
"And I'm not closer too.... I'm far away either, and I will not come back. On my way to Detroit-Metro".
Hankalinta yayi mummunan tashi. Saboda ita ne Amiru zai bar kasar da haihuwarsa ne kawai ba’ayi cikinta ba? Da sauri ta jefar da wayar. Da gudu tayi daki ta dauko mukullinta. Dina na kira amma bata juyo ba take fadin.
"Shima zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Banaso in samu wannan _heartbreak_ (karyewar zuciyar) a karo na biyu".
Dina tace.
"Bi shi Mairo. Shine ZABIN ALLAH!!!"
Gudu take shararawa a kan titin da zai kaita airport din Detroit. Cikin kankanuwar motarta GMC Terrain. Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke; wannan itace SOYAYYAH! Da gaske Dina ta ke Amiru shine ZABIN ALLAH! Da gaske Dina ta ke da tace ta kama mai sonta, ta rabu da JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA! Ta karbi soyayyah a hankali zata rikide ta zama kauna . To ga shi soyayyar ma zata gudu ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata fata. …………………….!!!
Koda Ta iso airport din ko kulle motar bata yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta shige cikin reception tana dube dube. Babu Amiru babu ko mai kama da AMIRU ! Ta karasa terminal bayan ta hankade ma’aikacin dake kokarin hanata shiga. Daidai sanda anka rufe kofar jirgin ( Lufthansa ) wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi, kafin ya daidaita sosai a sararin samaniya.
Mairo ta durkushe anan tana kuka. Kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin data samu cikin Michigan wanda Yaya Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne ya kara rusa komai. Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa unbearable kamar kamar uncle Junaidun? Me yasa ita bata da sa’a a soyayya komai kankantarta???
Ji tayi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. A sannu ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wanene wannan???
*A BARI YA HUCE* . ......
Littafin
*_Sumayyah Abdulkadir Takori*_
Wannan littafi tukuici ne ga masu sha’awar ganin rubutun TAKORI a yanar gizo. Ga mai son cikakken labarin (book 1-4) ya biya N1000 ga wannan account number
Sumayyah K Kabara
Zenith bank
2089357770
Sannan sai ya turo screenshot zuwa 07030137870
NAGODE
7/28/21, 10:59 AM – Buhainat????: KAUYEN GURIN-GAWA, 1988
Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al’umma masu sana’o’i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu.
Akwai sanannen hadin kai tsakanin al’ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin.
Duk da haka wannan bai hana al’ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba.
Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta hanyar ga-ruwa, sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da makaranta wadda dama idan dai ta boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa. Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a garin.
Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da kakanninsa. Sana’arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin Hausa, makani da gurjiya.
Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa ba wanda bai sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu, wanda tun yana karami Malam Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi sana’ar fataucin goron da yake yi daga Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga wancan lokacin kuwa ya koma Kano kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida mahaifansa wanda yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba.
Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a tsakaninsu ba. Duk wani burinsu na duniya yana kan ‘yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu ba sai bayan shekaru sha takwas da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma falillahil hamdu.
Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana kamin Malam Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu irin azababben itacen nan ne Allah Ya hadata da shi. A gefe ‘yar lelen ce zaune bisa tabarma tana dandasawa ‘yar bebin karanta kwalliyar juma’a da wani tsalelen yankin yadin mamar-mamar da ta tsinto a shagon tela. Ta daga ‘yar bebin tana cillawa tana cafewa tana wakarta cikin nishadi, ga dukkan alamu babu yarinyar da ke cikin farin ciki a gidansu a gaba dayan kauyen Gurin Gawa kamarta, sabida daurin gindin sangarta da cikakken gata da ta ke samu daga Innarta.
“Ke kam ‘yar gata ce, Ta-Ummule.
Ni uwarki “MAIRO” na tsaya miki.
A taba ki a tabo bala’i,
A duke ki, in rama miki.
Innata ta tsaya min,
Ni kuma na tsaya miki……..”
Sallamar Habibu ce ta katse ta daga wakar da ta ke rerawa ‘yar bebinta, cikin zazzakar muryarta kamar gyare. Ta yi cilli da Ta-ummulen ta kwasa da gudu ta makalkale shi, tana cewa,
“Yaya Habibu oyoyo!”
Ya ce “Ke da Allah kazamar banza, cika ni, dubi bakinki damale-damale da busasshen koko, hanci duk busasshiyar majina, sannan kalli hannunki duk bakin tukunya, kin zo kin goge su duka a jikina. Wallahi duk sanda na doso garin nan cikin fargabar cakumon da zaki yi min da kazantarki nake, shashashar banza an girma ba a san an girma ba”.
Ya rabata da jikinsa ta karfi, ita ko ko a jikinta, dariya ma ta ke abinta kamar ba da ita yake ba. Inna Hure ta cika fam, kiris ta ke jira ta sauke mishi kwandon bala’in da ke cike taf a bakinta, sabida wannan tijara da yake yiwa autarta.
A ganinta Habibu ya tsani Mairo ne kawai, don shi yana birni, ita tana kauye, duk da matsananciyar kaunar da Mairon ke masa. Babu ranar Allah da zata fito ta fadi, Mairo ba ta ambaci sunan Yaya Habibu ba. Shi kuma da zarar ya zo irin tarbar da yake yi mata ke nan, ita kuwa kamar dada tunzura ta yake ta yi masa oyoyon, da dukkan zuciyarta.
Ya matsa gaban Innar ya kai gwiwoyinsa kasa, ya ce
“Inna barkanku da gida, mun wuni lafiya?”
Ba ta juyo daga fifita wutarta ba, haka ba ta kalle shi ba, ta ce “Lafiya kalau”. Cikin danne bacin ranta.
Ya yi shiru cikin zargin kansa. Ya san tabbas ya tabo Innar, don ta sha ce masa idan ba zai daina kyarar mata auta ba, to ya daina zuwa, babu dole.
Cikin kasada ya ce “Amma Inna ga wannan katuwar yarinyar ki zauna kina hura wuta, ita tana wakar ‘yar bebi? Duk wani dan arziki kamarta ai yanzu ya dawo ne daga makaranta, yana haramar tafiya islamiyya, amma ban da wannan, ban da karare ba ta san komai ba, shi yasa duk wasu abubuwa na yara masu hankali, ba ta san shi ba…………”
A fusace ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta, ta ce “Kai saurara. Wai me ye gaminka da yarinyar nan ne? Me ta tare maka? In don oyoyon da ta ke yi maka ne ba ka so, zan hanata, amma wannan sababin da kake yi mata ya ishe ni. Ka zo gidan su ka uzzireta babu gaira babu sabar? Ba ta zuwa makarantar, idan kai ka haife ta sai ka dauketa ka kai ta”.
Ya sunkuyar da kai ya ce, “Allah Ya ba ku hakuri Inna, Inna Allah Ya huci zuciyarku”.
Ta ja tsaki, “Tsuuuu!” Ta ci gaba da aikinta tana ta sababi, shi kuma bai kara tofawa ba, bai kuma tashi daga durkuson shi ba. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, rataye da fartanyarsa da alama a gajiye ya ke likis, sai gumi ke disa daga wuya da goshinsa. Yana ganin Habibu sai ya fadada far’arsa, amma jin Inna Hure na ta sababi sai ya maida fuskarsa ya dinke. Ya dade yana sauraronta ba ta san ma ya shigo ba, tana ta fadan idan Habibu ba zai daina tsangwamar mata Mairo ba, to ya daina zuwa, don ba ita ta kirawo shi ba.
Malam Bedi ya yi gyaran murya, sai a nan tasan da tsayuwarsa. Ta ce “Ai gara da ka zo, dama binka zan yi yanzun, ka ja wa yaron nan kunne ya sakar wa diyata mara ta yi fitsari, tunda ba a gidansu ta ke zaune ba, balle ya ji kunya don an ce kanwarsa ce”.