dan kula sa. Kinga shi ya yi fushin amma ya sauko, saboda ya gane ba son sa ne ba kya yi ba, kawai ke mai aminta amana da alkawari ce!”.
Ta yi dariya har kumatun ya lotsa, Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami.. Ta ce “To me zan rubuta?”
“Ki ce kawai ya zo yayi joining dinmu break fast…..”.
Ta rubuta ta tura, amsar da ya ba ta ta sata yin murmushi. Domin ya ambato rabin-ranta (uncle Junaidu).
“…A’ah kirawo Junaid….”.
“He is far-away…!!”(Amsar Mairo )
“And am not closer too… am far-away either, and I’ll not come back…!!! On my way to Detroit Metro……”.
Hankalin Mairo yayi mummunan tashi, da sauri ta jefar da wayar, da gudu ta yi daki ta dauko mukullinta, Dina na kira amma ba ta juyo ba, cikin rishin kuka ta ce.
“Shi ma zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Bana son in samu wannan heart break (karyewar zuciyar) a karo na biyu”.
Dina ta ce “Bishi Mairo, shi ne ZABIN ALLAH!!”
Gudu ta ke shararawa akan titin da zai kai ta airport din Detroit. Cikin kankanuwar motarta GMC Terrain. Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke, Wannan ita ce soyayyah! Da gaske Dina ta ke, Amiru shine zabin Allah!! Da gaske Dina ta ke da ta ce ta kama mai sonta, ta rabu da JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA. Ta karbi ‘Soyayyah’ a hankali zata rikide ta zama ‘Kauna’. To gashi soyayyar ma zata tafi ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata fata…….…
Koda ta iso airport din ko kulle motar ba ta yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta sheka cikin reception tana dube-dube, babu Amiru, babu ko mai kama da AMIRU. Ta karasa terminal bayan ta hankade ma’aikacin da ke kokarin hanata shiga. Dai-dai sanda aka rufe kofar jirgin (Lufthansa), wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dumbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi. Kafin ya dai-daita sosai, a sararin samaniya.
Mairo ta durkushe a nan tana kuka, kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin da ta samu cikin Michigan wanda Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne don ya rusa komai . Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa unbearable kamar Uncle Junaidun? Meyasa ita ba ta da sa’a ko kankani a soyayya ???.
Ji ta yi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma, an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. Don haka ta dago idanunta jage-jage da hawaye… don ganin ko wane ne wannan???
Masha Allahu La Kuwwata Illa Billah!
Mu biyo Mairo da Amiru da Junaidunta a littafi na uku. Kafin nan ina sauraron ra’ayoyinku kan jaruman namu, AMIRUN ko JUNAIDUN???
Maman SAFAH da MARWA ce.
07030137870
8/3/21, 12:25 PM – Kawata: 444
Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne!
Cikin matsanancin mamaki ya ce, “Mairo?”
Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa
“Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?”
Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta.
A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce
“Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa kika zo? Ina zaki je?”
Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata, ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta yi fakin.
Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security ne cikin fararen kayan ma’ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata.
Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar.
Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka’ida da dokar duk da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har suna son motar su, don a ka’ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba, ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba.
Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo
“Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko?
Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin ‘yan sanda ba, don haka sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki je ku karata…….”
Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce
“Wallahi bazan je ofishin ‘yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba”.
Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun.
Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara.
“Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya.
Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini, na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba, kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?”
Cikin kuka ta ce
“Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba”.
Ya ce “To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?”